Siddabaru
Ko da yake yasan ba a mutuwa a dawo, bayyanar hotunan gayyatar auren Maryam da ya gani a Facebook tare da cikakken sunanta da ya gani sun Æ™ara tabbatar wa da Isah cewa lallai akwai wani É“oyayyen al’amari game da mutuwarta. Ita kuma Jalila ko ya za ta yi da irin halin ko in kula da mijinta ke nuna mata?
Hakabiyya
Yayin da fafutukar nemawa mijinta magani ya kai Zawwa zuwa ga tone kabarin wata budurwa mai ciki, hakan ya zamo matakin farko na cukurkuɗewar rayuwar Haƙabiyya tun kafin ta fito duniya. Hameedu, wanda ya canza sunan shi zuwa Huzaif yana ɗauke shi ma da wani ɓoyayyen sirri wanda ka iya fayyace komai ko ruguza komsi. Makirci ya haɗu da makirci, tsafi ya haɗu da mugunta, sirri ya ci karo da sirri, shin ko gaskiya ita kuma za ta yi halinta daga ƙarshe?
Bakar Tafiya
Basma, Jafar, Salma, Rabson Guy da Biba sun shirya tsaf domin yin wata doguwar tafiya, sai dai kafin su isa inda suka nufa dole sai sun bi wata shu’umar hanya wadda ta ratsa ta cikin wani baÆ™in daji da ake yi wa laÆ™abi da ‘Kai Ka Zo.’ Kowa a cikinsu tana da babban dalilin da ya sa zai yi wannan tafiya. Sai dai tun kafin a yi nisa kowannensu ya fara da na sanin yin tafiyar a lokacin da kwatsam direbansu ya mutu ba tare da sun san dalili ba.
Mijina Wukar Fidar Cikina
Salahuddeen na kwance tare da matarsa Muhibbat sai ga kidnappers sun yi musu dirar mikiya inda suka ɗauke shi tare da yi wa matarsa dukan tsiya. Bayan kwana huɗu da faruwar hakan sai suka buƙaci da a basu miliyan ɗari. To sai dai yanayin yadda suka san bayanai game da surikar Salahuddeen ya tabbatar da cewa akwai wani makusanci da ke basu bayanai a ɓoye. To amma waye?
Fatalwar Sinu
Katoɓara da ɓarin baki suka sa Haiman bayyanawa duniya irin abubuwan da yake so a bashi a matsayin kyautar barka da sallah. Sai dai ya samu kyautar da ta fi ƙarfin shi, yayin da wata kyautar ta fito daga lahira kuma daga hannun wani gagarumin maƙiyin da bai san yana da shi ba.
Fansar Fatalwa
Ƙawaye sun yi wa Amrah mummunan lahani a rayuwa, wanda hakan ne ya zamo silar mutuwar ta. Hakan ya sa ta dawo a matsayin fatalwa tare da shan alwashin ɗaukar fansa a kansu. A bisa wannan dalili ne ta kawo wa Afrah farmaki ana saura kwana uku bikinta da masoyinta, wato Anwar. Shin wa kuma za ta kai wa hari na gaba?
Mafarkin Deluwa
Malam Shitu, Malam Lawal, Malam Tsalha da Malam Zaidu ma’aikatan wata maÆ™abarta ce da ke Æ™auyen ÆŠanduÆ™us. Tsananin firgici ne ya ziyarce su a lokacin da suka ga wata ‘yar wada ta shigo maÆ™abartar da suke kula da ita tana neman taimakon su binne mata gawar. Saratu, wadda aka fi sani da Deluwa ta yanke shawarar kashe masoyinta Chibunzu, kamar yadda Alhaji Labaran ya umurta domin cika burinta na zuwa Makka.
Amrah
Tana da ikon da aljanu suke tsoro, tana da fushin da yake girgiza zuƙata, amma a cikin zuciyarta, akwai wani rami na kaɗaici da babu mai iya cikewa. A wajen mutanen ƙauyen Kiyawa, ita wata hatsabibiya ce da ba ta da maraba da shaiɗaniya, amma a gare ta, tana kare mutuncin waɗanda take ƙauna ne kawai.
​Shin laifinta ne idan kowa ya guje ta saboda ikon da ba ta san daga inda ya fito ba?
​Yayin da Amrah take zubar da jinin azzalumai a daji, a can birni kuma Hamrah tana zubar da hawayen tsoro a cikin daular dukiya. Yarinya ɗaya, amma cikin siffa biyu; rabi na neman rabi, amma ƙaddara tana neman raba su har abada.
​AMRAH… Labari ne mai cike da asiri, tsoro, da kuma gwagwarmayar neman asali. Littafin da zai nuna muku cewa ba kowane jinkiri ba ne yake nufin an manta da kai, wani lokaci, sai ka rasa komai kafin ka gano ko kai wane ne.
Death on Motorbikes
A fourteen-year-old boy, haunted by news of bandit attacks on motorbikes in Northern Nigeria, questions his uncle about the root causes. His uncle reveals that banditry is a million-dollar business fueled by powerful financiers, politicians and businessmen who use violence to destabilize governments. The riders are mere pawns, including brainwashed children. The only solution, his uncle argues, is to imprison the financiers, though their immunity makes this nearly impossible.