Skip to content

Sell Books

Sharudda

Hikaya na iya sayan littafi kammalalle ko kuwa marubuci yake bugawa babi-babi har littafin ya kammala.

Babbar hanya da marubuci zai bi wajen samun sayar da littafinsa ga Hikaya shi ne, da farko ya fara dora free book gwargwadon yadda ya ga dama ta yadda Hikaya zata fahimci salon rubutunsa da shahararsa. Wadannan sune matakan farko na sayar da littafi.

Baya ga wadannan matakan da aka ambata, sannan ga ka’idojin da zasu biyo baya wajen shiga yarjejeniya bayan Hikaya ta amince da sayan littafin.

  1. Da farko, marubuci ya tabbatar cewa littafin shi ne ya rubuta, ko kuwa shi yake da hakkin mallakar littafin ko ma duka biyu.
  2. Dole littafin ya kasance sabo ne, ba a taba buga shi a wata kafa ba, online ko offline. Idan marubuci na da muhimmin tsohon littafi da ya ke ganin za mu saya, sai ya tuntube mu.
  3. Littafin kada ya gaza a kalla kalmomi dubu hamsin (50,000 words) zuwa sama – kammalallen littafi ne ko kuwa na bugawa babi-babi.
  4. Da zarar an shiga yarjejeniyar, marubuci ba zai iya sayar da littafin ba (kwaya daya ko da yawa), ko sake wallafa shi a wani wuri, har sai bayan shekara guda daga ranar da aka shiga yarjejniyar.
  5. Dole marubuci zai saka (tallata) shafukan littafin guda uku zuwa biyar, gwargwadon yadda zai zama dandano, a shafukansa na sada zumunta da duk wuraren da yake da makaranta inda yake sanya labaransa. Sannan ya saka link din da za’a samu cigaban labarin, wato zuwa Hikaya.
  6. Hikaya na da copyright na juya littafin zuwa audio ko duk nau’in documents, ko ma buga shi a matsayin littafi a koda yaushe. Sannan Hikaya na iya dorawa a duk kafafenta na internet ko kuma wurare da take tallata hajojinta don sayarwa. Duk nau’in da aka juya littafin, da sunan marubuci za a buga shi.
  7. Tsarin biyan kudi na kammalallen littafi zai kasance gida uku: karshen watan farko na shiga yarjejeniyar, sannan sai karshen wata na biyu ko na uku, sai kuma karshen wata na uku ko na biyar, gwargwadon yadda littafin ya karbu.
  8. Tsarin biyan kudi na littafin da aka buga babi-babi zai kasance ne kowane babi zai iya kamawa daga N1000 – N3000 gwargwadon shaharar littafin. A tuntube mu don daidaitawa.
  9. Hikaya na iya gyaran fuska ga wadannan ka’idoji a koda yaushe, gwargwadon juyawar zamani.
  10. Karya daya daga cikin wadannan ka’idojin zai iya rushe baki dayan yarjejeniyar. Sannan marubuci zai biya kudin da aka biya shi.

Yadda za a turo littafi

Duk marubucin da ke son shiga daya daga cikin wannan tsari, to ya aiko mana da wadannan abubuwa a hade cikin document guda.

  • Tsakure (summary) da ba zai wuce kalmomi 1000 ba game da littafin baki dayansa, kuma ya kunshi bayanin babban hadafi da marubuci ke son isarwa a labarin.
  • Akalla babi guda shida daga littafin (babi na 1 da na 2; babi guda 2 daga tsakiyar littafin; da kuma babin karshe guda biyu).

A aiko da one document dake kunshe da abubuwan da aka lissafa a sama ta email namu: hikaya@bakandamiya.com ko kuma a tuntube mu a WhatsApp namu (09072304845) don neman karin bayani.

Sauran ka’idoji

Sauran muhimman ka’idoji da marubuci ya kamata ya kula da su su ne:

  • Jigo da salon labari
  • Ka’idojin rubutu
  • Bangon littafi (a yi designing nashi makamancin wadanda ake da su a Hikaya). Idan ba a samu damar design ba, Hikaya na iya yiwa marubuci design kyauta.

A tuntube mu idan ana bukatar karin bayani.