wp-content/uploads/2022/10/Hukuncin-Allah-by-Umar-bin-Ally.jpeg

Hukuncin Allah

Salim matashi ne da bai yarda da cewa abubuwa suna faruwa ba ne a bisa yadda Allah ya ƙaddara za su faru ba. Abinda ya aminta da shi kawai shi ne, duk wani mummunan abu da ka ga ya faru, to sakacin wanda abin ya faru gare shi ne ya ja mishi.


wp-content/uploads/2021/12/Baba-Dattijo-Dan-Bursin-by-Mukhtar-Spikin.jpg

Baba Dattijo Dan Bursin

Yayin da wani ɗan jarida ya je gidan yarin Kurmawa da ke Kano ya gamu da wani dattijo mai ban mamaki da ke rayuwa a wannan gida na kaso. Shin ko ta yaya za a iya shari’ar kashe mutumin da ya riga da ya mutu tun shekaru 29 da suka gabata?


wp-content/uploads/2022/01/Hoton-Mijina-by-Nana-Aicha-Hamissou.jpeg

Hoton Mijina

Muka amsawa da amin muna sakar wa juna murmushi. Tun daga ranar duk wasu makaman yaƙina na zubar da su, har mamakin kaina nake yi da tambayar kaina anya kuwa ni ce Rashida? Zaman lafiya ya samu matsuguni a tsakaninmu tamkar ba kishiyoyi ba. 


wp-content/uploads/2021/12/Daurin-Huhun-Goro-by-Rashida-Usman.jpg

Daurin Huhun Goro

Halin yunwa, talauci da kuma matsatsin rayuwa da ake ciki ne suka tunzura Tabawa har ta kai ga tana bin layi da lunguna tana zagin shugabanni, ‘yan siya da kuma ‘yan kasuwa. Domin ita a ganinta, duk su ne sanadin faruwar hakan a cikin al’umma. Ta kuma ƙudiri aniyar kawo sauyi game da wannan lamari.


wp-content/uploads/2024/02/Kisan-Boko-Na-Faisal-Haruna-Hunkuyi.jpg

Kisan Boko

Kyawun fuska da kyawun dirin jiki tare da dakakkiyar niyyar ganin ta yi karatun boko mai zurfi ne suka sa ake yi wa Sa’adatu inkiya da ‘Yar Boko. Tabbas ta yi bokon, domin har ta kai ga samun digiri na biyu. Ga gida da aiki duk ta mallaka. Babban tashin hankalinta shi ne rashin samun mijin aure. Ƙawayenta da yawa tuni sun tara ‘ya’ya, samarinta duk sun kama kansu, ga shi ita kuma auren take so.


wp-content/uploads/2021/12/Munafukin-Miji-by-Naima-Sulaiman-Sarauta-1.jpg

Munafukin Miji

Ridayya na matuƙar son mijinta Zameer. Ta mallaka mishi dukkan rayuwarta da duk wani abu da ta mallaka. Saboda shi ta rabu da iyayenta da ‘yan’uwanta. Sai dai shi kuma a nashi ɓangaren, Zameer cin amanarta yake yi, ha’intarta yake yi6, kuma amfani da ita kawai yake yi wajen cimma muradansa. Duk irin yadda Mardiyya ta so ta nuna wa Ridayya gaskiyar abinda mijinta ke yi ta kasa fahimta saboda makauniyar soyayyar da take yi mishi.


wp-content/uploads/2021/12/Ba-Kauyanci-Ba-Ne-by-Fatima-Abubakar-Saje.jpg

Ba Kauyanci Ba Ne

Alhaji Abdulƙadir mutum ne ɗan zamani wanda kiyaye haƙƙoƙin addini bai dame shi ba, to amma ‘yarsa Salma da mahaifiyarta Hajiya Bilkisu suna da kyawawan halaye kuma suna matuƙar kiyaye dokokin shari’ar Musulunci. Alhaji Sameer da Hajiya Samira suna da ɗa guda ɗaya da suka haifa mai suna Kamal. Duk iya ƙoƙarin da Alhaji Sameer yake yi na ganin Kamal ya shiryu, ita mahaifiyarsa gani take takura ce. Kamal ya kama hannun Salma a wurin wani taro inda ta wanke shi da mari. Sai daga baya yake jin ashe mahaifiyar Salma mahaifinsa ya fara so ya aura kafin mahaifiyarsa.


wp-content/uploads/2021/12/Laifin-Wa-by-Mustapha-Abbas-RLemo.jpeg

Laifin Wa?

Ladidi matashiya ce mai ji da ƙuruciya, hakan ya sa ta faɗa harkar bin maza domin ta hucewa kanta haushin rashin ɗauke mata ɗawainiya da iyayenta suka kasa. Duk da cewa sun san irin abin da ɗiyarsu ke aikatawa, amma ba su da ta cewa. Saboda wani lokaci ma wurinta suke zuwa su yi ‘yar murya.


wp-content/uploads/2021/12/Bakar-Kaddara-by-Haiman-Rarees.jpeg

Bakar Kaddara

Wasu lokutan ba sai ka aikata mummunan aiki ba kafin baƙar ƙaddara ta afko maka. A wasu lokutan kuma, halayen mutane ne ke kaisu ga faɗawa cikin bala’i.


wp-content/uploads/2021/12/Addininmu-by-S.-Reza.jpg

Addininmu

Abduljabbar wanda aka fi sani da AJ, matashi ne ɗan talaka jikan talakawa, sai dai kuma ya ƙwallafa wa ransa zama hamshaƙin mai kuɗi. A dalilin hakane yake yaudarar budurwarsa Zahra tana sato kuɗin iyayenta tana kawo mishi. Abdallah shi kuma ya tubure fafur kan cewa shi fa ƙanwarsa Maryam ba za ta auri ɗan bidi’a ba. Zainab Ambato kuma na shirin yin fito-na-fito da wani matashin mai wa’azi da ke sukarta.


wp-content/uploads/2021/12/Kukan-Kurchiya-by-Halima-Zakariyya.jpg

Kukan Kurciya

Ana gobe ɗaurin auren Mujahida da masoyinta da suka yi shekaru biyar suna soyayya, wato Nura ya ce ya fasa. A gigice ta shiga gida da taimakon ƙanenta Mujtafa, sai dai shigarta cikin gidan ya yi daidai da furta kalmar saki da mahaifinta wato Habibu ya yi ga mahaifiyarta wato Bilkisu.


wp-content/uploads/2024/05/Nakasar-Zuci-na-Kamala-Minna_20240513_130611_0000.jpg

Nakasar Zuci

Abubuwa sun taru sun yi wa Badi’a jingim a ka, sakamakon sakin da mijinta Adamu ya yi mata da tsakar dare bayan da ya gano cewa tana da cikin wata uku a jikinta, alhali ba su wuce wata ɗaya da ‘yan kwanaki da yin auren ba. Ga shi mahaifinta ya ce in har ta baro gidan miji kada ta zo mishi gida, ko yaya za ta yi?


wp-content/uploads/2024/01/Uban-Da-Ba-Namu-Ba-by-Maryam-Shuaibu-Aliyu.jpg

Uban Da Ba Namu Ba

Tanimu Sambo wanda aka fi sani da Baban Nawwara malamin makaranta ne da ke koyarwa a wata makarantar mata. Jajircewa da ƙwazonsa a ɓangaren koyarwa tare da tsayuwa akan gaskiya suka sa ya ƙi yarda ɗalibansa su ba da kuɗi domin a basu amsar jarabawar fita daga Sakandare. Maimakon haka, sai ma dagewa da ya yi wajen horas da su yadda za su amsa tambayoyin yadda ya kamata.


wp-content/uploads/2021/12/Mafarkin-Deluwa-by-Asmau-Abdallah-Ibrahim.jpeg

Mafarkin Deluwa

Malam Shitu, Malam Lawal, Malam Tsalha da Malam Zaidu ma’aikatan wata maƙabarta ce da ke ƙauyen Ɗanduƙus. Tsananin firgici ne ya ziyarce su a lokacin da suka ga wata ‘yar wada ta shigo maƙabartar da suke kula da ita tana neman taimakon su binne mata gawar. Saratu, wadda aka fi sani da Deluwa ta yanke shawarar kashe masoyinta Chibunzu, kamar yadda Alhaji Labaran ya umurta domin cika burinta na zuwa Makka.


wp-content/uploads/2021/12/Alkawarin-Allah-by-Khadija-B.-Ahamad.jpg

Alkawarin Allah

Alhaji Usman Ibrahim Matawalle ba ya barin kowa zuwa zance wajen ‘ya’yansa, watau Maryam da Fatima saboda mutum ne shi mai zafi sosai. Soyayyar Maryam ta kama Nuraddeen, kuma sai bibiyarta yake yi har sai da ya gano gidansu. Shin ko zai dace da samun soyayyar Maryam tare da amincewar mahaifinta?


wp-content/uploads/2021/12/Tun-A-Duniya-by-Nana-Aicha-Hamissou.jpg

Tun A Duniya

Alhaji Garba ya shiga wani irin mummunan hali na ban mamaki. Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci duk dukiyar da ya tara ta salwanta, sannan lafiyarsa ma kanta ta fara ƙoƙarin ƙaurace masa.


wp-content/uploads/2021/12/Fatalwar-Sinu-by-Haiman-Raees.jpg

Fatalwar Sinu

Katoɓara da ɓarin baki suka sa Haiman bayyanawa duniya irin abubuwan da yake so a bashi a matsayin kyautar barka da sallah. Sai dai ya samu kyautar da ta fi ƙarfin shi, yayin da wata kyautar ta fito daga lahira kuma daga hannun wani gagarumin maƙiyin da bai san yana da shi ba.


wp-content/uploads/2024/01/Akwai-Ciwo-by-Rashida-Usman.jpg

Akwai Ciwo

Akan ce ‘naka shi ke ba da kai’, Jidda ta ga gaskiyar hakan a zahiri yayin da ta tsinci kanta a matsayin marainiyar da ‘yan’uwa suka yi watsi da ita. Ƙuncin rayuwa tare da tunanin yadda za ta ciyar da kanta da ƙannenta ne ya sa ta faɗawa ashararanci ba tare da ta yi tunanin abinda zai biyo baya ba.


wp-content/uploads/2024/02/Almajirai-Ma-Yaya-Ne-by-Habiba-Maina.jpg

Almajirai Ma 'Ya'ya Ne

Sa’idu da Halliru sun zamo tsayayyu kuma bayyanannun misalai na irin mummunan halin da al’majirai ke faɗawa a cikin rayuwarsu ta al’majiranci. Duk da cewa an nuna irin yadda mugun halin mutanen zamani yake game da al’majirai har suke cutar da su, Hajiya Maryam ta fita zakka tare da zamowa misalin da kowa zai so zama kamarta.


wp-content/uploads/2021/12/Tsanin-Nasara-by-Hamza-Dawaki.jpg

Tsanin Nasara

Duk da cewa amaryar ta jima a gidan mijinta har ma ta tara yara. Gwalagwalan shawarwarin da mahaifinta ya ba ta sun zamo mata tsanin hawa matakin nasara a gidan aurenta da ma rayuwarta baki ɗaya.


wp-content/uploads/2021/12/Abinda-Babba-Ya-Hango-by-Fatima-Abubakar-Saje.jpg

Abinda Babba Ya Hango

Okasha Sani Sa’id matashi ne mai taƙama da kuɗi da kyawun halitta. Hakan ya sa yake wasa da hankulan ‘yanmata tare da ɓata musu rayuwa. Ƙaddara ce ta haɗa shi da Jameela, wadda ta bijirewa shawarar mahaifinta ta auri Okasha ba don suna so ba. Kash! Da ta san abin da zai biyo baya da ba ta yi wannan aure ba.


wp-content/uploads/2021/12/Na-Sake-Ta-by-Mustapha-Abbas-1.jpg

Na Sake Ta

Hamshaƙin matashin mai kuɗin da ake ji da shi, wato Usman One boy ya samu Kamal mayen kuɗi da batun wani irin kasuwanci mai ban mamaki. Usman ya yi alƙawarin ba wa Kamal kuɗi naira na gugar naira har miliyan biyar, matuƙar dai ya yarda zai saki matarsa Hajir domin ya aure ta. Ashe Kamal na gab ne da fahimtar cewa ba komai bane kuɗi ke iya yi wa mutum.


wp-content/uploads/2021/12/I-am-Not-Your-Punching-Bag-by-Hauwa-Sale-Abubakar.jpg

I Am Not Your Punching Bag

I Am Not Your Punching Bag And Other Stories is a collection of short moral and interesting stories depicting the daily struggles of African woman.


wp-content/uploads/2021/10/Kwaya-Tushen-Tsiya-by-Danladi-Haruna.jpeg

Kwaya Tushen Tsiya

Ƙalubalen rayuwa ya sa wani matashi yanke shawarar shan miyagun ƙwayoyi domin su taimaka mishi wajen ɗaukar fansa. Abinda bai sani ba shi ne, su ma ƙwayoyin tasu rigimar ta musamman ce.


wp-content/uploads/2021/12/Kwamin-Nadama-by-Rashida-Usman.jpg

Kwamin Nadama

Baƙin kishi ya sa Ladiyo cakumar wuyar mijinta tana mai sauke masa kayan rashin mutunci tare da tabbatar mishi da cewa bai isa ya yo mata kishiya ba. Shi kuwa Kabiru, don ya gwada mata lallai ya haifu bai yi wata-wata ba ya danna mata saki biyu. Tun daga nan ta shiga tashin hankali da ruɗani, musamman da ta tuna cewa za ta bar gidan kuma zai kawo wata.


wp-content/uploads/2021/12/Ta-Ki-Aure-by-Fatima-Abubakar-Saje.jpg

Ta Ki Aure

Sawwama da Kawwama yaya da ƙanwa ne da suka jima basu yi aure ba. Shekarar Sawwama talatin da biyar ba ta yi aure ba, yayinda ita kuma Kawwama shekararta talatin da biyu ba ta yi aure ba. Hakan ya sa kowa a dangi ke ta faman yi musu surutu. Kwatsam sai ga Jalil ya zo neman auren Kawwama, an sha biki an gwangwaje, sai dai kuma Jalil na ɗauke da wani ɓoyayyen lamari da ba kowa ya san da shi ba.


wp-content/uploads/2021/12/Izina-by-Khadija-B.-Ahamad.jpg

Izina

Aisha (Ma’isha) da Abdul’aziz ‘yan’uwan juna ne, kuma dukkansu lauyoyi ne. Sai dai a karo farko za su kara da juna a gaban ƙuliya domin kare mutane biyu. Iya Aisha tana ƙoƙarin ƙwato wa wata mata da ‘yarta
‘yancinsu ne a hannun wani mugun mai kuɗi. Shi kuma Abdul’aziz yana kare shi. A wani ɓangaren kuma, yayansu jami’in ƙasa da ƙasa, Deputy Commissioner of Police Abdulmalik Ibrahim Ahmad ya zo Nijeriya domin ya gudanar da bincike na musamman akan kisan da aka yi wa wani babban jami’in tsaro, kwatsam kuma sai ƙaddara ta haɗa shi da ‘Yar Jarida Intasar Mahmood Abdullahi.


wp-content/uploads/2021/12/Tsinin-Harshe-Ya-Fi-Na-Mashi-by-Sadik-Abubakar.jpg

Tsinin Harshe Ya Fi Na Mashi

Al’amura sun dagulewa Zainab tun bayan da bakinta ya jawo mata jalli-joga sakamakon sharrin maita da ta yi wa Jummai a gidan suna. Lamarin ya kai matuƙa a fagen tsamari ne ya yin da aka aiko mata da takardar sammaci daga kotu a bisa wannan zargi, ana tsaka da wannan kuma sai mijinta Auwal ya sake ta.