Skip to content
Part 7 of 9 in the Series Kaddarar So by Fatima Rabiu

ARMAN HARUN’S FAMILY HAUSE LOGAS NIGERIA

Yau ta kama weekend ne, kowa yana gida. Safiya ce mai cike da nishad’i domin garin hadari ne ya had’u sosai ya saki wata irin ni’ima, garin yayi luf-luf dashi gwanin ban sha’awa.

Babban parlon gidan ko ta ina ma’aikata ne ke aikinsu, masu shirya darning table nayi, sunfi ba darning table d’in mahimmanci wajan jera abincin safen da masu gidan ke gaf sakkowa domin su ci. Kamin a shafe y’an mintoci, sun shirya kan darning table d’in, had’e da gyara parlon ya d’au wani k’amshi na daban.

A hankali a hankali mutanan nan gidan suka rink’a sakkowa suna zama kan darning table d’in. Ga wata ma’aikaciya tsaye kana zama ita ce mai tabbayar ka miye kake son ci, zata zubama abunda kake ra’ayi da son ci, wannan shine aikinta kawai.

Kowa ya sakkowa harda su Daddy amma banda Arman a wajan. Salma ce ta d’an duk’a dai-dai inda Haj Shuwa ke zaune suna kusa da juna ta ce “Umma ya banga Arman d’in ya fito ba, kowa kuma yana ya hallara?”

“Hmm rabu da miskilin banza, yanzu haka yana can ya tsaya yangarsa, shifa ba wani abinci yake ci sosai ba, bari kiga koda ya zo ba wani zama yake ya dad’e a cikinmu ba”

Tab’e baki Salma tayi tana d’aga k’afad’arta irin ko a jikinta d’in nan.

Haj Zulaihat ce nufo darning table d’in, itama fitowarta kenan Bilkees dake danna waya ko kallon su Salma batai ba, bare ta san miye suke ciki. Humaira ce ma dai da Sa’adha dake kusa da juna, suke duban Salma yadda ta wani hakimce kamar wata sarauniyar gidan, Sa’adha bata dad’e da dawowa gidan ba, tana k’asar India tana karatu tazo hutu ne, Humaira kuwa d’iyar k’anwar Momma ce, dama ita gidan take zaune tun asali tare suke da Sa’adha, Humaira tafi son karatun k’asarta ta haihuwa, ita ko Sa’adha tana da ra’ayin fita. Hakan yasa iyayen Humaira dake zaune k’asar India suka bata goyan baya, take zaune a gidansu ita kuma d’iyarsu Humaira dama can ba zama k’asar take ba, tunda wayonta ta baro India ta komo gidan Momma, baka tab’a gane cewa ba Momma ce ta haife ta ba, haka itama Sa’adha idan tana can India baka tab’a cewa ba Iyayen Humaira ne suka haife ta ba, haka suke rayuwarsu cike da tsananin son juna.

Salma kuwa da biyu tayi dama, duk tana sane dasu. Tana cikin tunani Arman k’amshinsa kawai ya fara masu maraba da cewa gashi nan isowa. Su Sa’adha murmushi suka saki a tare, suna waigawa, suna duban Yayan nasu. Kai ita kanta Salma sai da ta had’e abincin dake bakinta ba shiri. Wani mayen kallo take binsa dashi, yaushe rabon data sashi a idonta, gani tayi yayi mata wani mahaukacin kyau, ita kanta bata san sadda ta saki wani murmushin munafurci ba, a zuciyarta take cewa. Tabbas Arman ka cika Zakin Maza dole y’an mata zasu rink’a harinka kota ina, na samu na shiga gidanka dai, amma ni nayi daban da y’an matan dake hauka kanka, ni dukiyar taka muke da buk’ata, ko kwanciya kayi dani wannan ma kad’ai ya wadatar dani. Ta k’are maganar tana k’ara fad’ad’a murmushinta.

Kowa ya gaisar dashi, amsawa yayi a takaice, shi kuwa kai tsaye sai da ya fara zuwa kusa da Daddy da Abba, ya kwashi gaisuwa suna ta samai albarka. Kamin yaje kusa da Momma ya rungumeta yana mik’a gaisuwarsa, cike da k’auna take samai albarka. Wajan zamansa ya zauna, da kanta Momma ta tashi ta zuba mai abunda tasan yana yana so.

Haj Zulaihat ta zunguri Bilkees tana d’agowa ta banka mata harara, k’asa-k’asa ta ce “wato ke dai baza ki daina halinki ba ko?, wato ke ta danna waya ma kike, bana ce idan ya fito ki rink’a zuwa kina amsar Momma ki rink’a zuba mai abincin da kanki ba?, da haka zai saba dake har ki d’an samu matsagunni a zuciyarsa sakarai dake komai sai ance kiyi”

Turo baki Bilkees tayi bata ce komai, itafa gaskiya abunda Momy ke son ta had’a tasan ba mai yiwuwa bane.

Haj Shuwa k’asa k’asa itama yadda Haj Zulaihat zata jita ta ce “hmmm ayi dai mu gani idan tusa na hura wuta”

Wani kallo mai cike da takaici Haj Zulaihat ke aikama Haj Shuwa tana kama leb’enta na k’asa ta d’an ciza, kwafa tayi tana kallon Salma, wato kenan Haj Shuwa ta canza shawara itama, so take wannan d’iyar y’ar uwar tata itama ta samu shiga wajan Arman kenan?, kan uban nan kayyasa ai ko da sake wallahi, ita Haj Shuwa zatai ma haka?, dan taga tana so itama tata yarinyar ta samu shiga. Wani dogon tsaki Haj Zulaihat ta saki, wadda yaja hankalin gaba d’aya mutanan wajan, kallo ne ya dawo kanta, basarwa tayi tana tashi gaba d’aya daga kan darning table d’in, tana ma Bilkees inkiya da ido akan ta biyo ta d’aki yanzun nan. Domin idonta ne yayi mata tozali da yadda Salma ke bin Arman da mayen kallo, kuma tuni ta harbo jirginsu ita da Haj Shuwa.

Bilkees na shigowa part d’in nasu, Haj Zulaihat ta kalleta ta ce “wai ke sai yaushe zaki gane abunda nake hango miki dangane da auran Arman ne?, har yanzu baki da wayo wallahi Bilkisu”

“Momy please wallahi kwata-kwata bana son kina min maganar had’a ni aure da Arman, na k’ara gaya miki cewa K’awata ke sonshi kamar ranta, bana jin idan Lilaah ta rasa Arman zata iya rayuwa”

“Ke dalla rufe min baki, kona d’ora miki ashar yanzu nan, harni zaki tsaya kina cewa wai k’awar ki idan bata sameshi ba akwai matsala, to tama mutu mana, ina ruwana. Nidai na k’ara gaya miki ki maida hankalin ki wajan jawo hankalinsa gare ki, idan ba haka ba kuma, wallahi Bilkisu ranki zaiyi mummunan b’aci ne”

Shuru Bilkees tayi, wani haushin Momy na kamata, kallonta kawaii take, yadda take ta sako mata maganar Arman, komai Arman kowa Arman, ita fa bata ga abunda suka hango har suka rud’e sai shi ba.

  Harta gama b’ab’atunta Bilkees bata ce komai ba, tana gamawa Bilkees ta juya ta fice daga d’akin.

 Tana fita Haj Zulaihat ta jawo wayarta, ta dannama wata K’awarta kira, bugu d’aya kuwa aka d’auka. Kamin ta cikin wayar ta ce komai Haj Zulaihat ta ce “Luba akwai matsala fa”

“Wacce irin matsala kuma Haj Zulaihat?”

“Akan abunda tun yarinyar nan na k’arama nake so na had’a domin cikar burina, amma yarinyar nan tana son b’allo min ruwa fa”

“Ai kece tuni Haj Zulaihat na ce miki ki fara aiki da Malaman tsubbu da bokaye, kiga aiki kamar yankan wuk’a, kika wani tsaya ai kissa da dabara zata sa ta fahimce ki, yo hatta mijin naku, keda wannan mai kama da ifiritan farko Haj Shuwa da tuni kin gama da ita wallahi, da yanzu sai dai watanta ba dai ita ba, bata isa ta d’aga miki koda d’an yatsa bane”

“Kinga Luba, nifa gaskiya zan k’ara gaya miki ban yarda da Malaman tsubbu nan ba, abu d’aya na sani nayi yak’i da kaina na samu abu yafi, kuma ko yanzu Mijina yana sona na sani, kowa da matsayinsa”

“To kin san da haka mi kika bugo nayi miki?, Fisbilillahi nifa kin sani da Malaman tsubbu nan na dogara, su suke min aiki har nake janyo y’an samari na tatse su kud’i yadda nake so, tunda na kaso aure na nake cin kare na babu babbaka”

“Hmm Luba kenan yanzu ba shawarar da zaki bani, ko na d’au haske”

“Haj Zulaihat kenan, nifa bari na k’ara gaya miki ga abunda zakiyi kiga buk’ata yanzu yanzun nan, ba b’ata wani lokaci, idan kuwa na ce ga abunda zakiyi to nayi k’arya ni ban san wannan y’an dabarun ba da kissar nan, a’a ni Malamai kawai na sani. Idan kin shirya binsu to ina sauraran kiran ki”. Tana fad’ar haka ta tsinke kiran.

Wani tsaki Haj Zulaihat taja tana magana ita d’aya

“Shi yasa fa ban son kiran Luba, komai ita sai kabi wasu bokaye abunda aikinsu na d’an kwanaki ne, nida nake so nayi abun ya zama sai dai mutuwa zata raba”.

Momma kuwa, duk tana ganin abunda ke wakana a tsakanin Matan K’anin mijinta, har tsakin da Haj Zulaihat ta saki tasan can tsakaninsu ne ita da Haj Shuwa. Wani murmushi ta saki tana k’ara sama d’an nata albarka.

Haj Shuwa ce itama tsaye tana waya da Binta. Salma ce ta shigo hakan yasa Haj Shuwa tsinke kiran. “Umma wai baki ganin yadda waccan matar Haj Zulaihat ke miki tsaki ne?, mi yasa baki ci ubanta bane?, nifa wallahi Umma bana d’aukar raini, shi yasa zuwa na gidan nan, muka had’u da waccar Humairar ta nemi tayi min iskanci na ce ubanta gaban Momma wallahi”

“Kin yi min dai-dai ai, shegiya sai ka ce ita ba cin arzik’in take yi ba”

“Hmm kema kin fad’a Umma, ai ko taji magana wallahi”

“Ni yanzu waccar Haj Zulaihat d’in ke son bamu matsala, amma abu d’aya zai tsaida mu shigowar yarinyar da Boka ya ce ne, amma data gane shayi ruwa ne, data gane cewa ba’a buga wasa da Haj Shuwa bata cinye wasan ba, amma nan gaba kad’an zata ga sakamakon wasan”.

Dariya suka saki a tare harda su tab’a hannu kamar wasu sa’annin juna.

SURURE LAGOS NIGERIA

Wayar dake manne a kunnansa ce ke shirin fad’uwa, tsabar yadda jikinsa ke kyarma. Ba shiri Mimi dake kusa dashi hankali a tashe ta tarbe wayar tana sata a amsa kuwwa yadda kowa zai ji. Miye ya tada hankalin Aliyu?. Sai tabbayarsa suke tun d’azo da ya amsa kiran, ya koma tashi a zabure amma yak’i basu amsa, gashi ya tsaya kamar wadda gangar jikinsa ta daina aiki.

Abunda suka ji ne suma ya kusa tarwatsa kwanyarsu da tunaninsu. Domin daka ji yadda ake magana da wata basamudiyar murya, irinta gaggan y’an Ta’adda zaka sheda wadda suka sace Husaina ne suka kira.

Suna cewa “da alama baka so matarka ta dawo da ranta, mundun kuka sake sa Jami’an tsaro a lamarin, to matarka zata iya mutuwa ako wane lokaci, a sadda kuka shirya ta dawo gare ku zamu neme ku, amma yanzu baka shirya ta dawo gare ka da wuri ba. Suna fad’in haka suka datse kiran. Wata irin hargowa Aliyu keyi yana amshe wayar daga hannun Mimi yana cewa “hello hello dan girman ku tsaya, wallahi na shirya amsar matata, ko nawa kuke so ku fad’a zan baku, kuma Jami’an tsaro za’a cire su daga zancan, baza mu sake sanar dasu abunda ake ciki ba, hello hello hello”. Maganar yake cike da fitar hayyaci.

Mimi da ke hawaye ta ce “haba Aliyu sunfa katse kiran”

Wata irin zabura yayi sai gashi ya zube a k’asa a sume.

Wata irin kururuwa Lilaah ta saki had’e da salati.

<< Kaddarar So 6Kaddarar So 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×