Sai dare mazajen yayyen Ayatullah ɗin suka zo ɗaukan su, ya so ya bi yaya Fatima, Mami ta ce be isa ba, ba inda zai je.
Hannun Abbakar mijin Zainab Ayatullah ya riƙo, yay ce pls yaya na karka bari matar ka ta dawo gobe, anman dai kasa ta dafa min tuwo sai ka kawon, gabaki ɗaya kowa yasa dariya Abubakar ya ce kar kaji komai nawan, kamar bata dawo ba.
Washe gari Ayatullah na bacci sai jin an bigeshi ya yi, da hanzari ya farka inda yaran suka sa dariya, tsuke fuska ya yi, wato sai yau kuka. . .