Da sunan Allah mai Rahma mai Jin Ƙai
Tsaye yake a jikin bangon wurin, lokaci zuwa lokaci yakan saka hannun shi cikin sumar kan shi, ba zai iya tuna ranar ƙarshe da wani abu ya ɗaga mishi hankali haka ba, yanayin yake ji ya zame mishi baƙo. Kayan da yake jikin shi ya bi da kallo, gajeren wando ne na kakin sojoji da ko gwiwar shi bai taɓa ba, sai rigar wandon mai yankakken hannu, wuyan shi da alamar sarƙar da ba ka ganin ko ta mecece, sai shi da take wuyan shi. Wani ɗan dogon ƙarfe. . .
Masha Allah vry interested stry
Very captivating story. Good luck
#haimanraees