Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Abul-Khair by Yarlele

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

A hankali kuma cikin isa da takama tare da izza, kyawawan samarin suke saukowa daga mattatakan jirgin, so cute.

Karasa saukowa suka yi, anan ne na shagala, domin a da, banga komai ma, kyawawan samari ne, guda biyu masu masifar kama da juna, wanda ina da yaƙinin ko Iyayensu ba lallene su iya banbance su ba saboda masifar kamar da suke yi da juna, kamar an tsaga kara.

A hankali suka cigaba da tafiya cikin kasaita da kwarjini tare da haibar da take tare da su.

Dogaya ne bawai chan ba tsawonsu dai-dai misali, sai dan jiki da suke dashi, wanda bawai jiki ne sosai ba, kawai dai su ba ramanmu ba kuma su ba masu kiba ba sosai, farare wanda farin nasu har wani jaja yake dashi, sai kwantacen sumar kansu da taji gyara, wanda har gyaran da akayi musu iri daya ne, kyakyawan cute lips dinsu na karewa kallo, wanda suke pink color, wanda ya yiwa , kyakyawan bakinsu ƙawanya, wanda sai kayi zaton tea spoon ma , bazai shiga ciki ba, saboda tsabar karantarsu.

Sai kyakyawan hancinsu, da ya yi, baka’in dacewa da cute face din tasu, komai nasu kala daya , dan banbancin kadane, inda daya yana da gold eyes, dayan kuma nada blue, sai sumar kansu wadda ta daya, tafi ta daya yawa, amna har kayansu kala daya ne, hatta yanayin tafiyarsu ma kala daya ne.

Wasu manyan motoci na ga sun nufa, wanda a kalla sunkai guda goma, ko wace kuma, an rubuta mata ‘ABUL-KHAIR.’

Wanda dukansu baƙaƙe ne, daya ce kawai fara wadda kuma itace tsakiyarsu tasha tinted amma duka sauran goma sha huɗun, duk baƙaƙe ne.

Shiga sukayi tare da haƙincewa a bayan motar, a hankali motocin suka fara tafiya domin barin Airport din, direct cikin garin na Damaturu , suka shiga, tafiya mai dan tsawo sukayi kafin su karaso, bakin tafkeken get din, masarautar wanda sa ka kalleta, zaka gane cewa ba karamar masarauta bace, masarauta ce mai dinbin tarihi da dadewa, domin komai nasu na Al-adane , hatta ginin masarautar na dane, domim gini ne na tubali.

A hankali motocin suka karasa shigewa cikin masarautar da na karewa kallo.

Bakin wani part , wanda tun daga waje in ka kalleshi kasan ba karamin kuɗi aka kashe mishi ba, motocin suka tsaya.

Daya ne ya fara fitowa ya shiga cikin part din kusan 1 hour kafin naji an kara bude kofar motar.

Dayan ne, ya fito shima tare da nufar part din da dayan dan uwan, nashi ya shiga, a hakan yake tafiya kamar wanda kwai ya fashe mawa a ciki, sai wani yamutsa fuska yake.

Wow! Ashema a waje ban ga komai ba, dan saida na yi mutuwar tsaye na yi saboda ganin tsabar haɗuwar part din, wani kofa na ga ya nufa, bin shi na yi a baya domin ɗauko rahoto.

Wai ashe bedroom ne, karewa bedroom din kallo na yi, shima ɗin dai ya hadu bed din, kuwa ya sha shimfiɗa ta alfarma, irinta gidan sarauta.

Bathroom ya nufa direct, da chan kofa na ji ana cewa , “Twins bari na haɗa maka hot water, ka ga garin da akwai sanyi, kuma ka ga yanayin jikinka bakajin dadi,” ya fada yana wucewa .

Bakin bed din ya zauna yana fitar da numfashi da dan karfin ga bugun zuciyarshi da yake bugawa da dan karfi.

Minti kadan, na ji ana cewa “Khair! Khair!! taho ka yi wankan”, ya fada yana fitowa daga bathroom din.

Kamar bazai tashi ba kafin ya mike a hankali, saida yazo kusa dashi kafin ya juya blue eyes dinshi tare da cewa “thanks”, a hankali wanda indai ba kana kusa da shi ba, to baza ka ji ba. Girgiza kai kawai ABUL ya yi, yana jinjina wannan miskilancin irin na KHAIR wanda ko mahaifinsu da yake sarki baya wannan takamar.

Saida ya share kusan 30 minutes, kafin ya fito, sumar kannan mai tulin yawa tana zubar da ruwa. Kan kujerar dressing mirror, ya zauna tare da fara goge kanshi da towel din, da ya naɗo sumar kanshi da ita.

Abul ne, ya shigo bedroom din, hannunshi rike da wasu kaya wanda ba wasu masu nauyi bane, sosai wanda kuma kalla daya ne da na jikinshi.

Ta mirror Khair ya kalleshi, ajiye kayan ya yi gefen bed din tare da matsawa kusa da shi, towel din da yake a kanshi ya ansa, ruwan da yake a kanshi ya shiga goge mishi, sai da ya gama, tas kafin ya shafa mishi, lotion saida ya gama, kafin ya dauki hand dryer, ya fara busar mishi da gashin kanshi.

Taya shi ya yi, ya gama shiryawa tas, kafin su fito Abul rike da hannun Khair fita sukayi daga part din, wani part suka nufa, wanda yake dan nesa kaɗan da nasu.

Wata tsohuwace zaune sai masifa, ta kewa wasu kuyangun da ke, zirga-zirga a parlour, ”shegu, ni kuyi sauri ku kawomin abinci naci, kar na mutu, ace tun dazun baza’a kawowa mai rai abinci ba, sai nasa Abdul-jabaru, ya koreku duk an kawo wasu tunda kudai salamanmu ne.” Ta fada tana wurga musu harara.

Suna shigowa naga khair yadan saki fuskarshi, Masha Allah , duk da ba dariya ya yi, ba amma sosai ya yi kyau.

“A’a, kunga dan Albarka ina kake a ciki, karaso nan, dama tun dazun nikeson zuwa gurin Abdul-jabbaru dan ya kiramin kai, ashe kana kusa ma”, ta fada tana washe hakoranta.

Matsawa kusa da ita Khair , ya yi yana cewa, ” Ayya sai kuma gani nazo”, ya fada fuskarshi babu yabo ba fallasa.

*****

Zaune suke sun hada kai da guiwa, su ba kuka suke ba amma yanayinsu ya baiyana halin da suke.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 2.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

2 thoughts on “Abul-Khair 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×