“Na sani Ablah akwai hatsari domin kuwa zama da mutum irin Amarya dole da akwai Babban hatsari, amma ki sani rayuwa cikin tsoro yakan karyawa Mutum zuciya, abinda zai ka iya ma sai tsoron yasa kaji ba baka iya ba, ya durƙusar dakai ya hanaka taka rawar gaban hantsi, ba’a Rayuwa cikin tsoro muddun zaki zauna da mutane irin Amarya to fa dole ne ki cire tsoro cikin zuciyarki ki kawo jarunta da rashin tsoro ki dasa su a zuciyarki, ina ji a jikina zakiyi nasara akanta Ablah muddun kika ɗaukk zuciyata babu abinda zai tsorataki a duniya, ki sani ke fa gaskiya kika riƙe akasin ita da ta riƙe zalunci, dole kuma gaskiya itace zatayi Nasara akan ƙarya, bazaki bar gidan AMBASSADOR AHMAD GIWA ba saboda ƙaramin abu dole zaki zauna domin kare rayukansu, ki sani babu wanda yasan munanan halayyarta sai ke Allah ya nunawa mai yiwuwa hakan yana nufin kece kariyarsu, zan miki addu’a a matsayina ta mahaifiyarki, na Tabbata Allah zai kareki domin kuwa mun dogara ne ga Ubangiji kuma zai zamo gatanki, Ablah bawai saboda muna ƙwaɗayin abin hanunsu ko dan abinda suke bamu ba, zakiyi wannan aikin, a’a zakiyi ne saboda Allah, Ablah karki sake suji halin amarya daga bakinki domin kuwa ko kin faɗa bazasu yarda ba, ta gama ciye zuciyarsu ta shiga jikinsu ta yadda zata cutar dasu ba tare da sun ankara ba, kiyi aikin da zaisa su gani da idanunsu wannan shi zaisa su yarda.”
“Kai Umma nikam bazan iya ba, Umma bazan iya wannan Rayuwar ba, idan har ta cutar da rayuwata Umma kece wacce zakiji ciwo ba suba, su kawai sai dai su mana jaje na lokaci ɗaya daga nan zasu manta su cigaba da hidimar rayuwarsu, amma ke fa bazaki taɓa daina jin ciwon ba, Umma ki gafarceni bazan iya rayuwa cikin wannan gidan ba, ni kawai gobe zan tattaro kayana na dawo gida.”
Numfashi Umma ta saki tana girgiza kanta tare da tuno abubuwa munana da suka faru da ita a Rayuwa wanda sukafi waɗannan haɗari, ta kuma daure zuciyarta ta ƙetare su, amma wai ita Ablah wannan ƙaramin aikin da Zatayi ba tare da sanin kowa ba, tana jin tsoron sa, ina ma ana arawa Mutum zuciya Tabbas da ta sauyawa Ablah zuciyarta da nata.
“Ablah na faɗa miki ki cire tsoro cikin zuciyarki insha Allah babu abinda zai cutar dake mun riƙe Allah bazamu cutu ba, ke dai kiyi amfani da Maganar dana faɗa miki na sani koda kin cutu babu wanda zai kaini baƙin ciki duk wanda yaji ciwo bayana ne, amma a hakan nake baki umarnin kije kiyi aikin Allah ba ƙaramin lada zaki samu ba.
“Shikenan zan miki biyayya amma sai dai Allah yana gani ina cikin tsoro da fargaba ina ji a jikina akwai abu marar daɗi da zai faru dani a cikin wannan gidan, saboda Aunty Amarya ba Mutum bace mai tsoron Allah, ni damuwata na rasa me take nema a wajen su da take ƙoƙarin cutar dasu, Umma duk mutumin da yayi ƙoƙarin kisan kai babu abinda bazai iya aikatawa ba.”
Murmushi Umma tayi tare da cewa.
“Ƙwarai maganarki gaskiya ce duk wanda zai iya kisan kai to babu abinda zai bashi tsoro, sanin abinda take nema garesu, wannan shi zaki fara bin diddigi, Allah ya rabaki da sharrinta.”
Da ameen Ablah ta amsa sun juma suna tattaunawa da Umma kafin ta tashi ta shiga gidan su ƙawarta Hafsa, ta samu ma bata nan bata wani juma ba ta dawo gidan su da magaruba kamar yadda ta cewa drevern haka yazo ya ɗauketa ta koma.
Washe gari da safe misalin bakwai kafin kowa yayi breakfast, Al’ameen da Daddy suka raka su Khalipa da Ashfat da Auntyn Faruq airport, basu dawo ba har sai da jirgin su ya tashi dawowar su har Ladiyo ta jere breakfast, bayan sunyi breakfast kowa ya kama harkar gabansa, shima Al’ameen wunin ranar yana gida bashi da zuwa Office, Ablah kuwa wuni guda bata fito falon ba, tunda ya zauna a falon yake dube duben ta inda zai ganta sai dai ko gilmawarta bai gani ba rabon da ya ganta tun lokacin daya mareta, haka kawai sai yaji babu daɗi da bai ganta ba, wataƙil ko marin da ya mata ne yasa taƙi fitowa.
“Anya kuwa tana lafiya bata fito ba tun safe gashi yanzu har 3:20.”
Ya furta a zuciyarsa, numfashi ya saki tare da miƙewa ya haura sama.
Aunty Amarya kuwa tana zaune cikin bedroom ɗinta tana tunanin hanyar da zata sake ɓullowa tunda wannan damar ta kufce mata, murmushi ta saki tuno da Ablah tare da miƙewa ta furta.
“Tabbas dole nayi taka tsantsan nasan yadda zan iya takuna Saboda akwai mujiya a cikin gidan nan, nasan dole zatayi ƙoƙarin kawo min farmaƙi, hmmm! Yaro kenan ta yaro kyau take bata ƙargo, bara na ɗan saki zaren naga ta inda zata fara kamawa domin sanin girman hukuncin da zan yanke mata, domin kuwa muddun tace zata ja dani, to kuwa Tabbas zata jefa kanta cikin wuta, *ABLAH* yarinya mai wayo wai dani zata ja, lallai kuwa zarenki zai tsinke baije ko ina ba, ni Amarya murucin kan dutse ne ban fito ba sai dana shirya, bara mu zuba mu gani, na dai yi nasarar kashe mutum ɗaya na kuma cirewa ɗaya ƙafa duk da ba ƙafar bane naso ta fita ran naso ya fita, bari muga ko zaki yi ƙoƙarin dakatar da nasarata domin kuwa muddun ina numfashi sai na mallaki dukiyar AMBASSADOR babu wanda ya isa ya dakatar dani muddun kuwa wani yayi ƙoƙarin wannan kuskuren shima zan yanke numfashin sa.”
Tayi Maganar tana sheƙewa da dariya, tare da ɗaukar wayarta ta fito falo, Ummi ta samu zaune cikin kujerun falon, zama itama tayi cikin daraja Ummi tace.
“Ummin Al’ameen barka da fitowa yau baki fito kinyi breakfast ba, na aika ihsan ta duboki tace baki tashi daga bacci ba.”
“Tunda mukayi Sallama da su Khalipa na koma na kwanta, ina azumi yau kin san an biyoni guda ɗaya a Ramadan shine yau na ɗauka.”
“Haka fa aini na manta ma, ina Maimu tayi ne ina son aiken su ita da wannan shashar Afnan gidan Hajiya Sauda.”
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
“Maimu ai tafi Afnan shashanci, yanzu na jiyo muryarta bedroom ɗin ihsan suna can suna game.”
Ummi ta ƙarisa Maganar idanunta na sauƙa akan Ablah da ta fito daga bedroom ɗin ta, idanunta sun ɗan kaɗa sunyi ja, Ummi kira ta ƙwala mata, ta ƙariso tare da sunkuyawa tace.
“Ina kwana Ummi.”
Da lafiya Ummi ta amsa tana dubanta tare da cewa.
“Lafiya kuwa naga idanunki sun sauya kala, tun jiya nake ganin yanayinki ya sauya meke damunki ko dai akan marin da Al’ameen ya miki kike ɗari ɗari damu?”
Ɗago idanunta Ablah tayi ta kalli amarya domin kuwa itace sanyin jikinta tun jiya, idanu suka haɗa Aunty Amarya ta sakar mata murmushi, kauda kanta Ablah tayi tare da cewa Ummi.
“A’a bashi bane, bana jin daɗi ne kaina yake ciwo.”
“Subahanallah! Sannu kinsha magani kuwa?”
Kanta Ablah ta girgiza alamun a’a, Ummi cikin kulawa tace.
“Ya kike wasa da lafiyarki haka, to maza ki shiga bedroom ɗina jikin drowern mirror akwai maganin ciwon kai ki ɗauka kisha, Allah ya baki lafiya.”
Da ameen Ablah ta amsa zata mike taji muryar Aunty Amarya.
“Sannu Ablah Allah ya baki lafiya, Allah Sarki shiyasa yau wuni guda banga kin fito ba, ki daina wasa da lafiyarki ki kula sosai.”
Murmushi Ablah tayi ta amsa mata da.
“Insha Allah zan kula na gode da tunatarwa.”
Tayi Maganar tana haurawa bedroom ɗin Ummi, murmushi Aunty Amarya ta saki tare da Binta da kallo.
Door ɗin ta tura tare da shiga da Sallama, drowern ta nufa sai idanunta suka sauƙa a kansa yana kwance a bed ɗin Ummi yana baccin sa cikin nutsuwa da kallo Ablah ta bisa, kyakkyawan gaske ne, sai dai kuma mugunta da baƙin hali da suka ɓata masa kyawun bakin ta taɓe tare da nufar drowern hanu tasa zata ɗauki maganin bisa kuskure sai ta bige cup ɗin dish dake ajiye saman wadrop, ji kake ƙas…ƙas…ƙas ya tarwatsa tare da yin tsawa, a firgice Al’ameen ya buɗe idanunsa yana ambaton innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Idanunsa ne suka sauƙa akan dish ɗin dake tarwatse a ƙasa daga ƙafafuwan ta ya fara kallonta har sai da ya ɗago idanunsa ya ganta kansa ya dafe tare da tsareta da idanunsa bakinsa ya cije ba tare da yace mata komai ba, ganin bazata iya jurar haɗa idanu dashi ba ya sata sunkuyar da kanta ƙasa zata bar wajen cikin tsawa yace mata.
“Karki kuskura ki fita!”
Turus ta tsaya cike da tsoronsa.
“Ki sunkuya ki kwashe wannan glass ɗin da kika fasa da hanunki.”
Zaro idanunta Ablah tayi tana kallon glass ɗin idan banda rashin imani ta yaya za’ace ɗan Adam ya saka hanunsa a wannan glass mai Uban kaifi, idanunta ta ɗago ta kallesa idanunta yayi raurau har hawaye ya fara taruwa a idanunta, ganin yanayinta yaso bawa Al’ameen dariya, sosai take burgesa idan ta shiga wannan yanayin ita dai kuka baya bata wahala ƙara tsuke fuskarsa Al’ameen yayi tare da zaro mata idanunsa.
“Bazaki sunkuya ki kwashe bane kike kallona, idan kika yarda na tashi sai na danna ƙarfarki cikin glass ɗin, tunda a rayuwarki bakya ƙaunar kiga ina hutawa.”
“Al’ameen dan Allah kayi hakuri zan ɗauko tsintsiya na kwashe, idan na saka hanuna zai yankeni kuma bada sanina ya fashe ba.”
“Au dama kina tsoron ya yankeki shine kika fasa shi, to kuwa tunda kika tasheni daga bacci, dole sai kin kwashe da hanunki oya maza fara.”
Tura bakinta Ablah tayi cike da fara jin haushin sa tace.
“To kai nan ɗakin kane da zakazo ka kwanta ni wallahi bazan saka hanuna ba naji ciwo.”
Ta ƙarisa Maganar hawaye na sauƙa daga idanunta, tare da ficewa da gudu ganin da gaske yake sai ya ji mata ciwo, dariya Al’ameen yayi har fararen haƙwaransa suka bayyana miƙewa yayi da kansa yaje tollet ɗin Ummi ya ɗauki tsintsiya da faka yazo ya kwashe glass ɗin ya juye a dosbin, ya koma ya kwanta na sakin murmushi.
Da la’asar lis Haidar ya shigo cikin shirin fita hanunsa riƙe da key ɗin motar sa, sama ya haura bedroom ɗin Al’ameen, ya sunkuya zai kwashi wayoyinsa Haidar ya shigo da Sallama dagowa Al’ameen yayi tare da yin murmushi yace.
“Yau dai Allah ya ƙaddara bazaka min ƙorafi ba, muje na shirya.”
Dariya Haidar yayi tare da juyowa suka fita wayar Faruq Haidar ya kira kasancewar tare sukayi zasuje wajen Nafeesa, kusan 3miss call Faruq bai ɗauka ba, da kansa Haidar ya shiga part ɗin nasu nan ma dai baya nan, haka suka shiga mota shida Al’ameen suka ɗauki hanya, sunyi nisa da tafiya Haidar yace.
“Yau dai Al’ameen zaiga Nafeesa Allah yasa ka yaba da zaɓi na.”
Murmushi Al’ameen yayi tare da cewa.
“Har kullum bazan daina faɗin wannan kalmar ba, a soyayya babu zaɓen kyau, an dai fi buƙata ka zaɓi ƴar mutunci wacce zata baka daraja da cikakkiyar kulawa a rayuwarka, sannan taga mutuncin ahalinka wacce zata kare martabar ka, mai cikakken ilimin addini koda kuwa bata da na zamani, idan ka samu wannan to Tabbas kayi kyakkyawan zaɓi komai munin fuskarta kuwa.”
Murmushi Haidar yayi yana cigaba da dreving ɗinsa yace.
“Shiyasa nake son naga zaɓinka Al’ameen domin kuwa duk macen da tayi nasarar samunka a matsayin miji to fa lallai ta ɗaga tuta.”
Still dai murmushin Al’ameen ya kuma yace.
“Zaɓi kam na riga da nayisa Haidar domin kuwa idanuna sunga matar da ta dace dani.”
Kusan sake sitiyarin motar Haidar yayi tare da furta.
“Whattttttt!”
Al’ameen saurin riƙe sitiyarin yayi tare da cewa.
“Au kashe mu zakayi ne meye abin sake sitiyarin motar.?”
“To ai dole na sake Maganar taka ce ta bani mamaki kai da baka kallon mata, a ina ka gano budurwar kaga Abokina faɗa min wacece wannan wacce tayi matuƙar dace haka.?”
Dariya sosai Al’ameen yayi tare da dukan kafaɗar Haidar yace.
“Tayi dace ko kuma ka tausaya mata, ko ba cewa kuke zama dani sai an saka haƙuri.”
Murmushi Haidar yayi tare da cewa.
“Ni fa ba wannan maganar ba, kawai so nake nasan wacece budurwar?”
Yayi Maganar dai-dai suna isowa ƙofar gidan su Nafeesa.
“Ban gama saita komai ba idan na gama dole zaku sani kai dai yanzu kira jarumar taka.”
“Kaga bara kaga mu koma gida dole sai ka sanar dani domin kuwa babu ruwana da ka saita ko baka saita ba.”
Yayi Maganar yana dannawa Nafeesa kira ya sanar da ita sun iso.
Murmushi kawai Al’ameen yayi tare da buɗe motar ya fito ya jingunu da jikin motar yana harɗe hanunsa a ƙirji tare da bin ƙofar gidan su Nafeesa da kallo shima Haidar fitowa yayi ya tsaya gefen Al’ameen ba’a juma ba kuwa sai ga Nafeesa ta fito, tunda ta fito idanunta akan Al’ameen suke, haka kawai take jin munguwar ƙaunarsa koda tana son kuɗin amma har zuciyarta tana jin soyayyarsa, ji take kamar ta ruga da gudu ta rungumesa, ashe ma yafi kyau a zahiri fiye da hoto, shi kuwa Al’ameen baima lura da ta fito ba domin ya saka idanunsa akan wayarsa, saurin saita kanta Nafeesa tayi tare da sakin murmushi tayi sallama.
Amsawa Haidar yayi shima yana murmushin yace.
“Barka da fitowa Duniyata, kinyi kyau fa.”
Ɗan dariya Nafeesa tace.
“Ban dai kaika kyau ba, sannu da zuwa abokinmu.”
Tayi Maganar tana duban Al’ameen, ɗago idanunsa Al’ameen yayi yana murmushi yace.
“Yauwa sannu, kece Nafeesa ko?”
Murmushi tayi tana ƙura masa idanu ta amsa da.
“Ƙwarai ni ce ya kk.”
“Ina lafiya sai dai fa jinki yafi ganinki, da alamu keɗin ruwa biyu ce.”
Wani irin tsinkewa zuciyar Nafeesa tayi tare da jin haushin maganarsa (jinki yafi ganinki to me yake nufi da hakan? Da gani wannan zaiyi izza da rainin wayo, Lallai dole sai nayi babban shiri akansa, gashi dai kamar a sace a gudu sai babu sauƙin kai) Tayi Maganar cikin zuciyarta, sai kuma ta ɗan saki murmushi tare da duban Haidar tace.
“Farin ciki na kana jin abinda yake faɗi wai jina yafi gani na, sanar dashi ban damu wani ya yabeni ba, Muddun dai kai ka yaba.”
Murmushin gefen baki Al’ameen yayi tare da cewa.
“Iya dai gaskiya ta na faɗa.”
Yayi Maganar yana buɗe motar ya shige.