"Momma na kasa fahimtar meke faruwa ne a cikin gidan nan mtsss hmmm! Yaya Al'ameen a yanda na fuskance sa yau bazai amince da maganar kowa ba akan wannan Nafeesan."
"Nima na fahimci hakan yanzu kuma mun janye ƙudirinmu Allah yasa hakan shi yafi alkairi."
"Ameen Momma shine addu'a."
Tayi Maganar tana tashi ta haura sama bedroom ɗin Haidar ta nufa tare da kwankwasawa sai dai bai amsa mata ba hannu tasa ta buɗe ƙofar sannan ta shige ciki yana zaune takure jikin bed ɗinsa sai kuka yake tamkar ƙaramin yaro, numfashi Rufaida ta saki cike da. . .