Rufe idonta tayi tana kankame jikinta tamkar za ta suma ta yi wata irin gigitacciyar ƙara.
Prince Adeel ya kalleta ya kauda kai, yaja towel din sa ya daura, yana kokarin sa kaya, ci gaba da ihun tayi kamar wacce aka sawa saban batir, har cikin dodon kunnensa yake jin saukan kararta.
Cike da takaici ya karasa inda take yana daka mata tsawa.
Maimakon ta nutsu tsawar da ya mata yasa ta ci gaba da kwallara ihu tana kokarin shidewa.
Rufe mata baki ya yi da hannunsa yana mata alamar tai shiru.
Ita kuwa ido ta kafa masa suna kallon. . .
Masha Allah
Gaji da abun Dariya kike wollah
Yareema abi a hankaki dai
Zayeeshatou Allah ya qara basira
Gajin yarima🤓 Allah ya yafe miki😂😂