“Fati Ina son yayar ki har fiye da yadda nake son kaina don zan iya fansar rayuwar ta da tawa rayuwar amma me yasa banyi sa ar da maza keyi wurin samun soyayyar abin son su ba? uhum fati me nayi wa yayar ki wanda ta kasa sona?
Ya furta yana zubawa fatin shanyayyun idanun sa Al’amarin da yayi matukar zuke jinin jikin fati taji Ina ma ace bata wanzu a duniyar nan ba? Ta samu da kyar ta iya motsa labban bakin ta tana fadin, “Ina ganin kamar in ka bita a sannu a hankali zata so ka ka san zuciyar mace cike take da rauni amma tafiya sannu kwana nesa.
“Banga alamar hakan a tare da ita ba fati domin kuwa na gama gane inda Nadiya ta dosa. na fahimci har da talauci na ya kara kashe min kasuwa shiyasa Zan tashi na nemi kudi wata Kil idan na dace na samu kudi zata iya sona tunda na kula har da zama a gidan nan ne yake turbudewa soyayya ta kwatami.
Wani irin abu ya tsayawa Fati a zuciya yau ga wani Al’amari so kenan da baya duban alkibla kuma mai sab’ani da yawa inda ake yin sa ba nan yake sauka ba sai inda ba a damu da shi ba.
“Wace shawara zaki bani fati akan wannan Al amarin? wane taimako kuma zaki bani ? Fati ke kadai ce madogara ta a yanzu.
“Madogara yaya kaisar ai Allah ne mafi cancantar a dogara dashi. banyi maka alkawarin wani Abu akan hakan ba saboda nima ba dadin Nadiya nake ji ba sai dai in bata tashi wulakanta ni ba amma nayi maka alkawarin Taya ka da ADDU A shima ba zance Allah ya baka nadiya ba sai dai zan roka maka Allah ya baka abinda yake shine alheri a rayuwar ka ko da ba shi kake so ba don sau tari muna son abu sai ya zamo ba alheri ne wurin mu ba wanda bama son sai ya zama shine alherin bamu sani ba.
“Haka ne fati Amma ki dai roka min na samu Nadiya na san zata zama alheri in sha Allah mai yuwuwa lokacin da zakiyi rokon kina dab da ijaba fati ba zan boye miki ba yadda nake son nadiya ko rayuwa ta sai haka . Ina jin tamkar na hadiye rai na na mace idan na tuna wacce nake so bata sona.
Wani tsini kakkaifa ya soki zuciyar fati wanda tayi matukar jarumtar shanyewa saboda ba karamin duka yayi mata ba akan son da yake kambama yana yiwa Nadiya.
“To yaya kaisar Allah yasa son ya zama samu fatan aminci aminci ni da kai da dukkan Al ummar ANNABI muje karatu lokaci n tafiya.
“Nagode sosai sister fati Anya kuwa zan iya karatun nan a yau? Ina fama da love sickness fa? Kar nazo Ina biya miki sunan Nadiya a littafin ki .
tayi wani murmushi mai ciwo takaici na naushin kirjin ta ta kasa cewa komai inda kaisar ya gane bata ji dadin maganar ba don haka yayi maza yace
“Muje k’asan umbrella fati yafi iska sai muyi bitar a can
Suka fita farfajiyar gidan suka zauna a fararen kujerun suna karatun sai ga daddy ya fito da jaka zai fita sai ya hangi su kaisar da fati sun bude littafi suna karatu.
Da sauri Kaisar ya mike ya isa ga daddy ya karbi jakar shi ya rike mishi da nufin raka shi bakin motar . Daddy ya dube su yana fadin, “Fatima karatu ake ne ?
“Eh Daddy yaya kaisar ya ke dan dora min.
“To Ina nadiya ne da ba ta zuwa daukar karatun?
su duka sukayi shiru.
“Kira min ita fatima idan tana cikin gidan me take nufi da bata zuwa dorin karatun?.
“Daddy ta fita ai.
Motar nadiya ta danno a guje ta shigo daddy yabi motar da kallo har tayi parking ta fito sai kuma ta hangi daddy da shegen dan anacen can sai gaban ta ya fadi.
“Zo Nan ! Cewar Daddy! Ta matsa da sauri don idan akwai abinda ta tsana to daddy ya zage ta a gaban kaisar ko yayi mata fada.
“Daga Ina kike? Daddy ya tambaye ta.
“Dinki na karbo daddy.
“Me ya hada ki da motar nan ? Aro kika yi ko kuwa kin nuna mishi halin naki koma kin zage shi? Tayi k’asa da kanta.
“Bani makullin motar nan kuma daga yau na haramta miki shiga mota ko wace iri ce a gidan nan duk inda zakije kisa direba ya kaiki . kuma daga yau yanzu ma ki dauko littattafan ki kizo kaisar yana dora miki karatu kinji na fada miki?
Ta Mika key din motar tana fidda hawaye don ta gama gane daddy Yana son bata kunya ne kawai Amma ta yaya za a ce duk inda zata sai dai a kaita kuma wannan banzan matsiyacin shine zai koya mata karatu? Dole ta bayar da key ta wuce tana jin tamkar zata amayar da zuciyar ta daddy ya mikawa kaisar key din motar yana fadin
“Kar ka kuma bata aron makullin motar nan kaisar Nadiya ba zata sake tuka mota a gidan Nan ba akwai direba a gidan zai kai ta duk inda zataje kuma karatu matukar tayi wani abu ka hukunta ta in kuma ba zaka iya ba ka sanar dani .
“To in sha Allah daddy duk yadda kace haka za ayi.
Ya bude mishi motar ya saka mishi jakar shi direban shi yaja shi suka wuce
Tun da akayi hakan Nadiya ta kara kullatar kaisar zata zo wurin dorin karatun amma ba zata bude littattafan ta ba sai dai fati tayi nata amma ita in ma yace ta bude sai tace bai Kai wanda zai koyar da ita ba matsiyaci da shi wanda suka rufawa asiri shine zai zo gidan su ya nuna musu son iyawa?
Rashin mutunci dai kala kala babu wanda Nadiya bata yiwa Kaisar amma dan bawan Allahn nan son ta yake da iyakar iyawar sa bai kuma tab’a ganin laifin ta ba bare aibata shi da take ko a gaban uban wa kuwa in kuww ta tabbatar da Daddy baya gidan ba zata fito dorin karatun ba in kuma yana nan to ko tazo zata karewa kaisar wulakancin ne mai daraja ta farko.
A yau da daddy yake gida ta fito farfajiyar gidan inda kaisar yake zaune fati na biyawa ita kuwa mandiyar tana rike da waya tana catt da show wanda yake cewa ta fito gobe akwai vedion wakar da zasu soma dauka kuma ta taho da sabuwar motar nan tata high land don yana son yayi show din ta a wakar
ta rasa ta yadda zata iya fita gobe ga dai daddy Yana gida gobe asabar kuma motar da yake magana an kwace an kuma hana ta fita sai dai direba ya kai ta.
tana zaune tana neman mafita don hakikatan dai sai taje daukar vedion wakar show amma kuma ta Yaya zatayi hakan ba tare da daddy ya san anyi hakan ba?.
“Allazi wahidun Allah da girma yake.
su duka suka waiga jin amon sautin tsohon yana doso su .
Nadiya ta juya inda taga tsohon nan ne wanda ta banke kwanaki shine yake shigowa cikin gidan nasu wanda yake cike da masu tsaron kofar ta yaya akayi suka bari ya shigo? gidan da babu mai shigo shi sai anji wurin wanda kazo?.
“A taimaka mana don arzikin manzon Allah. Wanda zai bamu don ANNABI kawai muke so in don Allah ne rike kayan ka bama so .
Ya fadi hakan yana dosar su nadiya da son lallai a cikin su yake son su bashi don ANNABI.
Mamaki ya cika kaisar da fati wacce tace
“Gaskiya ne don ANNABI akayi duniya ba don ANNABI ba da bamu san samuwar Allah ba .
ta mike tana Karbo kwanon tsohon tana fadin
“Baba kazo inda akeyin dokin ANNABI .
“Nagode diya ta don ANNABI kawai nake karba Mai yi don Allah ya rike kayan sa.
fati ta wuce cikin gida ta dawo mishi da abinci da kuma kudi naira dubu tana bashi ya karba Kaisar ma ya bashi naira dubu inda nadiya kuma take hararen tsohon kafin tace.
“Kaji min shegen tsoho kai har ka Isa kace baka son abu don Allah? To wa yayi ka in ba Allah ba ? wannan anyi tsohon banza matsiyaci kar ka kuma tako kafar ka gidan nan in sadaka kake so kake tsayawa a waje tunda kai matsiyaci ne har kace baka son abu don Allah? .
ya dubi nadiya da take nuna shi da yatsa tamkar zata tsone idon shi.
“Yarinya kibi duniya a sannu in baki gane falsafar ba tambaye ni mana na fsssara miki? tsoho kama ta kike cewa tsohon banza? dukkan wanda yaso ANNABI yaso Allah amma ba dukkan mai son Allah ne yake son ANNABI ba. ANNABI shine madubin duniya da ba don shi ba babu wanda yasan Allah bare yadda zai bauta mishi sai da ANNABI yaxo. kuma Allah yana son Mai son ANNABI ba kowane mai son Allah Allah ke so ba. duniya da lahira ma Allah yayi su duka don ANNABI kuma ranar Alkiyama ma masoyin ANNABI ne kawai zai tsira don haka ki gane manufar zance na kuma ki daina wulakanta mutane baki san baiwar da Allah yayiwa mutane ba !.
“Zaka fice ko kuwa sai na sako maka kare ya raka ka tsohon banza? fice daga nan wallahi ko na faska maka mari sai tashin dauda kake tsiya da talauci sun ishe ka amma kake mana yen yen yen .
haj Aliya da ta fito taji irin dibar albarkar da nadiya kewa tsohon ta iso tana bashi kudin tana kuma bashi hakuri.
“Yi hakuri don Allah baba kaji yi hakuri .
ya karbi kudin yana fadin
“Nagode Allah ya biya da gidan aljanna .
ya juya ya fice haj Aliya ma ta wuce abinta bata cewa nadiya uffan ba.
ta mike da sauri don tabi bayan tsohon don tunda mama ta ji abinda tayi mishi sai ta fadawa daddy gara ta galla mishi mari ko biyu ne ta san ta mari shege koma me zai faru ya faru.
Yana dab da fita kofar gidan ta figo rigar shi ta wanke shi da mari ta kuma wanka mishi wani sai da tayi mishi mari biyu lafiyayye har abincin da fati ta cika moshi kwano ya kife.
“In ka kuma zuwa gidan nan sai ka gane baka da wayo tsohon banza matsiyaci.
Daddy yana tsaye yana kallon ta yayin da tsohon kuma yake dafe da kumatu yana kallon ta.
ta hankada shi waje har Yana kifeewa inda take duban masu tsaron kofar tana fadin
“Uban me kuke da har kuka bari wannan kazamin tsohon matsiyaci ya shigo mana? waye yabar shi ya shigo?.
“Wallahi bamu ga lokacin da ya shiga ba to ta Ina ma ya bi ya shiga? suka soma tuhumar kansu amma dai su basu ko fada mishi magana mai zafi ba .
ya saki kudin da su kaisar da haj Aliya da fati suka bashi bai kuma bi ta kan kwanon abincin da ya kife ba ya fice yana dafe da kumatu Yana tsiyayar ruwan hawaye.