“Ba ni key da Allah malam ban son sharri waye kuma sarkin gida da har sai mun tsaya jiran shi? dama na gane akwai munafunci a lamarin ki shiyasa kika ce kafar ki na ciwo ba zaki iya taka mota ba .
Fati taja baya da sauri tana fadin
“Mama tace kar na baki don haka mu koma gida .
Kaisar ya fito inda yaga nadiya ta biyo fati da gudu tana fadin
“Ke ji min matsiyaciyar yarinya sai kace motar ta uban ki ce da zance ki bani key ki hana? To sai kin ban shi wallahi ko kuma yanzu jikin ki ya baki labari.
fati ta juya tana fadin
“ni kuma wallahi tunda mama tace kar na baki ba zan baki ba.
Sun kwasa a guje sai sukayi karo da kaisar wanda ya tambaye ba asi fati ta fada mishi komai yayi murmushi yana fadin
“Bani key din muje na kai ku.
Fati ta mika mishi key din nadiya na auna mata harara.
“Ni dai na shiga uku na lalace ni da gidan mu amma matsiyata sunyi min kane Kane da gulma da munafunci .
Kaisar ya shiga mazaunin direba fati da nadiya suka shiga baya yaja su suka fice daga gidan yana cewa fati
“Sai kina nuna min hanya fati kin san har yanzu ban waye da garin bauci ba
Da nunin fati suka Isa katafaren kantin na fantami flaza suka shiga shi ma kaisar yabi bayan su don yaga ko akwai abinda zai dauka
kaya sosai nadiya ta dauka yayin da kaisar kuma ya dauki turare da links na hannu
Fati ta dubi nadiya tana fadin
“Mama tace kar mu wuce kayan dubu dari biyu anty nadiya.
“Da yake kudin na uban ki ne shine kike min iyaka ? da Allah malama bada kati a fidda kudi Ni ban saba harka da matsiyata ba.
fati ta bada katin ATM wanda mama ta saka dubu dari biyu don ta san sai Nadiya ta wuce hakan
kati ya nuna babu kudin da suka wuce hakan gashi ita kuma ta lodi kaya har na dubu dari uku da hamsin.
Kaisar ya dubu mutumin da yake fada musu abinda ke cikin ATM din dubu dari biyu ne sai dai su dauki na iyakar kudin su.
Dole Nadiya ta soma Rage kayan amma sai taji kaisar yana fadin
“Ku hada mu su karbi wannan ATM din ka cire a ciki mayar musu da nasu.
Nadiya ta dube shi tana fadin
“ATM din daddy ne ka sato ko? ni na san dama sai ka tattakura ka zabga mishi SATA in ba sannu akayi ba Ina kaga wannan kudin ? ai duk zuriar ku wallahi babu mai su don akan su dai sai dai a kashe ka.
Kaisar yayi murmushi bai ce mata komai ba aka cire kudin aka bashi katin atm din sa fati na ta mamaki har dai tayi mishi godiya amma Nadiya kam sai fada take wai kudin Daddy ne ya sato
Aka hada musu kayan yaran shop din suka fito musu da shi zuwa mota sai dai suna fitowa wani Abun mamaki da ban dariya sai kawai suka ga wata mahaukaciya ta haye saman motar su Nadiya tayi kwance abin ta tayi dai daya sai kyalkyala dariya take abin ta.
“Ikon Allah! Cewar Fati, shi kuwa Kaisar tausayi ta bashi.
Yaron motar ne ya ajiye kayan su Nadiya ya zaro naira hamsin daga aljihun shi yana nunawa mahaukaciyar yana fadin, “Babatu sauko ga naira. Ta dube shi tana fadin
“yau ba na son naira babatu bata son naira mota nake so.
ta fada tana kuma kyalkyale wa da dariya
Nadiya da take kallon mahaukaciyar a fussce yayin da fati ke mata ADDU AR samun lafiya don sai ta kara girmama kudurar Ubangiji baiwar hankali kadai da akayiwa bawa ta ishe shi ni i’ma a duniya.
yaron shagon nan yayi ta yiwa mahaukaciyar nan hikima da dabaru Wai don ta sauko daga motar nan amma taki . ya dauko wata roba mai dauke da abinci yana cewa
“Taho ga abinci babatu ga kare a bayan motar nan fa.
ta kuma kyalkyale wa da dariya tace bana so.
Kaisar ya matsa shima ya soma yi mata hikima da dabara yana mika mata kudi amma sai ta Kara gyara kwanciya a saman gilashin motar tana birgima .
A fusace Nadiya ta figo wata sanda ga alama ta mahaukaciyar ce kawai sai gani akayi Nadiya ta rufe mahaukaciyar nan da duka tana maka mata sanda akan ta iyakar karfn ta.
“Shegiya mahaukaciyar banza don kinga ana rarrashin ki shine kike kara bajewa? bari jikin ki ya gaya miki ke da kanki zaki sauko.
Kan kace me? jini ya soma fita a kan mahaukaciyar nan sai gata kicaaaa ta fado daga saman motar jikin ta yana ta kyarma kaf kaf kaf kafin ta mike ta sandare ta daina numfashi.
Sai kuma kallo ya koma sama wuri ya tara dan mutum ana kan mahaukaciya yayin da wani ke fadin
“Matar nan fa bata numfashi wallahi dubi jinin da yake fita a kanta.
Da sauri nadiya da jiki ya dauki rawa ta sulale daga nan ta tare napep ta wuce ta bar fati da Kaisar wanda mutane suka rike da cewa sune suka dake ta in har ta mutu to su suka kashe ta
Dole wasu suka ce dole su kaisar su kaita asibiti in kuma ta mutu a dora shari a
Kan kace me ? hukuma ta shigo cikin case din aka nufi asibiti da baiwar Allah wacce babu almun numfashi a tare da ita kaisar kuma bai sanarwa Daddy ba inda har yamma suna asibiti Allah da ikon shi mahaukaciyar ta kawo numfashi smma fa tana cikin hali don haka Kaisar ne ya biya komai na magani da asibiti kafin aka bar su tafiya bayan an karbi bayanin su da address din su
Mama tana kame da baki tana kallon fati ta kasa cewa komai
“Kice in banda tare da kaisar kuka tafi da tuni labarin ya dade da shan banbam? amma kinga da yake ta san abinda tayi shine ta sulale ta baro ku ni kam nagodewa Allah wannan yarinyar bana jin mutum ce sai dai ibilishiya.
“Kudin nan fa yaya Kaisar ne ya biya su don kayan da ta dauko sun wuce yadda kika ce.
Daddy ya dawo mama ta fada mishi abinda ya faru da sauri y mike yana fadin
“Fati tashi muje ki kaimu muga matar nan ai ba zai yuwa mu barta a gadon asibiti babu kulawa ba duk da Kaisar yayi mana kokari matuka gaya.
Mama ma ta mike tana fadin
“Bari nima na tashi muje ga abinci nan sai mu tafi mata da shi wannan yarinya kaddara ce a garemu Allah ya yafe mana mahaukaciya ta gwadawa wannan rashin imanin
tuni haj Aliya ta cika kwano ni da abinci suka fita ita da Daddy da da fati kaisar ma daddy ya kira shi suka tafi tare yana tambayar shi yadda abin ya faru yana bashi bayani har suka karasa asibitin amma suka tara’s wai mahaukaciyar tayi tafiyar ta babu wanda ya dan tafiyar ta amma ance an ganta a bakin fantami flaza Wai ta koma dama can take tsayawa tana bara dole suka juya kan motar zuwa fantami flaza amma babu ita babu dalilin ta dole suka koma gida Daddy yana mamakin halin Nadiya da irin daukar da tayiwa duniya.
Tero yana duke gaban distinguish Mukhtar Biro yana fadin
“Yanzu daddy don kawai an maida Nigeria gidan marayu sai ace haka kawai take haye za a bayar da umurnin kama mutum ba tare da yayi laifin komai ba kuma a kama shi har a hukunta shi babu neman kadi ko laifin da yayi? haka kawai fa aka bada umurnin kama ni babu neman dalili kuma da yake an raina dan Nigeria har yana tambayar ta yadda take so ayi dani ko da kuwa tana son a batar dani ya yarda da hakan tunda za a bashi kudi.
Distinguish Mukhtar Biro ya dubi Mustafa wanda yake amsa sunan Tero yana fadin
“Waye wannan da yake zambatar k’asa Mustafa? ba abinda yayi maka ne yafi damuwa ta ba irin mugun aikin da yake k’ara mayar mana da Nigeria baya saboda cin hanci da rashawa wanda sune suka zama babbar matsalar Nigeria kuma bai san ko kai waye bane ? baka sanar dashi dan uwan Hameed bane dan gidan mukhtar Biro?.
“Sai da boss yazo ne yayi beli na don har yace a kaini gidan dutse .
“Ai kuwa da yayi hakan da ya jawowa kansa har da dukkan zuriar su don duk wanda ya tab’a ku mustafa ya tabowa kansa musifa ko baiyi ta kakin sa ba to zai dauki long rest wanda zaiji a jikin shi.
Ya figi wayar da take gaban shi yana kora kira a wata lamba.
“Habibu waye adamu a hukumar DSS? ya fada da sigar son ya ji ko waye shi.
“To wannan dan uwan controller? To ya jawo ni fada ba kuma zaici banza ba wallahi sai ya gane ya tabo abinda yafi karfin.
“A a ba zanyi hakuri ba wallahi in nayi hakuri na cuci talaka saboda shi aka raina ni kuma yaya na ba daidai suke da Ya’yan talakaww ba wallahi a yau din nan sai an saukewa adamu inusa kakin sa shege marar mutunci.
Ya katse wayar yana kiran wani laying wanda ya bayar da umurni a Rubuta takardar dakatarwa ga adamu inusa shugaban DSS na jihar bauci
Kan kace me? sai ga doguwar takardar Mai dauke da dogon rubutu akan adamu inusa
Aka kawowa distinguish mukhtar biro wanda ya rattsba hannu ya bayar a kaiwa adamu inusa
Tero da yabi dan Aiken distinguish mukhtar biro zuwa kai sakon
Shugaban jami an DSS din ya karbi takardar yana kallon Tero wanda yake busa hayakin tabar shi Yana hararen shugaban DSS din
Ya bude doguwar takardar yana karanta dogon bayanin da ta kunsa wanda tuni ya jike da fargaba da zullumi domin kuwa ya gane maganar yaron ce ta tabbata ta cire mishi kaki gashi kuma ya fada ya cika.
Ya dubi Tero da wata irin nadama wacce tafi kama da fargar jaji .
“A yanzu ka san ko ni waye tunda gashi na cika maka alkawarin ka don haka ba kai ba hatta wacce ta saka ka kama ni a yau wallahi ba zan bari a kuma dukar lokaci ba zan nemo ta na rama wulakancin da tayi min a bainan nas kaga kai da ita baku sanni bane da Baku fara abinda kukayi ba. ka mare ni ka zagi Uba na a zaton ka nima bsnza wofi ne,? amma kai yanzu ka san ni ko wani ka gani zaiyi abinda kayi zaka hana shi don haka na barka lafiya zan tafi neman wannan tsinanniyar yarinyar a yau itama zatayi nadamar abinda tayi fiye da irin nadamar da kayi don kai taka mai sauki ce zaka iya komawa kan kijerar ka idan har ka zo ka nemi yafiyar hakan daga gareni kunnen ka kawai zanja na sa a mayar da kai amma wanna yarinyar a yau zan tagayyara rayuwar ta ta yadda xan dasa mata mugun bakin cikin da zata mutu da shi bai gogu a zuciyar ta ba.
Ya fice daga office din shugaban wanda ya jike da gumin zufa ya zabga uban tagumi ya lula duniyar gajimare .
Wayar shi ce ta dawo dashi duniyar mutane ya yi firgigit ya dubi wayar sunan da ya gani a fuskar wayar shi ya kare gajiyar dashi ya dauka jiki a sanyaye inda aka tabbatar mishi da sauke shi daga kan mukamin shi
Ya ajiye wayar yana godiya
bai sha mamaki ba sai da yaji distinguish mukhtar biro ya tura sunan wanda yake so ya maye gurbin adamu inusa . kan kace me ? labarin sauke adamu inusa ya game duniya yayin da duniya ta dauki kunji kunjin yan gaza gani suna ta yawo da zancen a gari musamman ma abokan Aiki wanda mafi yawa suke son ganin gazawa don suyi dariya ko Allah ya kara. don haka Al amarin ya damu adamu inusa wanda yayi abinda yayi don ya samu wani abu daga hannun nadiya wacce ta saba wulakanta mutane ta hannun shi don ko bakar magana ka fada mata yanzu ne zata kira adamu inusa shi kuma ya wulakanta mutum baya jin komai. Nadiya ta san adamu inusa ne ta silar aiken da Daddy ya tab’a yi mata zuwa wurin shi ta kai mishi hasafi akan wani case da Daddy ya kashe na wasu ma aikatan shi da suka samu sab’ani akan kudi har daya ya kai abokin fadan don a wulakanta shi amma Daddy ya biya kudin kuma yayiwa adamu inusa alheri shine ya tura nadiya ta kai to tun daga nan ta sanar dashi ita yar gidan kudi ce diyar iro GIDAN KUDI. tun daga nan idan Nadiya ta so wulakancin ta sai ta hada ka da adamu inusa ta bashi kudi shi kuma babu ruwan shi xai watsa ka fiye da watsin da akewa ya’yan caca. sai gashi Allah ya nuna mishi iyakar shi ta dalilin su Tero wanda ya kawo karshen sa dama ance rana dubu ta barawo .
*****