“Haj mu fa umarni aka ba mu ko kyanwar gidan nan ba ace mu baro ba don haka kowa zamu wuce daku.
Ai kuwa haka aka kwashe su kaf in ka cire masu gadi biyu da aka Bari maccid’o da Zubairu watakil suma don an dan fafata da farko an gane jan wuya ne shiyasa ba a matsa da son tafiya dasu ba ko kuma don tsaron gidan aka barsu Allah dai mafi sani.
Aka kai su haj Aliya da fati da Kaisar har da bataliyar ma aikatan gidan iro GIDAN KUDI duk aka garkame inda distinguish mukhtar Biro ya Tada ma aikata har zuwa kasar Senegal don finciko alh iro amma ko mai kama dashi basu gani ba dole suka koma suka sanar fati kuka take tana fadin.
“Mama wane irin wulakanci ne wannan ? Ina ma Anty Nadiya ta shige? Me muka yi da akayi mana wannan wulakancin? .
“To Fati ai Allah shi kadai yasan nufin su ni dama tun da naga zuwan mutanen nan da irin salon da suka zo da shi nace tsiya ta auku sai dai Allah yayi mana magani kinga daga neman wata sai gamu a garkame Allah ya dauke wahala.
Haj Aliya da take ta neman layin daddy amma baya samuwa saboda katse network din layin sadarwa kasar Senegal tayi shima bai fara neman su ba.
Kwanaki biyu su mama suna a kulle inda kuma Allah cikin ikon shi a cikin kwanaki biyu alh iro da aminin sa alh sule suka gama abunda ya kawo su Senegal suka juyo gida.
Yana sauka a filin jirgi yy soma kira shafik direba amma bai samu wayar shi ba sai kawai ya dauko drop na napep ya nufo gida.
tun a bakin kofar ne kuma zubairu da maccid’o suka kwarmata mishi abinda ya faru ranar da ya tafi na zuwan ma aikatan suka kuma kwashe kowa na gidan.
Ya cika da mamaki amma ya shiga gida don ya ajiye kayan shi ya fito zuwa bin kadin iyalan sa.
Ashe abinda bai sani ba tuni labarin dawowar shi ya Isa kunnen distinguish mukhtar Biro wanda ya baza komar neman sa sai gashi an fada mishi ya dawo don haka kafin Daddy ya gama shirin fitowa har motar jami an ta iso kofar gidan shi tana sallama mishi .
ya fito da mamaki suna gaisawa da jami an da suka zo daukar shi suka kuma sanar da shi aiken zuwa tafiya da shi cike da wani irin mamaki na neman da ake mishi ya shiga motar suka nufi hukuma
A can ya ga yadda aka gwamutsa haj Aliya da fati da ma aikatan gidan sa .
Haj Aliya tana ganin shi ta soma kuka tana fadin
“Daddy kaga Al amarin da ya same mu da rana tsaka? don Allah a fidda mu daga wurin nan kwana biyu bamuyi bacci ba .
tuni daddy ya tabbatar mata da yanzu zai nemi alfarmar hakan amma kuma duk kokarin ganin ya samu an saki iyalan shi da ma aikatan gidan nashi hakan bai samu ba domin kuwa an tabbatar mishi da wanda ya sa a kama su bai bada umurnin a sake su ba wato distinguish mukhtar Biro.
don haka shima umurnin sakaya shi aka bayar amma kuma girma da kimar sa ta sa ba ayi hakan ba sai dai neman distinguish din don suyi maslaha.
Ya nemi a sanar da distinguish din aka kuma sanar dashi ya taso da sauri teero ya tuko shi har zuwa hukumar binciken wacce take tsare da alh iro GIDAN KUDI da iyalan sa har da ma aikatan gidan sa.
K’atuwar motar Prado ta kamfanin GMT fara tas ta shigo hukumar binciken ta faka Tero ya fito ya budewa distinguish mukhtar Biro kofar ya fito hannun shi rike da tissue paper wacce yake ta faman dauke kwallar idon shi wanda yayi jajir don tun kwanaki biyu da suka wuce Rabon distinguish mukhtar Biro da farin ciki tun kafin su tsinci mugun labarin na rasuwar abdulhameed
Don kuwa Haj laila har yanzu bata daina gunjin kukan mutuwar ba duk da sai da kyar aka raba ta da gawar abdulhameed wacce aka kai mutuware saboda wai sai an gama binciken ta yadda ya mutu ko za ayi mishi janaza a mika shi gidan mu na gaskiya.
Kai tsaye distinguish mukhtar Biro ya danna kanshi s cikin office din shugaban binciken babu ko sallama saboda Isa da izza yana faman share hawayen fuskar shi.
Da sauri shugaban ya mike tare da alh iro suna tarbe shi suna mishi barka da zuwa shugaban Yana aje mishi kujera ya zauna yana yagar tissue paper Yana fyace majina ya zubar da tissue din a nan tsakiyar office din yana sauke kallon shi ga alh iro GIDAN KUDI yana zuba mishi jajayen idanun shi masu kama da rushing wuta.
“Ranka ya dade ya ya katin hakurin abdulhameed? to Allah ta ala yayi mishi rahama yasa ya huta ya bada hakurin rashin sa .
cewar shugaban wanda yake magana cike da kwantar da murya yana nuna tsantsar ladabi da biyayya
Idon distinguish mukhtar Biro ya kara tara kwalla kafin ya kece da kuka marar sauti saboda nissan taxarar da ya hango mutuwa ta shata musu tsakanin sa da abdulhameed wanda ya gwammace ace ya rasa komai da ya mallaka akan rasa abdulhameed gashi kuma babu tabbaccin samun wani tunda an kayyade iyalin
Alh iro ya zubawa distinguish mukhtar Biro ido yana tausaya mishi don ya san yaya akeji a rasa masoyi iyaye ko ya’ya ye.
“Ayi hakuri mai girma distinguish mutuwa guda ce kuma tana da miki da Rad’ad’i ADDU A ce kawai abinda mamaci yake bukata .
Distinguish mukhtar Biro ya dago kanshi daga rusa kukan da yake wanda ya dora Kan shi akan tebur din shugaban Yana keta kuka marar sauti sai hawaye da suke faman tsere a fuskar shi.
A fussce ya dago kanshi yana saukewa daddy jajayen idanun shi masu kama da garwashi yana Jin tamkar ya hadiye daddyn wai a kashe mishi yaro kuma ana bashi hakuri?.
“Hakuri kake bani don an maida ni shashasha? yarka ta kashe min yaro kai kuma kana bani hakuri? kana nufin yarka ta kashe banza wofi kenan?
sai kuma ya sake kecewa da kuka a wannan karon kukan shi har da sauti da shessheka .
Wani irin matsiyacin tashin hankali da firgici ya shigi daddy jin yace yar sa ta kashe mishi dan shi? wane irin kisa yake magana? wace yar yake magana? duk da a rikice sai da yabi shi sannu don ya ware mishi mugun kullin mai wuyar warwara.
Da sauri daddy ya matsa gareshi yana bashi baki don ya gane a ciki yake magana kowace iri ce tana iya fusata shi tunda gashi ban hakuri yana saka shi kuka.
“Ka gafarrce ranka ya Dade wallahi ban san komai kake magana akai ba wallahi bana gari zuwan kenan na samu sakon nema na da ake wane irin kisa ?”
Distinguish mukhtar Biro ya kuma yago tissue paper yana fyace majina da dauke kwallar idon sa yana hararen alh iro yana fadin
“Dole kake barin gari mana tunda ka haifi janhurun masifa marar albarka marar tarbiya wacce take da jarumtar kashe namiji mace ta kashe namiji in ba haihuwar allah bani in yasarwa duniya ba yaushe za ayi haka? To amma ka sani dan kuka yajawa uwar sa jifa don na rantse maka da wanda ya aiko ANNABI da gaskiya ba zan iya yafe jinin abdulhameed ba sai yarka ta mutu kaima ka mutu uwar ta ma ta mutu ! sai na tabbatar da babu ahalin yarinyar ka a duniyar nan ko zan iya hakura da rashin abdulhameed a duniya don rayuwar abdulhameed shi daya tafiye min ta mutanen bauci baki daya kima da daraja don haka manufar kama iyalan ka da kai kanka don ku karbi haddin kisan da yarka tay min ne kuma babu mai iya Kare ta daga hakan dukkan mutanen da suke garin nan kuwa.
Shuru ta ratsa office din shugaban jami an bunciken sai fa motsin fyace hancin distinguish mukhtar Biro wanda ya dire zancen shi hawaye yana wanke mishi fuska har abun ma ya zame mishi jiki.
“Ban san wacece wannan wacce tayi aika aikar nan ba wacece? Nadiya? nafi zaton hakan daga gareta amma ta yaya akayi hakan? bana jin fati a wannan karfin halin ko a mafarki naga hakan zan karyata amma nadiya zata aikata amma abin tambayar shine meye silar? meye dalilin?
A fusace distinguish ya juyo tamkar zai kifaww Daddy mari yana fadin
“Tambaya ta ma kake ? Ina zan san kowace ce tsinanniyar yarka la ananniya ? amma ai kai da kanka ka san me iya aikata haka ko? to da wacce zata iya aikatawar da wacce ma ba zata iya aikatawar ba duka dunzo inda ba zasu matsa gaba ba.
“Ayi hakuri ranka ya dade Ina ganin kamar in akayi masalaha zaifi tunda ai aukuwa ta auku .
MCCewar shugaban ami an bunciken
“Inyi hakuri kake cewa? ayi maslaha? don ba danka aka kashe ba? kai in danka ne aka kashe zaka nemi maslaha? ni akwai ma wanda ya raina min hankali irin ka? ayi maslaha? In kyale yar tashi ta kashe banza kenan?.
“Ba haka nake nufi ba ranka ya dade a gafarce ni .
“Yaya kake nufi to in ba haka kake nufi ba? A cuce ni kuma ace hakuri za a bani ? wallahi ko wanda ya san yarinyar nan ba zan bari a doran duniya ba sai naga bayan su ta yadda babu mai tuna su kamar yadda akayi min .
“Ba zance kayi hakuri ba amma nayi mamaki ta yadda akayi hakan .
“Bakayi mamaki ba sai ka shafa a duniya baku ji numfashi a ruhin ku ba sai ka bar mamaki.
Cewar distinguish mukhtar Biro wanda yayi maganar a fussce yana zaro ido tamkar zai hadiye numfashi ya marawa dan sa baya zuwa lahira.
Distinguish ya kwalawa Mustafa Tero kira ya fito daga motar Yana shigowa office din shugaban yana fadin
“Wacece yarinyar da tayi min wannan abun? Kuje a fito min da su duka ka nuna min ita na gani .
Da sauri shugaban jami an ya mike yana kiran wani ma aikaci mai suna hambali
sai kuwa ga hambali ya shigo da sauri yana sarawa oga tare da distinguish mukhtar Biro ya kuma sarawa alh iro GIDAN KUDI .
“Kuje hambali a futo da mutanen nan da aka kawo daga gidan alh iro.
Da sauri kuwa ya fice Tero ya mara mishi baya har zuwa inda aka sakaya su haj Aliya da su fati
aka fito dasu tare da su kaisar zuwa office din shugaban
Distinguish mukhtar Biro ya zubawa mutanen da suke gaban shi ido maza da mata yana son cinko wacce yake kyautata zaton itace ta kashe abdulhameed .
Yayi ta kare musu kallo har idon shi ya dire akan fati wacce ranshi ya tabbatar mishi da itace wacce ta kashe abdulhameed.
Ya mike da sauri tamkar wanda aka tsunkula hannayen shi duka sanye a cikin aljihun shi tamkar mai neman wani abu sai kawai tamkar sihiri aka ga ya fito da karamar bindiga daga cikin aljihun shi yana dora ta akan goshin fati yana fadin
“Bana ko shakka wannan ce tsinanniyar da tayi min hakan don haka itama zatayi ta tata rayuwar wallahi ni zan kashe ku da kaina fansar ruhin abdulhameed.
Da sauri shugaban jami an bunciken ya dora hannu akan hannun distinguish mukhtar Biro wanda yake rike da bindigar yana shirin sakin harsashin bindigar yana shirin matsa kunamar .
“Ayi hakuri ranka ya dade doka bata bada ikon daukar hukunci a hannu ba matukar akwai hukuma . Ina ganin alkaline zai bincike komai ya baww mai hakki hakkin sa amma daukar doka a hannu to hukunci ne ga kowaye a barwa masu hukunci hukunci.
“Har akwai wasu masu bayan mu ne? Ishaq ka manta wani na saka aka sauke na bada sunan ka aka dora ka shine kake fada min doka a Nigeria? .
“Ayi hakuri ranka ya Dade matashiya ce nayi akan doka.
“Uban uban dokar don uban ta a kashe min yaron kuma ace min doka? dokar banza dokar wofi? to ni zan kashe dukkan ahalin yarinyar nan uwar ta da uban ta da dukkan wanda ya jibance ta wallahi.
“Daddy fa ita wannan bace. banga waccan da tayi kisan ba.
Da sauri distinguish mukhtar Biro ya janye bakin bindigar yana duban Tero yana fadin.
“Nuna min ita Mustafa tana Ina? nuna min ita a nan.
Tero ya soma wara idanu yana kalle kowa amma babu Nadiya babu mai kama da ita .
“Babu ita a nan Daddy.
Distinguish mukhtar Biro ya juya ya dubi alh iro yana fadin.
“Ok sai yanzu na fahimta wato ka boye yarka ne saboda gudun haddi ? wato ita ka dauka ka kai waje har kake fada min baka gari baka san anyi ba? to na rantse maka da wanda numfashi na yake a hannun sa ko dab lahira ka kai yarka bata tsira ba ina mai tabbatar maka da kai ma da kayi nufin boye ta ba zaka sha ba bare ita shawara daya zan baka shine ka fiddo min yarka na kashe ta tun kafin rayuka suyi k’ura don yadda kuka zo nan ka san ba zaku matsa ko ina ba sai na kaddamar muku da irin hukuncin da zan yanke muku da wannan abar ya fada yana nuna alh iro da bindigar da take hannun shi
Distinguish mukhtar Biro wanda yake nuna alh iro da bakin bindigar yana fadin.
“Wato yarka ita kadai ce mutum da har ka iya fidda ita waje ka boye don kar ta karbi haddin ta addanci da zaluncin da tayi har kake fada min baka san komai ba? kana zaton yarka zata tserewa ramakon ta addancin da tayiwa abdulhameed? to wallahi sai na kashe yarka kisan zaluncin da ya zarce wanda tayiwa abdulhameed ka bawa kanka magana kafin nan da awa goma sha biyu ka danka min yarka wata kil kai ko sauran ahalin kk ku iya tsira amma boye yarka yana nufin ka nuna min ita kadai ce mutum ni nawa yaron ya zama banza wofi to hakan ka iya salwantar da rayuka masu yawa don Abdulhameed ya wuce kai da ahalin ka har da zunuban ku wallahi.
Daddy ya ture hannun distinguish mukhtar Biro wanda yake nuna shi da bindiga yana fadin
“Kana wuce iyakar da yawa mukhtar. ta yaya muna gaban hukuma kana ta min ikirarin kashe ni da ahali na? kar ka kuma nuna ni ko zuria ta da bakin bindiga don baka kama wanda yayi maka laifi ba sai ka bar hukuma tayi aikin ta kana irin haka kuma s zagi Nigeria da cin hanci da rashawa? to kar ka kuma nuna ni ko iyali na da makami don zan nemi hakki na nima.
Da wani irin tashin hankali distinguish mukhtar Biro yake duban Alhaji Iro.
“Au ! Kai ? har ka kai ne da zaka dubi idona ka karanta min wannan rashin mutuncin? waye kai a garin nan? ni kake fadawa zaka nemi hakkin ka? to waye wanda ya isa ya kwatar maka hakkin? to ina jiran zuwan mai kwatar maka hakkin don uban sa kaga idan ya kuma kwana akan kujerar tasa ko waye shi kuwa.
Daddy ya mike yana duba su mama da fati wanda sukayi wurjanjan hankali a tashe Yana fadin
“Ina Nadiya ne Aliya da ban ganta a nan cikin ku ba?.
“Nadiyar da bata gida ma Al amarin nan ya faru Daddy? kasan kafin ka tafi Senegal nace maka bata nan wai ta tafi Rakiyar kawaye to bata dawo ba ne Al amarin ya faru amma na san yanzu tana gida .
Daddy alh iro ya dubi ishaq shugaban jami an yana fadin
“Officer ga yaro na nan ku hada shi da yaran ku aje s taho da yarinya ta ya duba ya gani idan itace wacce Yake magana akan ta .