Skip to content
Part 25 of 32 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

Cike da wani irin  matsiyacin fushi da son ya kife Tero distinguish Mukhtar Biro ya kifawa Mustafa Tero mari  hagu da dama har yana hankada shi da kafafu tamkar  zai rufe shi da duka, marin nan yayi matukar gigita da  shigar Tero wanda yaja baya yana kallon Mukhtar Biro.

“Ashe mahaukaci ne kai shashasha dabba da kai nonsense fuck you? halan kasha wani Abu kafin kazo nan din?.

Tero ya gyada kanshi Alamar bai sha komai ba.

“Karya kake wallahi sai a yau nayi nadamar shaye shayen ku hala ka sha wine din da kake Mustafa na tabbatar da kasha wani Abu kafin kazo nan. ta yaya zaka fadi wadan nan maganganun a gaban kotu banda kana mahaukaci?  shi kuma Sufin banda ya raina Ni har ya zaunar dani a cikin wadan nan mutanen yana ga zance ga magana? me yasa baka karyata cewar dukkan abinda yarinyar ta fada karya ne ba ? sakarai shashasha dabba marar hankali ni tashi a gabana tun ban buge ka ba .

kuma maza ka je gida ka kira min Sufi kace nace ya same ni gida .

Da sauri Tero ya fice ya bi bayan Alkali Sufi biro wanda sunan uban nasu Abdullahi biro wani mutum dan Boko wanda ya bawa boko amana har yayi nasarar amsa Abdullahi biro man . shiyasa ma kaf ya’yan Abdullahi biro man babu dan kasuwa a cikin su duk ma aikatan gwamnati ne sai fa Mukhtar Wanda ya fada siyasa amma ko shi kafin shigar shi siyasa ma aikaci  ne a hukumar duba gidajen man  fetur wato D P R  wanda ya shigabanci jihar bauci har zuwa lokacin da ya fantsama cikin siyasa inda ya fara da neman kujerar shugaban karamar hukuma ya Kuma samu . da tafiya ta mika ne sai ga Mukhtar Biro a kujerar gwamana jihar bauci na tsawon shakara takwas yana shugabancin jihar bauci inda ya sauka ya kuma neman kujerar sanator ya kuma sake samu har a yanzu akan kujerar senators yake .

Uwar su daya Uban su daya da chief judge Sufi biro. kasancewar uban su dan boko yasa mace daya ya rayu da ita itace sadiya wacce take bafulatanar bauci amma yar asalin giyade itama yar boko ce shiyasa gidan na biro ya taso cike da Ya’ya yan boko

Ya’yan su biyar maza hudu sai mace daya . Mukhtar shine babba sai Sufi wanda sunan mahaifin sadiya ne ake mishi Kara ta lullube sunan shi wanda asalin sunan shi Umar sai abubakar da Usman sai ummulkhairi .  dukkan su ma aikatan gwamnati ne suna ruke da aiki Mai kwari

Kaf din su babu wanda suka taka mataki mai girma sai su uku. Mukhtar da Sufi sai Usman . Mukhtar dai har gwamnan jihar bauci ya Rike yanzu kuma yana sanatan bauci centeral . Sufi Kuma shine chief of judge na k’asa sai Usman Wanda yake rike da gwamnan babban banki yayin da abubakar da ummulkhairi suka zamo tsaka tsaki

Mustafa Tero dan gidan abubakar ne wanda Allah ya hada jinin Mustafa da abdulhameed har ta kai ya tare a gidan uban shi Mukhtar Biro wanda ya kasance abdulhameed shi daya kwai distinguish ya haifa akasin Mustafa da suke da yawa a gidan su . sai hakan ya basu damar lalacewa duk da abdulhameed kam yana da sauki sosai akan Mustafa don shi baya shaye shaye Kai dai barshi da son ya latsa yan mata tun a waje da aka fidda su karatu idanun shi suka bude da mata shiyasa da yaga macen da ta hada abubuwan da yake so to yanzu zai mace shiyasa ya mutu akan Nadiya Kuma duk macen d yayi tarayya da ita baya Jin wahalar bata kyautar mota kudi kuwa tamkar hakkin daji

Tuni Sufi ya kula da Rayuwar yaran ta lalace har yaso yayi wani Abu akai amma Mukhtar yace duka a nawa yaran suke da za a matsa musu ? A barsu da lokacin nutsuwar su yazo zasu nutsu. dole sufi ya bar abun ba don baya cin ranshi ba sai gashi a yau ya tsinci wani abu marar dadi wai kisan Abdulhameed.

Tero ya iso gidan baffa Sufi ya same shi zaune a falo yana rike da takardun shari a yana dubawa ya zube a gaban shi yana gaishe shi ya amsa yana kare mishi kallo tun daga kayan jikin shi da askin kanshi.

“Baffa dama Daddy ne yace na fada maka yana son ganin ka yanzu

“Ok ina zuwa zanyi wanka na shirya sai nazo

Mustafa ya mike ya fice Sufi yabi bayan shi da kallon takaici yana kada kanshi

Motar Sufi ta faka a farfajiyar gidan dan uwan shi ya fito ya shiga ciki yana sallama yayin da distinguish yake goye da  hannayen sa a baya fuska murtuk kamar hadarin gabas ya juyo bai amsa ba sai ma zama da yayi yana shirin kamawa da wuta.

“Barka da yamma brothe.

ya fada yana kallon fuskar sa kasancewar  haka suke kiran juna wato dan uwa.

Da wani irin matsiyacin kallo Mukhtar ya dubi Sufi yana fadin

“Me kake nufin nuna min Sufi? ni kake zaunar wa a cikin mutanen da ke k’asa dani kana sauraren shari ar mu har baka kore ta ba meye amfanin ka wuri na idan har zaka saurari wata banzar magana wai shari dani bayan ni aka cutar? Ok? kana son ka nuna min ni kadai ke da abdulhameed haka ma kisan sa ni kadai ya shafa? kana son nuna min ni da wanda baka sani ba duk daya muke a wurin ka idan ka saka hular shari a? .

” kar ka saka son rai brothe nan fa ba kai aka cuta ba yarinyar can ce aka cuta kuma brother kana mantawa ko nace kana da son kanka da yawa gaskiya. Ok don kana dan uwa na sai naki gaskiya? ka kuwa san hakkin shari a? To ba kai ba ko da iyaye na shari a ta kama zanyi ta wallahi don ganin na tabbatar wa da mai gaskiya gaskiyar sa. nayi Rantsuwa kafin na karbi aikin nan cewa zanyi wa kowa adalci kuma hakkin masu shari a shine ka duba kowane bangare kayi musu sulhu da adalci. ni fa nayi mamaki da ya zamo wai anyi kisan Abdulhameed amma ban sani ba shin brothe bamu da hakkin ka sanar mana rashin? sai fa da akayi hakan na sani kuma ni shari ar da aka kawo min ta barazana ce da kake yiwa mutum da iyalan sa ba wai sunce yasu batyi kisa ba kuma ba a yanke hukunci ba shin brothe baka lura da irin Rashin tarbiyar da yaran nan suke da ita ba? duk yakin da nake don su nutsu su zamo mutanen kirki amma baka bani damar hakan ba shin yanzu inda sun zama na gari kamar yadda nake fata duk da Rayuwa tana hannun Allah yaushe zasu tsaya shashanci har suna biye yan mata? In da sun nutsu har aure yanzu da basuyi ba? wane mai hankali ne kake tunanin zai bawa irin su Mustafa aure?.

“Ok? Sufi in na fahimce ka dai kana kalubanta ta da lalacewar yaran nan ? har da rashin abdulhameed da nayi ban barranta da mugayen kalamai irin wanna ba?. to tashi kaje shari a kuma duk yadda ka yanke zan nuna maka akwai gaban da nafi ka sanin ta wallahi .

“Ka fahimce ni mana brother yaya kake kin gaskiya saboda son ranka?.

“Anki a fahimce ka Sufi tashi ka bar min gida na kuma ni gobe ba zaka ganni kotu ba ina jiran kadin jinin abdulhameed da zaka bi min .

Sufi ya mike ya fice bai kuma sauraren dan uwan nashi ba.

Haj Aliya kam cike take da mamaki akan yadda Nadiya ta dauki rayuwar ta har ana dauke ta da sunan ramakon wulakancin da tayi har ana keta haddin ta

 A ranar da akayi zaman kotun haj Aliya da alh iro sun jima suna tattaunawa inda a karshe dai suka barwa Allah ikon shi domin kuwa sun san Mukhtar Biro ba zai bar jinin danshi a banza wofi ba

Washe gari kuwa aka koma kotu inda Mustafa Tero ya tafi da CCTV camera wacce yake fatan ta zama shaida ta karshe

Lauyan distinguish Mukhtar ne kadai ya zo sai kuma Mustafa Tero wanda ya kawo CCTV

Kaisar da alh iro ne da alh Sule kawai suka zo inda mai shari a chief judge sufi biro ya sake sauraren karar inda aka halarto da CCTV wacce mai shari a ya bada damar a kunna ta aka kuma kunna yayin da Al amura suka soma bayyana tun gabanin faruwar al amarin har zuwa ranar da aka sato Nadiya wacce aka shigo da ita su kilin sun dora  mata wuka a makoshi da irin yadda Abdulhameed yake tab’a kirjin ta har zuwa inda su keso suka cire mata kaya da irin romantic din da Abdulhameed ya soma yi mata har zuwa lokacin da ya dauke ta ya shiga bedroom da ita . Al amarin da bai bada damar ganin ko me ya faru ba amma dai an tabbatar da ganin fitowar Nadiya daga bedroom din jikin ta faca face da jini ta tsince kayan ta kafin ta fice daga gidan a guje.

Daga nan kuma sai bayyanar su Mustafa da kilin har zuwa tabbatar da mutuwar abdulhameed.

Alkali ya dubi lauyan distinguish yana fadin

“Kana da abin cewa?

ya amsa da

“Eh ya mai shari a kar yarinyar nan ta fake da cewa fyade marigayi abdulhameed yayi mata da yardar ta akayi komai tunda bata nemi kwatar kanta ba.

Alkali ya tare shi da fadin

“me ake nufi da fyade barrister? Ina ce fin karfi ko barazana da rayuwa? Baka ga yadda aka shigo da yarinyar nan sun kafa mata wuka a makoshi ba? kuma baka ga yadda suka dauko ta a mota ba ko da son ranta ta shigo?

Lauyan distinguish yayi shuru

Alkali ya dubi lauyan Nadiya yana fadin

“Kana da abin cewa barrister?

ya amsa da cewa

“Ina dashi ya mai shari a a cikin adalcin da kayiwa kowane bangare adalci shine kadai fatana.

Alkali sufi ya dubi takardar dake gaban shi yana fadin

“A sakamakon shaidu da hujjoji da kotu ta saurara ta gane fin karfin da aka sakawa Nadiya yayin kawo ta gidan da akayi mata keta haddin kuma kotu ta saka kwararrun likotoci sun duba Nadiya ibrahim ko an taba verging din ta ko ba a keta shi ba? sun kuma tabbatar da an tab’a shi  don haka kotu ta wanke Nadiya Ibrahim daga zargin kisan Abdulhameed da tayi sai dai zata biya tara akan gangancin kisa babu ganin girman Rayuwar dan adam da zaman watanni biyu a gidan sarka saboda gangancin kisa . sann nan kuma karar alh sule ta barazana da distinguish Mukhtar yake wa alh iro nuni  da bindiga shimy za a biya shi tara saboda barazana da rayuwa kuma shi dan kasa ne ko da ba dan kasa bane kiyaye hakkin juna don zama lafiya wannan  shine karshen wanna shari ar wanda kuma hukunci baiyi wa dadi ba Yana da damar dauka ka k’ara zuwa gaba.

Ya buga gudumar sa a gefen sa kafin ya mike Mahalarta kotun suka hada baki wurin fadin kotuuiu.

Suma suka soma ficewa inda Kaisar yafi kowa farin ciki don ya san zaman wata biyu kamar gobe ne Nadiya tayi ta gama tara ma shi zai biya ta kafin daddy ya biya.

Daddy da alh Sule basuyi wata murna ba illah sassaucin da Nadiya ta samu amma halin Nadiya kam shine yaja mata

Kaisar ne ya Isa gidan sarkar yana fadawa Nadiya yadda shari a ta kaya tayi murna sossi inda Kaisar yayi mata alkawarin biyan tarar ta zai kuma nemo yadda zai biya kudin zaman wata biyun da zatayi don a sauwake mata zaman sarkar

Da haka Kaisar ya juyo bayan ya ajiye mata ledar da yake rike mata duk in zai je ganin ta kaza da fresh milk.

Lauyan distinguish Mukhtar Biro ya isa gidan Mukhtar din da mamakin irin hukuncin da mai shari a Alkali Sufi ya yanke  wacce yake gani a matsayin wulakanta dan uwan shi distinguish Mukhtar.

A yadda sukayi zato shari ar zata zama ja ya fado ja ya dauka wato hannu ya san na gida sai yasha mamaki akan irin hukuncin da ya zartas wanda yake shine tsabar gaskiya sai dai da Yake ba kowa ne ke son  gaskiyar ba tunda su duka dai tashe gudu ne kuma ba wanda zai so ya kunya ta nashi

Ya iso gidan distinguish din ya kuma gabatar mishi da takardar kotu da matsayin hukuncin da mai shari a ya yankee wanda yake cike da zaluncin marigayi abdulhameed ga Nadiya da irin fin karfin da ya nuna mata na kawo ta gidan shi da karfi da kuma irin cin mutuncin da yayi mata ya saka wasu yan iska suka cire mata Riga ya kuma yi Barazana da wuka wurin kawo ta gidan har ya keta mata haddi Wai banda ma baya raye da sai ya biya ta tara ta cin mutuncin guda biyar da yayi mata . 1 laifin sato ta .2 laifin kafa mata wuka. 3 kawo ta gidan shi ba bisa izinin ta ba. 4 sakawa a cire mata kaya naked. 5 da kuma fyaden da yayi mata.

<< Azurfa Da Zinari 25Azurfa Da Zinari 27 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×