Skip to content
Part 29 of 46 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

Kwanaki biyu kenan da zuwan shi wakafi inda Kuma tun ranar da aka kawo shi zuwa yanzu bai wuce sau hudu ko biyar ba da aka tuna dashi wurin bashi abinci.

A yau da ya cika kwanaki biyu yasa aka yankee hukuncin shi saboda babu amfanin ajiyar sa don haka tun da safe aka aika a dauko shi motar da ta dauko shi Kuma ta dauko shi ne daidai da zuwan su daddy da mama da fati inda lauyan da ya ke na distinguish shine ya sanar da su a yau din ne ma za a Rataye Kaisar har ma ya fada musu inda yake a gwarumfa don haka da wani irin matsiyacin tashin hankali haj Aliya da fati suka matsu da son zuwa amma sai suka samu sab’ani da motar don tuni ta dauki Kaisar ta wuce bayan gari inda tsoguwar ma aikatar shari a take inda a can ne ake irin wannan ratayar

Suna isowa gwarumfa aka tabbatar musu da an dauki Kaisar tuni don haka mai sanar dasu din ne ya fada musu inda zasu samu motar in ma sunyi sauri zasu iya riskar Mai laifin da suke son ganin.

Motar da daddy yayi drop ta kwashe su haj da Fati kuka kawai suke yayin da Daddy kuma tashin hankali ne fall dashi har bai iya gane a wane hali yake?

Mai motar suke ganin kamar baya gudu saboda sun matsu su zo hat dai Allah ya kawo su lafiya suka fito amma me? suna zuwa ana lullube fuskar Kaisar da bakin yankin yana tsye a saman dram din igiya sakale a kugiya  ana rufe fuskar shi aka zarga mishi igyar tare da zame dram din igiya ta zarge wuyan shi ya soma shillo a sama igiya rike da wuyan shi.

.Wata irin gigitacciyar K’ara da fati ta saka wacce ta amsa amon sautin ta a filing wurin  kasancewar wurin dajin Allah babu yawaitar mutane ganin an rataye Kaisar yana lilo a saman igiyar kafafun sa kuma suna harbin iska yayin da aka mayar da duka hannayen shi biyu baya aka daure don kar ya nemi kwatar kanshi da hannayen sa.

Haj aliya kam nan ta zube a kasa tana mayar da numfashi tamkar mai ciwon Asma

Idon daddy Alh iro akan Kaisar da yake sakale s saman igiya wacce take rike da kugiya yana wutsil wutsil yana jin hawaye suna sauka a saman fuskar shi yayin da zuciyar sa take fada mishi shi azzalumi ne irin azzaluman nan na karshen duniya mara’s imani  tunda har ya bari aka kashe yaron nan marayan Allah wanda ya tsallake rijiya da baya yayin kuruciya ashe ya gudu ne bai tsira ba sai gashi a taskar zalunci an kashe shi babu  hakkin sa me zai cewa Allah,? me duniya zata kalle shi akan wanda ya bar gaskiya saboda son zuciyar sa? ba shi ba duniya ma ta san Nadiya ce tayi kisa don shi da kanshi ya san Nadiya zata iya yin fiye da kisa amma Kaisar ba zai iya yin kisa ba sai gashi saboda son rai da son zuciya ya bari an fansar da ruhin karimin bawan Allah da azzalumar yarsa wacce yayi nadama fiye da shekarun iyayen sa in aka hade su akan ta da Al amarin ta .

Ya zube Yana kuka mai cin rai da zuciya Yana jin ina ma bai kawo kamar yanzu a duniya ba?

Fati ta mike a guje zata nufi inda igiyar da ta sakale Kaisar take amma sai taji kofar da aka kewaye filin tayi mata waigi me yuwuwar dama saboda irin su fatin akayi kofar wanda suke da burin kawowa ahalin su dauki yayin Ratayar.

Wani irin kuka fati take tana  jijjige kofar da nufin ta balle ta ta shiga amma abin tamkar harara cikin duhu dole ta zube a wurin tana kuka idon ta akan Kaisar da yake shillo a saman igiyar tun yana motsi da kafafu har ya daina hannuwa dama a daure duke s bayan shi don haka babu motsin komai a tare da shi dama sai na kafafu shima da ya dauki lokaci a rataye suma suka daina motsi Alamar dai rai yayi halin sa.

Jikin daddy ya dauki kyarma tamkar mai cutar farfadiya yayin da haj Aliya kuma numfashi ya soma gardamar fita tamkar wacce ta shaki hayaki da cutar Asma fati kuma kuka riris da shiga shock wanda ya haddasa mata firgita da tsoro to amma Al amarin zanen kaddara ne babu mai kautar da hannun agogo

Sun kai kimanin awa uku a wurin sun kasa tafiya inda adanun su suke kyam akan igiyar da take rike da wuyan Kaisar wanda babu kowa a wuri sai motar da ta kawo shi kuma ga alama nan suke shirin ya kwana ta yadda ko bai mutu ba zai mutu tsayin lokacin.

Ganin halin da haj Aliya ke ciki ya sa daddy tafiya don komawa gida amma kuma yana son karbar gawar Kaisar don ya tafi da shi gida ayi mishi sutura

Jikin haj Aliya kam ya rikice har numfashi yana daukewa dole suka yada zango a national hospital a Abuja aka shiga neman lafiyar haj Aliya wacce ta kwana bata san wanda yake kanta ba hankalin daddy da fati s tashe har sai da haj Aliya ta sake kwana kafin ta soma dawowa hayyacin ta Inda Kuma daddy ya samu nutsuwa har ya nemi sallama don su wuce bauci don ci gaba da kula da haj aliya ya Kuma karbi gawar Kaisar su wuce bauci

Ya sanarwa fati da haj Aliya da ke zaune  jiki ba dadi cewa zaije ya karbi gawar Kaisar yayi musu bicking din flying

Sai dai me?

yana zuwa da batun karbar gawar suka sanar dashi ai basa ajiyewa in dai yan uwan sa suna son yiwa gawar sa sutura suke tsayawa su karba in kuma basu tsaya ba suna biznewa kawai babu jiran komai don haka tun  ranar suka dubi hanyar mai zuwa karbar gawar ba zai zo ba shine jiya akayi mishi sutura irin ta musulunci don a hannun shehin malami limamin massalaci juma a shi ya sallaci gawar aka kaishi kabarin shi don kaka har kabarin aka kai shi don ya gani

Daddy yayi kuka a gaban kabarin Kaisar yayi mishi ADDU AR Allah ta ala ya jikan shi da gafara yasa aljanna ta zamo makoma a gareshi yasa can ta fiye mishi nan da haka  ya taho yana dauke kwallar idon sa

Haj aliya kam da ido ta bi shi bayan taji abinda ya gama fada mata

Suka baro asibiti zuwa filin jirgi suka dawo bauci cike da jimami da tashin hankali

Nadiya da ke a gida tana yarfe yan aikin gidan da masifa har da mari da zagi duk sun sha shi

A ranar da akayi ratayar Kaisar washe gari sai ga shi an nuna a tashoshin TV musamman NTA  news don haka akan idon Nadiya akayi komai ko a jikin ta ma wai an tsunkuli kakkausa

Daddy ya sanarwa Alh Sule da yaya halilu duk yadda akayi sukayiwa Kaisar ADDU AR samun rabauta a makwanci da kuma makoma

Kwanaki biyu da dawowar su daddy ya gama yankee hukuncin auren Nadiya wanda Yake jin nesa dashi kawai yake bukata don haka ya yankee bawa alabo auren ta tunda maccid’o ya maido yace iyaye basa so

Ya sanarwa yaya halilu kudirin da yake da shi na hada alabo da Nadiya yaya halilu kuma yace duk yadda yayi daidai ne don haka ba a ko sanarwa Nadiya da alabo ba  aka shiga sabgar biki

Alabo kam a duniya idan akwai macen da ya mutu a son ta to fati ce  ita kuma ga inda zuciyar ta ta kaita wato Kaisar wanda baya ma duniyar

Mahaifiyar alabo kam batayi maraba da auren nan ba  don ba son Nadiya take ba musamman da ta kula yarinyar bata da tarbiya don haka ita kam  batayi na am ba ta kuma nuna bata yarda ba.

“Ni fa ban gamsu da auren nan da kuke shirin kullawa ba halili gaskiya bana son yarinyar nan a canzawa yaron nan da wata macen amma gaskiya bana son wannan .

Yaya halilu ya dube ta a fusace  yana fadin

“me kenan in baki son ta? Iro ba zaiyi iko da yaron nan ba kenan sai kin tsomo min cikin harka? .

“Ai gaskiya na fada fada maka bana son yarinyar nan don kuwa ba zan munafunce ka na munafunci kaina da yaro ba.

“Sai dai ki munafunci kan naki amma aure tunda iro ya tsara shi sai anyi shi don in ba alabon ba babu mai auren yarinyar nan.

“Ni kuma nace wallahi ban yarda ba alabo ba zai auri gallafirin yarinyar nan ba.

Rigima mai dama taballe tsakanin  yaya halilu  da Inna  Hajara wanda yace babu wanda ya  Isa ya shiga tsakanin shi da dan uwan sa ciki daya suka fito kuma a rana daya don haka duk yadda yaga damar yi da dan sa yayi babu wanda zai ce don me? don haka  bata isa ta hana komai ba kuma ko shi alabon yace zai mara mata baya akan hakan  ranshi zai baci wallahi

Ya fice yabar gidan ya bar Inna Hajara da kafa tijara tikila tikila.

alabo ya iso gidan ya samu labarin abinda ke faruwa ta bakin innar sa da take ta masifa tana fadin sai dai ko auren alabo ya kashe nata auren.

Fadan da Inna Hajara ke yi ne yasa har alabo ya samu labarin abinda ke faruwa don innar bata boye mishi komai ba a game da auren da iro ya hada wanda ta kira da na cuta .

tashin hankali matuka gaya ya riski alabo  ya kuma maraww innar sa  baya ce baya son Nadiya

Rigima gagaruma tsakanin yaya halilu da Hajara wacce taja ta kafe akan bata yarda da auren Nadiya ba har ta Kai yaya halilu yace sai  ta bar mishi gidan shi matukar bata yarda da auren Nadiya da alabo ba ta kuma ce ta fi son haka wallahi da dai ace alabo ne mijin yarinyar nan gallafiri gara ta hana auren ita na ta auren ya mace da haka kuma Inna Hajara ta fice daga gidan zuwa gidan su abinda kuma baiyiwa alabo dadi ba har ya Isa bauci ya sanar da baffa iro halin da ake ciki

tare suka taho misau zuwa gidan su Inna Hajara daddy ya bada hakuri ya kuma taho da ita zuwa gidan yaya halilu wanda yace ba zata zauna mishi gida ba tunda har take kokarin raba mishi zumunci amma daddy yace ba zata raba zumunci amma aure kam dole a fasa shi  tunda shi da kanshi ya san yarsa abin gudu ce ba kuma zai ga laifin duk wanda ya guje ta ba .

“In kayi haka iro ai ni ka wulankata ni tunda duniya zata ce mata ta tafi karfi na tunda take zama a kan ra ayin ta ba nawa ba   kuma ka nuna mata ita da alabo sunfi karfina sai yadda suke so za ayi.

“Ba haka bane yaya halilu zaman lafiya yafi zama dan sarki su duka ba so suke ba to ayi hakuri Allah ya kawo mata wani nima da kaina na fara nadamar kasancewar yarinyar nan a tare dani yaya halilu shiyasa bana ganin laifin duk wanda ya k’ita kuma ai na san halin ta in ba nawa na jiki na ba wa zai iya?  don haka don Allah don ANNABI a bar maganar nan ta wuce shekarun sama da talatin kuna zaune da matar ka babu wani Abu da ya tab’a hada ku fada mai tsanani to a yanzun ma ba za ayi hakan ba .

Da jaka alh iro ya kashe wannan wutar ya dawo bauci

Haj Aliya kam jiki yayi sauki sosai ta warware amma kuma tana da matsala a zama tare da Nadiya don da gaske take bata son ta bude idon ta taga Nadiya ba don komai ba kuwa sai butulcin ta ga Kaisar wanda har yau din yarinyar nan bata nuna alhini ko jimami akan abinda ya faru ba. a da can haj Aliya tana yiwa Nadiya uxuri na rashin son talaka amma butulcin ta fa ga wanda yayi mata halacci? Idan akwai want abu da haj Aliya ta tsana a duniya to butulci ne ayi maka alheri ka saka da mugunta shiyasa taji ta tsani yarinyar nan don haka ta fadawa daddy cewa bata son ganin yarinyar nan a gaban ta don haka zata tura ta can wurin kanwar ta da take aure a jama are ko ba komai zata koyi ladabi don halima kam akwai zafi shiyasa ma yaran dukan su suke tsoron yakumbo hali

Shima daddy din ya ji dadin hakan shiyasa yace fati ta kira mishi Nadiya don yau din nan zata bar bauci zuwa jama are.

Haj laila da take asibiti wurin gawar abdulhameed tana faman dauke kwallar idon ta da tissue paper masu binciken gawar abdulhameed din suka same ta inda lauyan na distinguish ya nemi izinin duba gawar tare da  daukar hotuna

Haj laila da bata yarda an saka gawar abdulhameed cikin ma adanin da ake aje gawar ba a cewar ta In aka saka shi cikin akwatin gawar an tozarta shi sai dai a je Mata shi a wuri na musamman don haka sanin ko wacece ita yasa aka karya dokar ta dakin Adana gawarwakin aka killace mata gawar abdulhameed

A kwanaki biyu kacal da rasuwar abdulhameed amma kowa da ke wurin  ya gane Haj Laila saboda yawan zaryar da take wani lokacin ita da mai gidan wato distinguish Mukhtar Biro

Masu binciken suka gama bunciken su da daukar hotuna suka gama sukayi wa haj laila sallama wacce bata ji su ba saboda ta zubawa gawar abdulhameed ido tana kallon jijiyar wuyan shi wacce take ganin kamar tana harbawa .

Ta mike da sauri tana kai hannun ta a saman wuyan nashi ta tab’a sai taji harbawar jijiyar a hankali .

Ta zabura tana dafa gurbin zuciyar sa nan dai bata ji komai ba don haka da sauri ta fito ta nufi inda masu tsaron dakin gawarwakin yake tana kiran .

“Kai kuzo pls don Allah kuzo da sauri.

<< Azurfa Da Zinari 29Azurfa Da Zinari 31 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×