Bata daina kuka ba tana tambayar distinguish bai nemi wani abu sani ba ko akwai yadda za ayi? Ya fads mata komai.
Haka suka wuni cikin jimami har zuwa dare suka wuce hotel din da suka sauka distinguish Mukhtar Biro da mai dakin nashi haj laila suka bar shi da Mustafa wanda yake kwana tare da Abdulhameed duk da tsarin asibitin babu zaman mai jinya akwai masu kula da mai ciwo amma aka bar Mustafa yana kwana tare da Abdulhameed
Abdulhameed ya tashi zaune yana duban Mustafa Tero yana fadin
“Ka hada mana komai Tero? wallahi ba zan kuma kwana shegen garin nan ba tashi da Allah ka kama ni mu fice karfe nawa jirgin zai tashi,?
Tero ya tashi yana saka rigar shi yana fadin
“Sha biyu da rabi ne amma idan su daddy suka zo da safe basu Tarar da mu ba fa ?.
“To ni ina ruwa na da abinda zasuyi ? ba sai da na fada musu ba zan sake kwana a garin nan ba suna ta wani lallaba min lafiya sai kace sun fini son lafiyar tawa?
Mustafa ya kama shi ya sauya mishi kaya daga na asibiti zuwa nashi na gida har suka gama komai Mustafa ya kama shi suka fito inda ma suka so samun matsala kenan don garin da suka ci gaba komai a tsari yake amma da Tero ya nuna musu iskancin Nigeria dole suka barsu suka fice daga asibitin
Karfe daya saura na daren ranar jirgin su ya dauke su daga babban birnin washing ton zuwa gida Nigeria hankalin abdulhameed gaba daya yana kan Nadiya da yadda zata karbe shi shine kawai tashin hankalin shi. Tero ne ma ya shiga bashi labarin Al amarin da ya faru lokacin da Daddy yasa a kwaso kaf ahalin ta da irin yadda aka nemi Nadiya aka rasa da yadda daddy ya matsi iyayen ta har ta bayyana ya kuma saka aka yankee mata hukuncin kisa amma gayen ya karbi haddin ta yace shine yayi kisan ba ita ba aka kuma sake ta aka yi hanging din sa. duka Tero ya kwashe komai ya fada mishi har da shari ar da Baffa Sufi ya Yankee da yadda Daddyn ya saka aka sauke Baffa Sufi daga mukamin sa.
Abdulhameed ya gama sauraren Tero cike da tashin hankali musamman yadda Daddyn ya wulakanta iyayen Nadiya da kuma abinda yayiwa dan uwan sa Baffa Sufi sune abu biyu da suka fi tsaya mishi a ruhi da bata mishi rai.
Yakumbo halima tana cike da tashin hankali da rudani a wannan rana ko sana ar ta batayi ba sai zuwa ake amma bata cikin nutsuwa. shawara kawai take da zuciyar ta akan abinda zai zama mafita tsakanin zubar da cikin Nadiya da kuma mayar da ita bauci .amma dai ta gane maganar makociyar ta gude itace gaskiya ta sanar da iyayen yarinyar nan in ta ce ta kaita a zubar da cikin in ta mutu kuma fa?
washe gari kuwa yakumbo halima ta yo shatar mota ta kuwa loda kayan Nadiya kaf tace zasu wuce bauci
Kaisar yana tsaye a bakin kofar yana kallon furannin ana ta lissafin rayuwa da son ya gane alkiblar da daddy yake son kallo sai kawai yaga motar ta shigo wacce yakumbo halima tace har ciki zasu shiga aka kuwa bude mata kofar get ta shige sai kawai ya hango Nadiya a bayan motar yayin da yakumbo take gaban motar ta kuma fito direban ma y a futo yana fito da kayan Nadiya wacce amai ya saka ta fiyowa a guje.
ya fito daga inda yake yayin da yakumbo take aunaww Nadiya harara tamkar idanun ta zasu zubo.
“Sannun ku da zuwa yakumbo yanzu kuke tafe?
ya fada yana gaishe da yakumbo wacce ta amsa tana fadin
“Wallahi yanzu nake take tafiya babu shiri tafiya ta tashin hankali da Kai mugun albishir? Kai dai jawo min jakunkunan ka shigo min da su ciki in ta gama aman nata na rai da rai sai ta iso ciki.
Kaisar ya soma ja jakunkunan ya wuce ciki amma kuma gaba daya hankalin shi yana ga Nadiya da ys tabbatar da bata da lafiya har yakumbo ta kasa da ita ta maido gida.
Ya kwashe jakunkunan ya kai ciki ya dawo wurin Nadiya wacce take ta kakarin amai tamkar zata wmayar da yan cikin ta don ba karamar wahala take sha ba akan Aman nan.
Ya taho da ruwa ya duka yana mata sannu ta dago tana zuba mishi jajayen idanun ta da wahala ta rinar ya mika mata ruwan ta wanke baki ta karba tana wanke bakin ta ajiye gefe tana mayar da numfashi.
“Baki da lafiya ne sweetie?
ta kada mishi kanta alamar bata da lafiya ya kama ta ya mikar da ita tana fadin
“Muje na kai ki asibiti ni na san wannan yakumbon ba lallai tayi kirki ba tunda naga katuwar tukunyar da ta gurke miki kina mata jifan dan wake yanzu ma ciwo ya kama sai a kasa kai ki asibiti?
Yana rike da ita zuwa mota duk jikin ta ya saki saboda amai
ya shigar da ita mota ya shiga yaja zuwa asibiti inda a take ma aka jona mata drift tare da allurai na karin karfin jiki a cikin drift din
leda uku ta zuk’e na drift tare da magunguna kudi sosai ya kashe suka taho yana tambayar abinda take so a hanya ta Kuma fada mishi pineapple da da lemun bawo orange
ya kuwa siyo mata su tari guda suka taho yana kallon ta da yadda ta koma ta rame sai fari da tayi dauu kamar wacce aka janyewa jini
ya soma tambayar ta abinda yake damun ta tayi wannan farin ko bata da jini ne?
tayi shuru ta rasa amsar da zata bashi shin zata ce mishi ciki ne da ita ? ko kuwa tayi mishi banza kawai ta kyale?
ta dube shi tana fadin
“Ance ciki ne da ni shine yake saka min amai da wannan farin ance ciki ne dani .
Wani irin matsiyacin duka da ya naushi zuciyar shi shine ya kuma saka shi sakin sitiyarin motar wanda Yake dab da kaiwa motar iccen gaban su karo abinda ya yi matukar firgita Nadiya da take hango mutuwa Ido da ido har ta kwarara wata kara mai karfi da amsa amon sautin muryar wanda ya jawo hankalin mutane akan su kafin Kaisar ya samu ya dauke Kan motar ya kaucewa motar da yake shirin kaiwa karo.
Sallamar yakumbo Halima ce tasa haj Aliya juyowa a firgice don bata san da zuwan nata ba . shekaran jiya ma kuma sunyi waya amma bata sanar da ita zata zo ba duk da in dai zata zo to zata fada mata zata zo don ta tab’a zuwa gidan aka sanar da Yakumbo cewa haj Aliya sunyi tafiya abinda ya bawa yakumbon haushi dole ta koma jama are cike da takaici shiyasa duk in zata zo take sanar mata
Haj Aliya ta tarbe tana fadin
“Kai Halima wannan tafiya kuwa ta lafiya ce naga babu sanarwa?
Sai kawai yakumbo ta fashe da kuka tana fadin
“Ina fa lafiya yaya Aliya? wallahi babu lafiya wata shiga uku ce ta doka min kofa tun asubar farko dole na kuma na bude mata kofar amma a me zaku kalle ni yaya aliya? Da ina da yadda zanyi ma wallahi da ban yarda nazo ba sai dai kuji na gudu na tsere na bar garin don banda idon duban ku .
“Subhallahi Halima me nake ji haka kina fada ? me ya faru ne ? Nadiya ta mutu ne?.
“Ba gara ace mutuwar tayi ba da dai wannan mugun albishir din ? mutane nawa ne suka mutu kuma ba a fasa rayuwa ba,? yau ina annabawan Allah ina kuma iyayen mu ?.
“to yi hakuri ki gajarce min wannan dogon sharhin don Allah tun baki sa zuciya ta bugaww ba don tunda na ganki wallahi banji zuwan nan naki na dadi bane nafi zaton wani mugun labarin sai kuma gaki kina rusa kuka to taimaka mini ki sanar Dani.
“Maganar dadi fa ai babu ita yaya Aliya sai dai ba ku ba ni kaina ba zan yafewa kaina ba bare ku ina mai gidan nan yake,? kira min shi in sanar da kin a tare don bana son maimaita maganar nan tunda ba abin arziki bane ba amma kuma in duniya da adalci ai dole nake maimaita ta tunda nice ja gaban ta
Da sauri mama ta mike ta haura saman benen ta ta so Alh iro suka suka sauko tare yana kallon yakumbo Halima yana fadin
“Halima ce a gidan?
yakumbo da take ta share hawaye ta amsa tana shessheka tana fadin nice wallahi.
“Subhallahi halima ya da shesshekar kuka haka kuma?.
cewar haj aliya
yakumbo halima da take a wuya ta k’arasa rushewa da kuka tana fadin
“Kai ni kam a yau nayi kaicona fiye fiye da shekarun uwa ta da na uba na in an hade . yau kam na kunya ta ni halima zigidir nake kallon kaina.
Haj Aliya ta bushe a zaune don ta san wannan al amarin na Halima ba mai dadi bane tunda ta san halima da taurin zuciya ba karamin abu ke saka ta hawaye ba bare kuka sai gata a yau kuka kashirban.
“Kinga halima don Allah daina kukan nan shin kina ganin kukan zaiyi wani magani ne? duk abinda ya faru fa matukar bawa bashi da karfin ikon komai Akan sa to ya barwa Allah shi yafi mishi kuka kuma ai ni sai nace ban tab’a ganin shi a idon ki ba na kuma tabbatar da ba karamar jaruma bace ke d kike takawa damuwar ki burki.
“Da gaskiya kenan ake jarumta Alh amma bani da gaskiya ina jarumta? ni dai don Allah ku yafe mini tun kafin kuji ta adin da nayi muku wanda in kuka ce ba zaku yarda ba to ku kaini hukuma.
“Allah ya sauwake mu kaiki hukuma halima yanzu menene matsalar? Don Allah fada mana ki kuma daina wannan kukan.
yakumbo halima ta share hawayen ta da gefen mayafin ta tana fadin
“Kwanaki biyu da suka wuce yarinyar Nan Nadiya ta kwanta zazzabi nayi ta banka Mata maganin Basur har da dai na miyagu duk na hada mata don kwanaki akwai wata mata da ake zaton maita take nayi mafarki wai ta zo siyen kosai shine nake zaton ko itace ta kama Nadiya nice har da taxargade da lemun tsami duk a banza shine makociya ta mai koko tace muje asibiti wai fa zuwan mu asibiti sai ga mugun labarin wai ciki na wata biyu har da satittika ni halima da wane bakin ko idon zan sanar da ku? yaya Aliya ina aikin me akayi hakan?
Haj Aliya ta dafe kirji tana fadin
“Ciki halima? wane irin cikin wai ?.
“To yaya Aliya sai dai mu kwana tambayar juna amma nima tambayar da har yau na kasa samun amsar ta kenan ace yar nan batayi abin nan a gaban ku ba sai da tazo hannu na? da Ina da yadda zanyi da na gudu ban zo na sanar muku ba.
Alh iro kanshi yaji maganar nan matuka gaya babu abinda yake maimaita wa sai Inna lillahi wa inna ilaihir Raju un
Yakumbo kam sabon kuka ta sake.
Falon yayi tsit baka jin komai sai shesshekar yakumbo halima yayin da kirazan haj Aliya da alh iro suke cike fal da tashin hankali kafin Alh iro yayi karfin halin cews
“Halima bar kukan nan haka Allah ya tsara mu da ke da ita wacce abun ya faru kanta babu mai iya kautar da hakan sai mu roki Allah sauki a cikin dukkan al amarin mu ya bamu ikon cin kowace irin kaddara ai ba laifin ki bane.
Yakumbo dai sai share hawaye take
Haj Aliya ta dube ta tana fadin
“Kin tambaye ta wanda yayi mata cikin ne halima?
yakumbo ta cabe da sauri tana fadin
“Wallahi har da wuka na rutsa yarinyar nan amma tace ba ta san komai ba babu irin barazanar da ban yi mata ba har da kisa amma sai nace bari na kawo ta gaban ku wata kil ta fada muku gaskiya.
“Kafin haj Aliya tace komai sai ga Nadiya ta shigo Kaisar yana biye a bayan ta rike da ledar magunguna da kuma pineapple da lemun bawo da ya jido mata .
ta dire a gaban daddy da mama tana gaishe su Daddy ya dube ta yana fadin
“Matso nan Nadiya na tambaye ki.
ta matsa cikin azama tana kallon shi.
“Halima ta fada min baki lafiya kunje asibiti ance ciki ne da ke Nadiya kinyi min adalci kenan kinyiwa Aliya da ta tsaya tsayin daka tabaki tarbiya? sakamakon da zakiyi mana kenan? duk yadda take kaffa kaffa da ke sai da kika nunawa duniya bata iya komai ba? kuma yanzu ita halima da take rike da ke kinyi mata adalci kenan?.
Hawaye ya soma wanke fuskar Nadiya tana fadin
“Daddy wallahi ban san komai ba akan cikin nan ni tun da naje gidan yakumbo wallahi ban tab’a kula wani namiji ba sai wannan garbeben kuma shi babu abunda mukayi da shi amma sai akace ciki ne daddy wallahi daddy banyi zunubin da zai bani wannan sakamakon ba.
“Karya kikeyi kin dai boye ne kawai amma me yasa tuni bakiyi cikin ba sai da kika je hannun yar uwa ta don ki bata mata suna? anya kuwa kina son na yafe miki Nadiya? To in dai ciki ne da ke kin watse kin lalace zan barki da Allah.
Kaisar yayi maza yace
“mama kar kuyi mata baki ba laifin ta bane laifin kaddara ne ku yarda da ita don Allah ku fahimce ta mana .
“Kai Kaisar kar kayiwa zancen nan kwaskwarima wannan wanna yarinyar komai ma zata aikata kai kuma da yake idon ka a rufe yake komai kana mata uxuri amma kai bata yi maka kara a komai wacce irin zuciya ce da kai wai? In ba laifin ta bane laifin waye?
cewar mama wacce tayi maganar a fussce.
“Kaiser kayi nisa da yawa cikin lamarin soyayyar yarinyar nan har yanzu ma da take kunshe da wannan cikin na shege baka saduda ba?
cewar Daddy.
“Daddy kuyiwa Nadiya adalci mana ? ni na yards bata san komai ba sai dai ta manta ko kuma bata kawo hakan a ranta ba amma daddy kun manta da keta haddin da dan gidan Mukhtar Biro yayi Mata ? kun manta da kotu ta saka an duba ta likita kuma ya tabbatar da an tab’a ta ? shin wannan bai isa ya bata sakamakon ciki ba?.
“Inna lillahi wa inna ilaihir Raju un
falon ya dauka su duka suka hada baki wurin fadar kalmar don sai yanzu suka tuna da hakan.
Nadiya ta juyo tana duban Kaisar da ya tuna mata wannan matashiyar wacce ta tabbatar da tun da ga ranar da akayi hakan kuma bata kuma ganin bak’on watan ta ba
“Wannan magana haka take babu ko ja wallahi .
Cewar yakumbo halima wacce taji karfin gwiwar ba a hannun ta Nadiya ta lalace ba kamar yadda take zato .
Haj aliya ta sauke hannun ta daga kirjin ta tana Kara maimaita kalmar Inna lillahi wa inna ilaihir Raju un yau ga wani abu.
“Hakikatan Kaisar maganar ka gaskiya ce nima na yarda da hakan kuma babu ko tantama wannan cikin na dan gidan Mukhtar ne to amma menene abunyi?.
“Abunyi ya wuce a je a zubar? ba fa ta hanyar aure aka same shi ba.
cewar yakumbo.
Haj Aliya ma tace a zubar amma Kaisar yayi maza yace.