Skip to content
Part 4 of 23 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

Fati ta soma fito da kuloli da womers tare da kayan sanyi wanda haj Aliya ta shiryaww kaisar yayin da haj Aliya ke mita akan halin Nadiya

“Na rasa kalar yarinyar nan a rayuwa ta wallahi. menene wani together in ba iskanci da son watsewa ba? Kuma har ta iya fita bata sanat min ba don kar na hana ta? Allah ya maido ta gidan nan wallahi ba zan dauki wannan dabbancin ba Allah ya sani ba zan bar yarinyar nan ta lalace ba .

“Kiyi hakuri mama halin Nadiya sai ita wallahi sam bata ganewa wadan nan kawayen nata sunfi karfin ta domin kuwa sunfi ta wayewa wallahi in batayi sannu ba zasu halakar da ita ne .

“Ai ki barta Fati dani takeyi in da tana kallon rayuwar ki ke madubi ce a gareta amma da yake tayi nisa bata Jin Kira kuma babu damar a fada .

suka kwaso kayan abincin suka nufo falon fati ta soma direwa zata fara zubawa daddy yace .

“A a Fatima karasa ladar ki kai mishi dakin da nace ki gyara ai nan ba zai sake yaci komai ba amma acan kinga har wanka zaiyi ya huta sosai.

ta mike tana fadin

“To daddy bari na Kai mishi.

Ta wuce kofofin har zuwa sashin da daga shi sai farfajiyar gidan take inda ke da dakin da aka kawata da kayan daki dangin gado da kayan amfani wanda tun a satin da ya gabata su fati suka ga daddy ya soma gyaran part din duk da bai sanar da su komai ba ashe bako kaisar aka gyarawa shi.

sai da fati ta kwaso komai ta kawo dakin wanda yake ciki da falo biyu kafin wani babban falon wanda aka narkawa dukiya ta hanyar kujeru da tv manya plasma da kuma labulaye da fridge da dispenser kafet da kayan amfani

daddy ya dubi kaisar yana fadin

“Tashi kaje ka huta kaci abinci sai ka kwanta kasha hanya kaisar Allah ya huta gajiya akwai komai na bukata a dakin idan kuma kana bukatar wani abu ka shigo nan ga haj Aliya nan ka dauke ta tamkar mahaifiyar ka kaisar don ita din a dan cikin ta take kallon ka.

yayi kasa da kanshi yana murmushi ya amsa da cewa

“To daddy nagode sosai Allah ya kara girma mama bari naje na huta kayana suna mota .

Daddy alh iro ya dubi Fati yana fadin

“Fatima kira sarkin gida ya kwasowa yayan ku kayan shi a mota kuje ki raka shi dakin sai kiyiwa sarkin gida magana ya kwaso kayan daga motar  

Kaisar ya mike king kuma yayiwa su daddy sallama suka biyo bayan Fati wacce take Jin wani abu yana tab’a zuciyar ta akan wannan bak’o nasu da bata san ko waye ba abinda kuma ba zata ce gashi ba . amma dai koma meye tana Jin shi a zuciyar ta.

ta nuna mishi dakin tana turawa fuskar ta a sake shima yayi murmushi yana fadin

“Nagode kanwa ta fatima bari na dauko kayan a mota tunda basu da yaww.

“Bari na dauko maka kaifa bak’on mu ne.

ta fada tana murmushi suka nufi fita farfajiyar gidan inda king kuma ya shige dakin yana kallon yadda aka shirya shi tamkar wata daula sai ya yi tsaye yana kallon dakin

Kaisar ya bude motar yana jawo jakun kunan shi guda uku ya fito da su daga motar fati tana taya shi har ya gama fito da su ya dauki biyu fati ta dauko mishi daya har bakin kofar dakin nashi ta ajiye mishi Yana ta mata godiya ta wuce tana mishi subahul khair ya amsa da subahul noor sis Fati.

ya shiga da kayan inda ya iske king yana ta kwasar girki sai tausa naman kaza yake a baki don namomi ne kala kala ga abinci  nan shima kala kala

Kaisar ya ajiye jakun kunan shi kafin yazo yana cin abincin king yana ta xuba santy . ya dubi agogon hannun shi sha daya saura ya mike da sauri yana fadin

“Mutumi na dare yayi ban farga ba bari na wuce sai munyi waya.

“Ba zaka tsaya nan ka kwana ba king? Ni kadai ne fa adakin.

“Uuhum kasan nene bata son ina yin nisa da gida yanzu ne zaka ji ta danna min kira ni ban sani ba ko nene tsoro take kar na lalace oho?.

sukayi dariya Yana fitowa ya raka shi mota sukayi sallama da king ya tafi yana shirin juyawa ya koma ciki   sai ganin shigowa motar yayi wacce yabi da ido har ta shige katafaren gidan na iro GIDAN KUDI ya bi ta a baya inda yaga wacce ta fito a motar tana waya tana kuma warware dogon hijabin tana zurmawa cike da azama da zafin nama.

wata irin matsiyaciyar faduwar gaba yaji saboda ganin Nadiya ta nufi kofar shiga gidan tana ta sauri.

yayi tsaye yana dafe da gurbin zuciyar shi yana tunanin yarinyar nan a gidan Nan take? dama yar GIDAN KUDI ce ? dama gadarar ta gidan su da uban ta?.

sai yayi murmushi yana fadin

“Allah ya takaita min dogon nema ashe ma gidan da nazo nan take Allah kasa na cimma muradin zuciyar nan tawa Allah ka sani ina son yarinyar nan kamar raina idan har da alheri Allah ka mallaka min ita idan kuma babu ka fidda min sonta a zuciya ta.

ya nufi kofar dakin shi yana wara idanu da son ya hango Nadiya amma bai ganta ba don haka ya wuce dakin shi yana shiga wanka don a gajiye yake kwanciya kawai yake son yi.

da sand’a Nadiya ta shiga falon cikin sa a kuma babu kowa sai ta nufi dakin nasu ita da Fati a zaton ta zata iske Fati tabar gidan sai ta ganta akan gadon ta kwance tana bacci.

taja tsaki tana fadin

“shegiya mayya duk korar da nayi mata kaskar taki matsawa Allah ya kaimu gobe duk maitar ki sai kin bar gidan nan tunda ba na Uban ki bane matsiyata da ku masu naci .

ta kwanta tana waya da saurayin ta mai suna show wani mawakin hipop nee wanda yake tsaka da tashe a garin bauci. Ita kuma Allah yayi mata kaunar wakokin hipop har ta samu nomber show Wanda ba ma musulmi bane cristin ne yaren igbo amma a haka Nadiya take son show wanda yake tashen samun kudi kuma yake hawa manyan motoci duk da ba ga wakar kawai ya dogara ba akwai yan hikimomin  da akeyi yayin samun kudin ta bayan fage ko ace sakin layi.

Vedio call suke da show wanda suke ganin juna suna musayar kalamai har da na banza da maganganun wofi har da nuna sashin jiki duk da sunan wayewa ko soyayya.

Sun jima suna wayar da show kafin  tayi bacci.

Asubar farko Fati ta farka ta tashi salla duk da bata San lokacin da Nadiya ta dawo ba amma ta San ba zata tashi sallar asuba ba don ko ta tayar da ita to zata rufe ta da masifa ne gara ta barta sai ta tashi don kanta . Don haka bata tashe  ta ba tayi sallar ta ta koma bacci don sai takwas suke tashi in Daddy yana gari ta taya mama kayan karin kummallo idan kuma baya gari sai su Ade suyi masu aiki kenan.

Bakwai saura Nadiya ta farka inda taga Fati Alamar ta tashi salla har ta koma.

sai kawai ta soma shurin ta da kafar ta da sunan tada ita take.

Fati taji ana shurin ta ta bude idon ta taga Nadiya akan ta .

“Tashi mayya baki ga na hada miki kayan ki gasu can ba? Zto tashi maza wallahi ki tafi kauyen ku in dai nan din babu gadon uban ki shegu matsiyata wanda babu ta karewa komai naku Daddy ne amma har kizo gidan mu kina min munafunci? To wallahi sai kin koma misau a yau ko kuma na karya kafar ki wallahi don nan din gidan uba na ne ba na uban ki ba kowa ya tsaya a gidan uban shi kiji da munafuncin ki da kika gado a nonon uwar ki.

Fati tayi murmushi tana fadin

“nagodewa Allah duk da talaucin mu da kike magana dole dai a nuna Daddy ace shima misau ne asalin shi kuma uba na duk tsiyarshi dai dan uwan Daddy ne kuma ai ba mu roki ayi mana abinda kike mana gori ba shi Daddy ne yaga damar yi mana nagodewa Allah da ina da gidan uba nima da bani da shi a yau da sai bak’in ciki ya kashe Ni in sha Allah yau zan bar muku gidan ku Nadiya na gaji da gorin ki wallahi in sha Allah muma zamuyi arziki ba matsiyata bane mu tunda muna son manzon Allah kuma muna salla in sha Allah mun gama babban arziki.

Fati ta kare  fadin haka tana fidda kwalla.

“Chaiii a dai tafi a koma misau in da gaske ku ba matsiyata bane don Allah baban ki ya zama kamar daddy koma fin daddy matsiyata kawai.

Fati ta jawo akwatun ta tana share hawaye ta fice ko kaya bata sauya ba inda tayi nufin wucewa ko mama ba zatayiwa sallama ba don kar ta hana ta tafiyar sai dai tana fitowa sukayi kicibus da mama wacce ta fito don ta taso fatin su shiga kitchen sai gata ta gani fuska duk ruwan hawaye.

“Subhallahi Fati me ya faru kike kuka?

Fati ta share hawaye tana fadin

“ba komai mama zan dai tafi misau ne.

“to da akayi min wannan uban safkon? ke dai fada min gaskiya in ba kin soma karya ba amma ai bamuyi da ke zaki je misau ayau ba?.

“Mama dole tasa zan koma can din Nadiya tace mana matsiyata ne mu nan ba gidan Uba na bane idan babu gadon Ubana na bar musu gidan su tunda na yi mata munafunci ni kuma Mama Allah ya sani na gaji da gorin da take min ko kasa su baffa suke ci gara na koma can na zauna.

hawaye ya kawowa mama tayi wani murmushin takaici tana fadin

“Ina zuwa

ta juya da sauri sai gata da bulaliya tana fadin

“Ja akwatin muje dakin naji nawa ta cikawa mai gidan nan ya gina gidan shi kuma nawa ne nata a cikin kudin shi da har take miki gori? .

“Kiyi hakuri mama don Allah kar kice na zauna wallahi zuciya ta kuma ta koma misau.

“In kika sake kikayi min gardama wallahi tsaf zan buge ki da bulalar nan don nima zuciya ta a wuya take muje kar ki karasa fusata ni .

dole Fati taja akwatin ta suka juya dakin.

Nadiya na ganin Fati ta soma fadin

“To marar zuciya dawowa kikayi?.

“Ni na maido ta yar karuna masu kudin duk duniya jiya gidan Uban wa kikaje baki dawo ba har sha daya? Mama ta fada tana zuba mata bulaliyar dake hannun ta.

Ai kuwa ta fasa wata uwar Kara ta fito a guje tana dhirin ficewa daidai da shigowar kaisar wanda ya zo gaishe da daddy da mama sai kawai yaga nadiya ta fito a guje tana kuka ta kuma fada mishi amma abin mamaki ya cabe ta akan karon da suka gwabza wanda kowa zaiyi zaton zata kai shi k’asa wmma ya rike ta a jikin shi ita kuma mamakin ta ta yadda gayen nan ya shigo cikin gidan su ne yake dab da kashe ta  ta yaya akayi ya san nan ? kuma me ya shigo da shi?.

<< Azurfa Da Zinari 3Azurfa Da Zinari 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×