"Ai Aliya sunyi kuskure da suka bari na gane abinda suke so wallahi har abada kuwa zan tabbatar musu yau gareka ne gobe ga dan uwan ka. ke kinji irin cika bakin da yasha yi? babu irin wulakancin da mutumin nan bai min ba har yana nuna mu ni da bakin bindiga wai zai kashe mu ya kuma kashe banza. yanzu in da duniya da adalci ayi hakan? baki lura ba ma sai da dan nasu ya nakasa ne suka tabbatar da ba zai hauhu ba shine suka kwaso Kaya suka nufo ni? ba takamar sa sanin wasu a. . .