Skip to content
Part 54 of 58 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

Su keena suka karaso gidan Kan su tsaye suka wuce sashin haj Aliya yayin da luba ke duban sashin Kaisar tana ganin gyaran da akayi mishi ya burge ta har tana fadin

“Kai masha Allah wurin nan yayi kyau maza mutanen mu yanzu fa kina iya jin mai gidan nan ne zaiyi wuff da wata yar shawalwala.

“Ba zan musa maganar ki ba luba don maza kam sai dai nata suyi hakuri amma sun shiga gaban mu da tazara mai yawa sai kiga mutum girma ya kama shi amma ya dauko sa ar yarsa ta karshe yayi ciki da ita  da anyi magna sai ace ai ba haram bane amma kuma ai ana barin halal don kunya.

Basu Kare wannan fira ba suka shiga sashin haj Aliya dole suka rufe faifan.

Haj Aliya ta dube su tana tuna abinda fati ta fada mata akan kawayen Nadiya wanda sharholiyar su suke a makaranta wacce suka baro gaban iyayen su gari ya gari inda kuma ta gane lalacewar Nadiya ma ba zai rasa nasaba da su ba tunda kallo daya zakayi musu ka gano tsabar rashin kirkin da yake tattare da su .

Suka zube a gaban ta suna gaishe ta tana amsa su tana tambayar su karatu suka bata amsa da lafiya lau alhamdulillahi.

“Haj dama munga kwana biyu Nadiya shiru ga wayar ta ma bata samuwa shine muka zo don muji ko lafiya .

“Lafiya lau take tayi aure ne shiyasa kukaji ta shuru amma tana lafiya.

“Aure haj?

su duka suka hada baki wurin fada ita kuma haj Aliya ta tabbatar musu da hakan.

“Allah sarki to Allan ya sa alheri amma haj aure haka tamkar tashia duniya?

cewar keena da ta gama shiga tashin hankali musamman da ta tuna da shaid’an dake can Plato yana dakon ta kawo mishi Nadiya sai gashi tana jin Wai tayi aure ta Ina zata nemo kudin biyan shaid’an?.

“Haj a wane gari take ? ko zamu iya samun lambar ta?

duka keena ta jerawa haj Aliya tambayar yayin da su luba da safina ma suka cika da mamakin auren Nadiya mai kamar wahayi.

“to tana nan garin amma ban san wace unguwa take ba don ban san inda mijin ya samu gida ba kuma bata da waya gaskiya ko kun neme ta ba zaku same ta ba amma ku aje lambar ku in mijin nata yazo Zan bashi sai ya hada ku in sha Allah ai zumuncin makaranta har karshen numfashi ne in aka dace da mai zumuncin.

“To haj ko zamu iya Samun lambar shi mijis nata ?.

cewar keena.

“Eh akwai lambar shi amma wayar tawa ne ba caji amma kar ku daku ku ajiye taku in sha Allah zan bashi nace ta kira ku kawayen ta ne na makaranta

Keena ta rubuta lambar wayar ta ta bawa haj Aliya jiki a sanyaye ta mika mata sukayi mata sallama suna wa Nadiya fatan alheri a zaman auren ta

Haj Aliya ta amsa tana gode musu sukayi sallama

“Kai lamarin nan yana da mamaki luba na tsorata da auren nan na dare daya bana ko shakka Wanda yayi mata cikin ne aka raruma aka daura auren rufin wallahi in kuka bincika maganar kenan.

“Nifa kudin da na karba hannun shaid’an sune damuwa ta in ya neme ni a yanzu nace mishi me? Keena ta fada kamar zata fashe da kuka.

“Linke shi zakiyi har zuwa lokacin da zamu gano inda take ai tunda dai tana cikin garin Nan to in Sha Allah zamu gano ta.

Suka fito keena tana duban sashin Kaisar tana fadin

“Ni kam sai nayi ganin kwam a gidan can don in har mai gidan ne yayi wuff da wata hakika bai kyauta ba ace da kuruciyar ka ba ayi maka kishiya ba sai da girma ya kama ka?

suka nufi sashin wanda yake kulle cike da son ganin kwam din keena ta soma doka kofar.

Kaisar yana rike da Al Hassan wanda ya gama shan madara yana daga shi sama yana sambatar gefen fuskar yaron yaji ana doko kofar da take kulle.

Ya mike yana rungume da yaron a kafadar sa  ya nufi bodewa yayin da Nadiya ke can tana  faman kukan bak’in cikin da Kaisar ya guma mata.

Ya bude  kofar da son ganin waye? sai kawai yayi arba da kawayen Nadiya abinda ya saka shi saurin daure fuska yana kare musu kallo cike da gabata da izza suma cike da mamaki suke kallon shi suna kuma kallo jaririn da yake kan kafadar sa.

“Lafiya?

ya tambaye su cike da ginshira. don har ga Allah matan nan basuyi mishi ba kallon wasu gantalallu yake musu.

Luba ce tayi saurin fadin

“Don Allah zamu shiga bandaki ne  a taimaka mana muna bukatar zagaywa.

“Kuje a kwai na masu gadi yana nan dab da kofa ku shiga .

ya fada yana mayar da kofar ya rufe gararam har yana shirin make goshin luba wacce tayi saurin ja baya ya rufe kofar.

Suka juyo keena na dafe safina tana fadin

“Ni kadai naga wani abu ko kuma kun gani?

jariri fa a kafadar gayen nan? shine da wannan gidan ? anya kuwa in aka hada biyar da uku ba zasu bada takwas ba?.

“Nima abinda nace kenan keena anya ba gayen nan bane yayiwa Nadiya ciki ba shine aka hada auren rufin asiri? ga dai jariri mun gani kuma dama tuni muka san yana son ta to Allah ne kadai yasan uwar kwad’o .

“Lallai fa akwai kamshin munafunci a cikin al amarin nima na zan so ganin wace a cikin gidan nan Kuma ni banji na gamsu da amsar mamar su Nadiya ba yarki tayi aure kice baki san unguwar da take ba? akwai ayar tambaya a cikin lamarin nan ke keena ai shikenan kuma asiri ya rufu wai an jama uwar amarya da Ango wallahi ko na rantse ba zanyi kaffara ba wancan gaye ko dai shi yayi mata ciki akayi auren rufin asiri ko kuma an bashi gida da mota ya karbe ta ita da danta .

Keena da taji kamar ta suma saboda bak’in cikin auren Nadiya ga Kaisar don bata damu da yawa ba akan yadda zasu kare da shaid’an irin yadda zata kaya tsakanin ta da soyayyar Kaisar da ta dora tubalin gini a zuciyar ta .

“Amma kuwa garin nan ana shege wallahi waye zai haska mana al amarin nan da yake kwance cikin duhu?.

cewar safina.

Lubs kuma tace

“Ai munyi mai wuyar tunda har muka gane hakan ziyara kawai zamuyi ta kawowa gidan can har muyi sa ar shiga muga wace wainar ake toyawa?

Da haka safina taja motar suka fice tana Jin kamar zata rassu saboda jin sabon al amarin da ya kuma wanzuwa a gareta wanda ya kuma tsunduma ta a tashin hankalin kishi da Nadiya? Ita kam ba ta tsara zata raba Kaisar da kowa ba bare Nadiya da ta tabbatar da ta fita fita kuwa  irin ta wankan sukari.

Nadiya ta gama kukan ta tana saka irin rashin kirkin da zata tatawa Kaisar a zaman nan wanda shi da kanshi zai nemi rabuwa da ita.

tayi wanka ta sauya rigar night gown ta kwanta amma ta ji kirjin ta ya ishe ta saboda cikar da yayi in har bata manta ba tun rana rabon da ta bawa yaran maman su don haka ya cika ya ishe ta  da ta kwanta ma sai taji yana tsiyaya don kanshi alamar ya cika kuma matukar tana son kwanciya tayi bacci to dole ta bawa yaran hakkin su .

tana kwance taki tashi don tana ganin faduwa ce taje tace ya bata yaran

Tana nan kwance taga ya shigo da kwalin gadon jarirai guda biyu ya aje su Ramadan din yana hada musu gadon wanda yake hade da net ya shirya musu komai ya dauko su ya saka su kowane da nasa kafin ya sakar musu net ya wuce toilet yayi wanka don a yau kam zaiyi Angoncin.

Yana shiga toilet din dakin yayi wanka ya fito yana fadin

“Fito sweetie muyi sallah.

Bata tanks shi ba ta mike tana dauko su Ramadan tana fadin

“Ka fita daga harkar yarana ba ka da gami da su kar ka kuma tab’a su In kuma ka sake tab’a su zan wulakanta ka da duk kalar wulakancin da yayi min tunda baka da zuciya.

ta dauki Ya’yan ta koma kan gadon tana basu nonon amma abin mamaki suka k’i karbar maman suka barta da kayan ta duk wanda ta dungurawa sai su waske tamkar dai ace suna fahimta ko sun san dalilin da ya sa take son danna musu nonon shiyasa suka hade mata kai suka ki karba.

“In fita harkar ki kika ce ke da Ya’yan ki? amma kuwa ke butulu ce shi Wanda ya kuga miki cikin tunda ya san gallafiri ya samu kin kuma ganin shi da sunan yazo duba ki?  me yasa ne ina kokarin rufa miki asiri kina son kwashe min kafafu? me zaki cewa ya’yan nan idan suka ga sauran yara da baban su in kin datse mana alaka kice musu me? basu da uba ko kuws su shegu ne,,? to ki  rike wannan ko don gaba dan iskan da ya kuga niki cikin su ma bai isa ya tsunke igiyar zumuncin da ta soma kulluwa a tsakanin mu ba bare ke gallafiri Rijiya gaba dubu don kin samu ana binki shine kike wani daukar kai da hanci bayan baki da wani wbu da zakiyi daukar kan wani can banza a banza ya farke ya kwashe a me kike ne ?.

Yaja tsaki ya tayar da sallar sa ya Barta da sakakken Baki don Bata tab’a zaton gayen nan Yana magana haka ba bare kuma wulakancin da ya ke mata tsakanin dazu zuwa yanzu yana shirin sakar mata hawan jini da kalaman shi masu barazana gareta.

Ya gama sallar ya dauko gorar madarar zico tare da tuffa da kayan fruit ya na ci har ya gama yayin da itama ta gaji da turawa yaran no-no suna waskewa dole ta mayar da su cikin net din su  ta dawo tana kallon shi yana zuba madara a glass cup ya haye gadon ta yana jiran ta .

“tashi ka fuce min daga nan Kar ka kuma shigo min nan kuma ka rike a ranka ko nafi gallafiri Rijiya gaba dubu lalacewa wallahi nafi karfin ka har abada sai dai kazo a matsayin dan aiki na wallahi ba dai mijin aure ba sai dai ka amsa kalmar kawai amma jumlar ta sai dai wasu su amsa ba Kai ba.

Maimakon ya tashi kamar yadda tace sai kawai ya soma cire jallabiyar dake jikin shi yana fadin

“Ai banyi wannan lalacewar ba ta matata ta bani umurnin tozarci da ace gari lafiya ne zan zame miki bawa dan aikin ma duka zan zama amma dai wulakanci irin wannan ba zan yarda ba aure na zan tabbatar miki da aure ne cikakke ba jeka nayi ka ba.

“to zanga ta inda zaka tabbatar da hakan kuma kayi gaggwar sauka daga kan gadon nan matukar dai babu gadon tsaffin ka a ciki.

“Babu gadon su amma ai kin san kinyi karya na biya sadaki na kuma na kasa hawa gado baki karbi dubu dari bane ? to baki gane banbancin ni da wancan dan iskan ba Wanda bai biya ki ko sisi ba ? ni Kam har da fatiha da salatin ANNABI sa shaidu da  kuma siga .

taja filo tana sauka daga kan gadon tana fadin

“Ka kwanta a gado in don dubu darin da ka bayar ce sai dai iyakar ka kenan akan gdon .

ta nufi falo ta kwanta akan kujera tree seater

Ya jima kwance akan gadon kafin ya tashi Yana ADDU A yana tofawa su Ramadan ya nufi falon

tana kwance bacci ta soma fizgar ta taji mutum yayi mata rumfa da sauri ta bude idon ta ta sauke su akan Kaisar wanda yake  tsotse mata maman da yake zubar mata .

Da wata irin azama tayi nufin watsar da shi daga kirjin ta amma tamkar wacce aka daure ta kasa hakan . A zahiri zuciyar ta cike take da takaicin abinda yake mata amma kuma jin ta take kam ta kasa motsi  har Kaisar ya tabbatar da ita a matsayin matar shi ta kuma ji a jikin ta don ta gane abinda bata gane ba a harkar.

taji jiki matuka gaya a hannun wanda takewa kallon raini wanda bata samu wata dama a gareshi ba sai da yayi muradi don kanshi ya kyale ta ya barta da tsamin jiki kafin kuma ta samu sararin yin wani motsi na kwatar kayi

Bai kwana a dakin ba ya fice ya barta da bak’in cikin halin da ya barta dole ta koma dakin nata tanajin ya tabo abinda yafi karfin sa wallahi.

Ranar litinin din da tayi daidai da sha biyu ga watan biyar daddy Alh iro tare da Alh sule suka dauki hanyar garin Abuja don amsa kira Alkalin da ya aiko da sammaci wa Alh iro wanda bai boyewa Alh sule komai ba na zuwan Mukhtar Biro da abunda ya faru har kawo yau din da suka iso birnin tarayya Abuja

Wani arashi sai ga karar da distinguish Mukhtar Biro ya nemi a shigar  alkalin da ya cewa zai biya kudi don tabbatar da karya a gurbin gaskiya shi kuma sai yake ganin ta sama kawai za a biyo don turbuda hancin Alh iro Wanda distinguish Mukhtar biro ya sanarwa komai na game da Ya’yan abdulhameed wanda yake so a karbo mishi ko ta karfin tsiya ne haka ma yana son kotu ta tursasa alh iro bawa abdulhameed auren Nadiya ko ta wane hali dai a tabbatar da ya’yan abdulhameed ga distinguish Mukhtar biro haka ma auren ta a tabbatar da karya gurbin da ba nata ba don haka tuni akayi  zaman hakan aka gama kulla kowane irin makirci  aka kuma saki kudin na tashin hankali  magana ta fada yazamo rana kawai ake jira gashi kuma ta zo

Alkalin da ya tabbata a matsayin wanda zaiyi shari ar shine abinda ya fara kada hantar cikin distinguish Mukhtar Biro wanda yake mamaki da shakka akan anya wanda ya zauna da shi suka tsara komai bai yaudare shi ba? wa yake gani a matsayin Alkalin da zaiyi shari ar ? Sufi ? ya fadi sunan a k’asan ranshi yana kallon fitowar Sufin rike da tarin takardu wasu na biye a bayan shi suna take mishi baya har ya shiga mazaunin sa ya zauna fuskar sa cike da haiba da annuri ga tabon sallah a goshin sa kallo daya zakayi mishi ka tabbatar da yaci sunan sa na Sufi har ma fiye da hakan.

Gaban distinguish Mukhtar biro ya girde ya fado cike da fargaba da tashin hankali yake kallon dan uwan nashi mai shari a Sufi biro wanda tun da ya shigo kotun idon shi ya hasko mishi dan uwan nashi Mukhtar Biro wanda ya tabbatar da shine ya kawo karar da akasi ya kawo ta gareshi ba tare da sanin wurin shi aka nemi Alfarmar yin manuba ba tare da an gane Sufin bashi da hadama akan duniya da kyalkyalen ta ba. abinda ba su gane  ba shi din baya bukatar al amarin da babu gaskiya a cikin shi kuma matsayin da daukakar da yake ganin ya samu shi da kanshi ya yarda har da kamanta gaskiya da adalci yayin da wanda suka riki son zuciya da manuba a harkar shari a tuni ya gansu sun fado Al amarin basu kuma babu k’arko . dai ake zaton girman matsayi da ikon da yake a hannun sa zai sa ya zamo mai karbar na goro don juya magana ta koma zance. wanda sukayi case din ya biyo ta hannun sa babban Alkali ne shine Mukhtar ya biyo ta hannun sa ya kuma danno mishi kudi don tauye gaskiya aka kuma tallatawa mai shari a Sufi biro wanda yace su rike kudin tukuna sai yaga yadda zai hudowa shari ar don yana jin karatun da aka karanto mishi ya gano daga inda zancen ya fito wato dan uwan shi Mukhtar Biro.

<< Azurfa Da Zinari 53Azurfa Da Zinari 55 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×