Distinguish Mukhtar Biro ya tsurawa dan uwan shi Sufi Ido yana ganin yadda yake Rubutu akan takardu kafin friskito ya aranto karar sk distinguish Mukhtar Biro wanda yake karar Alh iro
Alkalin ya nemi ganin Alh iro ya kuma fito ya tsaya yayin da kwararren lauyan da aka dauka ana garin Abuja ya mike ya gabatar da kanshi kafin aka nemi ganin distinguish Mukhtar Biro wanda ya fito shima ya tsaya.
Mai shari a Sufi ya dubi Alh iro yana fadin
“Alh Mukhtar yana karar ka akan ka hana su Ya’yan dansu ko akwai dalili?
Alhaji Iro yayi murmushi yana fadin
“Allah ya gafarta malam ni ban san Ya’yan da Yake magana akai ba amma tunda gashi sai yayi bayani wata kil nine ban fahimci manufar tasa ba
Alkali ya dubi distinguish Mukhtar biro yana fadin
“Alh Mukhtar kayiwa kotu bayanin dalilin da yasa kake karar Alh iro.
Distinguish Mukhtar biro ya gyara rigar shi cike da izza da jin sune da madafun iko ya soma magana.
“Allah ya gafarta malam jikoki na ne suke gidan sa shine nayi magana nace a dawo min dasu amma bawan Allah nan wulakanci kala kala Babu kalar wanda baiyi mini ba ya min sharrin SATA yayi min na handama da baba kere yayi min zagin wulakancin har da gwamnati da kotuna yace babu alkalin da ya Isa karba min Ya’yan D’ana shine nake so kotu ta karbo min jikoki na.
Mai shari a Sufi biro ya yi rubutu a takarda yana duban alh iro yana fadin
“Alh iro ko akwai dalilin hana shi jikokin sa da kayi? In akwai kotu tana son jin su duk da karfin iko da aka san uba yana da shi akan Ya’yan sa fiye da uwa mace.
Alh iro ya dubi mai shari a yana adin
“Allah ya taimaki mai shari a ni ban san wata alaka tsakani na da mutumin nan ba haka kuma auratayya bata tab’a hada ya’yan mu ba to ta Yaya akayi har ya sami jikoki a gida na? ko kuwa dama ana samun jikoki haka siddan ba tare da auratayya ba? In kuma yana da shaidar da ta yarda dan shi ya auri diya ta to ya kawo ta.
Mai shari a ya dubi distinguish yana fadin
“Alh Mukhtar kaji abinda wanda kake kara ya fada .
“Karya yake mai shari a ya san komai ya boye ne saboda manuba.
“to allah taimaki mai shari a tunda yace na san komai ni kuma ban san dan shi ya auri diya ta ba bare har yayi mata cikin da zai daki kirji yace jikokin shi a hannu na sai muyi rantsuwa da Al kur ani mai tsarki ya rantse dan shi ya auri diya ta ni kuma in rantse da bai aure ta ba in kuma Yana da shaidar hakan ko wanda ya halacci daurin auren nasu ya kawo shi don naji ko nine nayi batan lissafi.
“Al amarin rantsuwa yana da girma kwarai sai abu yayi tsanani ne ya kuma zo a kulle ake Rantsuwa da Al kur ani don shi littafin Allan ne ba kuma abin wasa bane amma kuma idan ya zama dole sai ta hanyar Rantsuwar ne dole ayi hakan kai Alh Mukhtar ka dubi Allah ka fadi yadda akayi kaima Alh iro ku dubi girman Allah kar ku bawa shari a wuya ku fadi gaskiyar abinda ya kawo ku nan nan din wurin da za ayiwa kowanen ku adalci ne a tabbatar wa da mai gaskiya gaskiyar sa kai Alh Mukhtar ta yaya diyan yarsa suka zama jikokin ka?
Distinguish Mukhtar ya dubi alkalin da ya bawa cin hanci yana jin haushin yadda bai iya saita komai ba ya barshi da zubar magana gashi kuma dole ya tona abinda baya son tonaww wanda yaso ayiwa zancen kwaskwarima da boye shi kar ya fito ta yadda duniya ma zata kalli jikokin sa da wani aibu.
“Allah ya gafarta malam abinda yasa nace karya yake ya san dana bai auri yarsa ba sun hadu ne a kuruciyar su yana bata kudi da yi mata hidima yana wahalta mata ita kuma tana bashi kanta har ciki ya samu kuma a hakan ma yana mata hidima ita da cikin har ta haihu shine yace yana son ya’yan tun kafin a haife su don sunyi zata zubar amma yace zai biya ta kudin rainon cikin da haihuwar duk ta yarda sukayi a Rubuce ya biya ta kudin ta ga ma takardar da sukayi hakan kowanen su yana da copy akwai kuma shaidu da akayi hakan a kan idon su . ranar da ta haihu ma sai ta samu Yan tagwaye shine tace ai kudin daya ya biya ta ba na biyu ba in har yana son duka Ya’yan sai ya sake biyan kudin dayan ya kuma yarda ya biya ta amma sai mutumin nan yace bai san zancen ba ba za a bayar da Ya’ya ba tunda ba auren ta yayi ba haduwar titi ce to haka kuma zai zama rabuwar titi don haka na kawo shi kara ya bani jikoki na tunda har takardar kotu akwai da saka hannun su da na kotu don haka ni jikokina kawai nake so yh bani in ya so ya bawa D’ana auren yarsa tunda yace shi zai cika alkawarin da sukayi na zai aure ta in kuma uban ta ya hana auren wanna ba zanji komai ba amma ina rokon kotu ta karba min Ya’yan nan.
Mai shari a Sufi biro ya dubi Alh iro yana fadin
“to Alh iro kaji bayanin da mai kara yayi tunda har al amarin ya kasance da yarjejeniya sukayi Ina ganin babu bukatar jayayya tunda ma har da shaidu da kuma kotu to kotu tana rokon ka da kayi gaggawar bashi Ya’yan nan matukar dai hakan ne abinda ya fada baka da hurumin hana shi yaran.
“Allah ya gafarta malam kace mu dubi Allah mu fadi gaskiya to naso distinguish Mukhtar ya dubi girman Ubangiji ya Kuma fadi gaskiya kamar yadda aka roke mu wallahi da ya fadi gaskiyar das ka roke mu da nayiwa gaskiyar sa kara da halacci in kuma tabbatar da na bashi ya’yan nan ko don gaskiya da ya fada babu k’age babu sharri babu manuba in kuma kalli ya san gaskiya amma sai ya waske har da yiwa maganar gyaran fuska Yana aske ta yadda yake so to ni zan fadi gaskiyar da aka roke mu . Allah ya gafarta malam hakika dan sa ya hadu da diya ta duk da ba kamar yadda ya fada ba basa tare shi dai dan nasa ne yake son yar tawa amma kasan halin dan yau . ba zanja zance da tssyi ba mai shari a kai kayi mana shari a a garin bauci akan karar da alh Mukhtar ya shigar. akan yarta wa wacce yace ta kashe mishi dan shi . to sunyi abun su ne na yarinta shi kuma dan sa yasa ka aka dauko mishi diyar tawa wacce aka nunawa wuka da fin karfi har aka kaita gidan da aka keta mata haddi. anyi sheri a wacce ta nuna dan sa ne bashi da gaskiya don ita yarinyar ta burma mishi wuka ne lokacin da yake keta haddin ta inda shi kuma alh Mukhtar yace lallai yadda dan shi ya mutu sai yarinyar ma ta mutu inda a bauci aka yanke hukuncin dan sa ne bai kyauta ba amma ya daukaka k’ara zuww nan Abuja har ya tabbatar da anyi mishi yadda yake so to abubuwa sun biyo baya har wani yaro ya amsa laifin da ba nashi ba har yar tawa tayi free shima daga baya aka gane dan sa bai mutu ba suma ce yayi. to al amarin Ubangiji ashe haduwar nan ta kaddara ta basu rabo rabo kuma na mamaki har aka haifi yan biyu to shine suke son lallai wadan can ya’yan na dansu sai an basu ni kuma nace ban san zancen ba . akwai record na kotu na shari ar da mukayi nan Abuja da ta bauci idan aka duba za a iske wadan nan bayanin don haka ins so kotu ta fadawa Alh Mukhtar aure ne yake bawa uba ya’yan sa saboda darajar sadaki da albarkar aure amma matukar bai biya sadaki ya auri diya ta ba to ya’ya ko sun kai cikar duniya to ba nashi bane na tane ita daya in bai san shari a ba ni na sani .
Lauyan da aka dauka ne ya nemi izinin magana Alkali ya bashi ya soma fadin ai akwai shaidun da akay hakan na maganar yarjejeniya da alkawarin aure da kuma kudin da yaro yayi mata hidima da wanda ya biya ta na ladar rainon cikin da haihuwar har wanda ya kara mata saboda samun yan biyu
Alkalin ya nemi ganin su sai ga shaidun bogi an tanada suka fadi abinda aka shirya musu na su din shaida ne aka kuma gabatar da takardun kotun da na bogi amma kalma daya ce ta wargaxa dukkan shirin na su distinguish Mukhtar Biro.
“to kotu ta saurari bayanan mai kara da wanda ake kara kuma ta fahimci komai amma haduwar saurayi da budurwa babu wani sharadi ko yarjejeniyar da zasu kulla a tsakanin su matukar akwai iyayen su ko alwalin su . wannan sharadi ko yarjejeniya ya zama aikin banza matukar ba na aure bane ko shi din ma iyayan su ne da wannan aikin ba su ba. Kuma maganar kudin da ya bata ta rainan mishi ciki ta nan kadai zamu gane mun baro shari a in da ya aure ta ba zai biya ta kudin rainon ciki ba . Kuma sadaki shike tabbatar wa uba namiji dan sa ko yarsa amma dan gaba da fatiha na mace ne amma in ta so ko shi yaso suna iya badawa kamar shi da yace yana so amma zahirin mai shi mace ce ke da abinta sai in ta bayar don haka dukkan wata yarjejeniya ko sharadi sikin banza ne tunda can suka hadu suka watse . kuma idan muka koma akan Shari ar da na san anyi a bauci wacce ni na gabatar da ita haka abin yake babu gamin dan Alh Mukhtar da Ya’yan yar Alh iro sai in sun so ne su bayar haka ma auren ta in sun so suna iya shi in basu so ba kuma su hana. don haka idan har yarinyar da aka ketawa haddi bata nemi hakkin hakan ba ina ga shi wanda yayi aika aikar ba zai ce yana son Ya’yan nan ba tunda ba uban su bane in har yace uban su ne da wane sadakin ya auri uwar su? wane waliyyin ne nasa ya karbo mishi auren ta ? don haka Alh Mukhtar bashi da hurumi akan Ya’yan nan in aka koma kan shari ar farko da akayi ta kashe rai to za a biya diyyar ran da aka kashe saboda ga dan sa ya bayyana bayan an kashe want yanzu idan Nadiya ce aka kashe sai uban ta yayi hakuri kenan?.
Da sauri alh iro ya amsa da fadin
“Allah ya gafarta malam Ina neman hakkin wanda aka kashe wurin mai girma distinguish Mukhtar ya biya iyayen yaron nan haddin rayuwar sa in yaso ko massalaci a gina mishi ya samu tagomsshin rayuwar sa da ya rasa.
Mai shari a Sufi biro yayi rubutu a takarda yana fadin
“Alh Mukhtar kaji abinda wanda kake kara ya nema yana neman hakkin haddi don haka zaku biya haddin rayuwa yana nan a rubuce a takardar nan haka kuma dole ku fidda idon ku daga kan ya’yan yarsa in sun so su baku in kuma basu so ba to ku kalle su irin kallon da kukewa TV ga takardar nan zaku iya biyan kudin ta account din kotu kotu kuma ta biya su
daga haka kotu ta tashi aka doka gudumar alkali ya mike ya fice daga ciki ya wuce camba.