Skip to content
Part 60 of 64 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

A ranar kan keena ta kwana a rikice don shaid’an ya kwana yana kiran wayar ta abinda kuma ya tsorata ta har garin ya waye yana auna mata kira abunda ya sa  ta barin hostel din makaranta kenan ta kama gida a katagum road wayar ta kuma ta kashe ta gaba daya tana tunanin ta inda zata hudowa al amarin.

Bikin fati ba da nisa daddy ya saka shi ba don haka hidima ake tayi sosai tsakanin misau da bauci inda daddy ya ginawa alabo gida a bauci don tuni akayi mishi transfer aiki daga misau zuwa bauci don haka aka shiga hidimar biki yaya Hajara kam sai shiga da fita take yayin da alabo kuma mama ce ta zama uwar sa daddy kuma uban sa fati kuma Baffa da innar ta Hajara sune suke ta hidima akan ta

Babu wanda ya sako Nadiya a cikin sabgar duk da itama tana can tana yaya za ayi da wannan kallagaggen cikin wanda ya nace yaki fita? babu abunda bata Sha ba don ya fice Amma shiru magani dai wanda ta sha yafi a kirga har da su fetur dai da akace yana fidda ciki da omo duk ta sha amma shiru don haka ta yankee shawarar zuwa asibiti a markade dan banza ta huta

Haka kuwa ta shirya ta fice zuwa asibiti aka kafa mata karafan injin amma abin mamakin sai aka yanko wani sashi na cikin jikin ta ba a tabo inda baby Yake ba sai ga ciwo ta siyo da kudin ta wanda yasa ta zaman jinya smma fa ciki Yana nan zaman shi dafa an sai ma motsi da ya ishe ta da shi alamar dai yana nan lafiya.

Kaisar kam bai kuma tayar da hankalin sa ba don ya fahimci wahalar da kanta kawai take amma babu wata nasara da ta samu  sai ya kyale ta ya shigo harkokin sa da yan biyu hatta dakin ta da yake shiga yanzu ya daina zuwa

Shaid’an ya daina samun keena a waya abinda ya tabbatar mishi da ta so ta yaudare shi amma zata gane ba irin sa ake yaudara ba zai nuna mata shaid’an ci irin wanda bata san shi ba a duniya

Fati ta damu da ta saka angon da daddy ya zaba mata ido don tunda aka fara hidimar bikin babu wanda yazo yace mata ga mai kiran ta s waje ko ga angon yazo su tsara wani sbu na game da auren su amma shiru kake ji tun tana damuwa har ta daina ta zubawa sarautar Allah Ido. A ranar da show ya Kira keens Yana tambayar ta Nadiya don ya kira wayar ta bai same ta ba shine ya kira keena wacce tace ta kwana biyu bata je gidan Nadiya ba amma da ya matsa yana son ganin Nadiya sai tace zata zo ta kai shi gidan don tana so tayiwa Nadiya silar mutuwar auren don haka ta Isa studion show suka nufi gidan Nadiya keena na fatan zuwan show din ya kawo karshen auren Nadiya ko itama ta san ta hanyar da zata kamo bakin nata zaren na samu ta shigo gidan da sunan matar Kaisar din.

Har cikin gidan Alh iro motar show ta shigo dauke da keena wacce take fatan karen ta ya kai tsaiko.

Show ya soma karewa gidan na su Nadiya kallo Yana kallon yadda aka narka dukiya abinda yazo a Ranshi shima dole ya nemi hanyar da zai yagi kason sa kafin ya cimma burin shi akan ta .

Keena tayi mishi jagora har sashin Nadiya wacce take ta faman kakarin amai don sai shegen laulayi take mai zafi yayin da ta hakura da son zubar da cikin don ta kasa yin nasara ko da yake ba hakura tayi ba dukkan wani abu da aka ce mata yana zubar da ciki babu wanda bata gwada ba amma duk a banza kamar ma karawa cikin lafiya take.

taga shigowar keena da show ta mike  da sauri tana wanke bakin ta tana fadin

“My dear kaine nake gani? Ta fada tana fadawa jikin shi suka rungume juna show yana kai bakin shi a bakin Nadiya yana kissing din ta  suna ta tambad’ar su kafin suka zauna keena na kallon ta tana fadin

“Me nake shirin gani Nadiya? Amai ana zaune lafiya? kinyi kama da mai ciki yasin ya ake shirin kwana a Ragaya?.

“Ki bari keena nima abinda nake bulayi kenan in Kika fidda kamar ma amsar zata zama Eh ce.

“Kuma ke bakiyi wani motsi ba ne? ko kuwa tara yaran ya soma burge ki ne?.

“Babu kalar maganin da ban sha ba keena don cikin nan ya zube amma yadda kika san yayo gadon naci irin na uban sa wallahi ko gezau.

“Baki nemi wanda zaiyi miki hakan bane amma in dai kinyi niyar zubarwa ni da kaina zan kawo miki maganin da kina shan sa ko cikin wata tara ne sai kin fiddo shi waje bare wani karamin alhaki.

Karaf wannan maganar ta shiga kunnen Kaisar da yake turo kofar idon shi ya sauka akan show wanda yake sanye da wando tree quarter da rigar sheet wacce ta kama mishi jiki sai gashin Kan shi wanda yayi kamar wani awilo kallo daya zakayi mishi ka fahimci ahalul kitabi ne don har da katon cross din sa sakale a wuyan sa .

wani matsiyacin fushi ya sauka akan fuskar Kaisar ya dubi keena da Jin kalaman da take furtawa.

“Wa ya  baki damar shigo min nan har da guxurin wani kartakin Arne? kece jakadiyar kashe ruhin bawan Allah n da baizo duniya ba har kina fadar zaki kawo mata maganin hakan?.

Keena tasha jinin jikin ta domin kuwa bata zaci zatayi sara da mutum sama  ba .

Ya fita da sauri cike da fushi yayin da show ya dubi Nadiya yana fadin

“Waye wannan da yake kira na arne kai tsaye? Ya san meye arne da yake ce min arne? da addini na yace min Arne?wanda bashi da addini shine pegan.

“Tashi muje show tun gayen nan bai ballo mana ogas ba don waccan fitar akwai ayar tambayar ai kuma ni na saki baki da yawa har zan jawowa kaina janhurun masifa.

Keena ta mike Nadiya na Fadin

“Ke keena kuje ina? Wallahi babu inda zakuje in kuma tafiya zakiyi to dear ba yanzu zai tafi ba in naso ma sai gobe zai bar gidan nan.

“Ni kam wallahi ba zan tsaya ba kinga tafiya ta show mu hade a waje kawai.

Sai dai me ? keena na fitowa tayi arba da Kaisar a bakin kofar ya ce kar s bar ta ta fita har sai jami an da ya kira sun karaso.

Keena ta kara tsurewa kafin ta san abunyi sai ga motar jami an ta karaso inda ya nuna keena aka watsa ta mota kafin yace akwai kartakin Arnen da ta shigo mishi da shi har cikin gidan shi a matsayin kwarton da ta zama kawaliyar hada fasadi har cikin gidan aure

Ai kuwa aka shako show shima aka watsa su mota aka wuce da su ana tuhumar keena da kawalicin matar aure wato Nadiya shi kuma show da zuwa kwartanci duk da shi kam bai san Nadiya tayi aure ba don haka aka tsare show da keena.

Ciwon abdulhameed ya zama barazana ga rayuwar sa don babu wani ci gaba da ake samu . babu irin tashin hankalin da Haj laila bata shiga ba bare kuma distinguish Mukhtar biro dole aka dauke Abdulhameed daga asibitin bauci zuwa America

tafiyar da akayi  hankali a tashe domin kuwa abdulhameed ya koma gidan jiya don marabar shi da gawa kad’an ne hawa da saukar numfashi

Haj laila kam sai kuka take tana fadin idan abdulhameed ya rasa rayuwar sa ba kowa ne ya kashe shi ba sai alh iro kina wallahi danta ya mutu to za a dasa shari a har datissara.

Haka Abdulhameed ya Isa asibitin America aka shiga yaya za ayi? kwanaki ashirin da daya sati uku kenan distinguish Mukhtar Biro ya juyo gida saboda harkokin sa inda ya baro haj laila da mustafa Tero.

kudi kam ana kashe su don nemo lafiyar Abdulhameed Amma dai sauki sai wurin Ubangiji domin kuwa zuciyar kauna tayi nisa har na neman bacewa a wani daji mai yawan duhuwa.

Abdurrahaman Sufi da shafik wato Tsagera suna suka iso america don duba Abdulhameed inda sumayya kanwar abdurrahaman din da ke karatun low a chicago abdurrahaman ya sanar mata sun shigo america duba Abdulhameed. ta rude matuka don idan akwai wata jarraba da Ubangiji yayiwa zuciyar ta to kaunar abdulhameed need duk da shi bai tab’a sanin hakan ba abinda kawai ya sani sumayya she is sweet sister wacce suke mugun tare amma  a k’asan zuciyar sumayya she in love with brothe abdulhameed.

Don haka a can asibitin suka hade da su brothe abdurrahaman da shafi

Sumayya ta damu da ganin halin da Abdulhameed yake ciki don haka tun daga ranar da ta sani din kusan kullum sai tazo asibitin ita da Haj laila ne suke tsaye akan shi yayin da shafik da mustafa kuwa suke jan abdurrahaman shiga yawon zaga gari duk da ba so yake ba don shi kan dan Islamic ne amma su Tero kam an waye ne

Wayar distinguish Mukhtar Biro kullum tana hanyar zuwa kiran wayar laila don yaji yaya abdulhameed yake? anan ya ke samun labarin zuwan abdurrahaman da shafik.

Ai kuwa Distinguish ya shiga zubar da ruwan tijara wai don me dan gidan Sufi zai shiga Al Amarin sa da dan sa? bayan ya tsunke duk wata igiyar zumuncin da su da uban su? don haka ya bawa haj laila umurnin ta fidda mishi harkar sa da ahalin Sufi ta Kuma fadawa abdurrahaman din cewa ya tattara ya koma gida tun Bai iske shi nan ba.

Ita kam Haj laila ba zata iya yiwa ahalin Sufi rashin kirkin da yake so ayi musu ba ko ba komai su basu da laifi uban su ne mai laifi ko ita nan ta kullaci Sufi amma banda Ya’yan shi da a yanzu ma sumayya ce kan gaba wurin kama mata hidimar abdulhameed.

Kwanan su abdurrahaman biyar kamar sun san zuwan basu baiwa daddyn nasu dadi ba suka jiyo shi da shafik suka baro sumayya da mustafa da Haj laila.

Fati ta dauki abincin Yaya Alabo ta nufi dakin shi kai mishi ta iske shi yana lissafin abubuwan da ya kamata a bawa yan mata na hidimar biki amma bai san ta yaya zaiyi hakan ba. .

ta aje mishi abincin Yana fadin

“Wai ni kuwa kanwa ta kamar fa baki da lafiya nake ganin ki ko akwai damuwa ne?

tayi murmushi tana fadin

“Babu komai yaya kawai dai Ina kewar rabuwa da kune .

“Kar ki damu in don wannan in kika so ganin mu zan kwaso miki Baffa da Inna muzo ki ganmu.

Wata hikima  ta fado mishi yace

“Kai Kinga gara da Allah ya kawo ki jiya naje bauci sai Daddy ya bani kudi gasu yace wai Angon ki ya bayar yace a kawo miki ko zakuyi hidimar ku ta Yan mata ungo kin gansu.

Ya mika mata tarin kudin tana karba tana fadin

“Don Allah yaya Alabo ko ka san wanda daddy ya tsayar min a matsayin miji? hankali na ya kasa kwanciya saboda ban san waye ba,?.

Alabo ya dube ta cike da fargaba don yana ganin kamar zata gane shine mijin nata amma sai ya maze yana fadin

“Nima sai da nayiwa daddy tsegumin bamu san Angon ba shine yace wai in suffanta mijin ki da irin suffa ta koman mu ma iri daya ne shine nake ta tunanin to waye wannan da koman mu yake iri daya? nayi iyakar tunani na amma ban gane ba shine nace ko wancan yaron ne mai chemist? sai kuma na gane ai bamu ma kama da shi sai dai ko can cikin dangin mu na azare.

Fati tayi shiru tana tunani kafin tace

“Ni in ma dai irin halayen ka gareshi yaya Alabo ai da sauki tunda na san Kai din mai juriya ne akan Al amari na Allah ya sa ma koma waye ya zamo kamar kai a hali da kama din.

Kamar yace mats ko ni ne ? sai dai ya amsa ta da fadin ameen Yana fadin

“Ni yanzu me kike so nayi miki a matsayi na na Yayan ki?.

“Babu komai yaya Alabo sai ADDU A kawai kayiwa aure na fatan alheri na kuma sami farin ciki da biyayyar miji na har karshen numfashi ni da shi kuma Allan ya kade mana fitina da kowane irin kalubalen zaman auren mu don nayi nufin nunawa su Daddy ni din yar halal ce koma waye suka bani zan Karbe shi nayi mishi biyayyar da Ubangiji ya dora min.

“to Allah ya sa hakan amma duk da hakan dole nayi miki wani abu ina kuma miki fatan aminci mai yawa a gidan auren ki tare da mijin ki na kuma ji dadi da kika zamo yar halal din da kema sai Allah ya baki Ya’ya yan halal nima kuma dama nasihar da zan miki itace ki yi hakuri da duk irin hukuncin da su daddy zasu ysnke Miki in sha Allah alheri nee cikin hakan naji dadi sosai da Allah ya saka miki tunani mai kyau Allah ta ala ya baki miji na gari ya kuma azurta ki da Ya’ya masu albarka.

ta amsa da ameen ameen ta karbi kudin da ya bata yace ta siyi wani abu wanda in ta kalle shi zata tuna da shi

Satin biki ya kama mama ta iso misau aka shiga hidimar biki yayin da daddy ya narkawa Uban sa lefe na garari aka turo shi Misau lefen da ya sha talla kowa fadin lefen nan yake mutane kuwa sai cewa suke Allah yasa wanna miji da ya boye bai fito ba ya zamo alheri wata ta Karbe da fadin.

“Ai ya ma gama zama alheri ko akan lefen nan allah ya kawar da shaid’an a ciki.

Kaisar yana daga cikin abokan ango don suna jone da Alabo koman su iri daya inda Kaisar ne yayi ta shiga da fita a madadin Ango Alabo har zuwa ranar juma ar da aka daura auren fati da alabo ana ta hidima fati da kawayen ta in suna son ganin ango to aisar ne wakilin sa shiya wakilci komai duk abinda suke bukata ma shi zai basu har zuwa yamma da motocin daukar Amarya suka soma jerin gwano inda shamsu da bakari abokan alabo suka kawo motocin su suka soma kwasar yan matan amarya da duk matan da zasu bi rakiyar Amarya har cikin garin bauci gidan da daddy ya tamfatsawa alabo aka sadar da smarya gidan da ya zamo gagara gasa.

<< Azurfa Da Zinari 59Azurfa Da Zinari 61 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×