Ta juya ta bar shi nan cike da tashin hankali musamman akan yadda take cika baki akan cikin da ya kallafa ranshi akai.
tsamin da yake tashi a falon ne ya ishe shi ya Isa Yana kwashe fasasshiyar kwalbar ya na kwara ruwa yabi da hypo ya wanke kafin yaji tsamin ruwan bagajar ya soma bin iska.
Yana cikin aikin yaga ta fito da jakarta tana fadin
“Idan kana son cikin ka Kana iya biyo ni don in an cire s baka tsiyar ka amma ni ba ma zan Kuma kwana da shi ba wallahi na gaji har na gajiya.
Ta fice da sauri yayin da yaji shi kam yana son cikin sa ko babu komai bai mallaki wani abu bayan shi ba don haka da sauri ya suri key din mota ya bi bayan ta sai dai Yana zuwa bakin kofar sukayi taho mu gama da dattijon Yana dogara sandar sa.
“Kar ki bi ta barta zataje ne ta dawo babu abinda zata iya face wanda Allah ya rubuto kar ka samu damuwa babu abinda zai samu ciki da ikon Ubangijin musulunci kyale ta sai dai ina tsoron wani abu don yarinyar nan bata da I’mani komai zata iya amma kayi ta fadawa Allah komai zai wuce .
“To baba nagode a taya mu da ADDU A.
“Kar ka damu kai din yaro ne mai albarka yarinyar nan bata san ka bane da ta san ka da ba zatayi maka abunda take maka ba amma tayiwa kanta.
Ya juya yana tafiya har ya wuce Kaisar da ya koma ya zauna yana rufe fuskar sa da tafukan hannun sa .
Nadiya da ta isa asibiti tana ta fadi abinda take so ayi mata wato a fidda mata cikin nan ko ta theater ne .
Aka kafa mata computer don ganin watannin cikin da irin ikin da za ayi mata na theater ko kuma jona mata ruwan nakuda. .
Sai dai me? duk iya bincike na computer bata iya ganin cikin ba bare watanni haka akayi ta bincike bincike amma ciki kam yayi batan dabo .
“Yaya ga ciki a gaba na kuma ana maganar babu ciki? A bar wani dogon bincike kawai a fasa za a ganshi ni da har motsi nake ji ?
“Babu fa ciki a tare da ke sai dai ko wani ciwon amma nan babu ciki a nan
Duk yadda taso ayi theater hakan bai samu ba don ance akwai yuwuwar ayi mata aikin a samu matsala tunda ya boye .da aka tambaye ta watannin cikin tace shida sai suka bata baki akan kawai tayi hakuri ta cike watannin sa in ma akwai shi zai fito in kuma ba shi bane ta nemi magani .
Ta rasa ta yadda zata bullowa al amarin nan amma sai ta gane dole ta wurin show zata komawa ya sake samo mata wine din ta in yaso Tasha ta a can ba sai tazo gida ba.
Bata tsaya ba ta kuma ficewa zuwa studion show wanda ta fadawa fashewar kwalbar wine dinta bata kai ga sha ba don haka tare da ita ma suka tafi mashayar ta ya siya mata ta kuma yi tatul da ruwan bagajar suka taho tun kafin ta soma marisa ya aje ta ta shigo gida ta kwanta bacci wanda yake ta dibar ta tana layi .
Sai dai shiru kake ji wai mai kalangu ya fada ruwa har ta kwana ta wuni babu wani labari sai ma ciwon kai ma tsanani da ya addabe ta amma zancen ciki kam yana nan daram
Ranar da fati ta Isa misau tare da yan biyu taga tarba wurin innar ta wacce ta karbe ta tana ina ta ka saka da ita da yaran da take kallon Ya’yan Nadiya
Baffa ma da ya iso ya same ta yayi ta murna da zuwan ta yana fadin
“Uwa ta amaryar uba na nayi ta kewar ki har zan iso bauci ashe kina tafe
tana rungume da Baffa tana fadin
“Kuma Baffa sai baka zo ba? .
“Ina zan zo binta ai ba a zuwa gidan amare sai in sun so azo din ya kuke kuna lafiya?
lafiya lau Baffa.
Alabo ma ya soma gaishe da Baffa yana fadin
“Baffa shikenan kwana biyu baku ko neman mu?.
“To ba gashi kunzo ba? ya dauki sha aban yana fadin
“Masha Allah yaran nan sun girma Hajara dube su Allah ya sa naga yan kunne na ni ma uwa ta ta haifo min .
Fati ta bar wurin shima Alabo sai ya bar gidan Baffa yana ta murmushi yana fadin
“Gulma dai ajali ce ku nan har wata kunya ma kuka sani tunda har kuke jerawa a tafiya har ace ya kuke kuce lafiya lau?.
Inna Hajara ma ta mike tana rike da hannun Ramadan suka wuce don taga Yana neman magana ne.
Fati kam ta so kwana a misau amma alabo yace su koma gida dole kuww Baffa yace tabi mijin ta Inna Hajara kuma tana fadin
“Wannan iko da yawa Yake yaushe rabon yarinyar nan da garin nan kuma ace zuwan wuni daya don dai ana rikon igiyar auren ta?.
“To biyayyar miji dai wajib ne ganin gida kuma ni banga hadisin da yazo da shi ba in kuma mazhabar kuce ta uwa da yarta sai mu Kara ilimi .
Cewar Baffa halilu dole kuwa fati ta biyo alabo suka dawo bauci ba don ta so ba.
Keena da ta komawa ba I’mani akan aiki dai baiyi ba in ma sauya mata da wani za ayi zata biya kudi don tana son mallakar Kaiser ko baya so.
Sun Isa Niger ita da luba inda suka tara’s da ba I’mani suka zayyana mishi halin da ake ciki. Ya dubi keena yana fadin
“Yaron nan fa ba haka nan Yake ba akwai wasu fararen aljanu da suke dab da shi suna bashi kariya baki ga tun wancan lokacin ba ana neman karyata ni? To don ma sun san ba I’mani nee wuri na da ba haka ba amma bari mu gani idan zan iya fidda aljanin da yake tare da shi don matukar suna tare aiki ba zaiyi tasiri Akan sa ba dole sai ya matsa daga gare shi to Yana da naci tsoho ne amma mai zuciya da kwanji bai san tsoro ba bai kuma san zalunci ba shiyasa nake tsoron shi don in ya tusa abu a gaban sa sai ya ga bayan sa .
Ya fada yana makawa kwaryar gaban sa yizgar sa yana kwarara ihu bayan ya jefa takardar lambar Kaisar a saman ruwan yana fatan yaga Yadda yake so amma sai yaga takardar tayi k’asan ruwan tana nadewa kafin ma ta bacewa ganin ba I’mani wanda ya sake maka yizgar yana sambatun wofin sa amma sai ga kwaryar ba I’mani ta tarwatse haske yana fita wal wal wal hasken da ya walwale idon ba I’mani ya kuma kwartsa ihu mai karfi har yana tuma a k’asa yana faman murza idanu ga alama hasken nan ya tab’a idon ba I’mani wanda yake ta gaza yana neman dauki amma ga alama babu wannan mataimakin a nan dai don keena da luba dai neman guduwa suke don sun ga yana neman bi ta kansu don abun kamar turi.
babu arziki su keena suka baro wurin ba imani don ya soma watsi da kayan da suke dab da shi Yana runtumawa a guje yayin da dajin ya dauki rugugin hadari kafin a soma yayyafi wanda ya taho da walkiya mai tsanani wuta kuma ta soma zagaye dajin abinda ya gigita su keens da luba har suka shiga ya da kanin wani amma dai suka samu da kyar suka sha suna faman mayar da numfashin wahala.
Cike da mamaki luba ke fadin
“Haba gaske aikin ki keena yaki nasara nifa kallo daya nayiwa gayen nan na san akwai wani Abu tare da shi Allah ya sauwake fararen aljanu ai duniya ne in dai ta fannin tsaro ne ba dai mutum ba sai rabba ko aljanun ma dole suna tsoron irin wadan nan aljanun amma fa Ina tsoron kar ya zamo karshen ba I’mani ne yaxo don wannan tashin hankalin da ya same shi bana jin na lafiya ne.
“Ai kuwa bai Isa ba wallahi luba in ma karshen nashi ne yaxo to ya biyani kudi na in Amarya bata hau doki ba uban waye zai dora mata yaya? dole ne ma na komawa ba I’mani wallahi in ta kare mishi ya biya ni kudi na.
“Ni kam wallahi yanzu jiki na yayi sanyi keena tunda aka ambaci fararen aljanun nan.
“Ai kuma kin san kinci uwar karya kin kwana da yunwa luba kice ba zaki koma ba yadda muka dauko ta tun farko haka zamu sauke ta har karshe.
Kwanaki biyar a tsakani su ka koma Niger wurin ba I’mani amma abin mamakin shine sun sami ba I’mani ya makance baya gani amma kuma duk da makantar bai daina aikin shirkar sa ba Wanda yakeyi da lalube amma fa idanu babu hatta da gulalan idanun babu .
“Su waye a nan ?
Ya tambaya luba ta sanar da shi sune .
“Ke kune kuka dawo? To ta sanadin aikin ku kun kawo min wanda yafi karfi na har na rasa idanu saboda aikin ku kuma dama Ina dakon zuwan ku don wallahi ba zan yarda kuyi min sanadin idanu ba kuma ace kunci lafiya wallahi dole kuma ku rasa wani abu don yanzu aiki na ma yafi zafi ba kamar baya ba don rashin I’mani na a yanzu ya linka na baya.
“Nifa kudi na nazo karba gaskiya tunda aiki bai samu ba ba sai aba ni kudi na ba? haka kawai banci ban sha ba nayi asara ai karyar karya wallahi a biya ni kudi na tunda babu aikin.
“Ke ? na biya ki kike cewa? ni kina nufin nayi asarar idanu na a banza? To wallahi sai kin rasa wani abu a cikin jikin ki kamar yadda nayi .
“Wallahi karya kake tsohon najadu ko kana kwana da uwar ka sai ka biya kudin nan shege tsinanne banda warisar da kayi a kaina kuma kaci kudi na ka kwana lafiya?.
“Kika zage ni don ke tsinanniya ce? to wallahi babu ke babu rayuwa babu kuma mutuwa tunda baki da kirki.
“Uban uban ka in ka fasa abinda kayi niyya shegen matsiyaci tsinanne .
Ya soma lalube yana son ya damko keena inda ta mike tana auna mishi ashar ya jawo kwaryar gabsn shi yana maka mata har ruwan kwaryar Yana zubewa yayin da keena ta kwasawa ba I’mani mari tana marin tana auna mishi ashar inda kuma ba I’mani yaso nunawa keena rashin I’manin shi kan kace me? sai ga guguwa mai tsanani tana nufo su keena wacce ta mike ta auna aguje tana karanto ayatul kursiyyu da karfi inda luba ma ta mara mata baya suka fice amma guguwar nan ta bisu suna auna uban gudu tamkar zasu yage saboda daga kafa da suke daga haka suka fice suna karanto ADDU AR neman tssari har suka Isa gida basu daina ba.
Da wani irin sauri Kaisar yake kokarin figo Nadiya da ya gama fahimtar aika aikar da take kokarin yi mishi na jefa rabin ruhin sa a tanki amma tuni ya makara domin kuwa ta riga shi Isa tankin duk da kokarin Isa da yayi gareta da zafin nama har yana fincike kafafun ta da sunan ta kai k’asa ita da Siyamar zai fi sauki akan ace yayi asarar da take shirin jawo mishi.
Nadiya tana saka yarinyar a tank taji an shari kafafun ta da wani irin karfi wanda taji shi kamar na inji tayi k’asa yiff har tana gwaruwa da k’asa da karfi.
Kaisar Wanda ya ji tamkar ya hadiye zuciya ya mace saboda ya san yayi bankwana da siyamar sa fadawar ta ruwan can ta nutse har ma ta shaki ruwa ta daina numfashi.
Wasu irin hawaye suka soma wanke fuskar Kaisar yana jin wata irin tsanar Nadiya wacce bai tab’a ji ba har yayi dakacen abinda yayi mata na rashin sakin da ta nema ya hana ta ajiya da ya san wannan shine kullin da take kullawa da ya sahale mata igiyar auren ta wanda ta sanarwa matukar bai bata takardar sakin ba to zai yi nadama gashi kuwa yayi nadamar fiye da yawan shekarun iyaye sa in aka hade su gu daya. ba nadamar kawai yayi ba bak’in cikin da zai zama jagoran tafiyar sa Al kiyama ma ta jawo mishi.
Daddy da mama da suka fito jin karar da Kaisar ya saki lokacin da yake ganin Nadiya ta saka Siyama shi ya fito da su ga kuma kukan Ramadan wanda ya karade gidan saboda daukar mishi siyama da akayi sai ga abinda idon su ya gani na jefa Siyama tank da Nadiya tayi.
Da wani irin sauri Hajiya Aliya ta nufo Nadiya idon ta taf da hawaye tana fadin.
“Wallahi sai na kashe yarinyar nan kamar yadda ta kashe yar mala ikan Allah . wannan yarinyar duk yadda akayi jinin ta ba na ahalin musulunci bane wallahi wannan yarinyar bata zamo daga ahalin kirki da mutunci ba.
Hajiya Aliya ta danki Nadiya da wani irin ruko irin na sai naji ba a numfashi. Ai kuwa ta shake Nadiya tana gaura mata mari tare da nushin ta ko ta ina har tana jawo katako tana ta makawa Nadiya da son sai ta cika abinda ta fada na kasheta.
Daddy kam da wani irin sauri ya finciki hannun Kaisar yana fadin,
“Inna lillahi wa inna ilaihir Raju un yi maza Kaisar balle bakin famfon tankin can ruwan ciki ya fice yi maza da sauri .kai maccid’o zubairu kuzo nan da Allah.
Daddy ya kwada musu kiran .
Da sauri Kaisar ya kama tankin yana kokarin fincike shi idon shi da Ruwan hawaye don ya san ko an fidda ruwan ciki zafin ciki ya kashe mishi Siyama amma baiyi gardama ba ya soma kwance bakin famfon ba kama ya kasa.
“Hau saman tankin ka ga ko zaka iya juya shi.
Kaisar ya haye tanking amma abinda ya bashi mamaki ya kuma saka shi murmushi shine ganin wani katako mai kama da hannu da aka turo ta saman ruwan wanda akan hannun Siyama ta fada hatta da tawul din ta bai tab’a ruwan ba.baccin ta ma take sadidan .
Kaisar ya mika hannu ya dauko ta daga saman hannu hannun da ya tare ta yana son gane meye abinda ya tare ta fadawa ruwan? sai yaga abun ya bace bai iya ganin shi ba ya b’ace b’at.
Yana rike da siyama ya sauko yana mikawa daddy ita yana fadin
“Gata daddy a saman ruwan ta makale Allah bai nufi ta fada ciki ba.
Haj Aliya da take dafe da Nadiya tana kai mata duka har ta soma fidda mata jini don bata ji tana tausayin ta ba ko kad’an bata ki ta kashe ta ba sai gani tayi Kaisar yana mikawa daddy siyama wacce take motsa kafar ta tana shirin farkawa.
Ta saki Nadiya ta nufi daddy da yake ta tofe Siyama da ADDU A yana fidda hawaye yayin da aisar ya tsurawa Nadiya Ido yana jin lallai matukar yana son kansa da arziki to sai ya sahalewa Nadiya igiyar auren ta amma kuma idon shi da kunya ace ya rattaba wa Nadiya saki bai yiwa daddy kara da halacci ba.