Skip to content
Part 68 of 68 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

An fara show ne yayin da hall din da akayi show din a babban birnin washing ton don haka anyi cikar kwari mahalarta taro na kasashe da dama a cikin masu halartar taron har da abdulhameed da abokin sa jimy wanda shine ya gayyato shi sai kuma shaid’an Wanda shima ya iso don samun macen latsaww a cikin wacce ta zamo ta nunawa sa a to za a zube mata kudade a latsa ta ta yadda za ace babu kalar macen da ba a latsa ba.

Aka soma gabatar da mata kala kala kowace da kalar adon ta da irin kyau da tsarin ta ana haska su ta fuskar camera da coverege .

Idon Abdulhameed ya hasko mishi Nadiya wacce adon ta y sha ban ban da na sauran matan ga surar ta da bata boye a rigar da ta saka ba wacce tafi kama da net  gashin ta American din ma albarka ta fita kan da fitar ta don haka wuri ya dauki sowa al amarin da ya tayar da hankalin abdulhameed bare kuma shaid’an da yake ganin yarinyar tamkar a mafarki.

Sai da aka gama nuna fuskokinsu tare da adon su kafin katuwar computer da take kusurwa hudu ta hall din ta soma nuna hotunan su da sunayen su wanda Yake daidai da yawan adadin yawan su kafin aka bawa yan kallo damar zabin macen da suke ganin tayi musu kyau a matsayin venues wanda ta yawan adadin wanda suka zabe ki ne ake gane wacce ta ciji mutane har ta zama first position da yawan adadin followers din ta da kuma mazan da zasu aje deposit na son kadaicewa da ita  tunda taron dama saboda sada fasadi ake assasa shi don tallace kawai ake ta mata kyawawa mai so sai yayi magana a tsadance ya zube kudi masu dama don a matsayin venues zai biya ta ita kuma daga nan sai kasuwa ta bude mata ga shaid’anun maza da Kuma vedion fasadin da suke yadawa.

Ai kuwa shaid’an ne lambar farko wanda ya fara like da following din Nadiya ya kuma zube manyan kudade akan son ya same ta a daren yau ta debe mishi kewa.

Kudin da shaid’an ya zube sun Isa su girgiza talaka amma da yake a tsakiyar masu abun yake sai ga wani kartakin kafiri wanda shine na biyu da ya yi like da following din Nadiya ya kuma zube kudaden da suka linka na shaid’an shima dai Osting yaga kaddara a tare da Nadiya wacce zai karu da ita idan ya mallake ta.

Abdulhameed kam account din sa yake check inda dukkan kudaden sa suke account ne guda uku kuma kowane cike yake da karafan nasara Amma Yana son yayi bajintar da zai doke shaid’an da Osting don haka ya kira distinguish yace mishi yana son kudi masu nauyi yanzu zaiyi wani abu da su urgently need to helping my daddy.

“Kar ka damu zan tura maka

cewar distinguish Mukhtar biro

Ya katse wayar yana kiran haj laila itama ya nemi kudin urgently need to helping my mom please send me now.

Ya gama wayar yana sauraron yadda choose din yake tafiya yayin da wasu musamman masu akida suke zabar jinsin su da yaren su saboda suna da akida gaskiya mafi yawan su yare da addini shi suke wa amma duk da haka da ake cikin lokaci k’asa da awa Nadiya ta tara follower wanda babu wata mace da ta tara su domin kuwa tana passing din 599k yayin da sauran kuma daga mai 78 sai Mai 95 Amma Nadiya kam tana shirin zubar da mata kyawawa wanda suke na kasashen ketare.

Aka ci gaba da choosing wanda aka gama tsakiyar dare don karfe biyu saura aka kare choosing inda Nadiya ce ta tashi da follower 222000.  A mafi yawan followers sai mai bi mata heling wacce ta samu 119000. sai ai biwa heling maria mai follower 112000 daga haka sauran kuma duk k’asa daga haka ne yayin da Nadiya kam ta zama first position aka shiga Yaya za ayi? kowace kafa ty gidajen TV abinda ake ta yayatawa kenan yayin da kuma aka shiga gasar daukar Nadiya da zube kudade don mallakar ta

Mutum dari da sittin ne ya zuba kudin sa a account din su Vigo kowa da kalar bajintar da Yake nunawa wurin zube kudin sai ga account din su Vigo yana karbar sak’onni kudade suna ta hawa inda kuma aka higa canki canka din wanda zai dauka inda aka gano wanda yafi bajinta wurin saka kudade wato abdulhameed don dukkan sa da wanda aka tura mishi ya tura don haka shine wahnda zai dauka smma kuma akwai akida da kabilanci don aka Osting ake son bawa Nadiya a wannan dare inda kuma a take aka soma mayarwa mutane kudaden su amma sai ga shaid’an yayi wata fita ta tashin hankali inda ya sauke kudi har aka manta da batun wata akida aka juye zancen zuwa ga shaid’an wanda yake dama hausa fulani kamar Nadiya don kudin da shaid’an ya danno sun wuce na abdulhameed don haka babu wani dogon jira ake mayarwa mutane kudin su saboda ci gaba da aka samu ba sai ka tura account ba akwai wani links ne da suke amfani da shi wurin samun account details din ka sai dai kaji an maido maka da kudin ka.

Jimy ya dubi Abdulhameed yana tambayar shi yanzu yana son yarinyar nan ne? Ya amsa mishi da tun a Nigeria yake son ta amma taki shi sai gata ya gani yanzu a venues.

“Barsu za a samo maka ita in dai zaka saki kudi .

Ya bi jimy da kallo amma ya kasa tankawa yana dai kallon yadda ake ta haska fuskokinsu Nadiya jaruman da sukayi winning one position to five position.

Ganin irin go slow din da ake shirin hadawa ne Yasa aka so fidda Nadiya wacce aka bawa shaid’an tickets din tafiya da ita safe hotel wacce ba a bukatar wani ya san tana can don haka ta private aka fidda Nadiya wacce show ne ya fice da ita inda shaid’an yake abinda basu sani ba Osting ya gama farke musu laya har yayi nashi Shirin na gayyatar masu zafin kan da zasu taya shi kwato Nadiya don haka duk akan idon Osting aka so yi mishi manuba don haka aka fara sakin harsashin bindiga da watsa taron da barkonon tsohuwa tiagas al amarin da ya tashi k’ura har Osting ya samu dauko Nadiya wacce aka soma b’arin wuta amma a haka Osting ya shalle da Nadiya inda aka bar shaid’an da Rad’ad’in harbin da ya samu a hannu.

Wuri ya hargitse yayin da jimy shima ya nuna tashi bajintar yabi bayan su Osting abinda kuma ya so ruda Nadiya wacce sai yanzu ne hankalin ta ya dawo jikin ta ta gane manufar wannan taron na venus wanda yake kawai don tallata mata inda ita kuma tayi nasarar samun mabiya har ana shirin kashe ray gata ita kuma bata san  .

Osting yana cikin auna uban gudu da motar shi sai ga get wanda hukuma ke sakawa abinda ya tunawa Osting shi mai laifi ne kuma wanda ake nema wanted sai gashi a get din hukuma.

Kafin yayi wani yunkuri har an cimmasa dole kuma aka kama su su duka ukun da suke cikin motar da shi da abokan sa biyu wanda suma wanted ne sai Nadiya da ta bawa mutuwa amana sai gata a cikin wanda ake nema kuma an same su.

Case din Kaisar bai ja zare da tsayi ba domin kuwa daddy yayi tsaye ya karbi case din wanda yace shi da Kaisar a gida daya suke kuma in har Kaisar yana da alaka da abinda ake tuhumar sa to shima haka yake kuma a kara buncike in an samu wata Alama da ta nuna shi a dan ta Adda to shima haka yake.

Dukkan binciken ya kammala Allah ya wanke Kaisar wanda aka gane makircin Nadiya ne ya kawo shi wannan mugun matsayin don haka aka sallame shi suka koma gida Daddy yana ta bashi hakuri shi kuma sai fada yake babu komai fa daddy sai da jarrabawa Ubangiji zai daga darajar mu in sha Allah wani alherin ne Ubangiji yake nufin mu da shi.

Babu abinda yake ranshi daga yan biyu sai siyama don haka yana zuwa gida su ya rungume Yana sumbatar su yana kissing din su  yayin da yan biyu suka ishe shi da gwarancin su suna nanukar sa.

Siyama ta soma rashin lafiya abinda ya tashi hankalin Kaisar ana ta magani ashe wai madarar ta ce bata karbe ta ba nonon uwa shi take bukata fiye da nan abinda ya tashi hankalin Kaisar da mama har suka shiga neman wacce zata shayar da siyama amma aka rasa yayin da fati kuma take ja bata kai ga haife nata cikin ba.

Ranar da akayi show up venus anyi ta nuna shi a kafafen TV da setlight shiyasa mama ta samu ganin Nadiya da irin shigar da tayi ta Allah wadarai.

Kaisar ma ya gani mama ta kira daddy yazo ya gani.

mamakin su ashe da gaske take don basu zaci da gaske take son shiga Venus din ba sai ga shi daddy ya ganta cikin kayan da babu mai mata kyautar musulunci a cikin su don arniya sak.

Kaisar kam baiyi mamaki ba don ya san zatayi fiye da haka amma kuma yayi mamaki matuka gaya da ganin shigar kayan ta .

Kwanaki biyar da faruwar hakan fati ta tashi da nakuda wacce ta haife dan ta a gida mai kama da alabo abinda ya saka Baffa da daddy farin ciki yau ga dan Alabo da Fati Baffa sai cewa yake anyi mini kani na samu dan uwa uwa ta ta haifa min dan uwa uba na ya haifa min kani.

Fati da ta dade da sanin matsalar siyama ta kuma sanarwa Alabo zata karbi siyama ta shayar ya kuma amince mata don haka ta kira mama tace a kawo mata siyama don innar ta Hajara tace misau za a maida ita wankan gida.

Ranar da aka kira wayar daddy ana fada mishi an kama Nadiya a cikin mugayen criminal din America ta bada details din sa tace shine mahaifin ta don haka ana neman shi a America .

“Wacece haka kuma ? Daddy ya tambaya aka fada mishi Nadiya ce .

da sauri yace bai San ta ba bashi da alaka da wata mai irin sunan.

Nadiya da ke kuka kashirban ta karbi wayar tana fadin.

“Daddy nice  Nadiya wallahi azal ta kawo ni America an kama wasu mutane yan ta adda da ban san ko su waye ba ance tare muke wallahi Daddy ban san su ba don Allah Daddy kazo ka cece ni wallahi ance kashe mu za ayi.

“Don son Allah da ANNABI daddy ka taimake ni ka  cece ni ana shirin hallaka ni  wallahi daddy  nayi nadamar zuwa na America .

“Wai waye ke magana?

daddy ya fada a fussce duk da ya gama jin abinda Nadiya ta fada mishi wanda yaji dadin abinda ya same ta koma wane irin ne.

“Daddy nice Nadiya yar ka.

“Ki duba lambar da kika kira kin kira wrong nomber don ni dai sunana Alh iro ba Daddy ba kuma bani da Yar da take da suna irin naki mai irin sunan ki ma bani da alaka da ita Nadiya? gaskiya ban tab’a jin sunan ba.

Wani irin takaici ya shake ta domin kuwa ta gama tabbatar da daddy yana shirin saka ta a nadamar da yake fadar zai saka ta kuma ya bata mamaki.

“Daddy kayi min afuwa don Allah don ANNABI ka duba mini wallahi Ina cikin balaki na sani ban ban kyauta maka ba don Allah daddy ka cece ni daga gidan nan komai kake so nayi wallahi zanyi shi.

“Kin makara Nadiya ! da kinyi hakan tun kafin yau da na kara lullube wani sirri wanda har na mutu kema ki mutu ba zaki san shi ba kema zaki kare rayuwar ki ne cike da rufaffen sirrin nan bai fita duniya taji ko ta gani ba. amma kash kin zubar da garin ki ba zai kwasu ba sai da k’asa. In kika ce kinyi nadama ai kuwa da kin bawa irin ki kunya kuma ma ni a yanzu wane irin ceto kike so nayi miki? Ok kece kawai kike da bukatar ki saka ni nayi miki amma ni bani da hakkin nace kiyi min biyayya kiyi ? Ai sakamakon khairan ai da alheri. .

“Daddy nayi kuskure don Allah kar ka duba kuskure na wallahi Ina cikin balaki.

“Ba kuskure bane abinda kikayi ganganci ne wanda nake ta nuna miki kina runtsewa  kuma balaki ma ina mai tabbatar miki da baki fara ganin shi ba ko alhakin ya’yan da suke da hakki kanki kadai ya ishe ki. ni fa ban so naji kina cewa kinyi nadama tun kafin yau ne ya kamata kiyi nadamar nan shine zan yarda nadamar kikayi amma a yanzu balaki ne ya sa ka ki yin nadamar to koma dai meye wannan Nadiya kayan ki  ke kadai ya shafa wallahi bai shafe ni ba bai shafi wani na ba yadda kika tsallake dakin auren ki da mijin ki da ya’yan ki kika fice baki ji abinda na fada miki ba sai yanzu da duniyar ta soma fada miki ne kika tina Ina da amfani to ni ma haka zan toshe kunnuwa na daga kowane irin balaki ne ya same ki ke kadai ya sama kar ki kuma kiran waya ta ko ki bayar a kira ni ina ce America kika zo kika shiga Venus? kenan wanda ya baki shawarar shiga ko ya Kai ki yafi ni to ki Kama shi don ni yadda kika barni haka na barki koma fiye da irin barin da kikayi min   don ma kina amsa Sunan musulunci da nace koma wane irin balaki ne kika shiga yazo miki da sauki tunda har Kika tuna dani ai ban zaci zaki sake waiwayar mu ba ko da yake da kin laso inda zak’in yake na tabbatar da mun Rabu kenan har abada amma da akasi ya samu kika laso d’acin sai kika ce nine naki bayan but baki yarda kinyi abinda nace kiyi don ki zamo tawa ba. to duka dai maganar daya ce ki nemi naki a wani wuri amma Ni ko kin samu yin free wallahi baki da masauki a muhalli na don san fada miki gaskiya ne ban hada komai da ke ba sai taimako wanda ya sakamakon sharri a tsakanin mu to daga yau daga kuma yanzu ma ki ki rike wannan ni da ke musulunci ne kawai ya hada mu sai kuma taimako in ma kin dawo to zan kaiki gidan bak’i ne ki rayu a can amma gida na da ki kira ni daddy wannan kam fati ce halal malak ki kalli irin wulakancin da kikayiwa fati to itace ya kamata tayi miki abinda kikayi Nadiya na fita hakkin musulunci na fita hakkin mutumtaka amma baki tab’a tsayawa kin baje zancen da nake yawan nanata miki ba to in ma baki nema ni zan sanar da ke don ki gane kuskure daya ne tak ake mai ban haushi kuma kinyi tsalle daya kin fada rijiya wanda a million ma ba sai fito ba . da kin gane Kaisar kowaye da nake yawan fada miki AZURFA DA ZINARE kece AZURFA shi ZINARE ne da yake iya haska dukkan wata AZURFA amma baki lura ba to na shirya idan kema kin shirya amma maganar abinda ya same ki wallahi ko murya ta ba zaki kuma ji ba bare nazo na tsaya miki kar kuma ki yi mafarkin nayi hakan in da zasu ji ma ni da nace su rike don kin wuce yar ta addar da ake zargin ki sun rage miki mukami akan wanda suke kallon ki da sun san ko wacece ke da ba ma zasu tsaya neman wani ba asi ba zasu kaddamar miki to amma kalmar la ilaha illallah Muhammadur Rasulullah sallalahu alaihi wassalam da ta ratsa zan iya cewa Allah ya kare ya kuma baki mafita.

<< Azurfa Da Zinari 67

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×