Tuni kuwa Suka dauka suna fadin ba zasu yarda ba wallahi shekara nawa Bata haihu ba sai yanzu da Yake tana da manubar son cin gado? Wato in taga ta haihu sai ta kashe Al Mustafan tace dukiya ta Dan ta ce.
Al Mustafa Yana Kan hanyar tafiya Legos wurin siyen wani kanfami da aka talla ta mishi wayoyin su Rabi u da hamisu sukayi ta shigowa suna Kiran shi don yanzu kam kaf tarin kafatanin Yan Uwa da dangi kowa nashi ne shiyasa kowa Yana da lambar sa don Haka akayi ta Kiran shi ana fada Mishi maganganun da tukuro yazo da su Suma anan suke don mafi yawan Yan gidan Nasu ba son Amina suke ba Wai bare ce ita a cikin su abinda suka so ya dauko Mata a haular su yadda za ayi yadda ake so don Haka Amina ba Dadin su take ji ba.
Ya fada musu Yana hanyar Lagos tafiyar da mukayi ta tare don na duba mishi kamfani don Allah ya sa Alh Al Mustafa Dan kyana yayi min wata irin yarda da Aminci wacce duk abunda na Bashi shawara akai Yana karba ya Kuma ga alfanun Abun shiyasa muka tafi tare Kuma Ni ban San abinda ke faruwa ba shi kuma Bai fada min ba.
Jin yace Yana hanyar Lagos yasa sukayi taro su biyar suka nufi gidan nashi suka Sami Haj Amina sukayi Mata kaca kaca da cin mutunci har suna Shirin dukan ta karshe dai suka uzura Mata da lallai sai ta bar gidan a lokacin. Ganin suna Shirin ci Mata mutunci don da karfin tsiya suke son fidda ta gidan shiyasa ta fice tana kuka ta nufi Gombe
Lokacin da muka dawo ne muka Sami gida a kulle wayoyin Haj Amina Kuma duk a Rufe sai da muka Shiga ne Al Mustafa yaga wayoyin nata a gidan Wanda Rashin caji da tashin Hankalin da aka saka ta yasa Bata bi ta kansu ba ta wuce.
Yayi tsaye Yana kallon falon Babu ko gyara Yana Kuma tunanin inda Amina ta tafi Bata Sanar dashi ba ASALI ma Bata da lafiya.
Wayar mahaifin ta malam Musa ta shigo wayar ya dauka Yana gaishe shi inda Yake tambayar shi me Yake faruwa ne Amina ta iso hankali a tashe? Ya Sanar mishi Bai San komai ba don baya gari yaje Lagos sai yanzu ya dawo ya Tara’s da gida Babu kowa.
Washe gari mal Musa ya Sanyo Amina mota sukayi sammako inda ta zayyana abinda su tukuro suka zo gida sukayi Mata.
Ran Al Mustafa yayi masifar tashi Amma ya lallaba mal Musa ya Bashi hakuri don Yana ganin fasa maganar Nan a gaban shi faduwa ce babba don Babu yadda za ayi ya manta da Mal Musa a Rayuwa Kuma ba zai so abinda zai Bata Ranshi ba don Haka ya cika Mal Musa da abin arziki y wuce Gombe inda Kuma tukuro ya taho har gidan shi da gayyar Yan Uwan shi don nunawa Al Mustafan Bai Isa ya karbi cikin da ba na shi ba
Anan Kam Nima na San Halin da ake ciki don su tukuro sun Rantse sun sake Rantsewa Akan ciki nawa ne Kuma sai na Karbe shi har na fada musu ajandar da muka kulla Ni da Haj Amina.
Rikici Mai yawa har su tukuro suna shigar da Kara abinda Kuma ya Bata Ran Al Mustafa matuka Gaya na sharrin da sukayiwa matar sa da Kuma aminin sa Wanda yasa ya nuna musu kwanjin sa da bacin Ranshi a Karo na farko da ya fara fito na fito da su tukuro
Ranshi a bace Yake Fadin
“Gaskiya Baku kyauta mini ba Yaya tukur har da ku Yaya hamisu a wannan Abun ? Shin da kuke ta wannan Tayar da jijiyar wuyan waye a cikin ku ya Kama Amina da shi Ibrahim din Akan Hakan? Ni na fi ku sanin su waye Wanda kuke tuhumar Ni ban tab’a Kama Dayan su da laifi shigen hakan ba. Kuma da kuka Kai magana kotu da yawun wa kukayi? Kuna son nuna min ku yan Uwa nane? Ai Baku kware a Hakan ba tunda har almajirci aka kaini saboda Rashin gata waye ya tab’a tunawa da Yaya nake kwana nake tashi? Sai Yanzu ne zakuyi min abunda bance Ina so ? To yaushe ne ma kukayi min wani Abu da ya nuna Ni dan Uwan ku ne? Ko kuwa don kunga na kawar da kaina shine kuke son shige makadi da Rawa ? Ni da gida na da Kuma amini na sai anyi min over talking har da zuwa kai kara? To naji me ake son ce min ? Ni da mata ta har wani ne zaiyi mini hukunci? To kuyi hukunci a gidajen ku amma naww gidan nima a barni nayi hukunci ko na tab’a yi muku irin wannan shiga hurumin?
Akace mai hakuri bai iya bacin Rai ba ta inda Al Mustafa yake shiga ba ta Nan yake fita ba duk sukayi shiru suna sauraren shi har ya dire kafin Yaya Rabi u da hamisu suka dube shi suna Fadin
“Yanzu saboda mun nemi mu bi maka kadin cutar da ake Shirin yi maka shine kake keta idon mu kana cin mutuncin mu Al Mustafa? to mun gode Allah ya biya Amma Kuma ka Sani muna nan Kan bakan mu bamu yarda da cikin matar ka ba wallahi ko ta Haife shi Sai anyi gwajin jini don wallahi Bata isa taci gadon ka taka Haye ba .
Cewar yaya hamisu yayin da Al Mustafa ya dube shi yana fadin
“Ni dai na yafe Muku abinda kukayi min amma Amina da Ibrahim matukar Basu yafe muku ba ku tanadi hujjar Kare kanku a gaban zatin Ubangiji kuma koma meye amina zata haifa nawa ne halal bana Kuma in kari kuma ko da yadda kuke zaton ne ai D’ana ne su duka zan iya yi musu abinda ko ba sa Raye wa jinin su bare Kuma daukar hakki kawai kuke kuma in sha Allah matukar Ina Raye Babu mai mini wani gwajinn jini a haula ta don ban dorawa zuciya ta zargin komai ba Kuma Ni jar wanda ya kuma Tayar min da wata magana Mai irin wannan ba na so!
Da wannan maganar aka Samu saukin tashin Hankalin da tukuro ya kunno Amma Kuma a gefe suna ta kunzuga muguwar sata da son Sai sunga Bayan Al Mustafa Wanda ya zama kafin ALLAH ne Kuma turmi Sha daka kainuwa dashen Allah bai girgiza ba bare ya motsa sai ma gaba gaba da Yake don tuni kamfanin da ya siya a Lagos ya soma Aiki kamfanin shinkafa ne Wanda ya soma aiki cikin nasara ya ke kuma fito da shinkafa Mai inganci wacce ta karbu a fadin Nigeria
Watanni shida cif da fara Aikin kamfanin shinkafa Allah ya daukaka kamfanin har aka sake bude na fulawa shima a Nan lagos din shima da nashi nasarar kuma a wannan lokacin ne Allah ya sauki Haj Amina lafiya ta Haife cikin ta Sai ga yaro mai kama da uban sa sak Babu ta inda ya baro Al Mustafa dan kyana har da kankantar tamkar yayi kaki ya tofas .
Haj Amina da ta haihu a gida ta zubawa yaron Ido tana kallon shi cikin jini Yana ta tsala kuka Alamar ya iso lafiya Amma kuma ita Bayan ta Haife shi din wani irin zazzabi ya Rufe ta
Al Mustafa ya iso gidan saboda kiran da tayi mishi wanda Baya nisa tunda ta Shiga watan haihuwa
Ya iso ya samu yaro Yana ta kuka ya tsamo shi daga cikin jini Yana rungume shi Yana hawayen farin ciki musamman da yaga kamar yaron . Shi Kam Allah ya Sani ya San wacece matar sa ba mutuniyar banza bace Kuma yasan halin ta ya San Rayuwar ta Bata San wani namiji ba sai shi kuma shi din ma a macen ta kamammiya ya santa
Ya kira goggo makociyar sa ce da Yake dauke da takalifin ta itace ta gyara yaro ta kuma gyara Amina wacce zazzafan zazzabi ya Rufe dole aka nufi asibiti aka kuma Bata gado
A Ranar da aka kawo Aminan Al yana tsaye kanta ganin yadda tayi wani irin fari tss tana Rike da hannun shi tana fadin
“Ka yafe min Al mustafa Allah ya sani Al mustafa naso na Rayu da kai da zuriar ka amma kash kowane bawa yana da iyakar sa yana da lokacin sa ni kam nazo nawa lokacin sai dai kuyi hakuri ga yaron nan ya zama Amana a gareka bashi da wani Uba sai Kai ban San wani namiji a Rayuwa ta ba sai kai Allah ne shaidar hakan na Kuma yafewa yan uwan ka da suka jefe ni da wannan bak’in kazafin Amma don Allah kar ka Bari Rayuwar yaron Nan ta zama shima sun goga mishi bak’in ciki don Allah Al Mustafa ka kula min da yaron Nan Ina Roka mishi Allah yayiwa Rayuwar sa albarka irin yadda yayiwa taka Rayuwar Kaisar naso saka mishi suna smma duk sunan da ka saka mishi yayi.
Kuka Al Mustafa yake Yana rungume da Amina wacce Yake fadin
“Daina fada min haka Amina in kika barni na saka Rayuwa ta Ina? Kece gatan mu ni da yaron nan a hannun wa kika bar mu?.
“A hannun ALLAH mana Al Mustafa? Nima a wurin ALLAH zan koma Ni da ku duk muna cikin karkashin inuwar Ubangiji ne .
Ta soma tari tana fadin ya Bata Ruwa.
Ya dauko gorar Ruwan ya kafa mata a baki ta soma Sha sosai kafin yaga ta kwanta bakin ta Yana motsi duk da Baya Jin abinda take fada
Bacci ya kwashe ta Ashe tafiyar kenan sai fa a darussalam
Daren juma a Amina ta komawa Ubangiji Al amarin da ya gigita Al Mustafa Wanda ya shima a dole ya Kare a gadon asibiti har akayi Jana izar Amina Bai san Wanda Yake kansa ba sai fa su tukuro da suke ta yadda suke so don ko Jana izar Amina Basu halatta ba a cewar su Allah ya kassara mugun nufin ta gashi nan ta bar duniyar da burin mallakar dukiyar da Bata da tabbacci Akan ta gashi nan ta sheka barzahu.
Jariri kuma yana hannun tsoguwa goggo wacce take kukan rashin Amina wacce ta dauke ta tamkar Uwa mahaifiyar ta komai yarinyar nan ta girka da Rabon tsohuwar sai take ganin jariri kamar uwar sa.
Ni na siyi madara na kawowa goggo na nuna Mata yadda ake hada ta da Ruwan zafi Adama a bashi
Kwanan Al Mustafa uku a asibiti kafin ya farko ya ganshi a gadon asibiti Yana karewa tukuro da Rabi u kallo wanda sune suke tare da shi amma Babu abinda suke kullawa sai mugun Abu da Yadda zasu washi dukiyar Al Mustafan Wanda suke ganin kwanciyar sa itace lokacin su na cin zahamar su
Ya tsura musu ido yana kallon yadda suke kus kus kus din su na makirci ba tare da sun san ya farka ba sai da na Shiga dakin ne sukayi firgigit tamkar masu farkawa Daga bacci.
“Ibrahim? Amina ta Rasu? Da gaske ne ko kuwa mafarki nake? Don Allah kace min MAFARKI nake Idan har da gaske ne ta Rasu don Allah Nima zan so na bita.
Mtsss
Wani dogon tsaki da Yaya Rabi u ya sauke shine yasa Al Mustafa ya dube shi .
“Ba gashi ba? ba gashi Allah ya tona maka asirin matar nan ba? Tana ta son taci gadon ta Ashe itace zaka cI nata gadon. Duk wannan bai sa ka gane Allah ne ya nuna maka ita ba? To ka bita Babu mai asara sai mu din da kake taimaka .
Al Mustafa ya koma ya kwanta yana Jin maganganun jahilci irin na Rabi u wanda suke dafa zuciyar sa .
Ya lumshe sa yayin da na zauna gefen sa Ina Karanta mishi kalmar hakuri da daukar kaddara ga musulmi cikakke mai I’mani inda su tukuro suka fice shi da Rabi u wata kil dai tattaunawar su zasu karasa.
Al Mustafa ya bude idon sa Yana fadin
“Ibrahim? Ina Kaisar?
Na juyo ina fadin
“Yana hannun goggo ko a kawo maka shi?.
“A a Ibrahim don Allah ka karbe shi daga hannun ta ka Kai min yaron Nan inda Yan uwa na ba zasu samu labarin sa ba Domin kuwa a yanzu ne na gane yan uwa na matukar suka gane Kaisar shine kawai abinda na mallaka akwai matsala Ina tsoron tattaunawar can da ake naji Ana fadar jariri to taimaka mini ka Nisanta min shi daga yan uwa na kafin na bar asibitin Nan don Allah tashi Ibrahim Bani da komai sai Kaisar gashi Kuma yazo tsakiyar wanda ke son abinda na mallaka ko ta halin yaya komai zai iya faruwa gareshi to ko da na bar duniya a yanzu ibrahim ka taimaka mini ka cika min alkawarin da na daukawa marigayiya Amina Akan Kaisar .
Na mike tsaye Ina fadin
“Kar ka samu damuwa Al Mustafa in sha Allah ba zaka mutu ba bari na gani Ina zan Kai maka Kaisar?.
Yayi min nuni da hannu Alamar nayi sauri.
Na futa da sauri na Isa gidan goggo na fads Mata zan karbi yaro Bata ja ba ta bani tana fadin
“Wannan yaro kazo duniya cikin garari Rasa Uwa ai garari ne gashi dangin Uban sa dai bana Jin akwai mai zuciyar I’manin da zata tallafawa maraicin sa sai dai ko ga dangin uwar sa su kam dangin uwa suna nan da zumunta ni kam banda raunin tsufa wallahi da nayiwa iyayen yaron nan halacci fiye da wanda sukayi min to ina ! .
Ta fada tana share hawaye
Na karbi Kaisar ina fadin
“Kar ki damu goggo ayi mishi ADDU AR Allah ya dafawa maraicin sa in Sha Allah tunda Ubangiji ya nufi zuwan sa duniya to shine zai tallafawa maraicin sa mu da shi Allah kadai yasan waye shi.
Da wannan na karbi Kaisar na shiga mota duk da ban san inda zan nufa ba abinda kawai na Sani zan nesanta Kaisar da garin Jos.
Na tako mota sai gani a hanyar bauci abinda na yankewa zuciya ta shine na kawo Kaisar wurin Aliya na tabbatar da zata Rike yaron nan tunda itama bata samu haihuwa ba kuma alherin Uban yaron nan ya lullube mu har ita duk da yazo gida na sau daya sun gaisa da Aliya Haka kuma alherin sa kullum tafe yake gareta don Haka kai tsaye na iso gidan dauke da Kaisar ta tarbe ni tana karbar yaron ta kuma zuba mishi ido kafin tace.
Wannan yaron dan Al Mustafa ne? Kamar su kam ta Isa.
Ban boyewa Aliyah komai ba na zayyane mata komai ta ce ai dan Al Mustafa namu ne alherin uban sa ya wuce iya wannan alfarmar don haka idan yana bukatar wacce tafi Rukon Kaisar ya kawo mana ita zamuyi mishi in sha Allah.
Na jima banga mace irin Aliya ba wacce nayi zaton zata yi min bore koma ta kalubalen ce ni Akan yaron smma sai ta shayar da ni mamaki don haka naji hawaye sun cika Ido na na sakawa Aliya albarka nayi mata fatan Ubangiji ya azurta ta da zuria Mai albarka
Na aje mata madara ta jarirai na kuma fada Mata Al Mustafa yana gadon asibiti a yanzu ga kuma Halin da Yake ciki na tashin Hankalin Rasuwar matar sa Uwar Kaisar don haka nace mata zan juya amma zan dawo bayan kwana biyu tace nayiwa Al Mustafa ta aziyya kafin taxo tayi mishi mukayi sallama na juya Jos ina fatan na Isa na sami jikin Al Mustafa yayi sauki koma ace an sallame shi daga asibiti.