Skip to content
Part 90 of 99 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

Tukuro ya soma balle boturan Rigar sa Yana Fadin

“Me ya tayar maka da hankali ya Kuma baka mamaki Rabe? ni fa na zaci murna kazo min.

“Har murnar ma Ina maka tukuro amma me yasa baka sanar dani kudirin da yake ranka ba? nima ai da na mallake kamfanin sumuntin da nake Amma sai naji Duka biyun ka siye tukuro shine abinda ya bani Mamaki abinda ya Tayar min da hankali Kuma shine yadda muke komai a tare Amma ka zagaye shine ya nuna min har gobe dai gidan mu da Yan Uban ci tunda tare muka shirya nade dukiyar Nan don muga Bayan komai Ashe Kai ka Gama tsara komai Ni kake kallo a galhoman wofi.

“A a Yaya rabe Karka munana min zato Mana? Ni da Kai fa kowa tashi ta fissheshi ne Kai sai nace maka ga yadda ya kamata kayi? Kaine fa Yaya na Kaine gaba Dani kuma don lalacewa da toshewar kwakwalwar ka sai na saita ka? Kai me ya Hana da kaji yace zai siyar da kamfanin ka fito ka tsaya ka jajirce har ka siyi na sumuntin? Ni da Yake na shirya ai ban yarda kaina yayi murfi ba duniya ai Bata auren Rago.

“Haka ne amma ka san in ni na tsara hakan ba zan boye maka ba zan fada maka.

“Kai ai baka da sirri ne ni Kuma ciki na ba don tuwo yake ba ba kowane Abu nake iya fada ba ko ga Uwa ta kuwa don zukata cike suke fal da mugun Abu.

“Kwarai kuwa tunda na yarda na biye maka mun kulla mugun Abun ? Ai dama tsiyar ka hadu da mutun ba a hanyar Allah ba karshen ta Al Amarin naku ya kare da uwa ka Uban ka. nayi maka murna Allah ya sanya alheri amma Yaya zamuyi? zaka iya siyar min da kamfanin sumuntin na fansa na tayar naci gaba da business?

Tukuro yayi dariya Yana Fadin

“Gaskiya ba zan iya siyar maka ba Yaya Rabe don tuni mutane sukayi min caaaa Akan suna son na siyar musu  ni kuma ba zan iya siyarwa ba nima yanzu ne zakaji sunana ya soma zaga gari don ina mai tabbatar maka da Zan Shiga in fita sai Naga wancan mutumin ya Kai k’asa warwas don ya Gane wulakancin da yayi min ba Zan kyale shi ba don sai na mayar dashi abin tausayi sai ya koma nine zan cire Riga na Bashi ya saka karshe Kuma na kawo shi kofar gida na Yana min gadin Rufewa da budewa na kofar gida na ba takamar arziki yake ba har yayi Mana wannan wulakancin? To ya kwantar da hankalin da wallahi sai na tsiyata shi na mayar da shi wulakantacce ya Zama nine uban gidan sa.

Yaya Rabe ya dube shi ya tabbatar da zai iya abinda ya fada ai tukuro yaci sunan sa shaid’ani a fada a cika ne sai dai kawai ayi ADDU AR Allah ya tsare musulmi da Sharrin sa.

“Ni ba wannan ne matsala ta ba tukuro shin zaka siyar min da kamfanin sumunti ko kuwa zaka bani Hayar sa ne ?.

“Ko daya ba zanyi ba Rabe bakaji abinda nace bane? Da hausa fa nayi maganar nan nima na kusa zama done  ka dai Bari zan cigita maka wani ko ba a Nan Jos ba Kuma Kar kace na Ranta maka don gaskiya ba Zan iya Ara maka kudi na na to ka biya Ni yaushe? Kuma in ma cewa nayi Zan siyar maka saboda Allah kana da kudin siyen kamfani a Hakan ka? Kai da kanka fa kace ta soma kare maka to ta Yaya zan yarda na biye maka muyi Ragas?.

“Kallon da kake min kenan tukuro? Ai ko ta Kare min ka San Ina da kaddara ga mota ta ga gida na.

“Ai dukkan su Yaya Rabe ba zasu iya mallaka maka kamfanin Nan ba ko da kuwa har da bataliyar Ya’yan ka da matan zaka siyar ka kuwa san nawa na zuba? Milyon sittin da tara fa na zuba saba in ba daya saboda Allah kana da wannan kudin ? Wai fa kamfanin sumunti kadai ya lashe wannan kudin shi na takin zamanin ne ya lashe hamsin da shida to ba na sumuntin ba ko na takin zamanin kana da su?  Mu bar ma maganar Rabe don Kar kaji haushi na  ka dai Bari ana Kan gyare gyare ne in an kammala na fara Aiki in da yuwuwar daukar ka Aiki zan neme ka duk da ni kam gaskiya ba zan zuba Yan Uwa na ba gara kawai na nemi bare tunda na gane ciwon Kai ne.

Yaya Rabe ya mike Yana Fadin

“Nagode tukuro ba laifin ka bane da na Kame girma na da baka samu zarafin fada min Haka ba ina maka murna Allah yasa hakan shine alherin.

Ya fice yayin da tukuro ya amsa da cewa

“Ameen in da gaske kake Rabe zan kira ka amma in kana son gani na ka daina zuwa Kai tsaye ka fara Kira na don bana son ana katsse ni Ina Rayuwa.

Tuni kuwa aka kammala gyara kamfunna tukuro ya soma Aiki ana fidda sumunti da takin zamani Babu laifi Yana samun kudi Kuma Haka akayi yadda yace ba zai zuba Yan Uwa ba Haka ya kwaso kabilu musamman yarinyar sa ta watsewa Linda itace ta kawo mishi yan Uwan ta sai fa daidai ku Yan garin

Abunda Yake Ranshi shine ta yadda zai kassara Al Mustafa da arzikin sa don Haka sai ya Kira wani shaid’anin abokin sa Wanda shine gwani a shige shigen mushirikai wato kwalo wani tantarin Dan iska ne Wai shi kwalo a bakin kwalo ne tukuro yaji yadda kwalo ya karya Wani abokin shi  da yayi mishi gadara saboda kawai ya Roki ya Ara mishi Riga zai je wankar wata yarinya shine akayiwa kwalo gadara shine ya fasa wurin wani Dan tsubbu ya Samo Aikin da zai yi don kawai a tsiyata wani. Kuma da Yake Allah gwanin adalci ne Kuma Mai bayar da sa a ga kafiri da musulmi Kuma Mai saukar da kaddara daidai da lokacin saukar ta sai ga burin kwalo ya cika don Haka tukuro ma yasha alwashin hakan.

Ya tashi motar shi har majalisan su kwalo Wanda suke wuni suna caca inda ya dauki kwalon a mota suka fice fit kamar fitar harsashin bindiga.

Sunyi nisa ne tukuro Yake duban kwalo Yana Fadin

“Kasan me kwalo? Wurin malamin ka zaka kaini Wanda yayi maka Aikin da ka Karya Dan audu don Naga Alamar ya iya aiki ko? .

Kwalo ya sheke da Dariya Yana fadin

“Kai in kaji iya siki ma Daya. Ai malamin nan yanzu Yan Abuja sun dafe mishi ba lallai ma mu same shi ba don yanzu malam ya zama done kaga Rigar da malam yake sakawa? Ai wallahi duk layin su babu Mai iya saka ta  don ya samu hatsi kam tsiyataku kala kala har wata Rana gareshi wacce baya Aiki Allah yasa  ba yau bane kace kana son shiga hurumin wani ko wani ya shigo hurumin ka ne shaid’ani mai Abun shaid’anci?

Shaid’an ya dubi kwalo da yake tambayar wani ya shigo hurumin sa ne ko kuwa shine yake son shiga hurumin wani?.

“Ka bari kawai kwalo wani shege ne ya shigo gona ta shine har da guxurin wulakancin mai daraja ta farko shine na tuna da kai da malamin ka  don sai na rama wulakancin da akayi min amma kuma naji kana fadar malamin naka ya lalo wulakanci gal a kwali.

“Ka Bari kawai shaid’an ai wannan malamin shine shaid’an kai ka ga motar da yake hawa? Bakauye ne fa da keke mai Bai iya shi ba Yasin amma a yanzu shine Yake juya mota BMW. Ai malam ya gane dala ya Kuma gane gizna wallahi kwanaki ma Ina jajayen matan Nan da ake cewa jan banza na can cikin nijar? Yasin can yaje ya dauko wata tsaleliyar yarinya gashi har kan duwawun ta gata kamar ka kwantala jini yayi tsartu.  . kai ai naira maganin wulakanci wallahi ka kuwa san mutumin nan a lokacin da yayi min sikin nan? Wallahi bakin shi dagajaja Yake da yawun goro Amma yanzu wai duk ya kile ya san makilin ya goge abin sa wulakanci kala kala waccan shekarar ma hajji yaje har da lika farin hak’orin makka .

“Kace malam ya samu duniya kwalo ni fa in ka barni ma zance wani fakiri fakiri ne Amma naji kana zana min shi a wani multi miloniya don ni Yama fini mallakar duniya kwalo.

“Ai shine nace maka yanzu Yan Abuja sun dafe mishi har Gida gareshi a can na Nan din ma an Rushe shi an dora bene Kai ai Ni na Rasa irin aljanu ko rauhanai da mutumin Nan Yake Aiki da su Wanda suka dayre mishi katara Aikin sa fa kamar yankan wuka Sha yanzu ne magani yanzu Babu sab’ani ko akasi shiyasa aka Gane shi sai dai Yana da tsauri kwarai don shi Aikin shi sai an kauce in dai ana son Aiki yayi nasara sai an shigo da Yar shirka da kauce hanya .

“Ai kwalo komai yace Zan iya in dai Aikin Nan zaici Ni da na San da zaman malamin Nan tuni ai da nazo na Zama yaron sa nayi kwanciyar aska ya koya min shaid’ancin Nima da yanzu ai na wuce Haka.

“Ba zaka iya ba tukuro don shi fa a gaban ka ma zai Kira aljani kaji ya amsa ya Kuma zo . Kwanaki fa Akan Ido na ya shuka dawa cikin wata kasa a gaban shi take ta fito ya soma zuba Mata Ruwa har ta girma ta fidda Kai ya tsigo kwayar dawa daga tushiya ya hada siddabarun sa . Kuma Naga yadda ya tsira itaciyar tumfafiya ya ciri furen ta . Sai dai kawai matsalar tsada Aiki da Kuma kaucewar da zai saka Mai son Aiki . A gaba na yace da wata mata sai taje kabarin Uban mijin ta ta tono shi ya kwanta da ita alhalin ita tace ko lokacin da sukayi aure da mijin nata Uban nasa ya juma da Rasuwa Amma Gayen malamin Nan sai da ya Bata wasu Ruwan tsafi yace ta kwara a kabarin Uban mijin zata ganshi har ma ya sadu da ita kafin Aikin nata yaci. Shine tace mishi Bata San inda kabarin Yake ba a take ya haska madubin siddabarun sa sai ga kabarin ya bayyana a cikin madubin ya Kuma nuna Mata a gindin bishiyar kukar da take makabartar unguwar su. In takaice maka labari Haka matar Nan ta Debi dare ta je makabartar Nan a inda ya haska Mata kabarin Uban mijin Yake taje ta kwara Ruwan Nan ta Kuma tone kabarin sai ga Uban mijin nata da ya Rasu tun kafin ma a Haife ta don shi kanshi mijij nata Uban nasa ya Rasu ne tun Yana da shekara Tara Amma sai gashi hatsabibin mutumin Nan ya taso shi .

Tukuro ya dubi kwalo da sauri Yana Fadin

“To ya akayi kwalo? Shi Uban mijin ya sadu da ita matar ne? Kuma ita wannan Mata me take so ne da har tayi wannan kasadar?.

Kwalo ya kwanta a kujerar motar Yana Shan Rab’ar sanyin AC Yana Fadin

“Uhum kasan su Mata Basu da wata matsala da ta wuce kishiya da son su mallake miji abinda kawai take so Wai ta mallake miji Kar Kuma yayi Mata kishiya ya Zama sai abinda tace zaiyi ko uwar sa Bata Isa ya Gayar ba sai tace gaishe ta shine fa ta yarda ka dai duba yadda suke tsoron makabarta Amma har da karfin Halin tona kushewa ta kuma kwanta da gawar Uban mijin ta Kuma Ina Mai tabbatar maka da Aikin ta yaci Tana can tana juya mijin ko Uwar sa baya duba sai tace ya dube ta . Ai mutumin Nan ya Sha kwana wallahi ya Sami duniya.

Tukuro Bai iya cewa komai ba har suka iso kofar wani tangamemen gida Mai kofar get yayin da suka hango wata katuwar mota ta kamfanin pord fara tas a jikin lambar an Rubuta malam malam 3.

“Nan ne Gidan Nashi kwalo?

Shaid’an ya tambaya don hakikatan gidan Nan ya keru Babu karya tamkar gidan wani Dan majalisa.

“Nan ne ga ma motar shi Nan ga Alama kana da sa a mutum mutumi na dubi flat number shi malam malam 3 kaga ta uku ce ma wannan pord din ita BMW1 ce ko wacce ce 2 din ? Ai fa duniya ga na ku malam malam duniya sabuwa.

Tukuro ya fito daga motar inda kwalo ya tura kofar get din wani buzun Mai gadi ya taso Yana budewa Yana tambayar shi wurin Wanda yazo. Ya ce mishi malam malam yazo gunsa. Da sauri buzun Mai gadi ya auna a guje ya nufi wata kofa inda su kwalo da tukuro suka soma karewa gidan kallon kurullah har buzun Mai gadi ya dawo yayi musu jagora zuwa wani seat room ya saukar da su aka aje musu Ruwa da lemu buzu ya fice

Kamshin turaren da suka ji Mai masifar Hawa Kai Shi ya sa su juyawa inda suka ga malam Yana tahowa duk da ya soma kwana biyu Amma hutu da yanayin kayan jikin sa zasu tabbatar maka da lallai malam ya kwanta dala .

Da murmushi ya ke duban kwalo Yana Fadin

“Kai mutumin dama kana Nigeria? Sauka ta kenan daga Abuja aka ce nayi Baki yanzu nake Shirin shigowa da mota ta na  cewa Mai gadin duk Wanda yazo nema na ace bana gari sai ga ku Rabon dai ba Zan ja ku k’asa ba don gaskiya Ni da sauraren wani ko wata sai Bayan kwanaki biyar don Ina son na Karasa wani aiki ne sai ga ku.

Kwalo yayi murmushi Yana Fadin

“Allah ya kyauta aikin malam aboki na na kawo Ashe muna da sa a da yawa ne ayi Mana afuwa ya malam .

Malam ya mikawa tukuro hannu Yana fadin

“Sannun ku da zuwa fatan kun Sha Ruwan ko a kawo muku abinci ne?.

Da Sauri tukuro yace Alhamdulillahi sun gode.

“Masha Allah meye matsalar?

Malam ya tambaya yana duban tukuro wanda ya Amsa da cewa

“Wato malam wani ne yayi min wulakanci mai daraja ta farko shine na kawo shi wurin ka da son na Rama abinda akayi min . Uban gida na ne da nayiwa bauta da wahala amma da ya tashi wulakanta ni bai biya Ni hakki na ba sai ma ya siyar da kamfanin da nayiwa Wahalar shine nake son na dauki fansar tsiya ta Shi ya zama Rigar sakawa ma ta gagare shi na zama nine Uban gidan sa ko Ruwan da zai Sha sai na Bashi.

Malam malam ya gama suraren tukuro kafin ya aje ajiyar zuciya Yana Fadin

“Aikin karami ne Amma an fada maka Aiki na Yana da tsada ba kowa ma makewayi Aiki ba ? To aiki na sai Wanda ya tanadi kudi Kuma Ina da Sharadi Ina da k’a ida shin ka shirya wa aiki na? Ka kuma shiryawa sharadi na?  sharadi na fa in na fada ya Zama Dole a cika shi duk tsananin sa duk tsaurin sa don ba a cewa ba a iyawa don gardama ga sharadi na har haukacewa anayi.

Da sauri kwalo ya amshe da fadin

“Zai iya ya malam shima Yana da Dan Ruwan Shan sa saura kawai a fada mishi kudin Aikin da Kuma Sharadin Amma in Sha Allah Babu abinda zai gagara don shima shaid’an ne a fagen shaid’anci.

“To Babu damuwa ya sunan malamin ?

Malam ya tambaya Yana duban tsakiyar idon tukuro.

“Sunana tukur .

“Malam tukur zan maka tambaya wacce tana cikin Sharadin Aiki na Kar kayi min karya ko kayi ma zan Gane ka fada min gaskiya kawai. cewar malam Wanda ya zuba yashi a saman wani faifai Yana zanawwa da yatsun hannun sa Yana wani zane mai kama da gida gida.

“Malam tukur ka tab’a yin sata?

tukuro ya dube shi Yana Jin wani irin gingirim.

“Eh na sha yi gaskiya  malam amma dai ba sosai ba.

“Zina fa ? Ka tab’a yi?

“Eh itama muna dan tabawa malam.

“Kisa fa ? Ka tab’a kashe mutum? Da sauri tukuro yace

“A a malam ko maciji ban tab’a kwashewa ba.

“To zunubin naka ma ba Mai yawa bane Babu damuwa yanzu abinda za ayi zaka kawo min kayan sawar shi Wanda kake so muyiwa Aikin kamar Rigar da ya cire da hular da da takalmi da Kuma Wanda zai saka ma ana Wanda ya saka sukayi datti da Kuma wankakkin da zai saka . Sai Kuma Aikin da zamu baka shine ka nemi mahaukaciya ka kwana da ita  ka kuma shafo dattin tarayyar da kukayi da mahaukaciyar ka kawo mini Sai kudin aiki na zaka biya ni dalar amurka ba da naira ba inda zaka biya ni dala dubu Sha biyar in ka buga su zuwa kudin Nigeria zasu baka adadin milyoyin in ka Shirya ina sauraren ka.

Malam ya fada Yana share yashin faifan da Yake gaban shi ya dauke shi ya mayar a cikin wata wadrob

Suka mike tukuro yana Fadin

“In Sha Allah malam kamar yaushe zan same ka?

“Eh to Ina Nan har Nan da kwanaki biyar kafin na koma Abuja.

<< Azurfa Da Zinari 89Azurfa Da Zinari 91 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×