Skip to content
Part 91 of 99 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

“To a saurare mu zuwa jibi zan dawo ai na Shirya ba zan koma ba.

Sukayi mishi sallama tukuro yana karbar lambar wayar sa da alkawarin kiran sa.

“Tabdijan aikin ka yazo da babban aiki shaid’an neman mahaukaciya ai asirin mutum ne zai tonu don zai sha kwaratsi.

“Kwalo ni wannan bai dame ni ba irin yadda zan samo kayan Al Mustafa .

“Haba Kar ka bayar da maza Mana shaid’an? Ai samun kayan shi ba zai bada wani aiki ba ka manta gidan sa Babu kowa ? Ko ni zan iya haurawa na Sato maka su kar ka damu ni nafi Jin inda zaka nemo mahaukaciya ka kwana da ita.

“Shima ba zai yi wahala ba ko gidan mahaukata ai zan iya zuwa na toshe bakin wani jami I kaga komai ya tafi daidai Kai dai muje muga yadda za ayi ka samo min kayan.

A Ranar kuwa kwalo ya shirya yadda zai haura gidan Al Mustafa Bayan fitar sa gidan da yamma ana dab da magaruba kuwa kwalo ya samu nasarar haurawa ya Kuma debo kayan Al Mustafa kala biyu wankakkin da wanda ya cire masu datti ya Kuma dauki hula da takalma ya Kuma haurawa ya fice duk da kwalo ya so ya Dan zaga cikin gidan ko akwai abinda zai dauka amma Rashin lokaci da gudun tonuwar asiri yasa ya fito Baki alaikum

Ya ajewa tukuro kayan Wanda ya soma tafawa kwalo kafin ya jawo kudi ya Bashi Yana fadin

“Gaskiya aikin ka yayi kyau ko kawai ma na baka kwangilar nemo min mahaukaciyar da zamuyi Aikin Akan ta kwalo?.

Kwalo ya cabe kudin Yana Fadin

“Ina ne ma kuwa naga mahaukaciya ? Ya dafe kanshi Yana son tunawa Amma ya kasa tunawa inda tukuro yake Fadin .

“Tunana dai mutumi na ka karasa cin kudin gaba Daya.

“Kai wallahi ta shige min shaid’an amma yau din nan in sha Allah zan tuna gobe gobe zan zo maka da details . Ya fada Yana tulla kudin sa sama Yana cabewa.

Shekarun Kaisar biyar a duniya mahaifin sa ya shawarace ni Akan yana son ya fidda yaron waje yayi karatu amma nace mishi yayi hakuri y Bari ya Kai ko shekara goma ne Amma yanzu idan ya kaishi a wannan shekarun ton zai tashi da komai irin na can ne don inda yaro yayi kuruciya Nan ne Yake nuna asalin sa da wannan Al Mustafa ya yarda sai dai ya fada min wata magna me wacce ta tayar da Hankali na matuka gaya. domin kuwa ya fada min ya kusa mutuwa da gaske shiyasa Yake son yaga Rayuwar Kaisar ta in ganta.

“Kar kace Al Mustafa rai da Rayuwa duka na Allah ne Kuma Kaisar nayi maka alkawarin in dai ina numfashi kai ko bana Raye Ina da tabbacci Akan Aliya ba zata bar Kaisar ya zama koma baya ba don Kai da kanka ta fada maka tana kallon Kaisar a gudan jinin da y fito ta tsatson ta bare kuma ni din in Sha Allah zan tabbatar maka da burin ka kowa jiran tasa Yake.

“Haka ne Ibrahim amma ka Sani wannan maganar daga k’asan zuciya ta take fita ba daga Baki na ba fata na ka Taya ni da ADDU AR Ubangiji ya azurta Ni da cikawa da I’mani don haka a yau ma zan danka maka dukkan dukiya ta ta zama Amana gareka ka ci gaba da juya ta kana kulawa Kaisar da ita idan Allah yasa Yana da nisan kwana sai ka bashi idan Kuma Bashi da nisan kwana kamar ni da mahaifiyar sa ibrahim kaci Gaba da juyata ta zama taka abinda kawai nake so daga gare ka shine dukkan mutanen da ka San Ina tallafawa ka ci gaba da tallafar su Kar ka bar ayyukan alherin da nake  ko da Kaisar ya yi nisan kwana ga Rubutacciyar takarda zan bari ibrahim na bar maka kamfani Ni na takin zamani halal malak Haka kuma dukkan albashin da nake biyan ka duk wata da abinda nake baiwa Aliya a ci Gaba da baku amma sauran kaddarori na na Kaisar ne na Kuma bar Amanar sa a hannun ka don da gaske nake maka Rayuwa ta ba zatayi tsawon da zan Rayu da Kaisar ba ibrahim idan ya Rayu ka dora shi akan harkar kasuwanci musamman kamfanin sa ya Rike ya kuma taimaki Al umma da marayu da Mara’s galihu ka nema mishi mata ta gari ka Kuma nuna mishi dangin Uwar sa yayi zumunci da su amma dangi na Ibrahim kar ka nuna mishi su don in suka san shi zasu saka Rayuwar sa a garari Allah ya Sani ban yanke zumuncin su ba sai don Ina son Kaisar ya tsira da Rayuwar sa Kar su baddala mishi lissafi saboda daudar duniya to gara ya Rayu a gareka kawai Amma Yan Uwa na suyi tasu Rayuwar yadda muka bar shi ni da mahaifiyar sa shima Allah ya azurta shi da Ya’ya masu albarka.

Ban San maganganun Al Mustafa sun tayar min da hankali ba sai da naji hawaye suna bin idona sai da naji Yana bani magana ne na Ankara da Halin da nake ciki.

“Kar fa ka damu Ibrahim zanyi wata hikima ne don ba zai yuwu  muyi ta zama a duniya ba yadda muka zo haka zamu koma amma Allah ya Sani ban tab’a Jin hakan ba sai a wannan lokacin don haka kamfunnan bauci Babu Wanda ya San da su sai ni sai kai Sai Allah to dama bana son yan Uwa na su sani ka barsu a hannun ka . Kamfanin da Yake Lagos kuwa sune kawai suka Sani to suma din Ina d hikima akan su kaga takardun su ban ka Rike su wurin ka zuwa gobe zan Tara su na Kuma tabbatar musu da na siyar da kamfanin na karbi kudi na in yaso sai na San yadda zanyi da  su Amma ka tafi da su can bauci ka Aje su wurin ka kai kadai na yarda da kai ibrahim na kuma ke jin Kaisar zai tashi kamar a gaba na .

Na taho bauci cike da sanyin jiki don maganar Al Mustafa ta keta zuciya ta da rauni Na. nazo bauci na kuma sami Rikicin Kaisar Wai shi a Dole Sai na taho da shi wurin dayan Daddy shi wurin dayan Daddy zai zo. Kuka Yake bil hakki Bai yarda na barshi ba sai da kyar Aliya tayi mishi hikima inda na taho Kuma ina Kara kokawa ko dai maganar Al Mustafa ce ke son ta tabbata? Yaron nan Kaisar Bai tab’a kewar mahaifin sa irin haka ba. Sai hankali na ya kara tashi har nake Jin kamar ba zan koma bauci na Samu Al Mustafa da Rayuwa ba amma da Yake Rayuwa tana hannun Allah sai gashi na riske shi Amma kuma Yana cike da wani irin zazzabi da ciwon ciki ban tsaya ba na dauke shi muka nufi asibiti inda duk wata jarumta da karfin hali na ya Kare domin kuwa Al Mustafa ya Gama kwace tunani na bani da abinyi da ya wuce ADDU AR.

Yaya Rabe ya iso gidan tukuro duk da kashedin da ya yi mishi na kar ya Kuma zuwa sai ya Kira shi Amma saboda matukar jigatuwa da Yaya Rabi u yake ciki yasa Bai tuna da kashedin ba ya taho kai tsaye saboda zuwa wannan lokacin komai ya karewa Yaya Rabi u abincin da za a ci ma ya soma gagara shine yaxo ko gadi ne tukuro ya Bashi.

“Tukur kayiwa Allah ko koma wane irin Aiki ne ka bani zanyi wallahi a yau Babu ko kwayar dawa a gida na gani da k’ana Nan yara na je wurin Al Mustafa kuma baya nan wayar sa ma akashe take gani a gaban ka tukur na kaskantantar da kaina ka dubi Allah ka agaza min .

“Nifa bana son irin wannan Abun Rabe yanzu in na baka ba zaka jawo min wani ma yazo min Yana min magiya ba? Kuma in ina badawa nima ba zan zamo kamar kai ba Babu mai Tayar da wani,?.

“To ka taimaka mini da Aiki a kamfanin ka ko na gadi ne don girman Allah.

“Gaskiya ba zan iya baka Aiki a kamfani na ba Yaya Rabi u ka manta na San yadda ka munafunci Al Mustafa? to bani da tabbas din Ni ba zaka munafunce ni ba ungo dubu daya gata kaje ka siya musu garin kwaki zan duba na gani idan da yuwuwar na dauke ka gadin don ko shi Ina kokonto don zaka iya hada baki da wani a cuce Ni kai Yaya Rabe ka nema a gaba kawai gaskiya ba zan iya kawo ka kamfani na ba don ban yarda da kai ba  I’manin ka ma na Wahala ne da ka gyagije tsiya ce biye a Bayan hakan.

Yaya Rabe ya soma magiya tamkar zai kwantawa tukuro shi kuma yana kara kirne fuska yana hura hanci amma ko ta tafasa sauke Bai ce mishi ba sai ma hayakin tabar wiwin sa da Yake bankawa inda kuma kwalo ya Fado gidan a guje yana haki yayin da Yaya Rabi u Yake ta magiya da son tukuro ya taimake shi.

“Ya akayi ne kwalo ta samu hala naga sai haki kake,?

Ya dubi Yaya Rabe ya kuma dubi tukuro Yana Fadin.

“Sallami gayen Nan akwai news

Tukuro ya kuma zaro wata dubu Dayan ya mikawa Yaya Rabi u Yana Fadin

“Jeka da Allah zan kira ka zamuyi magana Rabe.

Yaya Rabe ya karbi kudin Yana mikewa Yana Jin ciwon abunda tukuro yayi mishi inda ya gane dukkan matsalar sa ta Samo ASALI ne daga cin hakkin marayu Wanda Al Mustafa ne farko sai Kuma cin Amanar da ya Kuma yiwa Al Mustafa sune suke wahalar da shi da dawainiya da shi amma in yace dama ya Sani Yake bai yaudari Kansa ba? Sai yaji lallai nadama da kuskure suna nan damfare ga masu son Kai da son zuciya.

Yana ficewa kwalo yacewa tukuro

“Albishir din ka shaid’an?

tukuro ya Kuma Jan hayakin tabar wiwin sa cike da gwanancewa yace

“Goro fari kwalele kwalo meye,?

“Yanzu na Samo maka mahaukaciyar da zaka kwana ka hantse da ita mutumi na taso muje ka ganta kuma wallahi full uption ce mai kuruciya sosai wacce zaka San mace ce ta sosai bana zaton ma ba budurwa ba ce,

Tafe muke a mota Aliya tana fadin don Allah nayi sauri kar jaririyar nan ta rasa Rayuwar ta. Tun ina ganin wautar ta har na soma tausaya Mata don na san wanda Bai haihu ba yafi wanda ya haihu son Ya’ya shiyasa nayi mata uzuri har muka Isa garin Jos inda muka tara’s da mahaukaciyar nan daurawa kafafuwan jaririyar nan igiya  tana shirin zarga ta wani wuri ne.

Da sauri Aliya ta fito mota tana Fadin

“Ka gani ko daddy? Dubi yadda take zarge yarinyar nan Allah yasa ba Rijiya take nufin zabaro ta ba . Don Allah Daddy taho ka agaza mini Kar ta kashe ta.

Na fito da sauri don Nima naga wauta ta ta Rashin ceton Rayuwar yarinyar nan har gashi mace tafi Ni tunani na abinda zaije ya dawo gashi kuma munzo daidai tana Dab da salwanta Rayuwar yarinyar.

Fitowa ta yasa mahaukaciyar ta dago kanta tana ganin mu ai kuwa  tace da wa Allah ya hada Ni ba da Kai ba? Ashe tunda tukuro ya soma keta mata haddi babu sauran shiri tsakanin ta da namiji duk namijin da ya kusanto ta zata yi mishi ature da Ruwan duwatsu sai kuwa ta soma auno min duwatsu tana makale da jaririyar har sai da na bacewa ganin ta kafin Aliya tayi mata hikima tana bata abincin da muka Rike har tayi nasarar karbar yarinyar da ko cibi ba a yanke Mata ba sai ma shacin dauri da jikinta yayi har wani wurin ma ya tashi .

A cikin sambatun da mahaukaciyar take ne take fadawa Aliya Wai Rijiya zata zura jinjirar yarinyar ta debo mata Ruwa in Kuma ta Gama debo Ruwan zata saka ta a tukunya ne ta dafa tayi farfesu da ita.

Aliya har hawaye ta zubar mata don tausayi ita tana neman haihuwar Ido Rufe Bata samu ita kuma ta samu tana Shirin kashewa duk da Aikin ba na hankali bane.

Aliya tana tare da ita tana son tayi Mata hikima ta wuce inda wani mutum yaxo wucewa Yana Fadin

“Kai gara kuwa da Allah ya kawo ki baiwar Allah Yar Uwar ki ce halan? Don Allah ku taimaki Rayuwar jaririyar Nan in kuwa ba Haka tsab Zata Kashe ta jiya fa Zama tayi Akan ta Wai kujera ce sai da aka turo wani namiji kafin tabi shi da gudu ta manta da Zaune Yar saboda Bata son maza suna kusanto ta kuma Babu ko shakka Wanda yayi Mata aika aikar nan shine ya saka Mata kyamar maza don lami lafiya matar Nan take kwana a makarantar Nan Amma muka wayi gari muka ganta da Uban ciki Rikiki a Gaban ta har gashi ta Haife . Dama ance ana ganin wani mutum Yana kawo Mata abinci Babu ko shakka dama nufin sa kenan ya keta Mata Haddi yayi Kuma ya huta koma ya cimma burin shi na neman duniya.

<< Azurfa Da Zinari 90Azurfa Da Zinari 92 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×