Skip to content
Part 95 of 96 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

Su Daddy suka amsa da ameen ameen suna Mamakin Al ummar mu a yau da suke son kawunan su har Babu Ruwan su da tuna Ranar gobe Alkiyama

Malam Yayi Rubutu ya wanke da Ruwan zamzam ya Kuma hada da garin magarya da da lemun tsami ya bawa su daddy Yana Fadin

Yasha wannan tsayin kwana arba in ya zama Ruwan Shan sa wanna Kuma yayi wanka da shi shima na tsayin kwana arba in din in Sha Allah kowane irin sihiri ne a jikin sa zai Kare Kuma wannan maganin sai ya shekara arba in Bai Kare ba kuma da izinin Ubangiji ba dai mutum ba sai dai ALLAH .

Su daddy sukayi mishi godiya sosai suna aje mishi sadaka sukayi mishi sallama

Tun da Daddy ya bashi maganin ya soma Sha Al Amarin Ubangiji ya soma sauka Akan alabo Wanda Yake wuni Yana Kiran wayar ladidi wacce take ta wankar kudi Amma daga Ranar da ya soma Shan maganin Nan Bai Kuma tunawa da wata ladidi ba abinda Kuma ya Bata tsoro ganin anyi kwana uku bai Kira ta ba ta soma auna mishi Kira inda Yake duban lambar da son ya San mai kiran Amma ya ki dauk sai da Kaisar yace mishi ana Kiran shi fa kusan 55 missed call.

Ya daga Kiran inda ladidi ta soma shagwaba tana Fadin me tayi mishi .

“Wa ke magana Wai ? Ya fada da murya Mai kauri abinda ya tsorata ladidi ta ce itace.

“Kece wa Wai da kike jera min Kira Haka?

“Ladidi ce fa sweetie Wai yau Kuma zolaya ta kake ?.

“Wace ladidi? Ya tambaya yayin da jikin ta yayi Sanyi tacw mishi ta gidan mandiya sai kawai yaja tsaki yana Fadin Kar ki kuma Kira na sakarai da ke meye kike ta Kira na ? Kinga Ina Shiga shirgin ki ne?.sai da nacewa Fati ta Hana ki shigowa gidan Amma batayi hakan ba. Ya Rufe ladidi da masifa kafin ya kashe wayar sa ya bar ta d Baki sake gaban ta Yana faduwa don ta gama gane Aikin ta yasha ruwa.

Alabo ya tashi Yana ta fada Kaisar yana tambayar shi abinda akayi Yana fada mishi Ladidi da irin kin da Yake mata itace fa take jera mishi missed call.

“A haba aboki na kai fa kace auren ta kake so Kuma yanzu kace ba Haka ba?.

Alabo ya jiyo da sauri Yana Fadin

“Allah ya sauwake Kaisar me zanyi da wannan matar mai kama da agwagwa? Yaushe nace Haka ? kuma da wa nayi ? ni fa ban San zaman da nake a gidan Nan ba ma .

Ya fice da sauri ya nufi cikin gida inda ya iske Fati tana wa khalifa wanka ya dube ta Yana Fadin

“Wai zaman me muke a gidan Fati,? don Allah tashi muje gida .

Ya fada yana dauko khalifa yayin da hawaye ya soma bin idon Fati wacce take fadin

“Muje gida muyi me kuma Yaya Alabo? Ai zama tsakanin mu kuma ya kare .

Ya duka a gaban ta yana kallon ta kafin yace

“Me ya karar da zaman mu Fati,? Meye kike kuka kuma? .

“Yaya Alabo Kaine kace ka sake ni har fa gaban Daddy kazo ka kawo mishi takardar kace ladidi kake so baka Sona .

Ya aje mata khalifa yana kallon ta da wani irin tashin hankalin kafin ya mike ya isa gaban haj Aliya wacce take jin  su day kallon su Yan Fadin

“Mama da gaske ne abinda take fada? Me Yake faruwa dani ? Don Allah mama kice MAFARKI nake ta Yaya zan iya sakin Yar Uwa ta mama ?.

“To alabo sai dai muyi hakuri mu Duka Amma kaddara kam ta sauka alabo ka saki Fati saki har uku.

Ya kama Kansa da yake Jin Yana Shirin tarwatse wa idanun shi suka kada jajir ya soma zubar da hawaye Yana Fadin.

“Mama ? don girman Ubangiji ku yafe mini wallahi ban san nayi hakan yanzu ana nufi Babu sauran zama tsakanin mu da Fati?.

Daddy ya shigo gidan ya Samu alabo da wannan bayanin ya cika da mamaki yana fadin

“Alhamdulillahi Uba na Alhamdulillahi jibi ne Daurin auren ka da ladidi kayi hakuri komai kaddara ne.

“Daddy ka taimaka mini bana son ladidin Nan ban San abinda ya faru dani ba wai nine na saki Fati saki har uku Daddy da wane idon zan dube ka?.

“Kar ka damu Allah ya kaddara haka tuni kuma nayiwa Fati madadin ka da Kaisar kai kuma akwai Yar gidan Alh sule da mijin ta ya Rasu zainab tana Nan ko haihuwa batayi ba kaje ka same ta ku daidai ta idan Fati ta Gama idda tare Zan hads auren ku insha Allan.

Wani matsiyacin kishi ya harde zuciyar alabo Jin Wai Daddy ya Bawa Kaisar auren matar sa Fati sai yaji Bai tab’a tsanar mutum irin tsanar da yayiwa Kaisar ba . Kai sai yaji ma dukkan kishin da ake magana duniya Babu ya nashi .

“Daddy? Kaisar ne zai auri matata ? Daddy Kar kuyi min Haka don Allah idan akwai gyara s gyara Mana.

“Babu wani gyara Uba na wannan shine gyaran tunda baka son ladidi shikenan Amma ko ita in Halin girma zamu nuna to ba zamu kaucewa auren ta ba tunda dai aure kuke nufin yi to Amma tunda lamarin nata babu tsoron Allah zan sanar dasu ka fasa abinda muka Basu Kuma mun bar musu.

“Daddy Yaya zanyi ?

“Hakuri zakayi Kuma ba na fada maka ga zainab Yar gidan Alh sule ba? Ka shirts kaje misau ka baww su Yaya halilu da yaya Hajara hakuri don sun dauki Al amarin da zafi sosai.

Kuka sosai alabo Yake ya tashi gaban Daddy Yana maimaita kalmar Inna lillahi wa inna ilaihir Raju un wannan mata ta cuce Ni yadda ta cuce ni Allah ka saka min yadda ta Yankee min farin ciki Allah ka yanke mata. Sai abin nashi ya zama kamar zautuwa amma Dole Daddy yayi mishi ADDU AR Allah ya Basu ikon cin jarrabawa.

Ladidi ta kadu jin maganar auren su ta watse inda uwar ta ke Fadin

“An lalata mana aiki Amma sunyi karya wallahi sai kin shiga gidan can ladidi sai mun Shana da daular da yarinyar can take Mana Barazana har da aike Mana da sauran abinci da wasu tsummokara Bari ki gani in tashi nice har gidan uwar bori sai na dangana wallahi.

Yaya Alabo durkushe a gaban mahaifiyar sa Yaya Hajara Yana kuka Yana neman gafara.

“Ni fa ai bakayi mini ba ba gashi ba ka saki har wani zai dauka,? kai Kuma ai gaka ga ladidi Nan wannan matar daga ganin ta ta kusa wari na don ba yarinya bace Amma kace Kai ita kake so a kalle ka ma ace wannan tsarar uwar taka ce matar ka ba kaji kunya ba?.

“Inna ki yafe mini wallahi ban san nayi duk wadan Nan abubuwan ba ina ta Alla ya isa ga duk Wanda ya shiga tsakanin mu da fati Inna kinji wai Daddy Kaisar zai Bawa Fati?.

“To kai kayi mata saki uku sai ace ba zatayi aure ba? Kayi ADDU AR Allah yasa hakan shine alherin ku don da Rabo Mai kashewa gara mai Rabawa kaje can ka haifi naka Ya’yan itama ta haifi Rabon da ya Raba ku na gaya maka amma  in ka yarda kenan in Kuma kana da ja Bismilla.

Baffa Halilu ma da ya dawo ya Samu Alabon hakuri ya bashi ya kuma ce kaddara kenan Dole Kuma Bawa ya yarda da kaddara in dai shi din musulmi ne.

“Hakuri fa ai ya zama Dole malam sai dai ayi fatan Alla ya tsayar a wannan . cewar Yaya Hajara.

Da kyar aka samo kan shaid’an bai wuka kiyama ba amma fa Yana Jin jiki don yaji shigar wukar Nan

Aka samu ya dawo Kan Doka da oder inda aka fito da keena da Nadiya hukuma na son tuhumar su dalilin da yasa Nadiya take son kashe shaid’an.

Aka fiddo su zuwa asibitin da shaid’an yake Wanda Yake duban Nadiya da mamaki Amma abin haushi baiji Yana son tsanar ta ba sai ma wani irin so da Yake ji Yana mata. Ita kuwa Babu abinda take so sai ta karasa kashe shi.

“Wacece ke da kuma dalilin ki na son kashe mutumin nan?.

Shaid’an ya dakatar da dan sandan da yake tuhumar Nadiya a gaban Shi.

“Officer a bar maganar nan na kashe case din nan yarinyar nan yarinya ta ce tona wani Abu daidai yake da tona sirri na kuje kawai ku bar su komai ya wuce.

Dan sandan ya Ansa a girma me yana shirin ficewa amma Nadiya ta tsayar da shi tana Fadin

“Dakata officer don ko ya kashe maganar nan ni zan tayar da ita kuma idan ba bin kadin maganar nan kukayi ba to Ni din xan cika kudirin da nake da shi a kansa na ganin na kashe shi har kiyama don haka ne kawai zanyi na hutawa abinda nake ji a kirji na Amma matukar mutumin Nan Yana yawo a duniya to in ban kashe shi ba ni kuma zan mutu ne.

Shaid’an ya dubi Nadiya yana murmushi yana Fadin

“In dai kisan soyayya zakiyi min zanyi Farin ciki da haka .

“Ban tab’a kin wani Abu irin kin da nayi maka ba ka Rike wannan .

“Me nayi miki ?

Ya tambaya Yana kallon ta.

” Me ka sani akan wata  mahaukaciya da tayi Rayuwar ta a kan bola take kwana a makarantar Bokon ta can karshen gari?.

Shaid’an ya zubawa Nadiya Ido yana kallon ta da wani irin tsoro da tashin hankali.

“Nice sakamakon mugun Aikin da ka aika mata . Nice sakamakon kisan Rayuwar da kayi mata kana zaton ba zan bayyana a duniya na Rama Mata abinda kayi Mata ba? To yadda na fada maka haka nake nufi wallahi nice ajalin ka  sai kashe ka ne zan huce  haushin da nake ji naka .

Dan sandan nan ya dubi Nadiya yana fadin

“Wannan maganar da kike fada itace zata daure ki dauri kuma irin na Rayuwar ki don haka dole a Rike yarinyar nan honorable. Ya fada yana duban shaid’an.

“Kar kuyi mata komai amma dai zan so na san wanda ya sanarwa yarinyar Nan wannan sirrin da na tabbatar Yan adawa ne suke  son batani don sunga siyasa ta taho don haka kuje da yarinyar nan ta nuna muku wanda ya sanar da ita wannan maganar.

Abdulhameed yana zaune Haj Laila tana ta masifa tana fadin

“Wai dama haka yarinyar Nan take  duk ka tashi hankalin ka Akan ta? Ta Yaya Kai din dan gidan daraja ace ka k’are da auren Yar mahaukaciya ? Ba zai yuwu ba wallahi wannan ai abin kunya ne ace surukar ka mahaukaciya ce ai zaka kunya ta mu ne ni da Uban ka don Haka gara kawai ka tsayar da Hankalin ka a inda  ya kamace ka tunda Sarena ta yarda zata aure ka a Haka dama Kaine baka yarda ba irin son da yarinyar Nan take maka ai ban zaci akwai wata mace da take son ka irin son da Sarena take maka ba.

“Momy Ni fa bana son wata Sarena a daina ma min zancen ta Ni fa yarinyar nan ta gidan iro GIDAN ita nake so ba hauka ba ko cuta gareta Ina son ta don in na aure ta Ina da tabbaccin zanga Ya’ya na kuma ni kadai na san wacece ita bana jin akwai wata mace da zata Kai min Nadiya don haka zan koma gidan su Ni kudin da na fanshe ta ma na yafe Mata su albarkar soyayyar ta a Raina wallahi momy  ba zan dawo ba sai na tabbatar da an bani auren ta dama iron yace ya bamu Daddy ne Bai yards ba to Ni momy na tafi in ma Baki ganni ba Ina can gidan na su .

Ya mike ya wuce Haj laila da distinguish Mukhtar Biro wanda ya saki baki Yana kallon yaron wanda saura kadan yace y haukace.

Motar abdulhameed na tsayawa motar yan sandan na shigowa dauke da Nadiya tare da keena da kuma jami an hukuma don tafiya da Alh iro.

<< Azurfa Da Zinari 94Azurfa Da Zinari 96 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×