Skip to content
Part 97 of 99 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

Yakumbo Halima ta iso gidan iro cike da sanyin jiki  haj Aliya tana tambayar ta zo bikine?.

“Yaya Aliya Ni fa ba biki nazo ba dubiya nazo asibiti Ina yar wajen makociyar nan tawa da nake fada miki ta hadu da lalurar tab’in hankali har ta gudu ta bar gida  an neme ta ba a ganta ba ta  Bata ba a san inda take ba? to jiya muka Sami labarin an ganta bana shekara da shekaru amma  ana cikin halin ciwo ana ta bauta hauka take tuburan baiwar Allah shine akace an ganta  tana nan asibitin masu tab’in hankali shine muka zo duba yarinyar nan Baki ga yadda ta koma ba Yaya aliya abin tausayi abin kuka Ni Halima wannan Rayuwa da wahala take Allah ka yi Mana kyakkyawan karshe da kyakkyawar makoma. Sai Yakumbo Halima ta soma kuka tana share hawaye.

Nadiya da taji zuwan Yakumbo Halima ta fito don ta tarbe ta don har abada ba zata tab’a manta Yakumbo Halima ba ko ba komai ta ta koyar da ita abubuwa Masu yawa na tarbiya.

Ta Rungume yakumbo Halima tana dauke mata kwallar idon ta inda haj Aliya ke fadin

“Sai Halima haka kaddarar Ubangiji take ga baww matukar an zana mishi ita to sai ta tabbata an dauke Al kaluma takardun ma sun bushe muje ki Raka ni na ganta ai mai kokko ta wuce nan a wuri mu muje a kai musu abinci na Kuma duba ta Allah yasa kaffara ne ya bata lafiya.

Nadiya da taji maganar mahaukaciyar Nan da ake sai taji wani Abu a zuciyar ta ba komai take ji ba sai wani yanayi da bata san ko meye ba.

Haka mama da yakumbo Halima suka fice zuwa asibiti suka bar Nadiya cike da wani irin sanyin jiki.

Shaid’an da yake kwance asibiti sai Al amarin shaid’an ya zama kamar hau domin kuwa sannu a Hankali sai wuta ta soma lashe komai na kaddarar shaid’an inda kamfanin sa ma wuta ta tashi aka Rasa komai ko hakki ba a dauke ba sai ya zama kusan kullum sai wuta ta tashi a wani wuri da shaid’an ne mallakin sa . Kan kace me? duk wani Abu da shaid’an ya mallaka sai da wuta ta lashe shi hatta da kayan tukuro na gidan shi sai da wuta ta lakume komai Sai fa na jikin shi da wanda suke asibitin.

Tuni ciwo tukuro ya dawo sabo saboda jin wuta ta lashe mishi komai sai ga firgici da fargaba ya haddasa mishi ciwon da yayi gaba da rabin jikin shi  wato fralays ya koma sai an tayar sai an kwantar.

Kaga rayuwa.

Wayoyin sadarwar da suke dab da kan honorable tukuro shaid’an kusan kai uku duka suka dauki tsuwwa a tare a lokaci daya yayin da tukuro din yake dafe da kanshi wanda yake jin tamkar zai tarwatse saboda dukan da maganganun yarinyar nan sukayi mishi .

Ya manta da babin wata mahaukaciyar da yayi dabdala da ita  ya manta da wanzuwar ta a duniya amma a yanzu sai ga wani Abu da yake shirin faruwa.

Yanzu yarinyar nan da ya gama hadawa yawu Yar mahaukaciyar nan ce har gata taxo tana kalubalentar sa? Anya kuwa ba hadin baki bane don a gurguntawa siyasar sa ba? babu ko shakka akwai hadin Baki tunda dama ko da ya fito yaci karo da Yan adawa wanda suke ganin Bai kai ba idan wannan maganar ta bayyana cewar ya nemi mahaukaciyar har ta haihu bai kai k’asa ba kuwa?.

Wayoyin sa suka ishe shi da kwarmato Dole ya jawo su Yana dubawa inda yaga shugaban jam iyya ne ya kuma dauka da sauri Yana mishi sallama.

“Me ke yawo a gari ne shaid’an? Wace magana ce taka ta fasu ko kuwa dai yarfen Yan siyasa ne da har an soma Baza Yan jarida su nemo cikakken Bayani?.

Tukuro ya mike duk ya manta da plaster da take manne a gefen cikin sa.

“Wai har maganar Nan ta fita shugaba? Wata yarinya ce kawai ta bayyana Tana fadar maganganu Mara’s tushe Ashe abinda nake gudu ya faru? Don Allah shugaba ayi wani Abu kafin maganar Nan ta game duniya.

“Ba wannan ba shaid’an shin da gaske ne a n soka maka wuka da nufin kisan? Kuma ka tabbatar da Babu Hannun Yan adawa? Idan har ka San ka tab’a neman mahaukaciyar Nan to ka sanar min don muyi wani Abu don in har aka Gane da gaske ne abin Nan Kaye kurum zamu Sha ka San sun fa Gane baka da takardun primary bare na scandry Amma Nayi musu manubar maye maka da na wani Mai irin Sunan ka . Yadda muka zuba kudin mu a siyasar ka idan bamu kawo rumfar ka ba ai munyi asara.

“Wallahi ba ma zan yarda na Sha Kaye a banza ba shugaba Dole ne yarinyar Nan ta bar duniya don in ba Haka ba cikin biyu tana Shirin yin Daya.tabbas na yi abinda take magana Amma waye ya San Hakan har ya sanar da ita? Kuma ita kanta mahaukaciyar Babu labarin tana Raye a duniya ma .

“To ka San abinda kikeyi in ba Haka ba kuwa muna dab da musha kunya wallahi don har Yan jarida sun fara neman ka da son suji Yaya akayi Yaya za ayi?.

Tukuro ya sauke wayar da wani matsiyacin tashin Hankali don idan akwai abinda ya saka a gaban sa yanzu to siyasa ce inda ya fito neman kujerar shugaban karamar hukuma aka Kuma sakke kudi da son a kawo kujerar duk da Babu wata takarda guda Daya da tukuro ya mallaka Amma da Yake Nigeria ce Sai aka Shiga aka fita aka sama mishi na bogi to gaba Dayan burin tukuro shine shugabancin Nan  don Haka Dole Hankali ya tashi

Wayar shi Daya tayi ta tsuwwa Amma bai dauka ba sai da ya Kira wata lamba ta Yan jagaliyar siyar siyasa Wanda suke tanada saboda irin wannan Ranar don Haka ya Kira mascow don Yana son ko ta Yaya ma sai Nadiya da take kokarin Bata mishi suna ta bar duniya daga ita har Wanda ya sanar da ita wannan sirrin in ma ya San shi in Kuma turo ta akayi ma gobe ba zata koma

Yana ta Kiran mascow din wayar sai tsuwwa take Amma ba a dauka ba Dole ya hakura da Kiran ya figo wayar da take tsuwwar inda yaga Daya daga cikin direbobin  sa ne da suke  dauko mishi man fetur don har gidajen Mai tukuro ya bude kudi yayi sosai shiyasa ma yaji Babu abinda Yake so a yanzu sai mulki shiyasa ya Shiga siyasa daga Nan Kuma sai ace sarauta ake so dama Haka kudi suke daga inda Mai kudi ya tumbatsa to sai ya Soma neman madafun iko da Kuma sayen sarautar Koda kuwa bai hada komai da sarautar ba.

Yana daukar wayar yaji wani na Fadin

“Mai wannan wayar ne ya fadi da motar Ga motar tana cin wuta shi kuma Bai ma San inda Kansa Yake ba shine muka Kira daga Nan asibitin warri idan kana daga cikin Yan Uwan sa muna bukatar ka a asibitin.

Ya aje wayar ba tare da yace komai ba don ba wannan ne abinda Yake gaban sa ba don yafi jin ta bacin sunan can don siyasar itace a Ransa.

Motar da suka dauko man fetur din tare da wacce ta fadi ita ta iso gidan man din ana cikin saukewa wuta ta tashi a gidan man. Wutar da hukumar fire service tayi kokarn kashewa Amma Bata mutu ba sai da ta lashe komai Daga gidan man har motocin da suka dauko man Allah ya kiyaye ba ayi asarar Rayuka ba Amma dukiya Kam anyi asarar ta don gidan man ma ba zai Moro ba sai ya lashi kudade .

Tukuro Yana tsaka da wannan tashin Hankalin aka Kuma Kiran sa da Wannan mummunan labarin

Ya koma ya kwanta Yana fitar da wasu hawaye Wanda shi da kanshi ba zai iya cewa ga ko na meye ba.

Nadiya da abdulhameed aka Shiga kallon kallo suka tsurawa juna ido Amma aka kasa Samun Wanda zai tankawa Dan Uwan sa.

Kaisar da iso kofar gidan  a mota daga  dauko su Ramadan daga makaranta don tuni yaran syka Shiga makaranta kuma kokarin gaske Ubangiji ya zuba musu ga wayo ga identical twin face din su wacce take burge kowa .

Ya faka motar ya fito yaran suna dauke da launch box din su da Jakar su inda Nadiya da Abdulhameed suka Dubi Kaisar da yaran da suke cikin Kayan makaranta sunyi kyau sosai . Suka zubawa yaran ido inda Abdulhameed ya matsa da sauri Yana yiwa Kaisar sallama ya juyo Yana amsawa har ya bashi hannu sukayi Musabaha.

Ya Rike yaran Yana Fadin, “Baby boy mu gaisa Mana ?

Yaran suka dube shi suka Dubi Kaisar suna fadin, “Daddy we great him?

Ya amsa musu da Sauri Yana Fadin.

“Yes my twins you great him.

Suka Mika mishi hannu suna gaishe shi ya Duka idon shi Yana zubar da hawaye Yana Fadin

“Twins me is your daddy don’t.

“No ! This is my daddy. Suka fada suna nuna Kaisar Wanda yayi murmushi Yana tafiya don yayi zaton gaisawa kawai zaiyi da Yaran Amma da ya San zai tsaya ya Karanta musu shine Uban su da Bai tsaya ba.

Yana tafiya Yan biyu suka Bishi a Baya yayin da Nadiya ta kafe a tsaye ta kasa wucews ba don komai ba kuwa sai kunya da muzanta ace Uwa irin ta Ya’yan ta su gan ta ko a jikin su bare su kalle ta .sai taji ta Ina yaran zasu kalle ta bare su kula ta?

Ta ja kafafu zuwa cikin gidan inda ta samu Yan biyu sun dafe Fati suna fada Mata abinda abdulhameed yace musu Wai shine Daddyn su.

Kaisar da yaga shigowar Nadiya sai yayi maza ya wuce sashin sa don Yana Jin Bai tab’a tsanar wata halitta a duniya ba kamar ta ba abinda tayu mishi ba ne damuwar sa A a sai don yadda Wanda ya samar da ita ya Zama Makiyi na mahaifin sa .

Nadiya ta zauna a Kan kujera tana kunyar hada Ido da Fati . Fatin ce tayi Mata magana  har tana Dora Mata khalifa a cinyar ta don taga ta kasa magana kafin Daddy ya sauko ya ganta ta zube a gaban shi tana gaishe shi ta Kuma kwashe komai da ya faru tsakanin ta da shaid’an Wanda ta Sha alwashin kashewa har kiyama da Kuma hukuma da ta taho don tafiya da Alh iro Wanda tukuro Yake zaton yarfen Yan siyasa ne .

“Nine Zan wanki kafafu na naje ga tukuro? Allah ya sauwake muje ga hukumar na fada musu idan dai shine Yake son gani na to yazo Nan ne muhalli na in Yana da magana sai yayi Amma tukuro baiyi isar da zai turo min hukuma naje na same shi ba.

Nadiya ta fito inda yan sandan suke Daddy ya Basu Sak’on da yake son isarwa ga tukuro inda yace su wuce da Nadiyar.

Abdulhameed da yake tsaye jiran isar da son ganin Daddy sai ga shi ya fito Amma Bai lura da shi ba sai da yaji ana Fadin a wuce da Nadiya kafin ya juyo Yana Fadin

“Daddy don Allah kar su tafi da ita a barta haka ta huta yarinyar Nan tana ganin garari.

Daddy ya dube shi Yana Fadin

“Abdulhameed in ba a wuce da ita ba ai ba zata Gane abinda ake so ta Gane ba.

“Kayi hakuri Daddy Ni Ina da magana ne don allah ka saurare ni.

Ya dubi Yan sandan Yana fito da kudi a motar shi ya Kuma Basu compliment card ya ce suje idan da bukatar ganin Nadiya su Kira shi zai kawo ta ko su nemi mahaifin sa distinguish Mukhtar Biro.

Ganin katin na gidan distinguish yasa suka sallama suka tafi kafin abdulhameed ya dubi Daddy Yana Fadin

“Daddy ban San da wace irin zuciya nake son Nadiya ba wallahi ko Yaya take Ina son ta  don Allah don ANNABI kayi min alfarmar na turo neman auren ta don ka Gane son da na Kira Ina Mata ba na Wasa bane ba Kuma a Sha awa kawai Yake ba .kaima ka cike Aikin ladar da ka fara Ina ganin ko a Haka Nadiya tayi karatun duniya Kuma a yanzu da ta Gane wacece Ina ganin gyara zata dauka Amma in aka Bari depression ya kamata to abin zai Zama na nadama ne don karshen abin ko ta samu tabuwa ko ta mutu Sai kaga an koma Allah sarki Amma idan Rayuwar ta inganta sai Al Amura su tafi daidai Daddy.

Daddy ya zubawa Abdulhameed Ido don hakikatan yaji wani Abu a cikin maganganun sa don Haka yace

“Abdulhameed na yarda s abunda kace Kuma na gamsu Amma ina Mai tabbatar maka da ba zan Kuma daukar bakin cikin yarinyar nan a nan gaba ba  kuma Kai da kunne ka kaji mahaifin ka na Fadin ko ma ta sun kare a duniya ba zaka auri yarinyar Nan ba Anya kuwa ba a cikin ahalin ka ne zata zata hadu da depression din gorin da zasuyi Mata na ita Yar mahaukaciya ce ba?.

“Nayi maka alkawarin ba zan bari aci zarafin Nadiya ba daddy. Nayi maka alkawarin son ta ba zai bani damar na Bari a wulakanta ta ba .

“To abdulhameed baka da matsala Dani amma ita din gata nan gaban ka jaraba ta ka gani ko ta sauya daga yadda take in kuma Bata sauya ba to bar yarinyar Nan da Halin ta wata Kil dai jinin Uban ta ne Yake yawo a jinin ta.

Daddy ya wuce ya barsu inda Nadiya ke kuka tana share hawaye ba don komai ba sai don yadda abdulhameed ya nuna mata halacci har a yanzu da yaji kowace ce ita son ta yake bai juya mata Baya ba.

“Kar ki min kuka don Allah Ina fatan a yanzu zaki kalle ni wani mutum sabo da yaxo ba Wanda Kika Sani ba don in muka ce muna nan a irin jiya to Halin mu ma ba zai sauya ba . Ina son na turo neman auren ki amma amincewar ki nake nema don matukar zaki ce baki sona Nadiya zanyi wa kaina adalci na Kuma yi miki na Kuma hakura da kowane irin so nake Miki wata Kil Ubangiji yazana wahalar son ki kawai zan sha amma sona gareki babu cutarwa a cikin sa.

Ta Rufe bakin ta tana son takawa kukan ta burki . Ya Miko Mata tissue paper ta karba ta soma share hawayen ta .

<< Azurfa Da Zinari 96Azurfa Da Zinari 98 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×