“Abdulhameed baka ji ko Ni wacece ba? kafi karfi na abdulhameed duk da nayi abubuwa masu yawa Wanda ba zan iya yafewa kaina ba . Abdulhameed idan nace ina son ka zai Zama yaudara tunda na amsa ne a lokacin da duniya ma take kyama ta idan na Rabe ka ko na kusanto ka na cuce ka Amma ka sani ba zan tab’a manta la Rayuwa ta ba . Idan ma har Allah yayi min tsayin kwana Zan Rubuta labarin mu Ni da Kai don na nunawa duniya Babu masoyi irin ka a duniya. Babu Kuma Wanda ya Kai ka sadaukarwa don yanzu na Gane kuruciya ce a cikin abinda mukayi don Haka na gode maka na gode maka Amma idan zanyi maka adalci to mace yar asali ya kamata nayi maka fata ba iri na da Babu komai a tare da ita ba sai bak’in tarihin da Uba ya gadarwa kuma Yar mahaukaciyar da akayi amfani da haukan ta aka ketawa haddi har ta haife ni cikin Rashin gata da k’azanta babu mutuntaww banda Daddy da mama abdulhameed da baka samu gani na a duniya ba don tuni mahaifiya ta ta zaune ni ko ta jefa ni Rijiya koma ta hasa wuta ta gasa ko ta dafa kamar yadda haukan ta ya karanta mata amma su daddy da mama sukayi min gata sai gashi ban saka musu da komai ba sai bak’in ciki da muzanta.ba ma wannan ba Abdulhameed mijin da suka bani wanda nake kallon a matsiyacin da na zarce komai nake kuma kallon yaxo yaci arzikin mu Ashe kalmar Daddy da yake yawan nanata min ta ni din AZURFA ce ban Kai matsayin ZINARE ba Ashe Kaisar shine alfarma a garemu ban sani ba. Ko shi nayi mishi abinda in Ubangiji ya kama ni ba zanyi Kyawun duba ba.Kai abubuwan da suke kaina abdulhameed suna da yawa don haka zan baka hakuri.
“Bar hakurin ki Nadiya ni dai naji na gani tunda kuma na samu yardar Daddy kema zan samu taki .kuma dukkan abinda kika ga ya faru to zanen kaddara ne Nima a yanzu da kike gani Nadiya abubuwa ne da yawa a kaina amma faruwar lamarin mu yasa naji Babu komai s cikin duniya sai wahala in ma baka zama nagari ba to sai lokaci yaxo ya wuce da Kai da duk irin Aikin da kake Kuma sunan ka ya tabbata a ko ya kake gara ma ka kame kanka.wata kil dama haka kaddarar mu take in haka Allah ya Rubuto Mana godiya ce ta mu Ramadan da sha aban kuwa Allah ya inganta Rayuwar su Ni da kaina a yanzy na yarda ba namu bane Allah yasa hakan ya Zama alheri a garemu da su Duka don ni da ke bamu kamaci amsa sunan komai a garesu ba in Kuma har munyi hakan to Ranar da duniya ta sanar da su mugun Aikin da mukayi har ya bada sakamakon su muce musu me ? Astagfurullah Allah astagfurullah Allah.
Sai ya soma dauke kwallar idon sa da tissue paper Yana tafiya ba tare da yayi Mata sallama ba.
Abinda ya motsa zukatan su kenan har ta Raka shi da ido ya shiga motar shi ya wuce yana dauke kwallar idon shi .
Ta jima tsaye a wurin tana share hawaye sai da Fati ta fito ne ta kama hannun ta suka koma ciki tana bata baki da cikar I’mani Yana nan ga yarda da kaddara.
“Fati kunyar ki nakeji . Kunyar yan aikin gidan Nan nake hatta mama kunyar hada Ido nake da ita bare Kuma daddy.
“Duka ki manta baya a tarbi Gaba abinda yayi saura na Rayuwar guda nawa ne ? Abinda kawai yafi abinda aka baro baya an barshi har abada a gyara sauran . Nadiya ta Rungume Fati tana kuka Tana Fadin
“Don Allah fati ki yafe mini ki yafe mini don Allah .
Ta Rufe mata baki itama tana kukan tana Fadin
“Damuwa ta tafi Taki Nadiya na Gina Rayuwar aure na da Yaya Alabo Amma wata munafuka ta Rosa min ita Nadiya ta Shiga tsakanin mu ta Rosa mana . Allah ya Sani a da naso Yaya Kaisar Amma tuni na shafe babin sa a Rayuwa ta Amma daddy ya yanke mini hukuncin auren say Amma Allah ya Sani zuciyata tana ga Yaya Alabo Yaya zanyi?.
“Kiyi hakuri fati da Rabo Mai kashewa gara mai Rabawa Yaya Kaisar mutumin kirki ne ina Miki murna don kin dace da miji nima ban gane hakan ba sai da Al Amari na ya lalace don yayi hakuri Dani da hali na har zuwa Ranar da Ubangiji y yanke mishi wahala . Fati kece daidai Kaisar zaku Dace halin ku zai zama iri daya Kuma irin alherin da ke tsakanin Daddy da mahaifin Kaisar haduwar ku shine cikar burin baban sa Allah ya yafe Mana ya gyara zukatan mu amma ni kam Ina cikin garari fati Ni da ksima ma ba Zan iya yafewa kaina ba Amma in Allah ya yafe mini sai yasa mutanen da na cutar ma su yafe mini.
Sumayya ta gama karatu ta dawo gida inda Kuma Mai Shari a Sufi yace ba zata dora da komai ba sai aure. Babu wani namiji a Ranta sai abdulhameed ta Yaya kuma zata zubar da ajinta tace shi take so ? Sai kawai tace da Baffa Alkali ya zaba mata mijin da yake ganin ya dace da ita don haka sai yace to ta bashi lokaci
Babu wanda yazo ran mai shari a sai Ya’yan Yan uwan sa Mustafa Tero ko shafik wato Tsagera cikin su ne yake ganin gara ya hada su aure ko don zumunci
Usman ne ya nema da wannan maganar ya kuma fada mishi yadda sukayi da sumayya.
“Alkali Anya kuwa sumayya ta Dace da yaran nan da kake magana? Dukkan su fa Babu wanda ya kama kansa sun tsaya Shashanci ko Aiki sunki su nema to Ni gaskiya ban ga dacewar su da kamila irin sumayya ba .
“Usman sai ka manta shi auren Yana gyara Mai shi mijin ko matar wanna ba zai hana na bawa Mustafa ko shafik aure ba don zanyi fatan auren ya zame mishi hanyar shiriyya.
“To gara abdulhameed Yaya Alkali don ko Babu komai za a gyara wata baraka dake tsakanin zumuncin mu idan abdulhameed da sumayya sun zama couple dole Yaya Mukhtar ya sallama tunda har yanzu banji Yana Shirin risunawa ba .
“Usman kar fa ku jawo min abunda yafi karfi na Yaya Mukhtar har gobe gaba Yake Dani t yaya kake ganin wannan Al Amarin zai yuwu?.
“Yama yuwu har ya Gama Alkali kai dai yi shiru abunka bari na nemi abubakar mune da wannan alhakin dama kuma Ni da Abu din Babu yadda yaya Mukhtar zaiyi damu idan yaji har mun gama .
Usman ya kashe wayar sa ya Kira wayar dan Uwan sa abubakar ya labarta mishi komai shima yace Bai yarda da tarbiyar Ya’yan Nasu ba Amma Abdulhameed ko Babu komai hanya ce ma ta gyara zumuncin su musamman abunda Yake tsakanin Sufi da Mukhtar.
“To Amma yaya Usman idan akay hakan ba a shiga hakkin yarinyar nan sumayya ba? Usman ya fada mishi yadda sukayi da mahaifin ta .
“Ok to mu hadu gobe a gidan Sufi din sai mu nemi Abdulhameed da Uban sa .
“A a Abu ba zamu neme su ba sai komai ya kammala don haka ni zan hada mishi kayan lefe don su gane mun shiryawa auren ne in ta kama ma suma Mustafa da shafik din sai su biyo Bayan sa ta yadda Mukhtar ba zai gane hikimar mu ba .
Tuni kuwa su Usman da abubakar suka Shiga hidimar auren da suka shirya da son gyara tsakanin iyayen su. Lefe na gani na fada aka hada hatta da sadaki mai daraja usman ya biya a aljihun sa don Haka Ranar asabar Usman ya Kira distinguish ya sanar da shi akwai daurin yar aminin sa da shine ya zamo alwali don haka Yana gayyar sa .
“In har ka san ka gayyaci Sufi hidimar abokin ka kar ka saka Rai da gani na don ko a kiyama bana fatan haduwa da Sufi in kuma don ka hada mu ne har kace mu gaisa irin na kwanaki to Usman zanyi maka wulakanci ne Mai daraja ta farko wallahi don ko a kiyama bana fatan haduwa da Sufi don ko ladar Sufi zata zamo saura daya ya Shiga Aljanna to zan hana shi ita. A makiyana ma Sufi lamba daya ne dashi Ashe ban kuma gane hakan ba sai da akayi walkiya na gano shi Ina amfanin dan uwan da ba zai rufa maka asiri ba? To in ka san ka gayyaci Sufi nu ka fada min don ba zan zo ba in kuma nazo na ganshi kaine zanyiwa wulakanci mai kalar ruwan hoda wallahi.
Isar su yakumbo Halima asibiti ita da hajiya Aliya suka zarce inda mai kokko take dab da gadon marar lafiyar wacce haj Aliya ta yi wa kallo daya hankalin ta ya tashi . domin kuwa matar nan ce wacce suka karbi yarta suka rike wato dai mahaifiyar Nadiya.
ta matsa gaban gadon tana kallon matar wacce har yanzu ake cikin halin jinya da hauka domin kuwa har a yanzu bata warke ba cikin haukan take sai dai tana Jin jiki ta Rame sosai har maganar ta ma ta dusashe ko tayi sambatun ta ba a ji Sosai.
Haj Aliya taji hawaye yana zarya a fuskar ta tana jin tausayin matar Nan da ta rayu a cikin wannan halin inda mai kokko ke bata hakuri tana fadin
“Yaya za ayi haj? kin san komai baya rasa sanadi daga maganar aure ana dab da bikin ta matar Wanda zata aura din ta samu labari Ashe irin matan Nan ne maras tsoron Allah har gida ta iske mu tay mana rashin mutunci mai daraja ta kums sha alwashin sai ta watsa al amarin sai ga lariya da lalura duk da ban dorawa kowa ba face kaddara daga Ubangiji . Ai rabon zamu gana ne shekarun da yawa fa ana ta bauta sai dai ace mana an ganta bauci ko ace Gombe ko ace mana Jos da yake haka Allan ya tsara mata Rayuwar s sai dai fatan muyi mata Allah yasa ya zama sanadin shiga Aljannar ta da mu Baki daya.
Haj Aliya ta mike tana Fadin
“Haka ne Allah ya bata lafiya
Ta dubi Yakumbo Halima tana Fadin
“Halima Bari na koma gida mu taho da Daddy da Nadiya su duba ta.
Ta fice da sauri ta iso gida ta samu Daddy yana Fadin
“Har kun dawo ne?.
Daddy muje asibitin Nan kaga ikon Allah wai ka San mahaifiyar Nadiya ce na gano?
ya mike da sauri aka kira Nadiya mama na cewa ta dauko hijabin ta zasu je asibiti.
Da sauri ta dauko Daddy ya fito zaija motar amma Kaisar yace shi zai tuka su don haka a tare suka taho asibitin.
Suna zagaye gaban gadon daddy yana ambatar kalamar ya hayyu ya qayyum Allah mai yadda yaso Ashe baiwar Allah nan har yanzu ana cikin bauta? To Ubangiji ya sa ta zame miki silar Samun Aljanna.
Ya kamo hannun Nadiya yana fadin
“Wannan itace mahaifiyar ki yau Allah ya kaddara saduwar ku.
Yakumbo Halima da mai kokko suka mike a firgice Yakumbo halima tana fadin
“Banji mai kake cewa ba alhaji?
Mai kokko kuwa sai raba Ido take tsakanin Nadiya da yarta lariya inda a take kuma taga wani Abu Wanda ya Bata tsoro.
Nadiya da take Rungume da matar da taji sunan ta lariya mai amsa sunan mahaifiyar ta sai ta rungume ta tana kuka tana mata ADDU AR Ubangiji ya bata lafiya.
Lariya ta rike hannun Nadiya ta zuba mata ido kamar mai karantar wani Abu a tare da ita sai ta kwantar da jikinta a jikin Nadiya tayi lamo abin tausayi abin saka zuciya kuka.
“Ikon Allah in ba shi ba wa ya Isa ? cewar Yakumbo Halima inda mama kuma take duban su Nadiya cike da tausayawa.
“Mama zan tsaya na kula da ita kuje gida in sha Allah zan yi mata dukkan abinda ya dace
Cewar Nadiya wacce take dauke kwallar idon ta saboda tausayin mahaifiyar ta wacce Allah Bai nufi su gana tana a hayaccin ta ba sai a jinya cikin jinya.
“Hakan ya dace ayi bari naga likitan sai muji abinda za ayi
Cewar Daddy wanda ya wuce Yakumbo Halima da mai kokko sai kara tsarkake Ubangiji da bauta suna ta mayar da zancen har suma nemawa lariya Aminci da lafiya
Abin mamaki lariya tana nanuke da Nadiya wacce take Bata madara da Ruwa inda kuma Daddy ya zanta da likitan har aka Yankee daukar ta a kaita waje domin a duba ta
An basu sallama ne suka taho gida inda zuwa jibi za a fidda ita waje.
Abdulhameed ya iso wurin Amarya amma ya samu labarin bayyanar Uwar Amarya ai kuwa shima neman fidda ita wajen Yake amma Daddy yace ya Bari an nemi komai zuwa jibi zasu fita sai dai Ashe Al amarin duka mai yankewa ne mai raba kauna ta raba kafin jibin da aka ambata Allah yayi ikon sa kan baiwar Allah lariya. ta Rasu cikin wannan hali Ubangiji ya yanke mata wannan bautar.
Kwanaki biyu ne kacal Nadiya tayi tare da mahaifiyar ta amma taji tsananin kewa da alhini kuka take tana dauke kwallar idon ta mama na ta Bata hakuri har lokacin da mai kokko da Yakumbo Halima suka iso akayi mata sutura zuwa gidan mu na gaskiya Allah ka bamu guzuri na alheri mu shiga da sa a.
Kwanaki bakwai aka share makoki Nadiya duk tayi Sanyi inda Kuma Daddy yace a sanya lokacin tarewar ta don tuni faty ta tare a sashin Kaisar yayin da alabo ma ya tare da zainab Nadiya ce kawai aka ce a Barta har ayi bakwai.
*****