Har sai da aka yi bakwai sannan gidansu Fatima ya tsagaita da mutane, yan'uwanta sun yi rawar gani, don kuwa har aka yi bakwai din sau biyu suke kawo abinci kullum, safe da kuma yamma.
Alhaji kuwa har gida ya zo ya yi masu gaisuwa.
Cikin dakunan bangaren Fatima Ummi ta gyara daya zaman ta ya koma bangaren.
Dakin Inna kuwa basu taba komai ba, kullum su kan shiga su share su gyare shi tsab, tamkar dai Inna ta yi tafiya ne suna jiran dawowarta.
Sau tari ma a nan suke hirar rana da cin abinci, hatta baccin rana. . .
I love you very nicely
Wow
Nice