INNER TURMOIL
Duniya ba gaskiya. Dukkanmu muna duba iya abunda zamu ribanta ne a mu’amalolinmu na zamantakewa na yau da kullum. Za kuga yawancinmu munfi son duk mu’amalar da zamuyi a rayuwa to ya kasance mun yita ne da wanda yake da maiqo a hannunsa. Yau an wayi gari a rayuwa idan wani mai hannu da shuni ya nuna ya sanni/ka/ki to hakan fa wai ba qaramin al’amari bane a wurina/ka/ki.
Duniya bata kyale ko saurarawa mutum sai fa in yana da farcen da idan an yakushe shi zai rama sannan kuma mutum ba komai bane idan har bai tara kumbar da zai iya sosa wurin dake masa kaikayi ba. Ko da wannan dalilin kadai, dan adam yayi ho66asa, ya tashi tsaye ya nemi na kansa.
*****
Five Years Ago
Bar Beach, Ahmadu Bello Way, Victoria Island, Lagos
“SUNANA ABDUL QADIR ADAM
WANDA KU ‘YAN JARIDA KE YIWA LAQABI DA “MYSTERIOUS MAN” KO KUMA “THE UNKNOWN WRITER” KUMA WANDA A ‘YAN KWANAKIN NAN POLICE KE KIRA DA PREDATOR, WANDA KUMA AKE NEMA RUWA A JALLO A BISA ZARGIN KISAN KAI KO KUMA A BISA ZARGIN WANDA KE DA SA HANNU A KISAN KAN”
Samun kanta tayi a cikin wani yanayi da bata ta6a tsintar kanta ba. Wani gumin tashin hankaline yake tsastsafowa daga goshinta.
A halin da take ciki, hali ne wanda tunani yakan cushe, hankali in yayi dubu to kuwa zaiyi fuka fukai ya tashi, daidai da yawun bakinta ya jima da qafewa. Maganganun daya fada mata ne suka samu gurbi mafi girma suka zauna daram a cikin kwakwalwarta.
Cewa fa yayi shine mysterious man. Kenan hakan na nufin shine wannan 6oyayyen marubucin wakar daya shahara?
Shin wannan ne mutumin da ake cewa yana controlling kusan kaso biyu cikin uku na music industry a garin legas?
Wannan mutumin dake zaune a gabanta shine fa mutumin da yaqi attending academy awards duk da kuwa anyi nominating dinsa acan qasar amurka, haka yasa kafa ya shure wannan damar duk don kar duniya tasan shi. Shin meyasa yake 6oye kansa baya son asanshi ma? Shine fa mutumin da wasu ‘dai’daikun mutane sukeyin impersonating dinsa, suyi qaryar cewa sune shi?
To kodai bataji daidai bane? Yana nufin shine mutumin dasu Gladys da Belinda ke playing wakokinsa kullum a radio station dinsu a sashen shaqatawa?
Shine fa wanda ake nema ruwa a jallo kan kisan gillar da aka yiwa matashiyar yarinyar nan Yvonne Ajayi budurwar Pedro, shahararren mawaqin 2nd wave. To amma ai akwai jita jitar cewa akwai alaqa mai qarfi tsakanin tagwayen 2nd wave din da kuma shi wannan mutumin daya kira kansa da suna Abdul Qadir.
Ita yanzu ai gonau ce ba jiyau ba. Bata bukatar wani ya fada mata cewa akwai alaqa tsakanin su ukun, ta riga tasan akwai ta, abinda bata sani ba shine wace irin alaqa ce a tsakanin nasu? Mai yasa bayaso asan shi? Kuma mai yasa bayaso asan cewa Pedro din yana raye? Sannan kuma idan..
“I can only imagine how difficult this must be for you to believe but trust me, nine wanda ki kaji nace miki nine shi.
Husky voice dinsa ce ta katse mata tambayoyin da kwakwalwarta ke jero mata babu qaqqautawa.
Tattaro duk wani qarfin hali tayi wanda yayi mata saura da wanda ma bata san tana dashi ba, ta kalleshi ido cikin ido ta furta masa tambayar da tazo bakinta, bawai saboda tafi kowacce muhimmanci ba
“Ya akayi kasan da wadannan mutanen da sukayi staging accident din?
Murmushin karfin hali yayi saboda tuno cewar duk abinda zai fada mata yanzu ba lallai ne yayi making sense a kunnuwanta ba, abune mai matukar wahala ma ta yarda idan yace zai mata bayani.
“This is a question for another day. Driver na yazo zai maida ke gida yanzu. You need rest, I will contact you soon.
Zuwa yanzu ta riga ta daina mamakin yadda yake gudanar da komai kai tsaye. In dai har shine wanda ake nema, ake kan gudanar da bincike mai tsanani akansa amma gashi zaune babu alamar tsoro a tattare dashi a maimakon haka ma sai wata nutsuwa da yake ciki, to kuwa babu wani sauran mamaki da zata sakeyi a game dashi da kuma duk wasu abubuwa da suka faru tun daga wayewar gari zuwa yammacin nan.
Kafin ta kai ga amsa masa wani mutum ya shigo cikin hut din, cike da girmamawa ya gaishe shi.
“Take her home Okafor. And drive carefully.
“Yes sir. Mutumin ya amsa hade da russunawa.
Lekki, Lagos
Yana fitowa daga dakin Mimi bai zarce ko ina ba sai nasa sashen dake chan bayan main building din gidan. Sai da yayi wanka ya kuma gabatar da duk wasu mustahabbansa kamar yadda yakeyi a kowane dare, sannan yayi shirin kwanciya kamar da gaske kwanciyar zaiyi.
Wayar Mimi daya ajiye akan wani study table ya dauka hade da danna power button, tsaki yayi ganin cewa sai yayi enabling password. Agogon robar da baya cirewa daga tsintsinyar hannunsa duk rintsi ya kalla, karfe tara da arba’in da biyar, yana fatan Nadia batayi bacci ba.
Brief case dinsa ya jawo ya hada matching numbers ya bude. Wata yar karamar screwdriver ya dauko ya sake dauko wayar Mimi ya kwance notukanta. Bude cikin wayar yayi sannan ya dauko biro da jotter ya kwafe wasu nambobi dake rubuce a bayan wayar daidai inda ya bude.
Wata wayar salula ya sake daukowa a cikin brief case din ya kunna, sannan ya danna kira.
“Hello. Muryar mace ce ta amsa kiran nasa cikin muryar bacci.
“I can tell from your voice, you are already a sleep. Sorry to wake you up
“Ba komai Sir, ban jima da kwanciya ba. How may I help you?
“Ina son kiyi min unlocking wani phone, I’ve already typed the serial TMEI number yanzu zan miki sending. I hope your server is functioning well?
“Yes sir.. What kind of phone?
“It’s an iPhone. Ya amsa mata a takaice.
“I will need double barriers to consult the Apple inc. Give me like six minutes at best seven. Dole sai na shiga through an override mechanism.
Komai nata a lissafe yake. Duk lokacin daya dora ta akan wani task sai ta qayyade wasu mintuna ta bashi, kuma da zarar wadannan mintunan data dibar wa aikin sun cika zaiga ta kirashi da sakamakon aikin daya bata. Kuma a iya saninsa bai ta6a bata aiki ba komai wahalarsa face ta dawo masa da result mai kyau.
Yana daga cikin abinda yake burgeshi da yarinyar tun lokacin data fara aiki da hukumarsu ta ‘yan sandan farin kaya.
“Nadia sai yaushe zaki daina bacci da computer by your side?
Ya tambaye ta cikin raha da murmushi akan fuskarsa, sai dai kuma baiyi aune ba, cikin bazata ya tsinkayo muryarta tana bashi amsar da tayi matukar razana shi.
“Yalla6ai duk ranar daka daina bacci da bindiga a qasan pillown ka..
Daga fadar hakan tayi saurin katse wayar tana dariya. Shi kuwa Najib zare idanu yayi bakinsa a hangame cikin tsantsar mamaki.
Who told her yana kwana da bindiga qasan pillown sa? Ya akai tasan hakan? How did she know that?
*****
Around Lagos
Tunda Okafor driver yaja mota suka bar wurin shaqatawar bakin tekun ta sake dulmiya cikin duniyar tunani. Tana da tarin tambayoyin da take bukatar amsar su. Menene dalilinsa na fada mata sirrinsa? Eh. Sirrinsa ne mana, da farko dai ya fada mata sunansa wanda a iya saninta babu wani mahaluki data sani a cikin garin legas da zai iya bugar gaba yace yasan sunansa na gaskiya bare kuma aje ga batun wanda yasan fuskarsa. Yau ita ta ganshi ido da ido harma sun zanta.
“SUNANA ABDUL QADIR ADAM
WANDA KU ‘YAN JARIDA KE YIWA LAQABI DA “MYSTERIOUS MAN” KO KUMA “THE UNKNOWN WRITER“
Tabbas haka zancensa yake, su ‘yan jarida su suka bashi wadannan sunayen biyu a cikin jaridunsu da kuma cikin labaran da suke karantowa a gidajen rediyo da talabijin, ita dinnan shaidace domin kuwa tayi addressing dinsa da wadannan sunayen guda biyu sau babu adadi musamman a sati biyun da suka gabata sakamakon wata sanarwa da rundunar ‘yan sanda tayi cewa;
“A binciken da muke gabatarwa na kisan gillar da akayiwa diyar kwamishina a Joe and Toyin Motel, babban wanda muke zargi shine 6oyayyen marubucin nan daya saba rubuta waqoqi ya siyarwa da mawaqa. Shi muke zargi da aikata laifin ko kuma yana da hannu a cikin laifin ko kuma yasan wanda ya aikata laifin. Duk bayanan da suke cikin waqar daya rubuta, bayanai ne da babu wanda yasan dasu, sai shi wanda yayi laifin, ma’ana wanda yayi kisan sai kuma su police da suka kai ziyara wurin.
Babu abinda ta manta a cikin kalaman da rundunar police din tayi amfani dasu a statement din da ake zarginsa da laifin kisan kan. Ita da kanta ta karantowa nasu gidan rediyon watau ” Devine Radio” a labaran yamma na wannan ranar, saboda itace mai gabatarwa a ranar da aka saki statement din.
“Madam I dey ask una, wey yo house dey?..
A firgice ta dago ta kalli Okafor direba wanda ya riga ya fahimci zurfin da tayi a duniyar tunaninta.
“Ehen na, Madam where we dey go?
“Agege. Ta amsa masa kai tsaye, saboda bata son yadda qatuwar muryar inyamurin direban take kara hautsina mata kai.
Dama a daidai kan wani shataletale suke, juyawa yayi a shataletalen ya dauki wata hanya da tayi yamma, ya cigaba da zabga gudu kamar zai tashi sama dasu.
Duk gudun fitar hankalin nan da Okafor yakeyi dasu ba damuwar Zahra bane, koda yake bata san ya nayi ba. Hankalin ta baa kansa yake ba ko kuma tukin da yakeyi.
Zuwa yanzu ya kamata ace ta sanar da Alhaja Lateefat cewar an biyawa Aimana kudin aikin dashen qoda, wannan ne dalilin da yasa tace da Okafor ya kai ta Agege a maimaikon asibiti. To amma fa bata san ta yadda zata iya bude baki tace mata ita ma batasan wanda ya biya kudin ba. Duk kuwa da iya gaskiyar kenan. Wanda take tunanin ko kuma zargin shi ya biya kudin, bai ma bata damar tambayarsa shin shine ya biya kudin ko bashi bane ba. A qasan zuciyarta dai tasan shine ya biya.
Gaba daya tunaninta na kan tashin hankalin da yake doso rayuwarta. Shin akwai wanda zata iya bawa labarin duk abubuwan da suka faru da ita a yau kuma a yarda da ita?
Wanene zai yarda cewa wai ita Zahra Aliyu Bindawa, a common journalist, a local girl an wayi gari tasan cewa Pedro, daya daga cikin ‘yan tagwayen mawaqan dake amsa sunan 2nd Wave bai mutu ba, kamar yadda ilahirin jama’ar legas da daukacin masoyan mawaqan a fadin duniya suke jajantawa?
Wanene zai yarda da ita idan tace hatsarin da wasu daidaikun mutane suka gani, miliyoyin mutane kuma sukaji labarinsa suka kuma shaida, shiryayyen hatsarine wanda magauta suka shirya? Da kunnuwanta biyu taji su a lokacin da suke fadar hakan kuma da idanunta biyu ta shaida.
Who’ll believe her idan tace Pedro baya cikin motar tasa a lokacin da motar ketayin qundunbala tana alkafira akan titi? Wanene zai yadda da ita idan tace ba Pedro bane ya qone qurmus a cikin motar nan, wani mutumin ne daban?
Tasan cewa idan akaji irin wadannan zantuttukan nata to kuwa za’a yi mata kallon irin masu yada qarairayin nan ne na shafukan sa da zumunta kuma za’a fassarata ne a matsayin ‘yar neman suna, nobody will take her serious.
The ultimate question shine wanene zai yadda idan tace yau taga Mysterious Man kuma harma ya fada mata sunansa, kuma ma ba sau daya suka hadu dashi ba, a takaice ma ko mintuna talatin basu yi da rabuwa ba.
“Madam we don reach agege
“Madam we don reach o..
Shirun da yaji ne ya sashi juyawa yaga ko lafiya, lafiyar kenan domin kuwa wannan karon ma sake ganinta yayi ta dulmiya a cikin duniyarta ita kadai
“Chai! Wetin dey worry this small girl sef? Pesin go tok tok but she no dey hear ram..
Juyowar da tayi ta kalli gefe ne ya tabbatar mata cewar sun iso Agege domin kuwa ko akan gadon mutuwarta take bata jin zata ta6a mantawa da sha taletalen oba akran, wato Oba Akran roundabout. Wuri ne wanda duk lokacin da tazo wucewa yake tuno mata da tashin hankalin da suka fuskanta a wurin, a wurin ne wata mummunar qaddara ta afka musu wanda ko mutum maqiyinta ne baza tayi masa fatan qaddara irinta ba.
“Madam agege na big place o..
Wey yo house dey in agege?
Qatuwar muryar Okafor ce ta sake dawo da ita reality.
“Oniwaya. A sanyaye ta sanar dashi inda zai kaita, sam bata son Alhaja Lateefat ta gano halin data ke ciki.
Me zata ce mata game da wanda ya biya kudin aikin dashen qodar da ake shirye shiryen yiwa Aimana idan Alhaja ta tambaye ta, wanda kuma tasan tilas ne ta tambaye tan. A iya tsawon lokacin da suka shafe suna zaune tare da Alhaja, baza ta iya tuno lokacin data ta6a yiwa Alhaja din qarya ba, koda kuwa laifi tayi a makaranta ko kuma sunyi fada irin na qawaye.
Zamansu da Alhaja Lateefat ita da qanwar ta Aimana, zama ne da aka gina shi akan gakiya da riqon amana, zama ne na fahimtar juna, zama ne na tausayawa da kuma mutunta juna. Bata san ta yaya zata fara kallon fuskar matar nan mai yawan alheri a garesu ta zabga mata karya game da duk abubuwan da suka faru da ita a yau ba.
“Go straight to the town hall, first corner by your right.
Ta kwatantawa Okafor daidai inda zai ajiye ta, dama tunda ta ankara cewar sun iso agege, nannauyan tunanin dake addabar kwakwalwarta ya saketa. Amma alal hakika ko shakka babu tasan she is in a state of inner turmoil. She’s on the verge of a nervous breakdown.
Akwai damuwa kuma akwai sarkakiya a cikin lamarin data tsinci kanta amma kuma dolene ta tattaro duk wata nutsuwa ta arawa kanta kafin ta fuskanci Alaja. Bata fatan saka matar a cikin damuwar da take ciki, damuwar da ita kanta Alaja din take ciki ta isheta ba sai ta kara mata da wata ba.
Bar Beach, Ahmadu Bello Way, Victoria Island, Lagos
Su Zahra na fita daga cikin bukkar shaqatawar da Abou ya gayyaceta, Ali ya shigo kamar wanda aka jeho. A yanayin da yake ciki baya buqatar yin bayanin komai kafin a gane yana cikin rudani da tashin hankali.
“‘Yan sanda sun sami arrest warrant na mutum hudu cikin marubutan waka guda bakwai daka saba collaborating dasu. Sannan akwai producers dinmu guda biyu da suka sanar da Ameer cewar suma an kira lauyoyinsu akan similar warrant daga hedukwatar ‘yan sanda.
Kada kai Abou Adem yayi dauke da wani shu’umin murmushi akan fuskarsa, hakan ne ya qara ‘dugunzumar da Ali.
“Karka cemin you’re not taking this seriously? No! Not now not again.. Please!
Cewar Ali kenan in disbelieve
Ya dade da sanin halin abokin nasa na rashin expressing emotions. Koda yaushe fuskarsa a cikin dayan biyu take, kodai straight face, ko kuma shu’umin murmushi kamar yadda yakeyi a yanzu duk kuwa da irin gararin dashi Alin ke hango musu.
Abou Adem wani irin mutum ne da ba’a gane idan yana cikin farin ciki ko kishiyarsa, hakanan kuma ba’a ganewa idan akwai tsoro, jimami da makamantansu a tattare dashi
“Ya kamata ka gane duk abinda kwanciyar hankali bai kawo ba, tashin hankali fa bazai ta6a kawoshi ba.
Ya fada still dauke da murmushin nasa
Sororo Ali ya tsaya yana kallonsa kafin ya nisa
“Bance ka tashi hankalinka ba amma fa kasani we are way outside the realm of calmness
“Karka manta, Pedro ya dade yana accusing dinmu akan muna son rabashi da yarinyar nan, which is true. Munyi yinqurin hakan ba sau daya ba ba sau biyu ba. Kwatsam sai aka wayi gari wata rana an tsinci gawar yarinyar tasa ko kuma nace an samu sassan jikinta a wani motel cikin mummunan yanayi.
“Idan ni da kai mun tabbatar bamu da hannu a kisan gillar da akayi mata, idan ni da kai bamu san komai ba, shi Pedro kana tsammanin hakan zaiyi zato?
Ka kuma sani sarai tunda yaji labarin mutuwar budurwar tasa we stop seeing eye to eye mu da shi.
“Secondly, bamu san hawa ba bare sauka muka sake jin labarin wai a cikin sabuwar waqar daka rubuta, an samu bayanan sirri na crime scene din don haka kaine main suspect din ‘yan sanda.
“Abu na uku, bayan an kasheta da sati biyu sai kuma aka sake wayar gari da labarin cewar shima saurayin nata yayi hatsarin mota ya qone qurmus, kai da kanka ka gano shiri ne hakan, he’s alive some where.
“Abu na hudu, yau dinnan an fara bin collaborators dinmu da arrest warrant. Ka bani dalili daya tak why we should stay calm?
Good. Muje zuwa
Yayi kyau