Skip to content
Part 3 of 10 in the Series Duniyar El-Dorado by Abubakar Abubakar

Note:

Masu iya magana suna cewa za’a gane riqon amanar bawa ne ta hanyoyi biyu, walau amanar dukiya; abinda yake kudi na kashewa (wanda wasu ke wa laqabi da ‘yan ‘yan banki ko masu gidan rana), ko wata kadara ko kuma wani abu mai daraja daxai kawo su kansu ruwan kudin.
Hanya ta biyu kuwa itace amanar mace. Amanar mace kuwa anan ana nupin; shin mace zatayi amfani da alfarmar da take da ita wurin da namiji ta sauya wani tunaninsa ko ra’ayinsa akan tunani ko ra’ayin da yake kai na gaskia ko kuwa shi namijin zai yi amfani da wata damarsa yayin da ya samu hakan akan diya mace da take karkashin wani ikonsa. Koma dai wace hanyar ce daga ciki, idan har ka samu bawa da riqonta lapia kalau ba’a samu wata tangarda ba to kuwa mutumin nan mai qoqarin riqo da ita amanar ne.

*****

Eight Years Ago

Victoria Island, Lagos, Nigeria

Wayar salula ce kare a kunnensa, a lokaci guda (at the same time) kuma yana kallon gefe da gefensa, alamun rashin gaskia da tsoro ya nuna qarara a kan fuskarsa, cikin axamar son wanda yake kira ya amsa wayar.

“Hello!..

Sassanyar muryarta ta doki dodon kunnensa.

Idonsa ya rintse tunowa da yayi cewa wannan shine karo na farko dazai ha’inci ubangidan nasa.

What do you have for me?..

Ta jefo masa tambayar da ta katse mai tunani.

Come quickly we are about to start in the next 5-10 minutes.
ALI ya fadawa yarinyar a gaggauce yana shirin yanke kiran.

Wait! What?

Abinda bakinta ya iya furtawa kenan tana mai sake juyawa akan gadon ta. Rigar baccin dake jikinta irin mai tona asirin sassan jikin dan adam ce domin kuwa santala santalan cinyoyinta a bayyane suke kuma duk da wutar dakin dim light ce (dushasshen haske) hakan bazai hana duk wanda ya ganta a wannan lokacin fahimtar baiwar fata mai sheki da take da ita ba.

Shine kuma zaka kirani yanxu?
You expect me to beat Lagos traffic and reach you in the next 5-10 minutes?
And in such a long journey?

Tayi masa tambayar cike da tsiwa a zazzakar muryar tata.

“From lekki?.. Ta qara da wata.

Well, qilan baki shirya cika burinki ba..

Ali ya mayar mata da martani irin in an I don’t care attitude dinnan, wanda kuma hakanne ya ankarar da ita ya kuma zaburar da ita ga tuna abinda ta dade tana nema. Wato cikar burinta!..

Lekki, Lagos, Nigeria

A dai dai wannan lokacin still kwance take kan gadonta cikin tafkeken bedroom din da mutum zaiyi tunanin daskarewa, idan har zai kwashi wasu ‘yan mintuna a cikinsa saboda tsabar sanyi da rabar air conditioner din dake aikinta matuqar mamallakiyar dakin na cikinsa.

Metaphorically speaking nake fada miki 5-10 minutes, amma kiyi duk yacce zakiyi kixo island this night akwai rehearsal..

Muryar Ali daga cikin wayar ne yasa tayi wuf ta diro da fararen sawayenta daga kan makeken king size bed din nata dama chatting take a WhatsApp group akan fixed lecture dinsu na ranar asabar  gobe kenan, wanda mafi akasari na ‘yan ajin nasu suke Allah wadai da wannan lakca da aka qaqaba musu. A cewar su ai asabar din hutuce ta karshen mako wato (weekend) inji masu jajayen kunnuwa.

I long for this!.. 

Ta fadi a fili hade da girgixa kanta alamun ko shakka babu she’s going for it.

Cikin abinda bai wuce mintina biyu ba MIMI ta gama shirinta na riga T-shirt kalar army green da wandon jeans high waist na mata shima irin kalar rigar, ta kuma samu hular face cap (hana sallah) ta dora bayan tayiwa yalwataccen gashin kanta messy bun saboda tayi niyar zuwa wurin ne in disguise (6adda kama) bataso taje wurin a matsayin mace, haka instinct dinta yake fada mata tun ranar da sukai making arrangement da Ali, amma a hakan ma ba qaramin kyau tayi ba, domin ita Mimi irin mutanen nan ne da komi suka sa yana musu kyau sannan komai nata classic ne, bata siyan abun da kudi baza suyi ciwo ba. Akan wannan layin aka dora ta, akan wannan tafarkin kuma take tafiya har xuwa anjima.

A gurguje take sakkowa daga stairs din ba tare da wata damuwa ba. Trainers ne a kafafun ta farare na kamfanin supra da yake wandon jikinta bai kai har inda trainers din suka rufe ba, ana iya ganin sarqar gwal ta qafa sanye a qafarta ta dama, acewarta hakan na nupin (she’s not available to any other guy, she’s taken).

Yanayin takalman qafarta ne ya taimaka wurin guje gujen da takeyi. Kafin ta karaso main parlour na qasan gidan, zai bawa mai karatu wani qayataccen view na ire iren tsaruwar cikin gidajen alfarma da muke gani a fina finai ko tallace tallace irin na showrooms dinnan. Parlour ne dai daya amsa sunan sa, an kashe masa kudi wurin ganin ya tabbata a doron duniya.  Kudi suna magana a cikin wannan gida.

Taxo front door kenan ta tuna keys dinta suna bedroom, ta mance a dalilin saurin da take ta zubawa, komai cikin gaggawa take yinsa. Tsaki taja tana mai girgixa kanta haka ta juya ta koma stairs din kamar wacce ta bar ajiyar ranta a inda take qoqarin komawa din.

Mimi ba karamin gudu tayi ba kafin ta qarasa destination dinta. Da kanta ta gamsu cewa she drives recklessly, koda yake gashi ta iso lapia, kuma idan hakan na nupin taka wata matattakalar kenan wurin ganin cikar burinta, then be it.

The distance between Victoria Island and Lekki is 74 km”..
Mimi ta fadi a fili bayan ta zare seatbelt dinta.

Tunda ta fito daga cikin gidan zuwa parking space din nasu ta shiga motarta ta, ta kuma bata wuta hade da matsawa Olu mai gadi wani irin wawan horn daya birkita mai tunani, yakuma sashi wartsakewar dole daga gyangyadin daya fara, yaje ya wangale mata gate, tofa Mimi overtaking kawai take at full speed, bata cin birki indai ba traffic ba ko checkpoint na police tunda tafiya ce ta dare. Checkpoint kuwa ba matsalar ta bace, yarinyace da kudi kuma diyar manyan qasa.
Mintuna arbain da uku da ‘yan daqiqu ne suka kawo ta a nisan tafiyar kusan awowi biyu.
Allah Ya qara tsarewa Mimi.

Wayar salularta qirar iPhone 6s Plus ire-iren wayoyin nan na yaran zamani tun a wancan lokacin, ta sa hannu ta dauko daga qasan ramin jikin giyar motar ta toyota matrix-3,  zata kira Ali kenan ta tuna cewa yabar mata saqo a waya cewa idan ta iso text zatayi masa kar ta sake ta kirashi, hakan zai lalata shirinsu ne farat daya. Hakan ne  kuma yasa Mimi canja shawara, tayi swiping salulartata, ta kumayi disconnecting bluetooth din data hada da radion motar domin jin sauti a yayin da ta shiga motar tun a farfajiyar gidansu kafin ma tayiwa Olu gate man ham.
Dama wannan dabiar Mimi ce, jin sautin waqar masoyin ranta kusan ko da yaushe. Walau tana tuqi, ko cin abinci, ko kuma sau tari a kwance kafin tayi bacci tabar wayar tayi ta aiki ita kadai, kai harta wurin wanka Mimi na saka waqar masoyin nata ta riqa bi kamar wacce ta rera.

Duk wani mutum makusancin ta yasan irin obsession (so mai tsanani da aka sa arai) din da Mimi take dashi akan wannan dan tahaliqin da bata taba gani ba, batasan kowaye shi ba, batasan ya yake ba, dai dai da sunan sa, Mimi bata da tabbacin abinda aka fada mata haka sunan nasa yake, kuma ta kashe kudade masu ciwo fiye da tunanin mai karatu amma babu tabbas a bayanan datake samu take kuma tattarawa akansa.

“I’m here..

Shine dan gajeren saqon da Mimi ta turawa Alin, take kuma zaman jiransa a cikin motar in an anticipating manner watau cikin qaguwa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.1 / 5. Rating: 14

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Duniyar El-Dorado 2Duniyar El-Dorado 4 >>

11 thoughts on “Duniyar El-Dorado 3”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×