Skip to content
Part 6 of 10 in the Series Duniyar El-Dorado by Abubakar Abubakar

TROJAN HORSE

A dabi’a ta zamantakewa ta kowace irin al’umma ba tare da anyi la’akari da addini, al’adu ko launin fata ba, zai kasance a koda yaushe al’amura daban-daban suna faruwa a zamantakewar, wani al’amarin zai zo ne wuce kamar anyi ruwa an dauke yayin da wani al’amarin kuma zai shafe satittika ko watanni, mutane su duqufa suna sharhi kamar sun sami wani maudu’n da zasuyi fashin baqi akai, harma a samu masu qarin gishiri a miya duk don labari ya qara dadi. Idan tafiya ta miqa wani lamarin ya sake aukuwa sai ya shafe na baya. Sabon labarin da aka samu kuma, mutane kanyi masa laqabi da “labari da dumi duminsa” ko kuma “zazzafan labari”. Musamman a irin wannan zamanin na shafukan sa da zumunta na yanar gizo wanda bature ya zabi kira da Social Media.. Ire-iren wadannan al’amuran sun hada da abubuwan al’ajabi da ban mamaki yayin da wani sa’in sukan dauki sifar abin tsoro, abin takaici ko ban dariya.

******

Kamar haka ya kasance da firgitaccen al’amarin kisan gillar da aka yiwa matashiyar budurwa Yvonne Ajayi, wacce sati biyu kenan da aka samu gawarta cikin mafi munin yanayi a wani motel.

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar legas zuwa yanxu sun qara zage dantse wurin tsananta bincike, domin kuwa daga faruwar alamarin kawo yanxu ankama mutane da adadinsu ya haura dari duk a qarqashin jagorancin Samuel Ajayi, kwamishinan yan sanda na jihar kuma mahaifi ga ita marigayiyar.

Al’amarin da har yanxu bai saki zuciyoyin jama’a ba. Ba’a ko farfa’do daga jimaminsa ba sai kuma ga labarin hatsarin mota da qonewa qurmus da fitaccen mawaqi Pedro yayi wanda shi mawaqin saurayine ga ita yarinyar. Ko makaho ya shafa yasan da walakin!

******

Five Years Ago

Saturday Afternoon Victoria Island, Lagos

02:15 PM

Mutanen da ‘yan sandan suke arresting a wace hujja ake kama su?

Yayi tambayar yana tsaida dubansa akan Ameer

Hujjar da ake arresting dinsu da ita bata wuce kasancewarsu daya daga cikin abubuwa ukun nan ba;
They are either songwriters, record producers or..

“Ok. Nagane

Wa suka kama namu?

“Sir, they have arrested none of ours.

Zamansa ya gyara akan three sitter din da yake zaune akai, sannan a karon farko ya dubi Ali, babban yaronsa kuma amininsa

“Ka samo hoton yarinyar?

“Eh. Komai na cikin file din dana ajiye maka.

Dubansa ya kai kan center table dake gabansa kadan sannan yayi motioning forward ya dauko wani white office file dake gefen wata mac book.

Hoton wata kyakkyawar yarinya ne yayi tozali da idanunsa.
Yarinyace qarama.. Barbarar yanyawa
Ya ayyana a zuciyarsa, yana sake hangowa da kuma bankado dalilan da suka sa Pedro ya birkicewa kowa ciki kuwa harda shi kansa, yanxu gashi ya jefa su cikin cakwakiyar da babu wanda ya shirya mata. Nobody saw this coming..

Yvonne qawar Mimi ce tun secondary school, kuma duk tare suka samu admission a unilag

Muryar Ali ta katse masa nazarin da yakeyi.

And you are just telling me this now?

“Baka taba bani damar hakan ba

Jinjina kansa yayi sannan ya sake duban Ali

Kaje asibitin?

Eh. I have settled the bills. Kuma baza tasan wanene ya biya ba.

Good. Zuwa yamma zamu hadu da ita a bar beach.

What!
Yar jarida ce fa!

Duk su biyun suka hada baki suna kallonsa a razane.

“You heard me.. Ya fada without an ounce of fear.
It is about time I started making my moves and very past.
Alot is at stake and there’s not alot of time.

Hakane sir, to amma baka ganin the fewer mutane suka san fuskarka the better? Cewar Ameer

She’s an exception. Taji abinda bai kaimata taji ba. Bana son tayi magana da kowa, we need her own our side.

Banda wadanda sukayi staging hatsarin da qonewar motarsa, da mu ukun dake zaune anan, yarinyar nan itace kadai third partyn data san cewa Pedro is alive. I believe she found herself there under coincidental circumstances. She’s not spying on anyone

Akwai buqatar nasan how deep ta fahimci abinda taji before I can think of what to do with her

“Na riga na bayyana mata fuskata a safiyar yau, anjima zan fada mata sunana

Duk girgiza kai sukayi cike da gamsuwa

Sake kallonsu yayi na wasu daqiqu, kafin ya nisa

“I need you two to tell me, which country have the best plastic surgeons

Kallon junansu sukayi sannan suka maida kallon nasu kansa suna masu neman qarin bayani.

“I need me a TROJAN HORSE!

Iya abinda ya fada kenan ya miqe yayi shigewarsa bedroom dinsa wanda hakan ke musu signalling qarshen tattaunawar tasu kenan.

Daga Ali har Ameer din sun riga sun saba da bau’da’d’den hali irin na Ubangidan nasu.

Shi kuwa Abou Adem ko daya bar parlourn ya shige bedroom dinsa, kwanciya yayi rigingine ya rufe idanunsa, domin nemo duk wata nutsuwarsa.

Kiran da yayiwa su Ali da tsakar ranar nan har suka tattauna, yayi shine a matsayin sharar fage kafin ya fara nasa nazarin akan yarinyar da aka kashe harma wai nemansa akeyi akan wasu dalilai wanda shi yama kasa tsayawa yayi relating kansa dasu da kuma case din.

Ikeja, Lagos
03:00 PM
Same Day

Lokaci yayi daya kamata ya sake shigo da Mimi cikin wannan sabon wasan da ake shirin bugawa. Ba’ason ransa zai aikata abinda yake planning ba, amma it’s all her fault. Da bata zabi wani ko ta fifita wani akansa ba, babu abinda zaisa har ya rinqa amfani da ita domin binciko wasu sirrika ba.

Wannan wani abune wanda ya kamata ace yabarshi a line of duty. Har cikin zuciyarsa yasan bai kamata ya sake amfani da Mimi wajen gano activities din Eldorado Records ba, musamman ma idan ya tuno cewa komai fa yana cikin wayarta ne, wayar Mimi a hannunta kuwa tamkar an saka mayen qarfe ne a jikin rodi.

Ba wai tana qulafucin riqe wayar tata bane saboda zargi ko rashin yarda, a’a ko daya ba haka bane, kawai dai she’s always on her phone ne. Da wannan dalilin ne shima ya gano cewar bincike a wayarta zai bashi reliable kuma vital info din da yake buqata.
Don haka wannan karon ma dole sai yayi drugging dinta kafin wayar tazo hannunsa har yayi binciken da zaiyi.

Wadancan bayanan daya samu game da ‘yan tagwayen mawaqan ma ai a wayarta ya samu, kuma sune informations din da suka zame masa lead a binciken dayake kanyi yanzu haka.

Babbar barazanar da yake fuskantowa kansa itace idan ya tuno wancan lokacin daya bawa personal maid dinta Linda, qwayar rohypnol ta saka mata a drink, kusan kwana uku tayi kafin ta dawo normal.

Wannan bama itace babbar matsalar ba, the fact that bayan an bugar masa da ita, ko daya shiga bedroom dinta domin dauko wayar a wancan lokacin, bai taba samun temptation a rayuwarsa kamar wannan ranar ba.

Ganinta da yayi a baje kan gado ko motsi batayi da ‘yar fingilar rigar bacci, mugun gani ne, saboda a ranar da kuma ranakun da suka biyo bayanta, ya shiga wani irin mawuyacin hali ne. Shi kansa yasan kiyayewar Allah ce tasa bai afkawa yarinyar nan ba a wannan daren.

Koda yake tunda har ta iya raba gari dashi duk da irin son daya ke mata, kuma a matsayinsa na ‘dan uwanta, he will definitely carry on with his plan ai dama masu iya magana sun ce; da dan gari kan ci gari..

Wannan duk a cikin shiri ne da nazari da tunanin zuci irin na Agent Najib Ahmad.

I’m coming for you Maryam, you and your writer boyfriend.. Ya fada a fili kamar bashi kadaine a bedroom din ba.

Daga haka ya miqe ya fara shiri domin zuwa ganin “ajiyarsa” wanda kuma yake fatan ya zama sabon “TROJAN HORSE” dinsa kafin zama na biyu a ongoing meeting dinsu wanda za’a zauna a gudanar a jibi Monday karfe sha biyu na dare a hedikwatar tasu ta ‘yan sandan farin kaya.

University Of Lagos Teaching Hospital

03:45 PM
Same Day

Da duk taku ‘daya da takeyi bugun zuciyarta qaruwa yake a lokacin data qaraso bakin office din Dr. Godwin. Gaba ‘daya bata cikin nutsuwarta domin kuwa har yanxu bata hada ku’da’den da ake buqata na aikin dashen qodar qanwarta Aimana ba.

To ina ma take da dalilin zunzurutun kudi har naira miliyan ashirin da uku da ‘yan kai? Gaba daya abinda ke cikin asusunta na banki naira dubu dari hudu da ashirin da shida ne, wai a haka ma don ta samu donations daga abokan arziki a wurin aiki, saboda Oga Isaac bi ya riqa yi kowane department yana sanarwa, har wasu organizations ya riqa informing, kuma she’s very grateful saboda a irin wannan rayuwar ta yanzu mai tsanani, idan aka nuna an san da kai to ka godewa Allah.

Banda wadannan ku’da’den da aka hada mata, kafinsu akwai ranar da aka wayi gari ko anini bata dashi don tun da akai admitting qanwartata a asibitin koyarwa na jamiar, kullum a cikin cacar kashe kudi take, wanda kuma daga bayane Dr. Godwin ya fada mata abin da ya kusan tsayar da zuciyarta daga bugawa baki daya

Your sister’s medical bill is almost twenty five million naira, I tried to reason with our other staff members but unfortunately, only two million naira reduction was approved by the management..

“Your sister seriously need this transplant she’s responding poorly for the last two weeks..

It pains kuma it alters alot yau ace ga ‘dan uwanka kwance amma babu yadda ka iya. Musamman ita da bata da kowa bayan Aimanar, kasancewarsu marayu. Aikin jaridar da takeyi shine rufin asirinsu. Baqin cikin da take ciki a game da ciwon na Aimana da kuma rashin kudin aikin is overwhelming..

Ya Allah! Ta furta a fili a lokacin data ‘dora hannunta kan handle din qofar office din Dr. Godwin da niyyar budewa domin bata buqatar knocking, shi da kansa ya shaida mata hakan, saboda likitan yana tausaya mata qwarai da aniya. Treating dinta yake kamar ‘yar sa.
Kafin ta kai ga budewa aka turo qofar daga ciki. Dr. Godwin din ne yake qoqarin fita.

Oh! It’s you Zahra? Ya tareta da murmushinsa

I’ve been trying to reach you..

Next abinda ya furtane yasa abubuwan dake cikin qwoqwon kanta yamutsawa.

Someone has settled your sister’s bills this afternoon..

Doc.. Doc..tor.. Kasa magana tayi gaba daya. Batasan tunanin me ya kamata tayi ba.

“Sit down Zahra, my attention is needed somewhere. I will be right back.

Ta dai jishi yana magana amma in qureta za’a yi baza ta iya maimaita abinda yace ba.

Dr. Godwin dai fita kawai yayi ya barta don ya fahimci ba saurarensa take ba.

Wanene ya biya kudin? Tambayar da kwakwalwarta ke ta azalzalarta kenan. Wani sharp tunanine ya ziyarce ta, da sauri ta zura hannu cikin aljihun wandonta ta zaro wayarta.

Nasan kina cikin rudani. Ni kuma nutsuwarki nake buqata more than anything. Ina fatan zuwa lokacin meeting dinmu kiyi resolving problems dinki. See you soon!

Shine! Wallahi shine.. Ta fada a fili kamar ba ita kadai ce cikin office din ba bayan ta gama karanta saqon.

Itama yanzu haka ta qagu taganta a bitch, akwai tarin tambayoyin daza tayiwa wannan mysterious mutumin domin ko shakka babu shiya turo mata saqon nan.
Shi kadai ne yake magana kai tsaye irin haka..

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.2 / 5. Rating: 10

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Duniyar El-Dorado 5Duniyar El-Dorado 7 >>

11 thoughts on “Duniyar El-Dorado 6”

  1. Mutumin da akayi amfani dashi wurin kifarwa ko kuma lalata mutanen dashi wannan mutumin yake cikinsu. Shine trojan horse.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×