Skip to content
Part 9 of 10 in the Series Duniyar El-Dorado by Abubakar Abubakar

ABDUL QADIR

Zamani riga, zamani kowa da irin nasa, sannan kuma suka ce mai laya ya kiyayi mai zamani.

Allah da Kansa Yayi rantsuwa da zamani a cikin littafinSa mai tsarki, don haka shi zamani ba qaramin al’amari bane.

Zamani in simple terms yana nupin lokaci, kuma kowanne bawa akwai ta hanyar da zai qarar da lokacin da aka dibar masa, akwai tarin qalubalen da kowanne bawa zai fuskanta a iya tspawon lokacin nasa ko kuma gajeriyar rayuwar da shi bawan zaiyi a doron duniya..

*****

Five Years Ago
Bar Beach, Ahmadu Bello Way, Victoria Island, Lagos

05:45pm

Mintuna ashirin da uku ne suka kawota wurin shaqatawar bakin tekun, daga babban asibitin koyarwa na jihar legas. Suna kawo kai wurin tun bata fito daga motar ba, ta fara jin wani irin cool breeze na ratsa mata jiki, ga kuma wani irin cunkoson motoci da sauran ababen hawa ta kowane gefen babban titin an pakasu musamman ma dayake yamma tayi.

Gaba daya hankalinta a tashe yake saboda taraddadin haduwarta da mutumin nan shiyasa sam bata lura da bakin tekun ba sai data fito daga motar ta sallami direban.
Mutane ne bila adadin a bakin ga6ar tekun, wasunsu suna kan kujerun shan iska, wasu na kan dawaki, wasu ma a barbaje suke a qasa daga gani picnic sukeyi. Kowa dai yana harkar gabansa ne kawai.

Duk wannan nazarin da Zahra keyi da idonta har yanzu bata kai ga tsallakowa gefen da beach din yake ba, sai data fahimci cewa indai kallo ne bata ga komai ba sannan ta tsallaka 6arin titin da ga6ar tekun take.

“Come this way”

Ta fara duba compliment card din daya bata kenan taji muryar mutum akanta.
Turus tayi a tsaye tana kallon mutumin da bata ta6a gani ba amma yake qoqarin janye ta zuwa wani wurin. Wai come this way. Cha6!..

“Waya sani ma ko saceni zaiyi? Ta ayyana a ranta

“Are you not here to see him? I’m here to escort you at his behest.

Muryar mutumin ta sake dawo da ita daga duniyar data tafi cin zango wato duniyar tunani.

“Him?”

Ta tambayi mutumin domin neman qarin bayani.

Dago mata irin compliment card din dake hannunta yayi, wanda hakan ne ya tabbatar mata da gaske aikoshin akayi don yayi escorting din ta.

Sai dai abinda zahra bata sani ba shine ko ta wane side ya saka mutane a wurin domin a saka masa idanu akan zuwan ta, kuma idan tazo a kai ta inda yake.

Idan ma ta kira numbern dake jikin compliment card din ba zata samu ba, shiyasa yayi assigning mutane ta kowace kusuruwa domin a gane masa zuwanta.
Ta bayan wani dogon gini mutumin yabi, ita kuma tana biye dashi, haka sukayi ‘yar doguwar tafiya suka fara barin inda ke da cukowar mutane.

Wani wuri suka qaraso mai tarin ni’ima, shima dai wurin a ga6ar tekun yake amma kuma wasu bukkoki ne (huts) manya na shaqatawa guda goma reras a jere, wasu dogwayen bishiyoyin kwakwa sun musu qawanya.

Hut-8 haka aka rubuta a saman bukkar data ga mutumin nan ya nufa, wato kowace bukkar da numbern ta kenan. Bata da wani za6i daya wuce binsa, hakan kuwa tayi.
Kamshin turarensa wanda tun data shaqa da safe har yanzu bata daina jinsa a qofofin hancinta ba, yanzu ma dai shine kamshin daya cika wurin gaba daya.

Shi kadaine a cikin hut din kum duk wanda ya shigo bayansa zai fara gani, saboda ya basu baya daga wurin da yake zaune. Yana zaune akan wata kujera da aka banqarata, hakan ne ya bashi damar kishingida akanta. Wani madaidaicin teburi ne a gabansa cike da drinks kala-kala.

“Sir. She’s here

Nodding kansa kawai yayi ba tare da yayi magana ko ya juyo ba, hakan yasa mutumin juyawa ya fice.

“Sannunki da zuwa

Wannan muryar tasa mai razanar da ita ta doki kunnuwanta. Gashi dai a nutse yake magana da tattausan lafazi amma tun haduwarsu da safe zuwa wannan yammacin da suke ciki, kuma haduwarsu ta biyu kenan, indai yayi mata magana ta kanji tane cikin wani baqon yanayi.

“Pls have a sit. Ya sake cewa da ita.
Sai a lokacin Zahra tayi qarfin halin ‘dago da kanta domin tunda ta shigo cikin bukkar kanta yake qasa sai kace munafuka.

Wani view idonta ya hango mata mai sanyaya rai, ruwa ta gani yana hanqoro a ga6ar tekun yana ambaliya shi kadai.
Daga inda yake zaune abinda yake kallo kenan tun dazu, ta ayyana hakan a ranta.
“Da alama kina son tsaiwa da yawa
Hakan yasa ba shiri ta zauna kan wata kujerar roba a gefensa.

“Lean in for a goodnight kiss.. mm.. you taste like forever.😘..

Abinda ke rubuce kenan akan screen ‘din wayarsa, saqon da aka turo masa ne yanzu, kuma akan idon zahra ya bude saqon saboda kanta a qasa yake, kuma akwai kusanci a zaman nasu. Harta sunan wacce ta turo saqon sai data gani, “Deejah” shine sunan sender din. Dama tasan mai kyau kamarsa, ga kuma kudi dolene mata su riqa binsa. Mamaki takeyi saboda samun kanta da jin haushin wacce ta turo saqon.

Da sauri ta maida kanta zuwa wannan view din na bakin tekun daya ke facing don kar ya gane ta ga saqon wayar tasa, sai dai abinda bata sani ba, shi din ko da yaushe a ankare yake sai dai ajizanci irin na ‘dan adam.

Juyowa yayi sosai ya fuskance ta, sai ya zamana view din tekun ya dawo musu side view. Kallo ‘daya tayi masa ta dauke idanun ta daga nasa, gani tayi yafi mata kwarjini fiye da daxu, bata sani ba ko idanun nata ne amma yafi kyau ma a yanzun fiye da haduwarsu ta safe.

Face cap din daya saka ta 6oye sumar kansa, sajen kasumbarsa kuma yasha gyara ya kwanta akan fuskarsa luf luf. Yana sanye ne da riga t-shirt brown anyi mata rubutu da manyan baqi. FORTIS FORTUNA ADIUVAT
“Fortune favors the bold..

Dago kanta tayi ta kalleshi jin abinda yace

“Shine meaning din abinda kike karantawa.

Yayi mata karin bayani.

“Ya Allahu!

Wannan wane irin mutum ne? Wato harma ya fahimci kallon rigarsa takeyi kenan?

“I hope you are bold enough for what ever comes your way.

Kin ‘dago da kanta tayi wannan karon saboda still tana jin haushin saqon data karanta a wayarsa some minutes back, kuji wani karfin hali.

“Drink?

Kallonsa ta sakeyi a karo na uku kenan, drink yake miqo mata bayan yayi serving ‘din ta.

“I’m ok. Thank you.

Maida glass cup din yayi ya ajiye.

Kallonta yake yana qara nazartar ta, gaba daya ya fahimci akwai tsoro a tattare da ita.
“Anya kuwa ba zaiyi kuskuren bayyana mata kansa ba? Wata zuciyar ta fara kwa6arsa a karo na farko tun daga haduwarsu. Share wannan sabon tunanin yayi daga zuciyarsa tunowa dayayi koda baiyi niyya ba dole ne ya fada mata tunda already akwai sirrin data riga taji, wanda kuma dole ne ya yiwa tufkar hanci a yanzu.

Zahra anata 6angaren kuwa lissafinta bai wuce tunanin abinda wannan mutumin keso daga gareta ba. Tana dai fatan kada ya saka ta yin abinda baza ta iya ba. Koda yake bata da wani za6i akan kome ya umarceta, tunda qila idan taqi bin umarninsa zai janye kudin aikin dashen qodar daya biya ayiwa Aimana. Ko bai fada mata cewa shi ya biya ba, tasan shi din ne ya biya. She’s not that fool.

Idan kuwa hakane to dole ta nutsu tabi umarninsa tunda bata da kudin kuma bata da dalilinsu.

Koma dai menene she’s very eager taji abinda yasa ya gayyato ta wurin shaqatawar bakin tekun da bata ta6a zuwa ba a shekarunta ashirin a jihar ikko.

“Nasan kin qagu kiji dalilin haduwarmu anan ko?

Kamar kuwa ya shi ga zuciyarta haka taji tambayar tasa.

“Eh. Ta amsa a darare

“Ko ban fada miki ba, nasan kin san hakan nada nasaba da abinda kikaji a safiyar yau. To kamar yadda na fada miki da safen, zan maimaita miki yanxu.

“Nasan kin fahimci abinda kika ji ana fada a wayar nan.

“Eh. Ta fada hade da rufe idonta. Ji tayi ba zata iya musa masa ba saboda wasu abubuwa da take hangowa a cikin nasa qwayar idanun.

“Kiyi min alqawarin babu wanda za kiyi sharing wannan secret din dashi. Bazanyi alqawarin cutar dake ba idan har kika karya alqawarin, amma inason kisan wani abu. Idan kika karya alqawarin, I will be hurt severely.

Gaba daya maganganun daya ke mata suna sanyayar mata da jiki ne. Duk da tana cikin damuwa, hakan bai hanata hango tasa damuwar danqare a cikin qwayar idanunsa ba.

“Nayi maka alqawari. Insha Allah babu wanda zai sani.

“Nasan ke ‘yar jarida ce, all my colleagues are against me meeting you, amma duk da haka ban bi shawarwarinsu ba, I’m just following my instincts.

“Sunana ABDUL QADIR.

Ya fada yana tsareta da idanunsa, kuma still da wannan shu’umin murmushin akan fuskarsa wanda ta rasa gane na menene
“It is very possible maybe kin san wasu mutanen masu suna Abdul Qadir a wasu wuraren like relatives, class mates, colleagues, neighbors and so on.

“Hakane.

Ta sake amsa mishi a sanyaye fiye da amsawar farko.

“Duk wani Abdul Qadir da kika sani, ni nasha banban dashi.

Dagowa tayi ta kalleshi saboda abinda taji ya fada, wanda ganin hakan ne ya saka shi jinjina mata kansa cikin tabbatar mata da abinda ya fada.

“SUNANA ABDUL QADIR ADAM
WANDA KU ‘YAN JARIDA KE YIWA LAQABI DA “MYSTERIOUS MAN” KO KUMA “THE UNKNOWN WRITER” KUMA WANDA A ‘YAN KWANAKIN NAN POLICE KE KIRA DA PREDATOR, WANDA KUMA AKE NEMA RUWA A JALLO A BISA ZARGIN KISAN KAI KO KUMA A BISA ZARGIN WANDA KE DA SA HANNU A KISAN KAN.

Lagos-Badagry Expressway

Jita jita ce ta fara ruruwa da kuma yaduwa a cikin al’umma, akwai mutanen da suka ce wai mawaqin yasha ruwan barasa ne yayi tatil, daga bisani ya tako motar tasa qirar Porsche a dari da niyyar ziyarar budurwar tasa a can birnin barzahu. Wasu mutanen kuma sun musa zargin hakan akan cewa iya sanin da akayiwa mawaqan biyu watau tagwayen na 2nd wave, ba’a sansu da kora ruwan barasa ba, sa’an nan basa mu’amala da miyagun qwayoyi.

“Off the radio!

Agent Najib dake kishingide a bayan motar ne ya dakawa John direba tsawa, babu shiri ya kashe radion daya kunna a bisa umarnin maigidan nasa. Bai san meya faru a cikin wannan gidan da oga ya shiga ba, amma tun lokacin daya fito ya san cewa akwai matsala.
Gaba daya 6acin ransa yana da alaqa ne da 6ata masa shirin da Pedro yayi. Da yasan cewa yaron zaiyi taurin kai he’ll have come along with an interrogation package from Abuja. Amma babu komai, next week dole yaron nan ya gane bashi da wayo.

Duk gudun da John yake tsalawa a motar nan Agent Najib gani yake kamar ba tafiya sukeyi ba. A yanzu ji yakeyi ina ma zai iya rufe idanunsa ya bude ya ganshi cikin dakin Maryam, he is hoping against hope Linda ta saka mata qwayar nan, idan kuwa ba haka ba, to tabbas Linda must face his wrath.
A zaman meeting din farko da akayi, akwai abubuwa da dama wanda ya bari a duhu yaqi bayyanawa ‘yan uwansa ‘yan sandan farin kaya. Information daya ne ya fada ba dai-dai ba abisa rashin sani domin kuwa haka ya gani a report.

Haqiqa bashi da masaniyar cewa Yvonne Ajayi aji uku take a babbar jami’ar legas din inda take karantar ilimin kimiyya da siyasa a maimakon wrong information da aka turo musu. Anyi mistaken din information din marigayiyar dana qanwarta mai suna Stella Ajayi domin kuwa Stella itace sabon shiga a jami’ar.

Sai dai yayi mamaki kwarai da har ya kai wannan lokacin bai gano cewa Yvonne din qawar Maryam dinsa ce ba, kodayake hakan zai iya yiwuwa tunda ai bashi da business da ita Yvonne din, sai da case din kashe ta ya samu nasarar qarasowa kan teburin su na ‘yan sandan farin kaya. Dama ai dalili ne yake tashin wani dalilin.

Lekki, Lagos

Yayi zurfi cikin tunanin daya tafi bai ma san sun iso ba sai da yaji qarar horn din da John yake latsawa. Da sauri John ya kashe motar bayan sun shigo gidan, ya zagayo ya bude masa tasa kofar cikin tsantsar ladabi.

Kai tsaye ya nufi cikin gidan saboda ya riga ya sa a ransa there’s no more time to waste. Karya akalarsa yayi zuwa upstairs inda dakin Mimi yake, babu buqatar ya kira wannan maid din yaji ko maryam din tasha qwayar ko bata sha ba, saboda idan har bata sha ba yasan yarinyar zata sanar dashi before hand.
Yana murda door handle din yaji ta bude, wani sassanyan kamshi ne ya dakar masa kofofin hancinsa, hakan ne yasa shi lumshe idanu. Takawa yayi ya isa bakin gadonta, a yadda take baccin nata duk wanda ya gani yasan bata shirya masa ba.

Daga gani she was typing on the phone lokacin da baccin ya dauke ta, saboda duka hannayenta biyu ne suka tallafi wayar, manyan fingers dinta kuma na duka hannayen suna kan screen din kamar dai yadda mutane masu yin typing da hannu biyu suke riqe waya.

Kallon manyan yatsun hannun nata dake kan wayar ya fara yi, a maimakon ya zare wayar ya tafi tunda itace maqasudin shigowarsa dakin. Idanun sane suka cigaba dabin jikinta da kallo har sai da ya kawo wuyanta, jelar gashinta da suka sauko suka kwanta akan wuyan nata ne ya tafi da imaninsa.

Rigar dake jikinta ba ta bacci bace amma doguwar riga ce nylon irin mai bin jikin nan, hakan ne ya qara taimakawa wurin sururutar dashi.

Idanunsa da suka kada sukayi jawur ya runtse da qarfi sannan ya sake bude su akan ta wadanda zuwa yanzu har wani maiqo suke.

Linda dake la6e bayan labule tana kallon duk abinda ke wakana amma ta kasa gane takamaimai abinda Agent Najib yake sonyi.
Tun da kunnuwan ta suka jiyo mata horn din da John yayi a bakin gate tayi sauri ta shigo ta la6e don ganin abinda zai wakana cikin dakin. Dama tasan Mimi ta dade da yin bacci. About an hour ago tun lokacin data kirata ta kuma bata umarnin ta hado mata green tea, anan ne tayi grinding qwayoyin rohypnol har biyu ta zuba mata a cikin tea din.

Ita duk a tunaninta yana son yayi having sex da Mimi ne. Idan har zai sa ta riqa saka mata qwayar bacci a cikin tea ko drink, to kuwa don yana son amfani da ita ne.

Tunaninta ne ya yanke lokacin data ga yasa hannu ya zare wayar Mimi daga hannunta, sannan ya miqe daga kan gadon yayi hanyar kofa sai rangaji yake kamar wanda yasha giya yayi tatil.

Kenan wayar ta yake son dauka? Lallai akwai abinda yake son checking a cikin wayar, tunda dai gashi akan idonta ta gani ko ta6a yarinyar baiyi ba. Wayar kawai ya zare daga hannunta ya fita. Lallai dole ne ita ma tayi qoqari ta binciki wayar Mimin ko za taga abinda Najib yake son gani a ciki wanda har sai yayi drugging ‘yar uwarsa akan hakan, wannan shine abinda Linda ta qudurce a ranta, bayan ta fito daga bayan labulen da take 6oye. Rashin sani yafi dare duhu, data san hadarin da zata saka kanta a dalilin hakan da ba ta soma tunani hakan ba ko da wasa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.8 / 5. Rating: 10

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Duniyar El-Dorado 8Duniyar El-Dorado 10 >>

9 thoughts on “Duniyar El-Dorado 9”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.