Ƙirrrrrrrrrrrrrrrrrrrrrrrrr!
Wata ƙarar kararrawar ta sake cika dodon kunnensu. A matuƙar firgice Linda ta runtse idanuwanta tana jan jikinta baya har sai da ta dangana da kujerar ƙarshe ta falon, tukunna ta buɗe su tar! A fuskar Faɗime da ke tsaye inda ta barta.
A cikin idanuwanta ta gane yanzu ko duniya za ta bawa Linda ba za ta je ta buɗe ƙofar ba, dan haka ta saki takardar hannunta da ta ɗauka ta karanta bayan Linda ta yi zaman 'yan bori, ta taka a hankali zuwa baƙin ƙofar, ta buɗe.
Wannnan karon Maigadinsu. . .