Skip to content
Part 10 of 53 in the Series Halin Rayuwa by Hafsat C. Sodangi

Kusan kullum sai ta kai maganarshi wurin Babana, wai yayi misi kashedi a kaina don lalata ya’ yan mutane yake yi, Asabe ma wai ta ki yarda dashi ne yasa ya rabu da ita ya dawo kaina. Sai dai ban san dalili ba, bai ce mata komai ba, nima bai taba yi min wata magana ta kashedi a kan shi ba, ban kuma zaci ya ta ba tunkarar Mubarak din da maganar ba.

Rannan ina zaune a dakina ina jin Babah Lantana tana cewa Babana wai dama ya bayar da rikona ga dangin uwata da suke raina mishi kokarinshi a kaina, ko ma don ya ga uwar da za su yi min tunda shi basa ganin kokarinshi.

Ya ce, mata a’a inda duk zai zauna zai zauna tare dani, ta tabe baki ta ce, ai sai kayi ta zama da itan tunda baka jin shawara, yar kankanuwarta da ita maza sun fara yaudararta da abubuwa tana binsu kana kallo an baka shawara ka ki dauka, in ta zama budurwa kuwa tafi karfinka taje ta dauko maka abin magana babu ruwana, tunda ko a yanzun wannan yarinyar ai ba na zaton in nayi rantsuwa a kanta nace ba budurwa ba ce zan yi kaffara.

Bai dai ce mata komai ba har tayi ta gama tayi shiru.

Ina zaune a zauren gidanmu kwarkwatar kaina ce ta dame ni ga wasu kurarraji ma su ruwa da wari da kaluluwowi a bayan kunnena da keyata, ni kaina nasan ina cikin wani hali da kwarkwatar nan saboda ko a makaranta ni kadainake zama a benci saboda yara guduna suke yi kar in sa musu kwarkwata.

Don ba ta buya ba yanzun nan ne za ka ganta tana bin jikina ko rigata ko hijabi ban da haka ga bashin da nake yi, kan haka sai ya zamo min jiki, duk inda na zauna in yi ta tsigota ina kashewa.

In kuma a cikin mutane ne nasa hannu cikin sa’a na kamo ta to sai kawai in saketa a kasa cikin hikima ba tare da na tsaya kasheta ba kar wani ya ganni.

Ina zaune a zaure susa nake yi da hannayena duka saboda dadi har yawu yana diga daga bakina, jifa-jifa kuma in na kamota sai in sata a kasa in kashe tayi kwas, na shagala ban san lokacin da ya shigo ba sai kawai idona ya kai kan kyakkyawar kafarshi da ke cikin wani kyakkyawan takalmi budadde, wato open shoe, A hankali nabi tsain kafar tashi da kallo zuwa jikinshi har kawó kan fuskarshi, da sauri na sunkuyar da kainà kasa daga dukkan alamu kuma na abinda na gani a fuskarshi ya dade a wurin yana kallon abinda nake yi.

Shi ke nan shima zan rasa shi shima zai fara guduna yana jin kyamata a dalilin tsananin kazantata ga kwarkwata kamar yanda sauran yara da mutanen gidannu suke kyamata, na mika haninu a hankali na jawo kazamin dankwalin nawa na sake kulle cukurkudadden kan nawa ban yarda na sake dago ido na kalli fuskarshi ba, fatana kuma da burina bai wuce na inga kafarshi da ke kusa dani ta motsa ta bar gun ba.

Ba zan yarda in sake hada ido da shi ba, abin da zuciyata ke raya min ke nan.

Wanke hannunki kici abincin da nazo miki da shi. Cikin wata irin murya mai sanyi yayi min wannan maganar, ban motsa daga yanayin da nake ciki ba saboda wani irin yanayi da na samu kaina a ciki na tsananin jin kunya.

Tashi mana kije ki wanke hannun.” Na ce, “To. Na mike da nufin in na shiga gidan ba zan sake fitowa ba, sai naji ya ce, Ko kuma muje gida kawai.” Naja na tsaya kaina a sunkuye na ce, a’a sai dai iyakar abinda zan iya yi ke nan tunda shi ne a ta kusa da kofar shiga gidanmu.

Uh’uh ki ka ce min? Za ki yi musu dani ne? Cikin natsuwa ya jero min tambayoyin ban san yanda aka yi ba sai kawai naga na juya na kama hanyar zuwa gidan su Mubarak.

Ba wani nisa ne sosai a tsakaninmu ba, sai dai duk da haka ba zan iya tuna rabon da in shiga gidan ba, watakila ma tun Innata tana raye.

Sashin gaban gidan shi ne bangaren da Mubarak yake, amma bai tsaida ni a nan ba can cikin gidan ya wuce da ni wurin Ummanshi, tana ganinmu ta saki murmushinta mai ban sha’ awa, Ahmad Mubarak bai fita ba ne?

Cikin natsuwa ya ce mata, Na fita Umma, dawowa nayi, to sannu da dawowa, Ubangiji ya kara shiryar min da kai ya kuma yi wa kokarinka albarka. Yayi murmushi amin Umma, Umma ba ki ga Maryam ba ne?

Umma ta sake kallona, Maryam? Cikin nuna alamar tunani kan ya ce mata komai kuma sai ta kama salati, uwa ce wannan? Yayi maza ya ce mata eh Umma, ta zuba min ido tana kallona tare da jinjina al’amarin yanzu Meron Ramatu ce ta zama haka? Cikin sauri ya sake cewa, eh Ummna. To Ubangiji ya jikan Ramatu da rahamarsa ya ce amin Umma.

To zauna mana, ta nuna min wuri na bi umarnin da ta bani. Umma! Ta yi maza ta ce na’am Ahmad Mubarak menene? Sha’awar mu’ammalarsu tayi matukar kama ni cikin zuciyata, na ce nima da Innata tana nan da haka zamu rinkayi da ita.

Umma kan yarinyar nan nake so ki duba ki ga wani abin mamaki, naji kamar in ruga da gudu don tsananin kunya, da na san abinda yasa ya ce in zo gidansu ke nan da ban yarda na biyo shi ba.

“Muga kan naki Maryamu. Na dora hannu a kan nawa cikin yanayin sanyin jiki sai dai ban iya kin bin umarnin da ta bani ba, zuba ido tayi tana kallon kan nawa babu alamar damuwa a tare da ita, ki duba ki gani Umma wai kan mutum mai rai ne wannan.

Umma tayi murmushi ta ce, eh ai babu komai anyi yafi haka maraici babu abinda bai sanyawa, wata rana kuma sai labari.

Ya ce, Haka ne. suka dan yi shiru yayin da ni kuma kaina ke sunkuye, ‘yan mintoci kadan sai naji Mubarak ya ce to amma Umma ya ya za ayi da kannan ta samu saukin shi.

Kin ga wani ruwa-ruwa ma inda yake gangarowa ta bayan kunnenta ko sai dai kawai a yi  aski? Da sauri na daga kai na kalle shi cikin wani irin yanayi na mummunar faduwar gaba.

Kamar Umma ta gane halin da na shiga, don ni kam duk da wahalar da kannawa ke ba ni ina son gashina.

Aski kuma Ahmad Mubarak don ka ganta a haka ko? Ai maraici ne da uwar ta tana nan da yanzu wata santaleliyar budurwa ce.

Yayi murmushi ya ce, budurwa kuma Umma? Ta ce, eh to ai bana shekara ina ganin tsakanin sha uku da sha hudu ta ke, ai kuwa kaga da ba haka ta ke ba tunda duk da wahalar da take ciki na kazanta da yunwa ai ta dan mike.

Don haka ba za a aske, mata kanta ba, bari in gama abinda naké yi kawai na aikin abincin nan sai in duba mata shi.

Ta mike ta shiga kicin tana aikin girkinta suna hirarsu da Mubarak ni kuma ina gefe a zaune a cikin hirar tasu ne na fahimci Mubarak ya kammala karatunshi na Jami’a ne a ba na.

Ta gama aikin abincinta ta rarraba ta baiwa kowa nashi ta kalli Mubarak ta ce mishi, To ba ni wuri mana ba ga naka can an kai ba, ko za ka tasa ni a gaba ne sai na wanke mata kan kana kallo?

Yayi maza ya ce, a’a Umma na za ta kina son zaman nawa ne? Ta ce a’a bana so, ya ce to ya mike yayi tafiyarshi.

Ta kalle ni cikin yanayin kamewa sosai shiga kicin kici abincinki gashi can na ajiye miki sai ki fito in gyara miki kan naki.

Na daga kai na kalleta da niyyar cewa na koshi, yanayin da na gani a tare da itan ya wuce na a kawo mata wani wargi, don haka na mike na shiga cikin kicin din na samu abincin da take ci shi ne nawa.

Shinkafa ce da dankalin turawa da miya, ga kuma nama zuku-zuku har guda uku ta zuba min a kai na kama ci sai da na cinyeta tas na fito da kwanon nazo gun wanke-wanke da nufin wanke kwanon da naci a ciki na hada har da kwanuka da tukwanen da na smu a wurin na wanke shi fes na kife.

Ina gamawa ta kira ni to zo daga nan mu gani, naje in da ta ce din wanda gaba kadan da inda nayi wanke-wanken.

Ni da Umma ta fara wanke min kai ina tsugune sai da ta kai ma nayi zaman dirshan sosai a kasa, ta wanke kurarrajin tun suna fari har sai da suka zama ja tun ina jin dadin wankin da ake yi musu har suka koma yi min zafi. Tana yi kuma tana yi min fada in ba ka da mai yi maka abu ai yi wa kanka ka ke yi, ina dalili za ki zauna da wannan kazanta haka, ji wuyanki fa, ji bayanki ta gogo inda take nufin da hannunta ta nuna yadda datti ya yi mujimuji a tafin hannun nata.

In uwarki tana da laifi ai ke ma kina da naki na sakarci, Umma ta gama wanke min kai sannan ta kama cuda ni da soso da sabulu, wuya, baya, kirji, ke tafi can ni tsaya in cuda ki da kyau ina ruwana da nonuwanki?

Kunyarta ta kara kama ni ta gama abinda take ganin ya dace tayi min ta mike da nufin barin wurin.

Kiyi wanka mai kyau kowane lungu a jikinki ki wanke shi, ki goge kafarki sai ki cikin gida ki same ni na ce mata to.

Nayi wanka da wadataccen ruwa naji dadi irin wanda na dade ban ji ba, na fito na shiga har cikin dakin Umma na tsuguna, ta kalle ni ta ce, Ga daki can nasu Rukayya shiga ki shafa ki dauki zanen da ke kan gadon ki daura sai ki zo in sanya miki magani, na ce mata to.

Ni da na shiga gidan su Mubarak tun wajen sha dayan rana ban fito ba sai bayan Azahar, kusan ma za a yi La’asar ina rungume da ‘yan kayana da na wanke suka bushe ta hana ni canza na jikina da na sanya a gidan ta ce in je da su.

Rannan kwana nayi ina wani irin bacci mai dadi, ashe-ashe dama can ba kwanciyar kasa ko rashin abin ruhuwa ke hana ni yin bacci ba, masifar kwarkwata da kurarrajin nan ne yafi komai takurawa rayuwata.

Sa idon da Mubarak yayi kan karatuna da ma duk wani abin da ya shafi al’amarina sai na dan samu saukin wasu al’amura, kullum za ni Makarantar boko da ta allo sai dai na daina zuwa ta Asuba da ta dare saboda ayyukan da na kan yi da safe kafin in je ta bokon.

Da daddare kuwa Babah Lantarna ta ce ba Makaranta nake zuwa ba, gun samari nake zuwa, don haka na bari.

Sanin da Babah Lantana tayi na ina yin lattin Makaranta Mubarak zai zo har zauren gidanmu da bulalarshi ya fita dani yasa ta fita harkar hana ni karatun, tunda tayi tayi Babana yasa baki ya hana shi yin hakan ya ki.

Don haka ko baya nan “zuwa Makarantata nake yi saboda ba ta ganewa.

Rannan ya dawo daga tafiyar da yayi da Babanshi kasancewarshi wanda ya karanta zane zane yayin da shi kuma Babanshi Alaji Muhammadu yake dan kwangila yasa tun bai gama karatun nashi ba yake matukar taimaka mishi kan ayyukan nashi.

Ina zaune a zauren gidanmu ni kadai littafaina na Makaranta nake dubawa, yayin da naji motsin shigowa da sauri na daga ido don ganin wanda ya shigo din.

Ban san lokacin da nayi murmushi ba, ashe ka dawo? Ya dan saki fuska kadan ashe kina zuwa Makaranta? Ai daga can nake amma me yasa yau ba ki je ba? Cikina ne yake tayi min ciwo yanzu ma ya dan lafa min ne na fito.

Ciwon ciki kuma? Yayi tambayar yana mai kallon cikin idona yayin da ni kuma nayi maza na kaucewa kallon nashi. Kin sha magani ne? nayi mishi karya na ce eh, to zo muje gida.

Nayi kamar zan yi musu, sai naji ya ce ai ba ki da kirki, Umma ta ce min ba ki taba zuwa kin gaisheta ba. Kunya ta kama ni gaskiya ban kyauta ba, irin hidima da dawainiyar da tayi da kazantata ga shi kuma hakan ya zama sanadin warkewan kan nawa.

Kurarrajin ma duk sun warke, kwarkwata kuma ta mutu nima kuma tun daga ranar ban sake fashin wanka ba, balle wanki ko zan yi ana zagina sai nayi.

Sabulu kuwa bana tambaya a irin kudin break din da suke bani nake saye har da man shafawa na (Vaseline) ina adana abina.

Tashi muje, ban musa ba na ce to. Yayi gaba yayin da ni kuma na bishi daga baya, kai tsaye nayi nufin wucewa cikin gidan kamar yadda naga rannan mun yi sai na same shi a tsaye a zauren gidan, shigo nan.

Na shiga kofar da ya ce in shigan maimakon in ga dakin zaure kamar yadda nasan dakunan zaure wani lafiyayyen falo na gani mai dauke da wasu kofofi guda biyu wadanda suke rufe komai na wurin kamshi yake yi.

Yau ke ba bakuwar Umma ba ce wurina ki ka zo, yana fadin hakan ya wuce ya shiga daya daga cikin kofofin dakin da ke rufe bai wani dade ba sai gashi ya fito rike da wata leda mai kyau a hannunshi. Zauna mana kin ja kin tsaya a tsaye ko kina tsoro ne? ban yi magana ba, na nemi wuri na zauna a gefen kujerar da ya nuna min, gwada wannan in gani. Sandal ne mai kyau na asalin fata, don zuwa makaranta na karba cikin farin ciki na gwada a kafata kamar donni a ka yi shi.

Ya kalli kafar bayan ya mike tsaye ya juya zai shiga daya kofar yana tafiyar yana fadin nayi zaton haka shi yasa na saya miki shi.

Bai wani dade a ciki ba nan ma sai gashi ya fito da tire a hannunshi, gasasshen nama ne mai zafi har yana tururi tare da wuka a gefen tire din yazo ya zauna a kasa kusa da kujerar da na ke yana yanka naman da wukar.

Sauko kici, na ce a’a na koshi. Ya dago ido ya kalle ni ya dan yi wani irin dan kankanin murmushi da bai kai a kira shi murmushin ba, shi kuma ba yake ba ne.

Ya maida hankali kan abinda yake yi kin taba ganin na shiga gidanku sanda Mama take nan ta bani abu na ce na koshi?

Shiru nayi ban ce mishi komai ba, raini ne babba na gaba da kai ya baka abu ka ce ka koshi, ko da ka koshin sai kaci kadan don yasan girmamawa ne ya sa ka yin hakan.

Don haka sauko ki ci ban sake yi mishi musu ba, ya ci kadan ya mike yą bar sauran in kin cinye ga kankana nan ki shnaye, ya shiga dakin da ya fara shiga ya dan dade bai fito ba har na gama abinda nake yi.

Naji tsoron kawar da tiren tunda ba zan shigar da shi in da naga ya fito da shi ba, don haka na mike na bar komai a wurin na fito waje cikin sa’a babu kowa a wurin, don haka maimakon in shiga wurin Ummanshi gidanmu kawai na dawo nayi zamana.

<< Halin Rayuwa 9Halin Rayuwa 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×