Skip to content
Part 18 of 58 in the Series Halin Rayuwa by Hafsat C. Sodangi

Kwana uku da tafiyar Babah Lantana sai ga ta ta dawo, tsofaffin kawayenta suka dawo da ita, su Delu da sauran su. Suna kallona ina kallonsu ban ce musu kala ba sai gyada kai suke yi nuna alamar mamaki, in gumu ta gumu kuma su juya suyi kus-kus din su.

Watakila don a kaina suke maganar yasa suke yin kus-kus din don daga baya naji su suna cewa ai dan halal bai manta mafari, to ita Lantana da ta samu fili ta mike kafa sai ta ce babu shegiya sai ni, Ummm in banda dai hannunka bai rubewa yanke shi ka yar kuma Hausawa suka ce wai naka sai naka yaushe zan sake shiga wannan maganar?

Ko ni cikin zuciyata na yarda da maganar Delu cewar da sa hannunta Babah Lantana ta samu yin abubuwan da ta yi wa Babana, don haka na kudurawa raina wannan karon ba zan taba yarda in ga za a sake yi mishi wani abin in zuba musu ido ba, sai dai ko suyi a boye amma ba kiri-kiri ba irin na da.

Suka fito suka wuce ni a tsakar gida ina jin Delu tana fadin lalle wannan yarinya ta rike, ita kuwa Babah Lantana fadi take yi, ai ta wuce duk yanda ku ke zato, ni kuwa na bisu da kallo a zuciyata na ce duk sun kode sun yamutse babu wata mai kyan gani a cikinsu in banda Babah Lantana saboda ba su sake samun wani mai tsautsayin a ka ba da zai kwashe su a matsayin aure ba.

Washegari da safe na shiga kicin na koma can lungu ina aikina na bar wa Babah Lantana nata wurin da na tabbatar zał isheta, tana isowa sai taja ta tsaya daga waje, to fito ki bani wuri ko? Don ba zai yiwu in zauna ni da ke a ciki ba ga kuguna ga naki. Mai wuri yazo sai mai tabarma ya nade, nayi kamar ban ji ta ba, ina ci gaba da aikin da nake yi.

Ko ba ki ji ni ba ne? na ce ki dauki kayanki ki koma zaure ina ce dama a can ki ke aikinki? Na ce gaskiya ba zan rinka girki a zaure ba, bayan ga kicin a gidanmu, iye?

Nayi shiru ko kallon in da take ban sake ba, to ba ri yazo ya raba wannan fitinar don na gaji da rashin kunyar da kike yi min ta juya ta tafi ni kuwa nayi girkina na zuba na zuba yanda na saba, naje na kaiwa Babana wurinshi na dawo da kwanukan sannan na zauna naci nawa yara ma suka ci nasu suka watse.

Kwana biyu a jere Babah Lantana bata girki bata baiwa Babana komai sai in ya fita tasan abinda taci ta baiwa Sallau, wai ba za ta sake yin girkin ba sai ya raba rigimar da ya hada ya hana ni shiga kicin don yin komai tunda ai kicin na matar gida ne.

Ni kuwa komai nayi in zuba da yawa in kai mishi ko mai fura da nono mai kyau na gani sai na saya na kai mishi ko ta lura ta gane bai samu matsalar da take so ya samu ba ne, tunda in dai don yayi magana tayi hakan ai tasan ba zai yi ba saboda ita tayi mishi wannan sanadin.

A karin banza ta koma shiga kicin din tana yin girkin ga kuturin nawa ga natan.

Gabadaya al’amura suka cakudewa Babah Lantana saboda ta gane kwata-kwata na daina tsoronta, ya’ yanta da take sawa su azabtar da ni kuma ta gane ba zai yiwu ba saboda su dukansu sun tsorata da abinda ya samu Sallau.

Rannan ina zaune a dakina sai ga Asabe ta dawo har da Jakarta da ta tafi da ita a kan za a kaita gidan ubanta ita ma. Ina ganin ta na daga hannayena duka biyu sama na ce Ubangiji na gode maka da kasa uwata ta haife ni tare da ubana da ka jarrabe ni da maraici ma ba ka jarrabe ni da na uban ba sai ka rufa min asiri ka zaunar da ni tare

dashi.

Ka kuma sa shi ya so ni bai taba yarda da shawarar mugaye na ya bada rikona ga wasu ba, na shafa a fuskata. na gyara zamana a bakin gadona.

Da wa ki ke wadannan maganganun? Tayi tambayar a fusace na ce da wanda ya tsargu tunda ni dai ban ambaci sunan kowa ba, ina zaune a gidan ubana kuma to ai babu wanda ya isa ya hana ni ‘yancin yin magana, haka kawai in mutum yaga abinda nake yi ban yi mishi ba to kowa yaje gidan ubanshi mana.

In da gaskiya cikin lamazin ai cewa aka yi kije a kai ki wurin naki. don ki huta gorin da ake yi miki to sai kuma ki dawo mana yau?

An dawo din sai kiyi abinda za ki yi na ce babu abinda zan yi sai gori babu kuma mai hana ni.

Muna cikin haka sai ga Isiyaku ya shigo da saurinshi, murmushi yake tayi alamar yana cikin farin ciki, na kalle shi na taya shi murmushin don in zolaye shi, na ce mishi yaya na gan ka da jallabiya har da bagaruwa da dabino, ko makwabcinku Alhaji Madugu ya dawo ne?

Yaja wani mummunan tsaki kafin ya ce na rantse Anti Mero da gangan kike yi, Alhaji Madugu da ko katangar gidanshi bai yarda a taba ba shi ne zai dawo Umra ya bimu da tsaraba irin wannan? Yaya Mubarak ne wajen mu goma ya Daiwa ya shiga lissafa min yaran na gidaje daban- daban, na ce Ubangiji ya karba musu badar da suka yiwo, addu’o’in da suka yi mana ya karba mana ya ce amin.

Dadi mai yawa ne ya kama ni don kuwa ba karamin kewar Mubarak nayi ba, dan sauki-saukin abin ma shi ne Mansur ya rage min kewar tashi da ba karamar wahala nasha ba.

Za ka share zauren nan ne? Isiyaku yayi murmushi cikin yanayin nokewa, gaskiya kiyi hakuri Anti Mero gida zani inyi wanka,  in sa kayana zan je in raka Yaya Mubarak sallar Juma’a, na ce to babu laifi sai kun dawo.

Na koma daki na zaro tsintsiyar zaburi na nufi zaure don in kara kalelece zauren saboda in yazo ya samu wurin cikin tsabta tunda nasan saukowa daga Masallaci nan zai zo.

Ina sharar zauren ina lissafin rabon Mubarak da gida a zuciya, na ce kwana ashirin da uku daidai, kwanakin sun tafi da yawa al’amura masu dama sun faru a bayanshi ga shi dama mun dade babu wata mu’amallah a tsakaninmu tun kafin tafiyarshi hidimar kasa, ko da dai shi ba mai hira ba ne balle in ce zamu baiwa juna labarai masu yawa.

Ni kam zan yi kokari in koyi ba shi labarin abubuwan da aka yi baya nan, ina cikin haka sai kawai naga wata gabjejiyar kafa ta tako cikin zauren, in daga ido don ganin mai kafar bakon Babah Lantana na gani yau ma ya dawo, ko me ya kawo shi kuma oho?

Wani lallausan faffadan murmushin da ya sake bayyanar min da hakoran gwal dinshi yayi min, nan da nan kuma ya sake kifta min ido wai signal yake yi min, nai maza na sake banka mishi wata irin uban harara kamar dai yanda muka yi da shi wancan karon.

Ya wuce cikin gidan ya bar ni ina tunanin maza suna tafiya Masallaci don yin sallar Juma’a shi kuma ya shigo gidan mata zai zo ya nade kafa yayi ta zuba zance.

“Me ya kawo ka gidannan yau kuma? Tayi mishi tambayar bayan ta mike tsaye ta tsura mishi idanuwanta tana kallonsa, “Kai ke kam Hajiya Lantana ba ki iya karbar bako ba, to alheri nazo miki da shi.”

“Ai ba ka da shi ne ko ka ambace shi an ganshi a farko to sai ka biyo bayanshi da wani sharri.”

To babu laifi, duk abinda ki ka ga dama ki gaya min ni naga abin ki nasa rai a kai.”

Ya gyara zama kan tabarmar mishi, na shigo gidan da nufin wucewa in je in yi wanka, idona ya kai kan sunkin kudin da ya tura mata tare da fadin “Ungo wannan rike naki ne ki da ta shimfida soma taba su, in maganar da na zo miki da ita ta samu karbuwa a wurinki to wannan din ba komai ba ne illa somin-tabin alherin da za ki samu a wurina”

Ta zuba mishi ido tana kallonshi ba tare da ta taba kudin ba, ai sai kayi min bayani naji in da zancen naka ya dosa, sannan in naga za su ciwo in taba, ai babu abinda ban sani ba a hali irin naka baka fidda kwabo matukar ba ka hango yanda za’ ayi ya jawo maka sisi su zo tare ba.”

Na shiga wankan na bar su suna maganganunsu ban jin abinda suke fadi saboda bayan gidan a lungu ne na kuma rufo kofa, wanka mai kyau sosai na tsaya nayi saboda a yau ina matukar dokin saduwata da Mubarak.

A wannan lokacin na riga na zama budurwa na kai munzalin yan matancin sosai nayi sha shida da yawan mutane musamman Mansur sunan da suke kirana kenan yanmata, ban san dalili ba sa nake jin zuciyata ta soma so da begen kalmomi masu dadi Tsakani na da wanda nake ganin ya dace yayi min hakan.

Ko da dai shi Mubarak bai taba furta min wata magana ko nuna wata alama ta gane na kawo wannan lokacin ba, a wannan lokacin ina ganin zai gane hakan ko daga irin tarbar da nake shirin yi mishi.

Kullum a Makaranta kawayena ba su da wata hira wadda ta wuce ta samarinsu da irin kalamansu masu dadin ji da sanyaya zuciya, amma ni ba ni da mai furta min irin wadannan kalaman, dan dama-dama ma Mansur.

Ga shi kuma kusan kowa ya ganni zai yaba kyakkyawar halittar da aka yi min gani da tsabta gani da gyara, ga ni da ado daidai gwargwado ga shi kuma a wannan lokacin auren yara kan faro ne daga sha biyu sha uku sha hudu in ta dan yi tsayi sha biyar ko mu abinda yasa muka kai sha shida ba a damu ba don muna Makaranta ne, amma shiru ba ni da kowa.

Na fito daga wanka daidai Nalami ya fito da Wasu soyayyun kaji daga cikin wata leda da ya shigo gidan da ita, gashi nan komai dan kankantanshi. Yana ganina sai ya canza maganar yana fadin da hannuna na soya miki ita don dai kiji-kiji dadi ki tuna da girkin maza, ban sake kallonsu ba na wuce na bar Babah Lantana ta fara yagar wata cinya tana ci.

Kwalliya sosai nayi na sanya kayana, maimakon ma in zauna a cikin gidan sai kawai na fito zaure na zauna ina sauraron isowarsu, ana cikin haka sai ga Mansur ya shigo da dardumarshi a hannunshi alamar ya dawo ne daga Masallaci.

“Barka da Juma’a. na daga ido na kalle shi nayi murmushi har an sauko? Ya taya ni murmushin an sauko ranki ya dade, na sunkuyaar da kaina kasa ban cika son kana kirana da irin wadannan sunayen ba, kana sa ni ina jin wani iri.

Yayi maza ya tsuguna a gabana ya zuba min ido yana kallona, me za ki ji don nayi miki addu’ar ranki ya dade? Ai bar ni kawai in ce miki ranki ya daden, ko na dan ji sanyi a raina, kin san yanda kike a wurina kuwa?

Ai kallonki nake tamfar wata tauraruwa in ban da kin takura ni kin hana bakina furta miki kalmomin da yake son furta miki da kin sha magana.

Tsuke fuskar da nayi yasa shi yin maza ya canza maganar da tambayata, amma dai kwalliyar nan da ki ka yi ba unguwa za ki ba na zo na tsare ki da magana? Nayi maza na ce mishi a’a, cikin zuciyata kuwa fadi nake yi ina son jin irin wadannan kalaman amma ba daga bakinka ba, kwalliyar taki ce na ganta ta zama ta musamman ta bambanta da irin kwalliyar da ki ka saba yi kullum wannan din tana da wani abin datake nufi ta kara miki kyau tasa ki kin zama budurwa ta sosai-sosai da ganinki kuma an san ke din babbar yarinya ce mai daraja taimake ni ki gaya min gaskiya kwalliyar nan saboda wa ki ka yi ta?

Kalamanshi suka yi dalilin da na ce mishi saboda kai, yayi maza ya ce ke bari zance Maryamu, kar, ki zuga’ abin nan da ba a fadan sunanta ta hau kaya donni ki ka yi? Na ce, uhh, don in ganki in ji dadi? Na sake cewa uhh.

Sai naji ya ce, To in dai donni ki ka yi da gaske don in gan ki in ji dadi saboda kina tattalin farin cikina to bani izini kawai in je gida in shaidawa Babana don yazo wurin Mahaifinki ya gabatar da zancena a wurinshi.

Maganar tashi ta firgita ni ba abinda nayi zaton zai fito-daga bakinshi kenan ba, don haka na dago ido da nufin kallonshi, kafin in san irin amsar da zan ba shi, abin mamaki Mubarak na gani tsaye a bayan nashi cikin wani irin yanayi, ga dai kwalliya ta burgewa’ yayi amma kuma fuskarshi takai matuka wajen daurewa alamar bacin rai mai yawa a tare dashi.

Gabana yayi matukar faduwa, na firgita da ganin nashi nayi maza na sunkuyar da kaina kasa, ban san yanda a ka yi ya shigo cikin zauren ban ji motsinshi ba.

Ban san me Mansur ya gani ba da yayi dalilin da ya waiwaya cikin sauri, ganin Mubarak a tsaye bayan nashi ya sa shi hanzarin mikewa tsaye tare da mika mishi hannu. “Assalamu alaikum, barka da dawowa.” Suka vi musabaha bai sake tsayawa ba ya wuce ya tafi.

Kusan minti biyu zuwa uku Mubarak yana tsaye kallcza kawai yake yi, ba tare da ya ce uffan ba, jikina sai rawa yake yi, ji na nake tanfar na aikata wani zunubi.

Cikin zuciyata sai tunani nake yi in ya tambaye ni me zan ce mishi? Ina cikin wannan zullumin ne sai kawai naga ya juya ya tafi ba tare da ya ce min komai ba, tafiyar tashi a sani cikin wani irin yanayi da na kasa jin dadin raina, jimawa can dai na wartsake na ce oho.

Na mike na nade tabarmata a nufi cikin gida, har lokacin Babah Lantana tana ta da bakonta, sai dai ga alama sallama suke yi saboda na ! Shi yana cewa, to sai yanda ta yiwu, ko me a ke ciki zan turo in ji bayani, ko kuma in zo da kaina, ta ce to duk wanda a ka yi. Nayi mamaki a raina yadda a ka yi hirar tasu ta kasance sabanin ta ranar da ya fara zuwa gidan.

<< Halin Rayuwa 17Halin Rayuwa 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×