Na kawar da wannan tunanin daga zuciyata na daga ido na kalli Babana cikin natsuwa na ce mishi Baba wa ka ke nufin baiwa ni? Na dan sunkuyar da kaina kasa don kunya da girmamawa.
Auren ai na zumunci ne, cikin hanzari na dago na kalle shi a zuciyata kuwa dadi ne ya kama ni, wato dama Baba yana sa ne da zumuncinshi da kullum ake yi mishi gori a kai, wato dama yayi niyya a kaina ne zai gyara zumuncin nashi ta hanyar bada aurena gare su?
Ai kuwa dai duk wanda ya baiwa ni zan zauna da shi da zuciya daya in kuma yi mishi ladabi da biyayya irin na aure. Amma don in kara samun natsuwa cikin zuciyar tawa sai na tambaye shi cikin ‘ya’ yan wanka ne ko na kannenka za ka baiwa ni Baba?
Sai da yayi gyaran murya saboda yanda ta make take nema kuma tayi rawa kafin ya iya ce min a’a wannan dan uwan uwar taki Lantana mai zuwa gidan nan Mahammadu Nalami shi zan baiwa ke, don kara karfafa musu zumnuncinsu ai kin san abokin wasanta ne?
Kadan ya rage in suma a tsugune saboda tsananin kaduwar da nayi. Nalami fa kace Baba? Ya gyada kai tare da cewa eh shi nace, ban san yanda a ka yi ba sai tsintar kaina nayi ina yiwa Babana tambayoyi.
Zumuncin Babah Lantana yasa ka baiwa wannan mutumin ni naka zumuncin fa Baba?
Shiru yayi yana kallona bakina ya sake yin subuta ya ce mishi, ba zan auri Nalami ba Baba, domin babu abinda ya hada ni da Babah Lantana balle zumuncinsu da har zan je ina auren danginta.
Tuni na soma kuka ina fadin me nayi maka Baba? Me nayi maka da ka ke taimakon masu son ganin nayi bakin ciki a kaina? A gabana kayiwa Innata alkawarin ba za ka bada rikona ba ne saboda ba za ka iya rabuwa da ni ba to me yasa za ka bada aurena a inda kasan zan yi bakin ciki.
Nan da nan kawai sai naji zuciyata tana raya min babu abinda yasa a ke yi min irin wannan musgunawar illa don uwata ta rasu, Yaya Dijah da aka yi aurenta Innarmu tana raye ai bata irin wannan tozartawar ba nan take na soma kuka da iyakacin karfina.
Kan ka ce meye wannan sai ga makwabta suna shigowa tambayar me ya faru? Babah Lantana ta tsaya tana yi musu bayani ai ba komai a ka yi mata ba tunda ga uban nata nan a zaune wai daga yace zai bada aurenta ga wani dan uwana shi ne take wannan borin kar ku dada kar ku rage.
Maimakon a gamsu da bayariin nata sai kuma a hau salati dan uwanki? In ta ce eh sai a gyada kai a’a tayi ihu, to wane dadinki taji balle aje ana baiwa wani dan uwanki ita? Wannan ya gayawa wannan mutane sai shigowa suke yi yayinda ni kuma nake kwance a kasa ina ta faman kurma ihu.
Gaba daya a wannan lokacin fatana bai wuce dayan biyu ya faru da ni ba, in ma dai Babana ya tausayawa kukan da nake yi ya fasa bada ni ga Nalami ko kuma azabar kukan yayi dalilin da nima zan bi bayan Innata in huta da bakin cikin zama da Babah Lantana.
Ban san yanda aka yi ba har Umma taji tazo ba sai jinta nayi ta katse Babah Lantana tana mai cewa, In ban da ‘ya’yan yau ba su san biyayyar iyaye ba yaushe za a ce ka tarawa ubanka irin wannan Jama’ar mu da yaushe? Umma tayi maza ta ce mata ke dai kam Lantana ba ki san biyayyar iyaye ba da kin santa kuwa da ba haka ba, da ba ki a1kata ma irin abubuwan da ki ka aikata ba.
Ke wannan sharrin ma da ba ki kulla shi ba, me yasa baki ba shi tsohuwar yarki da ki ke tashe da ita shekara da shekaru ta rasa mijin aure ba?
Wannan ai ba huruminki ba ne ki ka shiga don kuwa ba ki yi mata rikon da za ki zartar mata da irin wannan hukuncin ba.
Da sauri Babah Lantana ta shiga fadin ai ni ce ma ni ce na hada? In ke ce in ma ba ke ce ba ce dai duk daya, yi kokari kiyi hakan a kan “yarki da kika bari tana tanbada kina kallo in ba nema ki ke sai taja miki irin abinda kema ki ka jawa iyayenki ba.
Mero kam ai tayi sa’a tana da uban da za a sa shi yayi mata aure da mijin da aka san ba nata ba ne don a cutar da rayuwarta, sai dai ba tanan take wai an danne buduri a ka yace ai ba nan take ba.
In kin yi ne don kin ga duk abinda ki ka yi mata a zaman da ki ka yi da ita bai ishe ki ba ruwanki kema kina da ‘ya’ya abinda ka shuka kuma shi ka ke girba, mai rabon ganin badi kuma ko ana dakawa a turmi sai ya gani, haka ana muzuru ana shaho zakaran da Ubangiji ya nufa da cara sai yayi.
Don haka tashi mu tafi Mero, ta sunkuyá ta kama hannuna na mike na tashi tsaye tana fadin ke ai kin yi arziki da Ubangiji ya ce yayi miki miji wasu ba gasu nan ba sun tsufa a titi da suna da iyayen na gaske ai da ba su zuba musu ido ba.
Ki tafi da ita ina za ki kaita? Ko za kije ne ki kara bijirar da ita? Umma ta waiwayo ta kalleta cikin nutsuwa tace mata ai mu ba mu bijirewa iyayenmu ba balle mu haifi masu bajirewa, ba zan bar miki ita ba ne balle kiji dadin cusa mata wani bakin cikin tunda ke ba Imani ne da ke ba.
Babu wata za dai ki kai mishi ita ne yayi abinda ya saba, ta ce eh zan kai mishi ita biyo ni ke kuma ki hana ni ko ki kwace ta.
A kofar gida muka samu Mubarak yana tsaye, ganina tare da Umma ya sa shi wucewa gaba ya fara tafiya muna shiga gidan yaja ya tsaya, wacce irin musiba ce wannan Umma? Ta ce, Eh ai rayuwa ta gaji ganin al’amura da dama sai addu’a kawai don haka ba’ yana nufin komai ya kare ba ne.
To me ya saura Umma? Tayi murmushi tare da fadin da yawa. Ni kam in ban da kuka babu abinda nake yi, duk bayanan da Umma ke yi na zai wuce watarana kuma sai labari jinta kawai nake yi kullum abinda a ke gaya min ke nan wata rana sai labari, har yanzu kuma ban ga alamar abubuwan za su wuce ba tunda kullumn wasu muna nan abubuwan sai kara samuna suke yi, duk wata fitina ko tashin hankali da na gani a rayuwata ban taba ganin abinda ya kai cewan da Babana yayi wai zai ba da aurena ga Nalami ba, in dai ba tashin hankalin rasa uwata da nayi ba ne.
Ana cikin haka sai ga Baban Mubarak Alhaji Muhammadu ya shigo, menene ne haka a ke ta kuka ke kuma kin tasa ta a gaba kina kallonta?
Umma ta shiga rattaba mishi bayanin abinda ya faru.
Hankalinshi a kwance ya ce to ba shi kenan ba ina ce yarshi ce? Kowa yayi shiru har da ni din saboda ba zan iya ci gaba da yin kukan a gabanshi ba, jimawa kadan sai kuma yayi tsaki kafin ya sake cewa amma bai kyautawa kanshi ba da ya bari a ka maida shi abinda a ke cewa an maida shi din, bari in je wurin Mallam Sule mu tafi wurin nashi tare muji yanda za a yi.
Umma ta ce, To Ubangiji yasa muji alheri, ya ce amin. Nayi kukan bakin ciki a wannan lokacin har sai da na rasa hawayen a idona, na rinka jin tanfar ni din komai nawa ya kare ciki kuwa har da farin cikin rayuwata.
A duk lokacin da Mubarak ya zaunar da ni da da nufin rarrashina ko ba ni hakuri kan balin da nake ciki bana sauraronshi, saboda ni kam can cikin zuciyata bana jin haushin Babana da mutane ke ta fadin maganganu marasa dadi a kanshi, nafi iin
Ciwon Mubarak gani nake tanfar inda yayi wani abu mai karfi da wuri tun lokacin da nayi ta fata da burin yayin watakila da wannan abinda ya farun bai faru ba.
To wai sai a yanzu da Babana ya riga ya furta wannan maganar shi ne suke ta faman zirga-zirga aje wurin wannan aje wurin wancan ana kamun kafa wanda bana zaton zai yi wani tasiri don magana daya kawai Babah Lantana zata yi ta birkita komai shi ne kai din ba Dattijo ba ne tunda ga shi kayi alkawari za ka canza.
Daga ranar da Alhaji iuhammadu yace bari ya kira Mallam Sule suje wurir Babana zuwa cikar kwana bakwai ya tura wa Baba mutane daban-daban har sau biyar daga ciki akwai tawagar da Liman ya jagoranta ta Malamai wadanda suka yi mishi nasihohi a kan muhimmancin bayar da aire a inda ya dace wato bin kufu’i don a samu zimatu lafiya fahimtar juna da girmamawar da a ke bukata tsakanin miji da matarshi.
Haka nan mai unguwa ya jagoranci mayan unguwa bayanshi Alhaji Muhammadu abokanshi Sun je har sau biyu.
Yanda na samu kaina cikin kunci da bakin ciki haka Mubarak ba zan ce ya fini ba ne, kawai don ni kadai nasan abinda zuciyata ke ciki, amma ko daga jin irin aiken da Babanshi ke yi daya bayan daya an san lura da halin da dan shi ke ciki yasa shi yin hakan duk wanda yaje ya dawo kuma maganar guda daya ce ita ce ta ya riga yayi alkawari don haka ba zai saba ba.
Daga gidansu Mansur ma an turo suma ba su yi nasara ba. Yaya Dijah da mijinta ma sun zo suma duk a banza, haka Yakumbo Halima wacce ita kam kaca-kaca suka sake yi da Babah Lantana, a wannan lokacin bana iya zaman gida ko da na mintuna ne, Babah Lantana da Asabe ba su da wata hira sai ta bukin nawa suna lissafin irin kwalliyar da za su yi.
Don haka ina idar da sallar Asuba in na mike gidan Yaya Dijah nake tafiya a hanya nake gama lazimin da nake yi da addu’o’ina a gidan Yaya Dijah ba ma komai sai kuka ko kuma muyi shiru amma duk da halin da muke ciki na bacin rai taja ta tsaya kan bata yarda in tafi ko ina ba.
To ki tafi ina Maryam? Kuma ki tafi ki bar ni da wa? Ki bar ni ni kadai? Tambayoyin da ta jero min kenan lokacin da na gaya mata niyyata ta barin gida in yi tafiyata in shiga duniya ya fiye min auren Nalami sauki.
Tana maganar tana kallona, yanzu nan za ki iya tafiya ki bar ni ni kadai? To ni kuma in zauna in yi me? Ba a karbarwa mutum ne Maryam da na karbar miki wadannan fitintinun da ki ke rayuwa a cikinsu, tana fadan hakan ta kama kuka, kuka kuwa mai tsanani.
Hakan yasa shi kawar da wannan tunanin saboda sanin da nayi gaskiyar magana ta gaya min da ana karbarwa dan uwa wani al’amarin na kaddarar rayuwarshi na yarda da Yaya Dijah zata iya karbar min don ban taba shiga wata fitina ta bar ni na shigeta ni kadai ba.
Gaba daya na bijirewa Mubarak na daina sauraronshi na daina shiga gidansu gani nake tanfar har da sakacinshi ya kara jawo min abinda Babah Lantana tayi min na hada ni da Nalami.
Kina nufin ke kin fini shiga fitina ne yasa ki ke nema ki hada min da wulakancinki Kan halin da nake ciki? Tambayar da yayi min kenan a ranar da ya biyo ni gidan Yaya Dijah na ki fita ia ba shi umarnin shigowa har cikin falonta in da nake kwance tunda har falon mijinta da ya fara shiga na ce ba za ni ba.
Niyyata yayi maganarshi ya gama ban ce mishi uffan ba amma ban san yanda aka yi ba hakan ya gagare ni, na’ samu kaina da tambayar menene fitinarka ba abinda kake so aka yi ba?
Zuba min ido yayi yana kallona cikin matsananciyar kaduwa me yasa ki ka gaya min wannan maganar? Na kawar da kaina gefe don kar in ga kallon da yake yi min. A hankali na ce ai ba yau ka ke ganina ba.
Yayi maza ya ce kuyo Maryam kwadayi ne da ni a kan karatunki ganin badi kamar yanzu kina shirin fita ne yasa yin hakuri na danne zuciyata.
Dago ido nayi na kalle shi cikin natsuwa na ce mishi ‘Boko? Ya ce eh, na ce to na daina yin shi daga yau har abada kuma ba zan yi ba tunda dai saboda shi ne kayi sakacin da kaja min wannan musibar.
Don haka gara kawai ka daina wahalar da kake yi a kaina tunda bokon da zai sa ka aure ni ban yi shi ba, ba kuma zan yi shi ba. Cire ni kawai cikin matan da za ka aura, koda yake ma ni ban taba sanin kana son aurena ba in ban da wannan karon ban taba jin ka ce kana sona ba na soma kuka.
Ka kyale ni kawai ka fita hanyata bana sonka bana kuma son komai naka, daga yau kuma kar ka sake yi min wani aike ba na so ka daina jin tausayina.
Mikewa yayi ya fita daga falon ya tafi ba tare da ya tsaya yiwa Yaya Dijah sallama ba.
Yaya Dijah ta shigo bayan tafiyar tashi, da kin daina yiwa Mubarak irin wannan abinda ki ke yi mishi da wanne zai ji ne? ni dai ban taba jin tausayinshi irin na yau ba kinga irin zubewan da yayi?
Bakin ciki ai baida kyau, ni kuma ban tabbatar ma za ayi aurenki da Nalami ba don jikina da Zuciyata ba su yarda da hakan ba nafi zaton wata hanya zata bullo da zata zame mana wata mafita ta warwarewar al’amuran kałamanta suka sanya ni na samu natsuwa har na yarda nayi wanka na shafa min na sanya daya daga cikin kayanta.
Muje kicin muyi girki ka utanen gida su ji yunwa ba mu ba su abinci ba, na kalli agogo na ce ga su Inna ma sun kusa dawowa daga Makaranta, muna cikin girkin Isiyaku ya sake shigowa ya gaida Yaya Dijah kafin ya gaishe ni ya kuma shaida min tare da Mubarak suke.
Yaya Dijah tayi maza ta kalle ni ya dawo, to kar ki yarda ki sake 6ata mishi rai na ce to na tashi na fita na same shi gaba daya idanuwanshi sun kada sun yi jazur.
Ki ka ce ba ki taba sanin ina sonki ba saboda ban taba gaya miki ba? Shiru nayi ban ce mishi komai ba, ya sake yi min wata tambayar shi yasa ki ka nemi wulakanta ni saboda wasu suna gaya miki su suna sonki?