Skip to content
Part 31 of 58 in the Series Halin Rayuwa by Hafsat C. Sodangi

Na yi maza na katseshi, dakata na fadi hakan taré da share hawaycna da bannayena duka biyu, maida mishi kudinshi tare da wasikar na rokeka ka gaya mishi yayi hakuri ya fita harkata bana son kulanin da yake yi bana so bana so, ka gaya mishi na

ce bana so. Zai yi min magana na yi maza na sallaka ce mishi, na ce bana so ko kuwa dole ne? Ya mike ya fita, ya tafi ni kuma na kwanta a nan wurin naci gaba da kuka cikin tsananin bacin rai da takaici, wautar kudin ce ta fi komai kona min rai wato ni kudi ne bukatata, duk abinda akayi min na wulakarici da tozartawa aiken kudi ya kanmata a yi min? Na tuna kalmomin da na ji Baba Lantana tana furtawa na rainin arziki ne yasa iyayenshi suka hanshi aurena saboda sun ga babana ba kowa bane face mai saida timatiri, zuciyata ta sake rayamin wasu abubuwan, ya yi aurcnshi ban kulashi ba ban shiga harkarshi ba yana nema ya rinka shiga nawa bayan an tabbatar min da cewär har da fita hanya ta cikin sharadin da babanshi ya’sanyå mishi, ya amsa sannan ne ya cce ya yafe msihi ya dawo gida; to menene kuma ya saurä tsakanina da shi? Ban san dalilk bå sai na samu kaina da bacin rai mai yawa da na-kasa daurewa zaman gidan ma ya gagareni na nemi izini wurin babana na shirya na tafi gidan yaya Dija.

Tana ganina da yar jakarta dana zabe yan zannuwana na canji a ciki ta saki murmushi, ‘haba to ko ke fa? Ai tun ba yau ba nake fama dake ki baro unguwar nan ki zo nan mu dan kwana biyu tare ki dan huta, ni hun ban cika son barin baba bane a gidan nan shi kadai yanzun ma na dan fito ne kawai. Na kwashe bayanin komai nayi mata ban boye mata komi ba.

Cikin natsuwa ta kalleni, kin san abin da yafi bani tausayi a cikin al’amarinki? Na yi maza na ce mata a’a, sai kawai na ji ta ce min, wai son Mubarak da kike yi. Nayi maza na ce mata ni? Ta ce eh ke.

Nace la yaya Dija ni ai ba son shi nake yi ba. Tayi maza ta ce, ke matsa can ki bani wuri karki nemi maidani yarınya karama mana in bakya sonshi me ke sawa ki na yin bacin rai a kanshi, meke saki kuka? Ai so ne Mero, ya yi miki aike ba yau ko jiýa ya fara ba ya dade yanayi ba wulakanci bane in yanzu kin daina karba shi kenan babu bacin rai a ciki da har za a je ana ta kuka shawarar da zan baki ita ce ki fidda shi a cikin ranki fito da miji kawai ki yi aurenki ga Mansur.

Na yi maza na katseta ta hanyar fadin kai Mansur? A’a ni yanzu bana son kowa. Ta sake zuba min ido saboda Mubarak da iyayenshi sun ki mu shi ne shima Mansur laifin zai shafeni, ai in ban manta ba a nan ne mukayi maganar nan da ke cewar da Mansur din da kuma Mubarak dukansu daya ne wanda duk maganar auren ta kama za a yi da shi, to ba za ki samu mas’ala ba za ki zauna lafiya da shi za kuma ki yi mishi biyaiya domin su dukansu biyun masu alheri ne babu kuma wanda zai iyakacin lokacinki a kanshi.

Nan take na soma yi mata kuka saboda jin irin kalaman da ta tsareni da su na baro gide na zo wajenta don in huta ita kuma ta zo tana yi min wasu maganganu da suke karawa zuciyata nauyi.

Assalarmu alaikum, wai ana sallama da Mero a waje. Sau biyu yayi maganar kafin na takarkare na daka mishi tsawa wanda watakila tsayar da nayi mishi ne ya yi dalilin fusatar yaya Dija tayi maza ta zabura ta mike tsaye ta ce min, maza tashi ki je kiga waye mai kiran naki ai don Mubarak ya yi aure ba zai zamo dalilin karewar maza a duniya ba, da ke wata mai zuciya ce ma da tsayawa kikayi kika fidda mijinki nan da kwata talatin a yi bikinki ki tafi gidan mijinki kije ki yi zaman aurcnki kowa ya huta.

Na tashi na fito don ba zan iya yin jayaiya da ita ba.

Mubarak na gani tsaye a kofar gidan tsaye jikin motar tashi da ga shi har ita sai wani sheki suke yi suna daukar ido, ga dukkan alamu dai shi Mugbarak dadinshi kawai yake ji bai da wata mas’ala a tarc da shi, wanna shi ne abin da yafi komai bata min rai wato ni ce mai damuwa, ni ce a cikin bakin ciki, ni ce rashin zuciya ya hanani samawa kaina zaman lafiya da kwanciyar hankali, ina ma dai ace nima halina irin na yaya Dija ne? Saurayi na yi na katse tunanin nawa saboda ganin ya nufoni zai zo in da nake tsaye, nayi maza najuya zan shiga gida, caraf naji ya kama gyalen da nake rataye da shi ya rike, abinda ya yi dalilin tsayawata.

Kina ganin kamar kin tsayawar da za ki yi ki saurareni yana da wani abin da zai amfanar da ke ne? Ni da ke ai muna bukatar fuskantar juna ne don musan abinda muke ciki.

Kaina a sunkuye saboda nauyin shi da nake ji, muryata tana rawa alamar idanuwana suna shirin zubar da hawaye na ce mishi, sake min gyalena bana so kar kuma ka sake yi min haka bana so. Da sauri ya sake min gyalen nawa, ban tsaya sake sauraron komai ba na yi maza na shige cikin gida na barshi nan wurin a tsaye, maimakon in tsaya wurin yaya Dija tunda har lokacin tana zaune a inda na barta wucewa nayi naje can cikin dakinta na hau gadonta na kwanta ina kuka, na kasa gane dalili, na kasa gane al’amarina, na kasa fahimtar yanda za a yi in zama jarumar kaina in fita hanyar Mubarak in daina ganinshi ina jin wani abu gani da shi, na zafi ko ciwo ko faduwar gaba a cikin raina.

Ina kwance ina yin kukan yaya Dija ta shigo ta sameni, nayi zaton wani fadan zata sake yi min sai na ji ta ce min, ki yi hakuri Maryamu wani lokaci zai zo da ke da kanki za ki gane ba Mubarak ne mijin da ya dace da aurenki ba, mijin da baya rarrashima me za a yi da shi ne? Ke kanii kika ce min bai iya rarrashi ba, bai iya bada hakuri ba, bai iya fadin maganganun soyaiya ba, to ai Mansur ya iya wadannan duka yana kuma sonki domin ko bayan aukuwar wadannan al’amuran ya zo gidan nan sau biyu yanzu ma don baya nan ne yasa kika ga shiru, to don me za ki damu kanki, akan mutanen da suka ki mu? Kin mu fa suka yi sun kimu ne saboda sun rainarmu in ba haka ba wane irin wulakanci ne haka su zargi lalacewa tsakaninki da dansu sannan su barki su aura mishi wata? Wannan wane irin son kai ne wannan? Wannan wane irin rashina dalci suka yi mana? Bana sonsu, bana son dansu, bana son duk wani abin da ya shafesu.

Tana fadin maganar tana kuka, nima kuma ina kara jin tsanar Mubarak da iyayerishi da duk wani abinda ya shafeshi cikin raina.

Assalamu alaikum, wai a gayawa yaya Dija tana da bako a waje. Sau biyu yaron yana shigowa yana fadin irin wannan maganar a tsakar gida, tana jinshi bata tanka mishi ba.

Yaya Ibrahim ne ya fito daga dakin su yana yi mata magana, wanene bakon na ki da yake wajen?

Mubarak ne kuma bana son ganinshi, bai yi magana ba ya fita wajen sai kawai gasu sun shigo tare, falon yaya Dija ya shigo da shi. Sannu da zuwa Mubarak, ya nuna mishi wuri ta zauna shima ya zauna suka gaisa sosai har yana tambayar shi anyi hidima lafiya? Ya amsa lafiya lau to Ubangiji ya sa alheri a ka hada ya amsa mai.

Jin shigowar tashi ya sa yaya Dija ta matsa kusa da bakin kofar dakin nata ta labe bayan labule suka gaisa ba tare da sunga juna ba, itarma  tayi mishi murnar auren nashi sai dai ita kam bai amsa addu’ar da tayi mishi ba, a hankli cikin natsuwa ya soma yn amgana wanda yake kamar dama ya samu na gaya musu abinda ke ranshi watakila don ya wanke kanshi.

Mafi yawancin lokaci mutum yana shiga cikin wani irin al’amari da bai taba zatarwa kanshi ba, al amuran da suka faru a cikin watannin nan uku zuwa hudu da suka wuce wadansu irin abubuwa ne da babu wani abin da zamu ce sai dai mu kara hakuri mu kara yarda da cewar komai yana tafiya ne bisa tsari da rubutun kaddarar da take kaddara mana komai.

Yaya Ibrahim ya ce, haka ne, sai ya ci gaba da magana, ni dai gaskiya a bangarena na shiga wani irin al ‘amarin a kunci da damuwa, gami da bakin ciki da tsanani irin wanda bana fatan wani wanda ban sanshi ba ma ya samu kanshi a irin wannn yanayin, duk wata fitina ina ganin kanar tana da sauki kwarai in har ta zamo babu fushin iyaye a ciki.

Da sauri yaya Ibrahim ya ce mishi, kwarai kuwa fushin iyaye ai musiba ce mai hankali kuma baya yarda ya zauna a irin wannan yanayin domin kullum fata muke mu rabu da su lafiya suna sanya mana albarka.

Maganar da yaya Ibrahim ya yi ta zama tamkar susa ya yi mishi inda yake yi mishi kaikayi, da sauri ya ce, yauwa na gode da ka fahimce ni ina fata kuma itama yaya Dija tayi min irin wannan fahimtar halinda na samu kaina a ciki na fushin da’mahaifina ya yi da ni shi ne dalilin da ya sanyani karbar auren da suka ba ni don in samu in fita daga cikin wannan al’amarin amma ba yana nufin wani abu zai canza ” bane tsakanina da Maryamu.

Cikin natsuwa naji shima yaya Ibrahim ya soma yin tashi maganar bayan ya yi gyaran murya, to amma Ahmad abinda kayi haka ai ina ganin baka kiyayi bacin ran iyayen irin kiyayewar da ya kamata ka yi mishi ba, ci gaba da mu’amala da Maryam kaima kasan ba zai zamo karbabben abu ba a wurinsu domin rabuwa da ita yana cikin sharadin da suka sanya maka, ina ganin maimakon ka dage kan ci gaba da mu’amala da ita har hakan ya sake jawo maka wata mas’alar tsakaninka da su da rabuwa da ita kawai kayi tunda ai ka riga kayi aurenka itama ta fidda miji tayi nata, ina ganin wannan shi ne abidna zai fiye mana sauki domina aI’amura sun riga sun faru marasa dadi masu bata rai da tayar da hankali, ya kamata ace mu dukan mu mu kiyaye sake aukuwarsu, don haka ina so in yi amfani da wannan zaman namu in rokeka ka fita hanyar Mero ka daina bibiyarta ka barta ta samu natsuwa da kwanciyar hankalin da zata fuskanci al’amarin ta, kaima ka samu natsuwa tare da iyalinka don ka samu zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da iyayenka.

To amma yaya Ibrahim kana nufin don na karbi auren da iyayena suka yi min sai hakan ya zama dalilin da ni kuma ba zan yiwa kaina nawa auren ba?

Eh haka zaka iya yiwa kanka, bance ba zaka iya ba to amma kuma gaskiya ba Mero bace wannan matar domin mun riga mun samu labarin komai don haka ina so in gaya maka cewar na rokeka ka fita hanyarta kawai. Ya ce to babu laifi na gode. Ya yi musu sallama ya mike ya fita.

Yana fita daga gidan yaya Ibrahim ya kirani dakin na zauna cikin ladabi ina sauraronshi, kin ji yanda muka yi da Ahmad, na ce mishi ch, ya ce to ki fitar da miji ki yi aure kinji ko baki ji ba? Na ce mishi naji, za ki fitar ko ba zaki fitar ba? Na sake cewa zan fitar.

Ya ji dadin yanayin da na bashi amsar a ciki, to Ubangiji ya yi miki albarka, na ce amin.

Ya tashi da nufin fita yana magana, daga nan zuwa rana ita yau ina so in ji bayani wurin Dija, na ce mishi to.

Da daddare rannan ina kwance kan gadon yaya Dija yayin da ita kuma take wurin mijinta bacci ne yaki daukata na rasa abinda ke yi min dadi, cikin raina na sani ni da kaina na gayawa yaya Dija cewar da Mubarak din da kuma Mansur duk daya ne wanda duk aka bani zan zauna da shi, amma a yau sai na kasa jin irin kuzarin da nake tare da shi a wannan lokacin da nayi wancan maganar, gaba daya dai halin da nake ciki nayi jarumtakar daina hana kaina yarda da cewar son Mubarak ne yake haddasa min abubuwa da nake fama da su na faduwar gaba da kauracewar bacci a idona, na yarda da cewar bacin rai ne na wulakanci da tozartawar da aka taru aka yi min.

Washegari da safe ina kicn ina kokarin sallamar ya’yan yaya Dija su tafi makaranta saboda bata fito ba a dalilin ta san ina gidan, ina cikin aikina sai kawai na jiwo muryar matar wan yaya lbrahim tana cewa wata da ban sheda ta ta muryar ba, lalle ne su hadu su je wajen uwar mijinsu su kai karar yaya Dija kan neman da take yi ta jawo ni ta dawo da ni nan gidan da zama bayan duk abin kunyar da na akata na jawowa iyayena da yan uwana abin magana, tana nema sai tayi dalilin da na shafa musu na bata musu sunan gidansu, in mu bamu damu da abin kunya abin magana ba saboda bamu da yawa ba wasu dangi ne da mu ba ai su nan gidan dole su ji tsoron abin kunya ko don yawansu.

Ko kadan ban ji dadin maganganun da na ji ba to amma kuma sai na kudurawa raina kame bakina in yi shiru ba tare da na gayawa yaya Dija abinda naji ba, iyaka dai kawai in hanzarta barin gidan in koma namu tun ban haddasa mata wata fitina ba, don nasan in taji ba zata yarda ba aurenta kuma aure ne da bashi da wani tarihi na wata fitina mai karfi sai danabin da ba za a rasa ba, kawai wanda zo mu zauna zo mu saba ke haddasawa musamman ma kuma da yake kusan a hade suke da iyaye da ‘yan uwa a wuri daya, ginin da yayi baisa ya yi nesa da su ba don haka ina gama aiyukan da zanyi mata sai kawai na yi shirina na jira ta fito nace mata za ni gida, tayi ta tambayata menene ban ce mata zan kwana biyu ba? Nace mata eh amma ai na fasa saboda zan bar baba shi kadai a gida.

<< Halin Rayuwa 30Halin Rayuwa 32 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×