Ta gallamin harara, Baba shi kadai matarshi fa?
An ce miki zaki yi ta zaman gida ne saboda baba? Kema zaki yi aurenki.
Nayi dariya kawai na kama hanya na tafi.
A gida ina zaune ne kawai bana komai bana kuma zuwa ko ina, ba makarantar boko babu ta allo, bana kuma fita ko ina ko daidai al'amura sun dan lafa na wakoki da rashe-rashen mutuncin da akayi tayi min a baya, na dan samu sauki na dan samu saukin ciwon da zuciyata take yi min a kan Mubarak saboda na daina yarda ina zama in bata lokaci. . .