Skip to content
Part 41 of 58 in the Series Halin Rayuwa by Hafsat C. Sodangi

Littafi Na Hudu

A wannan lokacin ba zai yiwu in iya kwatanta halin da nake ciki, ba na tsoro, abu guda daya dai da zuciyata ta kasa yarda da shi, shi ne a in bar Rauhani ya yi min abin da yake son yi min, da in har shi ya yi min hakan sai na gwammace ma kawai gara duk abin da zai faru da ni ya faru koda kuwa wani abu ne da ya fi hauka muni.

Tsayarwa kaina wannan hukunci da zuciyata ta yi, sai ya zama dalilin da na samu kuzarin takarkarcwa na kurmawa Rauhani ihu da iyakacin karfina.

A bar ni ba na son aikin, a bar ni kawai na ce a bar ni. Abinda nake ta fadi kenan.

Iskar da ke kadawa a dakin ta tsaya, nan take kuma haske ya bayyana a dakin, sai ga Mallam a zaune awurin zamanshi, hularshi zaune daram a kan shi, nima nayi maza na mike na zauna muka fuskanci juna ni da shi.

Maryam kin bata aikinki, kin yi duk abinda aka ce miki kar kiyi, kin yi musu, kin yi gardama, kin yi jayayya har da kokawa. Ya tafí yana fushi yanzu ya ya kenan?

Ban iya buda bakina nayi magana ba, balle in iya amsa mishi tambayar tashi, saboda har lokacin ina cikin tsananin tsoro, jikina ma bai daina barin da yake yi ba. Ban sani ba ko ya gane hakanne yasa shi kawo shawarar cewa ya sake kiran Rauhanin ya ba shi hakuri, ya yi aikin da ya zo yin don kar haukan da ya yi alkawari ya same ni.

Nayi maza na ce mishi “Aa, a bar ni kawai.” “A bar ki hauka ta same ki? Nayi shiru ban amsa ba, “Kin gwammace kiyi hauka ko?” Na sake yin shiru, “To shi kenan tunda abinda ki ka zaba kenan, duk abinda ya faru da ke dai ba za a sake kawo mana ke nan mu karbe ki ba, tunda kina cikin bijirarrun mutane masu taurin kai.

Sakamakon taurin kai kuma nadama ne. Ina kuma yi miki albishir da hauka kafin fitarki cikin wannan dajin.” Yana fadin hakan naji an daka min wata irin tsawa, wanda saboda tsananin tsoro na kasa fahimtar daga in da tsawar ta fito tashi ki ba mu wuri.”

Abinda naji an fadi kenan da karfi.

Ina jin hakan nayi maza nayi waje, yankawa kawai nayi da gudu ba tare da na tsaya neman takalmina ko tunanin ta ina na fito ina kuma ya kamata in dosa?

Gudu kawai nake yi a cikin jejin nan, bana ko waiwaye ban kuma san inda na dosa ba.

Gabadaya fatana da addu’ata bai wuce in isa gaban mahaifina kafin haukar ta same ni ba. Ina gudun ina kokarin jaddadawa kaina har yanzu dai da hankalina, hauka bata fara samuna ba tukuna, tunda duk abinda nake gani ina ganewa, ina kuma iya tuna komai nawa sai in yi maza in ci gaba da karanta addu’ar da nake ta karantawa Hasbunallahu wani’imal wakil.

Ina cikin haka na hango wani mutum a gabanta, tsoro ya kara kama ni, ina tunanin ko Mallam ne ya turo shi ya zo ya mayar mishi da ni, Nayi kamar in juya da baya saboda tsananin tsoratar da nayi, sai kuma naga to ai in shi dinne ma zan iya juyawar ya sake tare ni a inda na koma din, don haka na dake zuciyata na ci gaba da tafiya ta har naje kusa da shi zan wuce naga ashe manomi ne yake aiki a gonarshi, sai dai ban iya buda baki na tambaye shi hanya ba, saboda kar ya gane ni din bakuwar jejin ce.

Nayi tafiya rannan har na raina kaina, amma zuciyata bata gaji ba, ko tsayawa in huta bana yi, kokarina kawai in fita bakin hanya ne in ga gari in ga ta inda na bulla don na riga nasan na kauce hanya.

Ina cikin haka na sake hango wani mutum da sauri na nufi wurinshi daga nesa kadan na tsaya na gaishe shi nayi mishi tambaya kan hanyar da zan bi in shiga gari.

Barin abinda yake yi ya yi ya taya yana lallona, ke kuwa ya ya aka yi ki ka kawo yanzu cikin dajin nan? Ban iya ce mishi komai ba, don haka ya gaji ya ce min kina kusa da gari sai dai akwai tabkeken rafi a tsakaninki da shi, in kin iya ruwa za ki iya bin nan ki fada rafi ki tsallaka, in kuwa kin san ba ki iya ruwan sosai ba, sai ki bi nan don rafin yana da zurfi, in an yi ruwa ya kawo ba karamin ta’adi yake yi ba.

Na ce, Na gode. Har na fara tafiya ta nan din da ya ce, sai naji ya daga murya ya ce min kiyi ta tafiya har sai kin ga yar gada sai ki hauta ki tsallaka za ki ga kauye a nan za ki samü abin hawa zuwa cikin gari.”

Na sake cewa “To na gode. Wannan hanyar da ya nuna min din ita nabi nayi ta tafiya har na kai inda ya ce zan ga gada, gadar ta langa-langa ne, wanda mutancn wurin suka hadu suka yi don su rinka samu suna tsallakawa zuwa inda gonakinsu suke in ban da gudun ceton rai nake yi babu abinda zai sa in iya hawanta.

Na isa kauyen, a lokacin da duhun dare ya riga ya sauka ya mamaye ko ina, gashi babu haske ko kadan, don kuwa babu wutar lantarki a kauyen, babu kuma hasken farin wata saboda watan ya kusa karewa.

A haka na wuce kauyen nan nayi tafiya har inda na samu wani mai mashin da ya yarda ya fidda ni bakin hanya a dalilin tsananin gajiyar da ya gani a tare da ni.

A kofar gida na samu Babana a tsugune yana tashe da fitilar kwai, daga ganinsa kuma nasan ya yi wahala ya neme ni har ya gaji.

Ina isa gabanshi na fadi a kasa ina kuka tare da fadin “Ka yafe min Baba.” Ban wani tsaya bata lokaci ba nayi maza na rattaba mishi bayanin komai, tunda nayi saa nazo gabanshi da hankalina, shi yasa nayi maza na gaya mishi don ya sani saboda kar haukar ta same ni yayi tunanin zai yi ta wahalar neman min magani tunda ba hauka ce da zata warke ba, ka taimake ni Baba ka tsare ni wuri daya kar ka bar ni in yi ta yawo a tube irin yadda nake ganin yan uwana mahaukata ana barinsu suna yi.”

“Ke Yahcuwuna. Ya kira sunan nawa cikin wani irin yanayi na damuwa, “Ki daina yin haka bari fadin irin wannan maganar, ya ya kike yi wa kanki mummunan fata irin wannan? Nayi maza na ce, “Baba mai Rauhani ne ya gaya min ai har kokawa da Rauhanin ma nayi.

Ya mika hannu ya kama nawa “Zo mu shiga gidan, na godewa Ubangiji da ya dawo min da ke lafiya.”

Baba Lantana ta galla mishi harara ta ce, “Uhun, ai kai kam ka shiga uku, yarinya ta tafi taje ta gama barikinta ta dawo tana dingishin ta samu wadanda suka fi karfinta, amma kana bari kana fadin wai ka gode Ubangiji saboda ta maida kai sakarai.”

Isyaku ya yi sallama daga tsakar gida ya tsaya yayi tambaya, “Baba wai Anti Meron ta dawo?” Da sauri Babana ya ce, “Eh, ta dawo.” Ba tare da ya tsaya tambayar in ji waye ba, ta sake fadin “Ka ji wani irin rainin hankali ma Malam, sai ka ce ba tare suke ba, sai ka ce ba shi ya kawota ya ajiye ya wuce gidanshi…”

Tayi maza tayi kasake ta bar maganganun da take yi ta koma sauraron bayanin da Baba yake yi min.

Ai ba za ki yi hauka ba, ai karya yayi miki ba Rauhani ba ne, shi mutumin ne da kanshi yayi miki wannan abin don ya samu ya tsoratar da ke, ki yarda yayi lalata da ke. Ba mutumin kirki ba ne, Boka ne. Ko Malamin tsubbu. Ba da Rauhani ki ka yi kokawa ba, bai yi nasara ba ne a kanki saboda ke din mutuniyár kirki ce, uwarki ma haka, Ramatu mutuniyar kirki ce sannan bata da tsoro.

Baba Lantana taja mummunan tsaki “wannan Ramatu ai bata kyauta ba da bata jaka ku ka tafi tare ba.”. Tuni sai ta bar maganar da take yi ta ni da Mubarak muka fita yawo, ta koma ta Rauhani da hauka don tafi yi mata dadi.

“Hauka kam ai sai kin yi tunda Rauhani ya ce sai kin yi, to shi yana karya ne ma da za’ka ce mata ba za ta yi ba? Ba dai har nan dama Dijan take kai ki ba? Ai kuwa dai kun tsokano tsuliyar Dodo.”

Sallau yayi sallama ya shigo tare da fadin “Baba ashe ta dawo?” Ai ta dawo Sallau ya sake fita ya sayo min shayi da biredi in banda yayi wannan dabarar watakila da haka na kwana ni da Babana ba muyi wannan tunanin ba, balle Baba Lantana.

Kwana muka yi Babana yana rike da allon karfenshi yana rubutu yana wankewa yana bani ina sha, saboda na kasa ko da runtsawa ne in yi saboda tsananin tsoron da nake ciki.

Washegari da sassafe sai ga Yakumbo Halima da Yaya Dijah sun iso, ita kam Yakumbo taje wajen Yaya Dijah ne wai ta ji taje na karbo sakon ko ban je ba naki zuwa? Yaya Dijah ta ce, “Ai ma wunin jiya ba a ganni ba ana ta nemana kan haka suka rankayo gida don su gani na dawo ko ban dawo ba? In ban dawo ba a nufi gidan Malami.”

Sai suka zo suka same ni, Babana ya kwashe bayani yayi musu, suka yi wa juna barka saboda ban yarda na ambaci sunan Yakumbo Halima cikin bayanin da nayi mishi ba, da ban san yadda suka kwashe ba.

Bayan fitanshi ne Yakumbo ta rinka rantsuwa wai tana so in yarda bata san haka yake ba, don bai taba nuna mata ba. Yaya Dijah ta ce mata “Haba Yakumbo, bari wannan rantsuwa da ki ke yi, za ki kai ta in da za a cuce ta ne da saninki.”

Wai a wannan dan zuwan da suka yi sai da Baba Lantana ta sossoka musu maganganun da Yakümbo ta tanka mata suka yi fada kaca-kaca.

Ba karamin rashin lafiya nayi ba saboda wahala da kuma ciwon da kafafuwana suke yi, tayi a dalilin raunukan da suka samu ta hanyar taka kayoyin da ke watse kan hanyoyin jeji da kananan itatuwa.

Duk da halin da nake ciki na kusan kullum sai Babana yasa allura ya cire min wata kaya a kafa, ba wannan ne abinda yafi damuna da tsaya min rai ba, irin tabbatar min da Babana yayi cewar shi wannan mutumin da muka je wurinshi ba kowa ba ne illa Boka saboda ni da kaina na taba kamanta wani hadisi da ya ce, “Wanda duk yaje gun Boka ya kuma yarda da abinda Boka ya gaya mishi, to ya kafurta da abinda Manzon Rahama (S.A.W) yazo da shi, in kuwa yaje wurin Boka bai yarda da abinda Boka ya gaya mishi ba, to zai yi kwana arba’in yana ibadar da ba za a karba ba.”

To wannene mai sauki a ciki? Sai na samu kaina cikin wani irin yanayi ma tsananin rashin lafiya a dalilin tsananin tsoro da tasin hankali, babu abinda nake tsoro irin mutuwa a tsakanin wadannan, ban samu yar nutsuwar zuciyaia ba sai da Babana yayi min bayani dalla-dalla, lokacin ne na dan samu natsuwar zuciya ta na koma yin Istigifari da kyautata zato wurin Ubangiji tare da kudurawa raina ba zan sake ba.

Ba zan sake zuwa wurin wani ba da sunan neman taimako akan aurena ko a kan wani dalili na daban, dama can ban taba ba, in ban da warinan lokacin to ba zan sake ba gaba daya lamurrana dama ga Ubangiji suke, gareshin kuma zan kara maida su, in kara dogara in har da rabon zan yi aure an rubuta cikin kaddarar rayuwata, to zan yi. Don nayi Imani da kaddara mai kyau da mara kyau.

Sanna rashin auren in har an kame kai ba zai zamo munnaunan kaddara ba in har ba a rinka watsewa ba, nan take nä shiga tunano manyan mata da suka gama rayuwarsu ba tare da sun yi auren ba, ko suka bar shi a shekarunsu naa kuruciya suka maida hankulansu kawai wajen yin Ibadarsu, da auren da ba a san ka’idarshi ba, ba a tsare mutunci da sharuddodinshi ba, ai gara barin shi yafi.

Nan take sai naji zuciyata tana kara raya min tsare budurcina da yin komai wajen ganin budurcin nawa yaci gaba da kasancewa a tare da ni, matukar ina cikin hayyacina saboda in zamo daga cikin ‘yanmata masu mutunci da ke kaiwa mazajensu yanmatancinsu, ko kuma suke gama rayuwarsu su koma ga Mahaliccinsu da abinsu a tare da su.

Kan haka sai na kara kudurawa raina cewar zan kara kyautata sana’ata in kara riketa hannu bibbiyu don ta zamo min abinda zan rike wajen ganin nayi ta karatuna, ban zamo mai dora nauyina ga kowa ba.

Kusan satina biyu a gida ban fita ko’ina ba, ina jinyar kafafuna a kwanakin nan duka babu wata rana da gari ya waye har yamma tazo ba tare da Baba Lantana ta jaddada min haukan da Rauhani ya ambata min zai same ni ba, don kuwa in ita muna yi mata rashin mutunci muna kwana lafiya, don kawai kaddarar wahala ta kawo ta gidanmu, ta auri tsohon ubanmu, to ai shi Rauhani ba zamu yi mishi iya shege ya kyale mu ba, tunda ba tsoron ubanmu ya ke yi ba.

Ko kallonta bana yi, maganar tata kuma ba ta damuna saboda a yanzu, na ragë damuwa da al’amarinta, ban da haka kuma nafi yarda dá maganar Babana a kan tata, don haka ina cikin kwanciyar hankalina, ga kuma neman auren da nasan Yaya Dijah tana yi wa Babana, wanda nasan ba da dadewa zai tabbata, tunda na shaida abubuwa da dama da ta gabatar. Na soma zuwa Makaranta, wai ashe dan wannan neman nawa da Babana yayi a gidajen makwabta da ke kusa ma wai abin magana ne, ya madidi ake tayi da ni da shi ana fadin wai ai gashi nan ya ki aurar da ni yana jira sai ya samu’ dan mai kudi irin Mubarak.

<< Halin Rayuwa 40Halin Rayuwa 42 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×