Skip to content
Part 48 of 59 in the Series Halin Rayuwa by Hafsat C. Sodangi

Cikin natsuwa da yanayi na rage murya naji Babana ya ce mishi, to ai banga kamar har yanzu yana kan maganar nan ba tun yaushe rabon da ka ji sun turo kan maganar? Sannan tunda akayi aikin nan da kwana biyu har zuwa yanzu ban sake ganinshi ba.

To in baya cikin neman saboda wa yake hidimar da yakeyin’? In ana tunanin ko makwabtaka ne shi yafi kowa sanin hakkin makwabtaka baba? Ai ya gaji da turowar ne yasa ya hakura ya zuba ido yaga iyakar al’amarin.

To tunda ya nuna ya gaji yanzu sai a yi yaya da shi Tbrahim? Ba shi kenan ba sai a yi da wanda bai gaji ba yake ta kai kawo. Cikin zuciyata na sake cewa a to.

A’a Baba a basu hakkinsu tukunna sai in sunce basa so shi kenan sai a yi da wannan din, a ra’ayina ina ganin a yi musu aike a gaya musu in suna so su zo in suka ce basa so shi kenan.

Hannu biyu na saka na dafe kirjina saboda tsananin harbawar da yake yi cikin tsananin karfi saboda tsoratar da nayi da maganar tashi, ban taba jin muguwar shawara ba irin wacce ya baiwa babana a yau.

A tambayi Mubarak da iyayenshi sai in sunce basa so na ne za a aurar da ni ga wani wannan wane irin zace ne? Tambayar da nake yiwa kaina kenan sai naji ya cigaba da bayani yin hakan ba komai ba ne baba ba kuma wulakanta kai bane aure ne shi kuma auren darajarshi ta wuce duk yanda ake zato, in wasu sunyi mana mummunar fassara ma to mu kam ai babu ruwanmu tunda mun san alheri muke nufi ba kuma don wani abin hannunsu ba. Bayani sosai ya yiwa babana har dai ya gamsar da shi ya yarda da shawarar tashi.

Cikin zuciyata na ce, na shiga uku yanzu bayan duk abinda na wuce a baya kuma bai isa ba har sai an sake jawo min wani wulakancin mai salo na daban.

Yaya Ibrahim yana barin gidan naje na samu Anti Safara wai in yi mata magana ko zanyi sa’a ta yarda ta yiwa babana magana kan rashin dacewar abinda suke shiryawa sai kawai naga ta kalleni cikin natsuwa ta ce min, to ai yana jin maganarki kema ki sameshi mana kawai ki gaya mishi. Yanayin da ta yi maganar a ciki yasa na gane abinda take nufi don haka na wuceta nayi tafiyata.

Ina jin baba Lantana daga dakinta tana fadin ina ma dai in anje su koro wanda yaje din kwadayi mabudin wahala, in da kwadayi da wulakanci, kuda wajen kwadayi yake mutuwa, yaron nan da iyayenshi ba tun yau ba sunce basa so basa so ba sa so amma kun ki yarda ku hakura kun manne sai dole sun karba kai tir.

Duk da irin wadannan kalamai da baba Lantana ta wuni tana yi basu sa babana ya canza daga abinda suka shirya ba.

Washegari da safe naji yana cewa anti Safara, yau fa za ni sallar juma’a da wuri kuma zan tafi don sai naje gidan Alhaji Muhammadu nayi mishi maganar nan kafin in wuce masallacin.

Da kanka kenan zaka? Ya yi maza ya ce, ei ai gara inje kawai da kan nawa babu komai ai maganar aure ne ya yi magana da dan shi ne in suna so shi kenan su zo in kuma basa so shi kenan mun fita hakkinsu sai a yi da wannan da yake tsayen, ta ce haka ne Ubangiji ya zaba mana mafi alheri, ya ce to amin.

Hankaline ya yi matukar tashi ban taba ganin yariyar da aka yiwa irin wannan tallan ba sai ni dama dai inyi sa’a suce basa so shima Dr. Bellon ya ji labari ya ce baya so na ya fasa in ga yanda babana da yaya Ibrahim za su yi da ni tun da dai na lura gajiyar da sukayi da ni ne ya sa suka yanke hukuncin yi min irin wannan wulakancin.

Ban san abinda ya faru tsakanin babana da Alhaji Muhammadu mahaifin Mubarak ba illa iyaka dai da daddare Isiyaku yayi sallama a zauren gidanmu da anti Safara ta amsa mishi kuma ya shigo har dakina ya sameni cikin fara’a ya soma gaisheni ina amsawa a natse, sai da muka gama gaisuwar sai ya kalleni cikin murmushi yana sosa keyarshi ni da yallabai ne ranki ya dade, ya dade ne yana zaure yana son ganinki, nace to madalla.

Ya dan saurara ko zaiji na sake yin wata magana bai ji ba ya gaji ya sake tambayata, me zance mishi? Ban kalleshi ba na ce mishi abinda kaga ya maka, ya gaji da tsugunno ya tashi ya tafi ban san yaya suka kare ba. Kwana biyu a jere ko leken kofar gida ba saboda bakin ciki da takaicin yadda yaya lbrahim da Babana suka hadu suka zubar min da ‘yancina, ban sake jin wani motsi ko wata magana. daga wurin kowa ba sai kawai na gane Mubarak da iyayenshi sun karbi tallan aurena da su babana suka kai musu a daliin wasu yan al’amura da na lura da su.

Shiryawa nayi da safe cikin kwalliya mai sauki mai kuma ban sha’awa riga da-siket din atamfa ce a jikina ni na yiwa kaina dinkin don haka ba sai na tsaya cewa sun dace da jikin nawa ba, na Sanya takalmi silifas dan Italy tare da ‘yar karamar jaka ta pos a hannuna, maimakon in yi tafiyata haka ko in yi damara kamar yadda ‘yan mata a lokacin sukeyi sai na jawo wani dan madaidaicin gyale na yane jikin nawa sai dai bai hana kwalliyar tawa bayyana ba.

Na fito tsakar gida ina gayawa anti Safara zanje wajen yaya Dija yanzu zan dawo.

Ta tsaya tana kallona nuna alamar bata gamsu da yadda nayi mata bayanin ba, sanarwa kenan ba neman izini ba, na yi maza na ce mata yi hakuri anti ba sanarwa ba ne neman izini ne, ba zan dade ba.

Ta yi murmushi ta ce, to ki gaisheta, nace mata to za ta ji, na kamo hanya na fito daga gida ina jin baba Lantana tana fadin, anyi jiran anyi jirani abin ya gagara har an koma yin talla, ban kulata ba çikin zuciyata dai na shirya zuwa wurin yaya Dija ne don in san menene ake ciki, in kuma gaya mata ra’ayina kan hakan da aka shirya don ta sani.

Yar tafiya ‘yar kankanuwa na fara yi, nufina in karasa bakin hanya inda zan samu abin hawa sai kawai ga Isiyaku ya biyoni da sauri har yana haki, wai ki dawo in ji shi.

Na ja na tsaya ina kallon Isiyaku cikin takaici, kai Isiyaku… kafin in gaya mishi abinda nake nufin gaya mishi sai naga ya saki wani lallausan murmushi, ai ba daga ni bane ya fada da rantsuwa kafin ya ce shi yallabai ranka ya dade din ne ya ce in zo in gaya miki kar ki tafi ko ina gashi can suna tsaye shi de bakinshi.

Ban san dalili ba bana iya karya dokar Mubarak ko da dai a lokacin zuciyata tana raya min ne wai zan bi umarnin nashi in komá gidan ne in bar tafiyar saboda kar in kunyata shi a gaban bakin nashi amma can cikin raina ni da kaina na sani ba haka bane, ba don su ba ne, maganar guda daya ce a duk hali ko yanayin da muka samu kanmu a ciki ni da shi bana iya sabawa ko bijirewa umarninshi.

Na juyo da baya na koma gida a makogarona ina fadin don dai kana da baki ne kawai a zuciyata nasan ya zama min tilas in koyi jaruntakar da zan koyi bijirewa irin wadannan dokokin nashi ba komai ya ce min shi kenan ba.

Ina tsaye a kofar dakina ina kokarin bude kofar tare da yiwa anti Safara bayanin sai an jima za ni sai na jiyo sallamarshi a cikin zauren gidanmu da kanshi ya yi sallama alamar bai zo da dan aike ba nayi kamar kar inje sai kuma naga to ai baba Lantana tana kallona ni kuma bana so ta sheda wani al’amari a tsakanina da shi don haka na juya na koma zauren tuni har kamshin shi ya mamaye ko ina a wurin kwalliyar kananan kayan kuma yi matukar karbarshi.

Ina zaki da safen nan kikayi wanna kwalliyar haka? Ban san yanda akayi ba naji bakina ya bashi amsa, gidan yaya Dija, to yaya za ki fita baki gaya min ba? Ba ki ji maganar da babu yaje ya gayawa baba bane? Nace ban ji ba na fadi hakan a daidai lokacin da succinate ke nanata maganar tashi, ba ki ji maganar da Baba ya je ya gayawa Baba ba ne? Wato Babana ne ya je ya gayawa babanshi cewar da nayi banjin ba da yanayin da nayi maganar a ciki ya sashi zuba min ido yana kallona, ba ki ji bane ko kina da wata magana ne, tsakanina da ke ai babu wani boye-boye ko kin yi nufin buyan ma ba zai yiwu ba don babu wani al’amarinki da ban sani ba, don haka fadi gaskiyarki kawai in kina da wata magana ne kuma kiyi.

Na daure fuska sosai kafin nace,  ina da ita, da sauri cikin natsuwa ya ce, ai kinga hakan yafi fadeta inji. To ni gaskiya ba da yàrdata aka yi miin hakan ba a ma. Shawarceni ba don haka bana so karma ka dauki hakan da wani muhimmanci da har zaisa ka rinka neman ka shiga harkokin rayuwata bana so.

Ya dan gyara tsayuwarshi kadan kafin ya tambayeni bakya son me? Na yi shiru ba kya so kamar yaya? Aima gana za k yi don in gane abinda.

Na sunkuyar da kaina don kaucewa kallon da yake yi min in kuma ji dadin gaya mishi abinda nake son gaya mishi. Nace bana son auren da ake shiryawar saboda bakai nake son aura ba ina son auren saurayi ne dan uwana kamar yadda nake budurwa ba inje ina auren mijin wata ba.

Hankalinshi a kwance ya tambayeni, to yanzu yaya kike so a yi? Na ce rokonka zanyi ka fita hanyata ka daina kulani ka daina shiga harkokin da suka shafi gidanmu.

Wani irin lalataccen kallo ya yi min kafin ya tmabayeni, kenan har kina da wata harka taki da ake shiga, yaushe rabon da kika ga na daga ido na kalleki.

Kirana aka yi kirjina ya bada wani irin sauti na dum, a dalilin jin kirana aka yi nan da ya ambata na shiga uku ni yasu tawa ta sameni, yaya Ibrahim ne ya yi min sanadin wannan wulakancin gashi tun ba a je ko ina ba an soma gorantamin ban iya daurewa na soma kuka ban iya tsayawa ba na juya da nufin in shiga gida sai ya yi maza ya tura kofar zauren dake wurin ya rufe ya hanani shiga ban daina kukan da nake yi ba.

Kin shiga uku ke ‘yasu taki ta same shi yaya Ibrahim ne ya yi miki sanadin wulakanci gashi tun ba a je ko ina ba an soma goranta miki, to da aka yi miki me? Kina so ki gaggan tsaramin maganganu ina kallonki inja bakina in yi shiru? Ya soma yin magana kamar yana nufin yin rarrashi, nayi naza na bijire mishi gabadaya tunda gori ai shiga cikin maganar ai kuma shi kenan magana ta kare ban shiga ba ma kenan ina kuma ga na shiga gaskiya ba zan iya ba da wanne zan rinka ji da gorin da zaka rinka yi min ko da wanda da ‘yan…

Kinga Maryam kinga, nayi maza na bar maganar saboda jin kinga-kingan da ya fara ambatawa don haka na koma yin kukan kawai ina fyace majinata da bakin gyalena.

Nace in kina da magana mai ma’ana ki yi ina jin ki na tsaida kukan da nakeyi cikin natsuwa na ce mishi a fita hanyata kawai, ban sake yin wata magana ba ya juya ya fita yayi tafiyarshi na dawo cikin gida na zauna ina tunanin al’amurana da na Mubarak babu wani alherinshi ko taimakonshi a kaina da ban tuna ba ko ince na manta a’a komai irin sa ne dashi sai dai yadda zuciyata take rike da wannan lissafin haka kuma take rike da abubuwan da suka faru tsakaninmu da gidansu, da abubuwan da mutanen unguwa suka yi ta fadi tuni dama mutane da yawa suke fadin wai babana yaki aurar da ni ne yana jiran Mubarak din saboda kwadayin dukiyar gidansu, ba wannan ne abinda yafi komai damuna ba irin dauke kafar da ya yi tun muna asibiti har kawo dawowarmu gida bai zo ya gaida babana ba yana ganina ina ganinshi sai ya yi kamar bani yake kallo ba sannan a hakan wai an bisu har gida ance in suna so su zo bayan ga wani yana takai kawo a kaina an san za a bashi ni me yasa ba a bashi din ba tuntuni tun sanda suke zirga-zirgar aike shi da mahaifinshi sai a yanzu da suka tattara mutane suka yi watsi da su?

Ina alwalar sallar azahar a tsakar gida Rukaiya ta yi sallama ta shigo, ran amaryarmu ya dade, ban wani kulata ba don ana jin kamar ina son wasan nata, anti Safara tayi mata sannu da zuwa ta kuma jagoranceta zuwa dakinta hakan ya kara tabbatar min da cewar ba wurina tazo ba, a cikin zuciyata dai na kasa tunano yaushe rabonta da shigowa gidanmu? Dakina na wuce na soma gabatar da nafila kafin in yi farillar har ta bar gidan kuwa ban san yanda na tashi daga kan sallayar ba don amin amin, dakina ta shigo ta samen, ke kuma menene haka kika shige daki kika hau gado kika zauna ba za ki bar gidan ba sai masu kawo kayan sun zo sun sameki?

Na tashi na zauna ina kallonta, kayan me za a kawo? Harara da dakuwa ta hadamun gaba daya, ba fa na son rashin kunya, na ce to yaya dija ni ina sanin abinda ake ciki ne? Kin san irin bakaken maganganun da ya zo ya dankaramin kuwa? Ni gaskya, ta ce to ba yanzu ne lokacin fadin gaskiyar taki ba mai gaskiya tashi ki shiga gidan baba Sumaye don kar su zo su sameki a nan a ce kin yi rashin kunya tunda ina ganin kamar za su zo da yawa saboda ya ce min zai hada komai a azo da shi kayan na gani ina so kayan sa rana, kayan aure da kuma na sakun lalle don baya so a saka mishi lokaci mai nisa.

Ban iya ce mata komai ba saboda hayaniyar da ake yi a cikin gidan alamar mutane suna kara shigowa, anti Safara kuma sai kai kawo take yi tana kokarin ganin kowa ya samu abinda zai kai bakinshi.

<< Halin Rayuwa 47Halin Rayuwa 49 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×