Skip to content
Part 49 of 53 in the Series Halin Rayuwa by Hafsat C. Sodangi

Duk da kokarin da yaya Dija tayi na ganin na fita gidan ba tare da an ganni ba sai da wasu suka gannin basu kuma ja bakunansu sun yi shiru ba sai da suka yi tambaya, ai dama amaryar tana gidan ne? Sai dai ba su yi sa’a sun sami mai basu amsa ba muka wuce kofar baba Lantana a kulle kamar bata nan nayi maza na kalli yaya Dija na ce mata, tana ciki fa ta kulle kofar ne kawai irin yadda tayi ranar da aka je jeran anti Safara, bata amsa min ba.

A gidan baba Sumaye dakin da muka saba zama sanda muke yara na shiga na hau dan gadon bonon da ke wurin na kwanta, maimakon zuciyata ta tsaya wajen tunanin alamarin dake faruwa a kaina a halin dan ake cii sai ta koma tunanin da rayuwar kuruciyata tun sanda nake yar karamata sosai mu’amalata da su Jumare har kawo ranar da na wayi gari a wannan dakin ina baccin da ake kira baccin hasara na rasa Innata ban sani ba, hasken rana ta tashi na fito waje idanuwana suka sheda dimbin jama’ar dake sallatar wata gawa dake shimfide cikin makara a ka kuma lullubeta da zanin Innar tawa amma ban gane itace a kwance a ciki ba, hawaye suka soma zuba min ganin babu kowa a gidan sai ni kadai ya sa ni na sake nayi kuka har sai da na gaji nayi shiru don kaina ban kuma wani dade ba bacci mai nauyi ya daukeni wanda ban tashi ba sai da naji ana taba ni na bude ido naga baba Sumaye a firgice na ce mata, magariba har tayi baba?

Ta ce eh, nayi maza na ce ban fa yi la’asar ba, ta ce to ai sai ki tashi ki yi, na idar da sallar magariba ina addu’a ita kuwa baba Sumaye sai fadi take yi, kai uh-uh uhhh, ta gyada kai jimawa kadan ta sake nisawa ta ce, mu mata muna da aiki shi namiji a kan matar da yake so ai maganin shi hakuri ne kawai in kayi hakuri komai sai ya wuce amma in ba haka ba ai abin da wahala wannan irin kaya da Alhaji Mubarak ya yi miki dame sukayi kama ni Sumaye? Ta kama baki ta rike tana fadin, kinga ni ko kayan auren ban gama gani ba na tashi balle kuma sauran komai fa a ciki sha biyu ne dozin sai bayani baba Sumaye take yi min tamkar dai ta mance ni ce amaryar a wancan lokacin namu kuma ba a hirar aure ko kayan aure da wacce za a yiwa aure.

Ban samu ganin kayan auren da baba Sumaye ta bani labari ba saboda gaba daya kayan babana ya ce yaya Dija ta tafi da su can gidanta ta adanasu.

Kwana uku da kawo kayan auren Mubarak ya zo a zauren gidanmu na sameshi da ganinshi nasan zuciyarshi a soshe take saboda yanayin da na gani a tare da shi, daga wurin yaya Dija nake naje wajenta ne don ina so in yi muku adalci dake har ita da na so da sai kawai in samu malam Ibrahim in nemi alfarmar lokacin da nake so a sanya min na biki to banyi hakan ba sai naje na sameta don in baku damar ku me kika gaya mata da yasa ta ce min wai zai shiga wannan maganar ne kawai in mun warware mas’alar da ke tsakaninmu? Menene a tsakanina da ke? Me na yi miki? Me yasa ke baki da sassauci kan abinda ya shige daga shekaru biyar zuwa yau za ki iya tunawa da wani abin da kika yi min guda daya da niyyar ki in ji dadi? Kina tsammanin in banda wani al’amarin na daban a tsakaninmu da ke zan lamunci irin wadannan abubuwan ne? Ai bana son bacin rai Mero.

Abinda ya kenan ya tsare mutum ya yi ta gaya mishi maganganu in banda haka bai iya komai ba gaba daya samarin da nayi ban taba ganin wanda baya zama ya gaya min irin son da yake yi min ba sai shi tsawon rayuwata da shi bai san ya yabi kwalliyata ba sai dai ya saya min kayan adon kawai dana kai munzali na ‘yan matanci gaba daya burina ya yabi kwalliyata ne don inji dadi bai yi ba ko ince baya yi na kai wani matsayi na bukatar ace ana sona bai yi ba wasu suka yi ta furta min, hakan na kasa jin dadin kalmar a bakunan su saboda ba a wurinsu nake son jinta ba, bai buda baki ya gaya min irin son da yake yi min ba sai a loakcin da al’amura tsakanina da shi suka rikice ko ince suka lalace ya fadeta a sanda fadin nata bai amfanar mana da komai ba tunda wannan lokacin kuma bai sake gaya min wata magana makamanciyarta ba da zata sani in ji sanyi ko inji dan wani sassauci a zuciyata, ban san yanda aka yi ba naji nakina ya ce mishi, nifa nafi son auren mutumin da zai rinka furta min kalmomi masu dadi yana gaya min irin son da yake yi min.

Maimakon da ya ji hakan ya gaya min wata magana mai dadi sai na ji ya ce min, to ya ya za ki yi da kaddarar rayuwarki Mero? Ko wace mace ai da irin kaddararta ke taki kaddarar ita ce ta ba za ki auri saurayi ba mijin wata za ki aura ba kuma za ki auri wanda zai zauna yana yi miki irin wadannan kalmomin ba don bai iya ba.

Na 6ata rai na ce ko kuma a kaina ba? Eh to watakila a kankin ne kawai nake hakan da kuma za ki yarda da shawarar da zan baki da kin daina kawo zancen wata a tsakanina da ke.

Na yi shirn shima ya tayani yin shirun na dan wami lokacin kafin ya kawar da shirun da tambayata, da ma damuwar kenan? Ban kula shi ba, sai na ji ya kara sassauta muryarshi a hankali, cikin nutsuwa a soma cewa, ban yarda na koyi irin wannan rayuwar ba ne Maryam saboda nafi so da sha’awar rayuwa irin wacce na samu iyaye da kakannina a kai ina irin rayuwa ta kunya da kawaici kan abindą kake so musamman mace kin gane? Shiru nayi ban ce mishi komai ba har ya yi min sallama ya tafi a kan gobe zai yi sammakon tafiya Legos nace to Ubangiji ya kiyaye hanya, ya ce to amin.

Na gode.

Kwana hudu bayan tafiyar Mubarak aka yi bakon wani dattijo a gidanmu ganin shi da zanen barebari irin na babama da nayi da kuma sanin da nayi cewar babana yana mutunta duk wani mutumin da ya gani da irin wannan zanen a fuskarshi ya sa nima na mutunta wannan dattijon ta hanyar shimfida mishi tabarma a cikin zaure, na kawo mishi ruwan sanyi tare da butar alwala da kuma abincin da aka girka wanda bai yarda ya taba komai a ciki ba in banda butar da ya dauka ya je ya taba ruwa ya sake daura alwalarshi da ta kárye a sanadin taba ruwan da ya yi sannan ya dawo kan tabariar ya sake zama ya zubamin ido yana kallona cikin natsuwa ya tambayeni a daidai lokacin da ya ci gaba da jan dogon carbinshi yana kos kos kos, to ina malam Bukar din da tace nan din gidanta ne tace babanta ne?

Kai tsaye na fahimci inda yake nufi tunda shima baban nawa shigen irin hausar da yake yi kenan na ce msihi e maiam shi ne babana, ya gyada kai ya ci gaba da abinda akeyi.

Ni kuma na mike na shiga gidi na dauko gyaiena bayan na shedawa anti Safara cewar zanje kiran babana saboda wani bako mai irin zanen shi ya zo wai yana son ganinshi ta ce to yi maza ki kira mishi shi nace mata to na fita.

Bako da irin zanena ya zo nema? Ya yi min tambaya cikin yanayin murmushi na yi maza na ce mishi ci baba, ya ce to muje gani nan zuwa, na ce mishi to na dawo na cewa bakon gashi nan zuwa na Wuce ciki bayan ya amsa

min ta yanayin gyada kai saboda ya riga ya shagala da mu’amalar da yakeyi da carbinshi.

Ina daga cikin dacina a zaune na ji isowar babana saboda kaurewa da yayi da wani irin barbarci na sha jin shi yana furta lcalmomi har da hira cikin harshen nasu idan yaga abolkan harshen nashi amma ba irin na yau ba aa hankali na sake fiitowa daga dakin nawa cikin sanda na leka zauren don in ga meke faruwea mutumin na gani a tsaye ya saba gorarshi ta ruwa da tun sanda na kai mishi buta ya sake cikata da ruwa alamar tafiya zai yi yayin da shi kuma babana ya bajea kasa yasa hannu biyu yana rike da kafafuwanshi cikin yanayi na bada hakuri.

Ka yi hakuri Abba Gana ka yi hakuri kar kace zaka tafi nasan nayi maka laifi amma tunda har ka iya nemana to kayi halkuri ka zauna.

To tayi hakuri ta zauna tayi menene? Ba ta riga ta ganta ba ba shi kenan magana ta kare ba, ai ta ganta taji dadi ta gofe tasan tana raye itace kawai bata je wajenta ba.

Gabana ya fadi kar dai dan uwanka ne wannan ga zatona a zuci nake yin maganar ashe ban sani ba ta fito sai kawai naji babana ya ce min, eh Yacuwuna babanki ne wana ne uwarmu daya ubanmu daya, ban san sanda na kama ihu ina buga tsalle tamkar wata zararriya da sauri anti Safara ta fito tana tambayata menene? Ban iya bata amsa ba kartawa kawai nayi da gudu na nufi gidan yaya Dija don in kai mata labarin, gaba daya muka dawo har da yaya Ibrahim da yaran ya kwaso mu a motarshi saboda na sameshi a gidan.

Tuni har zaurenmu ya fara cika da jama’a makwabta baba Bairu da baba Hodijo da ma wasu makwabtan sun hadu sai taya babana bashi hakurin ya zauna suke yi, shi kuwa yaja ya tsaya sai nanata kalmominshi yake yi ta riga ta ganta ai ta gode ta ganta da ranta da lafiyarta to inta zauna me zata mata?

Ka yi hakuri malam ka yi hakuri ka zauna na rokeka ka yi hakuri, cikin yanayi na natsuwa da girmamawa yaya Ibrahim yake bashi hakurin baba Baidu ya kaelshi ya ce mishi, kayi mana malam wannan mai rokon naka ai surukinka ne shi ne mijin babbar yar taka?

Abba Gana yana jin haka jikinshi ya yi sanyi alamar surukuta tana da karfi da muhimmanci a wurinshi, a hankali ya koma kan tabarmar ya zauna sai dai kuma yana zaman sai ya daso ido ya kali mutanen da ke wurin cikin wani irin yanayi ya tambayesu to da da saa ta zauna ta hanata tafiyan nan kam me zata yiwa Bukar ne bayan ta tafi ta barta shekara talatin da daya? Yana fadin hakan ya soma shisshikar kuka shima baban nawa haka, nayi maza na karasa cikin gida da gudu ban tsaya gurin ganin abinda ya ci gaba da faruwa ba.

Kafin magariba dai har makwabta sun fara zirga-zirga a gidanmu kowa ya ji dan uwan malam Habu mai timatir ya zo sai yazo wai ya zo gaisheshi, kowa ya zo ya fita kuma da abinda zakaji ya zo fadi, wanshi aka ce ne ko kaninshi? Abokin magana ya ce a’a wanshi dai sai ace a’a to ai ma yafi malam Habun karfi da kuruciya, a’a ba zai fishi ba barijn gida da dangi wasa ne? Sannan shi malam. Habu wannan ja’irar mata da ya gamu da ita ai sa’a ma akayi da aka sam eshi a haka kasan ba karamin amfani auren nan yayi mishi ba don ma yayi jinya kanan nan ai duk sanadin ta ne duk masifar ta ce ta jawa mutumin nan wannan Wahalar.

Wasu kuma suka ce oh ka ji wani abin mamaki wai yana da ‘yan uwan shi har da shakikai amma shekara talatin da daya bai nemesu ba ko me suka yi mishi haka oho? Kai koma me suka yi mishi bai kyautawa kanshi ba ko da yake dai ance wai in ka ga bera ya rugo da gudu ya fada wuta to binda ya koro shin ya fi wutar zafi.

Daya mutumin ya ce uhun ai gara da kai da kanka ka fadi hakan don ni yanzu babu abinda ke kadani ya razanani in tsorata irin inga yanda mutnae suke wasa ko suke cin mutuncin zumuncinsu sai ince oh oh anya a irin wannan hali da muke zumunci dake kan siratsi kuwa da akace zai rinka fisgo mutanen da suka tozartar da shi a rayuwarsu ta duniya ya rinka jefasu cikin wuta a ranar alkiyama? Rabbi sallim sallim gaba dayansu suka ce amin amin nima nayi maza ciki zamu tsallake makatan na tayasu fadin amin din.

Ban taba ganin babana a yanayi na farin ciki kwatankwacin wanda na ganshi a ciki ba rannan cikin zuciyata na ce oh ashe dai yana son ‘yan uwan nashi in da suke ne kawai bai son zuwa, ita kuwa baba Lantana wacce itace mai abincin gidan nan nan taki ta tsaya ta yi wani abin arziki sai tsaki takeyi tana fadin, uhun malam wai shi ma nan yana da wayo yaga ya samu zai cusa yarshi gidan masu kudi yaje ya nemo dattijon babarbaren wai shi ne wanshi don ya wanketa daga gorin rashin dangi da asalin da kishiya zata rinka yi mata to dadin abin shi ne babu abinda ban sani ba.

<< Halin Rayuwa 48Halin Rayuwa 50 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×