Itace ta sarrafa duka abubuwan da ta samu an kawo din ta adana na adanawa ta girka na girmawa irin kayan shan farfesu ki sha romo sosai saboda kula da jikinki bayanin take yi min bayam ta titsiyeni na ci na sha adadin da yake nema yafi karfin cikina, ai garama da tayi miki. Haka mu kishiya wacce iin yunwa ce bata gana mana ba ga abin nan a wadace amma bata sarrafa shi ba balle ta baka sai ita da ‘ya’yanta ta san hikimar da tayi ki kula da kanki na gaya miki ki ci gasasshe nama ki sha farfesu ki kuma hora kanki ba yadda za ki citu ba kama hanya a tafi ta bar Inna tana gyaran wajen.
An idar da sallar azahar Mubarak ya shigo baba da yaya Dija suna gaisheki naje na yi musu bangajiyar baki, nace ina amsawa ya ka barosu? Lafiya ni zan kwanta ko za ki zo mu je tare? Na ce uh’uh na nuna mishi Inna da ke kici bai yi magana ba ya wuce ya shiga daki sai wajen hudu ya fito.
Rannan da daddare muna kwance a gadonmu gwanin dadi yana manne da ni a jikinshi hira yake yi min yana bani labari baki sani ba Maryam a hankali na tambayeshi menene, cikin nutsuwa ya ce min, sai in rinka ganin tamkar a mafarki nake sai na ganki a zahiri ko na jiki a jikina sai in gane ba mafarki bane, sai in tuna lokacin da Baba yake lallashina yana gaya min cewar in matarka ce zaka aureta wani ai baya auren matar wannan ashe ashe ashe kuwa haka din ne, a hankali cikin natsuwa na ce mishi Baban? Ya ce eh mana ance miki ni na iya irin wannan noke noken ne irin naki? Kana son abu kana kaiwa kasuwa? In banda na nuna mishi zahirin al’amarina zai yi ta wannan zirga zirga ne da ya rinka yi ke fa kina jin yanda nake ji ko na rinka ji, gaya min gaskiya sau nawa kika taba yin mafarkina? Ni bana karya Maryam bana kaiwa kwana ashirin ban ganni tare da ke ba a tacina har na rinka sanmun mas ala na wankan da nakeyi ban san dalilinshi ba na yi kamar ince ishi ai nima ganin nake tamkar mafarkin nake yi sai na fasa neyi maza na ja bakina na tsuke, a hankali kuma sai na ce mishi to mu yi bacci mana yallabai ko zaka samu ka kara wattsake gajiyarka.
Kwanaki uku a jere ni nake hidimomina ni nake yin girkina babu fashi kuma kullum yaya Dija zata aiko min da abin karyawa mai dadi da gamsarwa Inna zata zo tayi min duk aiyukan da suka dace ta kuma tayani hira sai lokacin makaranta ta yi shiri ta tafi in ta taso ma nan wurina zata sake dawowa haka shima Isiyaku kullum zai kawo min cefane..
Rannan na cika kwana hudu cikin daki ban ito ba saboda gajiyar Mubarak bai yarda munyi irin kwanciyar da muka yi a kwanak biyun da suka biyo bayan daren angwancinmu ba ina jin sanda Inna ta shigo ta gama abinda zatayi tazo ta tsaya daga bakia kofa ta gaisheni ta ce min zata je makarantar allo ta dawo na ce mata to kin karya ne? Ta ce eh nace to sai kin dawo, ina cikin hakan ne Mubarak ya sake shigowa dakin ko za ki zo muje can wajen Rumasa’u mu karya, kamar in ce mishi tuntuni bata kirani karyawa ko cin abinci ba sai yanzu da na riga na zama ‘yar gar? Ban iya yin hakan ba na ja, bakina kawai na yi shiru.
Ya nemi wuri a bakin gadon ya zauna, bana so wata mas’ala ta taso ace ta wurinki ne Umma ta kirani ta ce min wai anyi mata fada taji kuma zata gyara kuskurenta, don kar in yi musu da shi ya sa na tashi na dauki gyalena na yafa a kan doguwar rigar da ke jikina na bi bayanshi zuwa dakin nata na kalli zirga-zirgarta na gaisheta kafin na nemi wuri na zauna a kan shimfidar da na samu ya riga ni zama.
To ki yi ki kawo mana ruwan zafin mana, ya yi magana saboda ganin bata gama kammala abubuwan ba, ta ce to ta kawo ta ajiey taje zata zauna kadan ta rage ta hau kan cinyar shi in banda ya yi hanzarin kawar da jikinshi ina tunanin nan din ta zama, nan da nan naji zuciyata ta yamuise wani bangaren na ta ya rinka rayamin cewar so take ta nuna miki cewar nan din wurin zamanta ne kokari mai yawa na yi kafin na dawo da kaina ga natsuwata nan take kuma nayi ta tunawa kaina da cewar matarshi ce matar sai ce a hankali na zuba ruwan zafi a kofi na tsoma lifton a cikin a soma sha.
Wane irin karyawa ne wannan Maryam? Kina mufin duk abubuwan da ke nan ba za ki ci komai ba sai ruwan lifton, daurewa na yi in banda haka da nayi mishi kuka na dago idanuwana do in yi mishi magana karab suka hadu da na Rumasa’u itama ni take kallo ba kuma kallon dadi ba ne, watakila ‘yar kulawar da ya nuna ne ba ta yi mata dadi ba, sai yau muka ga juna ido da ido daga ganin da nayi mata a asibiti da suka zo duba babana zuwa yau din ta zabge sosai sai dai in aka barni sai ince tafi kyau a hakan don da ta bar kanta ta ajiye teba mai yawa. A hankali na ce.mishi, na manta ne na fito ban yi brush din bakina ba ko inje in yi in dawo? Har ya ce eh ban san abin da ya tuna ba sai naga ya miko min kwano guda daya na karba na dawo na ajiye na shige bandakina na kwanta cikin zuciyata ina tunanin ba zan sake yarda ya dorani a kan cinyar shi ba wato dama shi dabi’arshi kenan dora mace a kan cinya to na daina yarda in hau nan take naji zuciyata tana raya min Wasu al’amuran da nan take na ji babu abinda nake so iri in yi kuka shi ne mutumin da nake so a rayuwata na yi ta bunn auren shi sakacinshi da sharrin baba Lantana su ne suka taru suka yi sanadin da burin nawa bai cika ba a wancan lokacin har yaje ya auri wata matar ya Soma yi mata abubuwan da ya kameta a ce ni kadai zei yi wa, motsin shigowar da ya yi ya sani nayi amza na share hawayena amma duk dahaka sai da ya gane kukan nakeyi, me ya saIneki? Na yi shiru zuwa dakin nata ne bakya so? Nayi maza na ce mishi a’a, to menene? Na ce mishi bana jindadi ne, to in bakya jin dadi sai ki yi kuka ba za ki gaya min ba? Ko dai wani abu yana yi miki ciwo ne, nayi amza na ce mishi a’a, a kaiki asibiti nas ake cewa a’a Isiyaku ya siyo min maganin zazzabi.
Ya ce in to ki yi wanka ki yi kwalliya in ganki in ji dadi na ce mishi to a haka na wattsake, ana gobe zai fita dakina ma sai da ya sake takurani ya yi yadda ya so da rannan kam kuka nayi ta yi mihi saboda na kasa hakuri in jure tun yana rarrashina har va soma mita wato kenan baki gamsu da adalcin da nake vi miki ba kenan ko so kike in tattara hannu in zuba miki ido ina kallonki, banyi magana ba iyaka dai ranar ya koma dakin Rumasa’u ni kuma na kwana tare da Inna shi ne ya cewa yaya Ibrahim kar a ga bata dawo ba zata tayani kwana yace mishi to.
Tunda karyawar safe ta zama ka’ida za mu yi ta tare har da shi sai ya zama ka’ida kullum sai ta san abinda tayi ta bata min rai da na yi tunani naga abin bana karewa bane sai na yi maza na cire abubuwan da nake ganin tana yi mishin a raina tunda dai ni ba zan iya yi mishi hakan a gabanta ba balle ince zan rama.
Satina uku da zuwa gidan aka soma azumin watan ramadan babu yadda banyi da shiba ya barni in je in yiwa babana barka da shiga watan mai albarka ya ki wai shi ya je ya yi mishi hakan itama yaya Dija ban jeba bata zo ba nayi aike har na gaji na hakura taki zuwa sai ana gobe zamu tafi umarar da aka yi ta rikici akan tafiyar da yace zai yi da ni har sai da babanshi ya sa baki cikin maganar shine wai tazo yi min sallama, na sunkuyar da kaina kasa na ki kallonta naki yarda kuma nayi shiru in daina kukan da nake yi mata, wata uku? Wata uku bamu ga juna ba amma baki yi marmarin ganina ba? Baki kuma ji tausayina ba? Tayi murmushi, to yi hakuri Maryamu yi hakuri Merona ai Meron Alhaji Ahmad kwanaki talatin din nan da kikayi a gidanshi kinga yanda kika zama? Ko da yake dai shima naji babansu yana cewa wai kwanciyar hankali dai shine wani abu banga yadda Alhaji Ahmadu ya zama ba amma zai yiwu ne inyi tayi muku zirga-zirga a gida? Yanzu ma ba ki ji ana cewa kullum sai na aiko Inna ta kawo miki magani ba da sassafe? Na daga ido na kalleta saboda jin maganar tata tayi maza ta kawar da zancen ta hanyar fadin in kin yi dawafin Umra kiyi addu’a Ubangiji ya baki ‘yan tagwaye, ban kulata ba na shiga daki naje na kawo mata abinda nake nufin kawo mata watakila sai gab da salla mu dawo watakila sai bayan sallar ki yi wa su Inna sayaiya ta ce min to.
Sati uku cif muka yi sai ana gobe sallah muka dawo, kudin sadakina da wanda baba Abba Gana ya bani kyauta ya ce a kawowa ‘yar uwata ta sai min abinda ya dace su yaya Dija ta kawo min da zamu tafi da su na sayo ra rai masu kyau don ma naki karbar aka gudan da Mubarak ya bani na ce ya rike su.
Hirar da Mubarak ya yi min a car wanda a ciki ya tabbatar min da labarin da baba Sumaye ta taba bani na cewar ba ummanshi ce mahaifiyarshi ba ya sani yiwa ban gaya mishi ba, nayi rabon tsaraba na dai dai mahaifiyar tashi sayaiya mai yawa don tsarabarta sai dai gwargwado na kuma yi rabon har da mutanen Gaidan na aika musu da shi.
A wannan lokacin ni da Mubarak amarci sosai mukeyi saboda duk abubuwan da a farkon l’amarin suke masu tsanani da sanya faduwar gaba a tsakani sun zamo masu sauki a yau da sanya nishadi in tsaya fadin ji da ni yake yana tarairayata ya zama tamkar sakarci ne zanfi gwammacewa in ce muku duk abinda yake so shi nake yi mishi.
Ashe duk wannan kwaramniyar da wannan kai kawon Maryam ashe dai ke din matatace, ince mishi eh yallabai ni taka ce da rabon dai kawai za a ji jiki ne, sai ya yi maza ya ce a babu komai ba gashi yanzu ya wuce ba darussan da muka koya tare da mu kuma suna nan zamu rikesu iya tsawon rayuwarmu? in ce mishi eh, sai ya ce to ai shi kenan.
Kwananmu shida da dawowa randa mka dawo ya sauka a dakin Rumasa’u ne ni ma ranar ban wani damu ba, so nake in dan samu sararawa ya yi kwana biyu ya dawo wurina ranar ma ina hutun sallah ya yi biyu ya koma can, ya sake yin wasu biyun ranar zan karbeshi ya shigo wurina da safe akwai wata mas’ala ne? Na ce mishi, a’a, ni kin fara salla ikuwa? Na sake ce masa a’a har ya juya zai tafi sai na ce mishi da ina so in rokeka wata alfarma, ya juyo yana kallona, kamar wace iri kenan, nace so nake ka sa a kaini jaji ina so inje wajen su Inna.
Ya danyi shiru kadan kafin ya ce min, to ki saurareni na ce mishi to ya juya ya tafi.
Banda wannan girkin da nayi da ya koma wajen Rumasa’u zai sake dawowa wurina sai muka tafi.
Wajen karfe hudu da rabi muka isa duk da ya ce sammako zamu yi mu isa wajen sha daya ko sha biyu in mukayi la’asarm mu wuce Kaduna gidan Abdulhamid mu kwana a can ban san yanda akayi sammakon bai yiwu ba.
Hirar baki ba za za ta iya fahimtar da mutum ya gane irin son da Mubarak yake yiwa mahaifiyarshi ba sai yaje inda take da zama yaga irin gatan da yayi mata shi bam utum ne ma yawan magana a kan mahaiñyarshi baa sannan bakina da nashi sai ya tabbatar min da cewar yana dadewa baije wurinta ba a dalilin babu wata shakuwa a tsakaninsu ya santa ne bayan ya girma har ya soma karatu a jami’a ya nemeta don kanshi ita bata taba waiwayowa ta kalleshi ba, watakila an bata mata rai ne ya sa tayi mishi hakan watakila kuma don ta ga ta haifi wasu masu yawa ne ya sa ta hakura da shi tunda shi kadai ne.
Cikin natsuwa na ce mishi, ko kuma don kunyar kai din dan fari ne ba’? lyayenmu ai masu kunya ne, yayi shiru ya bar maganar.
Muna isa Jaji na sha mamaki gidan da aka tsaida motar da muka yi tafiyar a ciki gida ne ginin kasa ko ince block din kasa ginin mutanen karkara sai dai babba ne sosai cikin zaure gidan muka shiga muka fada tsakar gidan mai matukar girma, Isiyaku ne yake jagoranta ta, dan daga hirar da nayi ma sai naga kamar yafi yallabai din yawan zuwa garin a’a a kar dai amarye ce yau a gidan namu? Na daga ido a yanayi na girmamawa ina sauraron kalamanta cikin zuciyata na tabbatarwa kaina da cewar itace dattijuwar da ban gane ba a Gaidan ashe daga nan taje can din.
A’a wuce mana wuce ki karasa ina nan shigowa, na bi umarmin da ta bani naci gaba da bin bayan Isiyaku ban karasa inda zanin ba naji tana cewa sannu da zuwa Alhaji kun zo ba? To hannurkn da zuwa hannunku da zuwa.
Wata kofa na shiga wacce na dade ina hange saboda nisanta wani tabkeken gida na gani a cikin wata kanmalalliyar katanga ginin block, sannunku da zuwa ta yi min sannu da zuwa cikin matsananciyar fara’ar da ta baiyanarda jajayen hakoran makkanta guda biyu dan kamannin da ke tsakainta da shi kadan ne sai dai kuma hakan ba zai hanaka sheda cewar ita din mahaifiyarsa ce ba shi dogo ne ita. kuwa bata da tsayi shi ingarma ne ita mai dan jiki, ita fara shi wankan tarwada a lokacin kuma su na da dan wani abinda ya hadasu da ya danyi shigenta kadan sai dai ban gane menene ba?
Har kun fito? Cikin ladabi na ce mata, ah to sannu da zuwa shiga mana na shiga falon na ta na samu daya daga cikin luntsuma-luntsumarn kujerun da ke wurin na zauna a cikin ina mamakin wurin nata yafi kama da na sabbin amare saboda irin kawatuwar da akayi mishi, sannu da zuwa ta sake fadi daidai ta zauna a kan kofar shiga daya dakin nima na sauko kasa na zauna muna gaisawa tana tambayata yaya gida? Yaya manyan duka? Ina amsa mata da na ji ta danyi shiru sai na tambayeta Inna ina Izzatu, tayi dariyar jin dadin tambayar yar autar ta ta da na yi ta ce, ai kuwa dai yanzu na aiketa wurin yayarta dake nan bayanmu.
Mubarak ya yi sallama ya shigo ya koma can gefe sannu Inna, daga yanayin maganar tasu na kara gane gaskiyar abinda ya gaya min, baba baya nan ne? Ya yi tambayar bayan sun gaisa ta ce eh ya zaga baya can kasan sun fara sharar gona saboda ana ganin kamar damuna tana gab da zata fara zube ya ce haka ne.