Skip to content
Part 22 of 24 in the Series Hasashena by Khadija S. Moh'd (Matar J)

A falon na dawo na same shi, kamar in yi banza da shi a kan maganar na shi abincin, Sai kuma na shige kitchen na hado mishi komai da komai na kawo mishi.

Na wuce dakina, yau gabadaya duk bata min rai yake yi, sosai raina yana baci a kan yadda baya sakani cikin ko wacce sabga ta shi, Sai dai kawai in ga ana yi, ko in ji an yi, sabanin Sakeena, da komai da shawararta yake yi.

Aiki gonarshi na bana ban san ko me ya samu ba, zakka da ya fitar ma ban san yadda ya fitar da ita ba, amma lokacin Maman Khalil na raye duk wadannan abubuwan da yake yin su. Ni kuma ina ta wahala a kanshi da yaranshi baya gani. Jin alamun shigowarshi ne ya sanya ni juya baya kamar ina bacci.

Yadda na ji kamshin turarurrukan kwanciyarshi ya cika dakin, na tabbatar har ya yi wanka.

Ina jin lokacin da ya sauka saman keken, ya hau gadona amma ban motsa ba.

Without anything ya shiga shafa ni, na ji kamar in buge hannun, takaicinshi ya kara kama ni.

Wannan dabi’ar tashi na masifar bata min rai, ta yadda bai dauki fushina a bakin komai ba, zai fahimci ina fushi, amma sai ya share kawai ya shiga harkokinshi, ga ni ni ba Sakeena ba, da ta iya danne abu, idan ban magantu ba; ban jin dadi.

Shi ya yi kidanshi, na kuma ya yi rawarshi, hakan kuma bai sanya ya damu ba, Sai ma kawai ya shiga baccinshi, kamar a duniya babu abin da ke damunshi.

Toilet na shiga hade da gyara jikina, na yi raka’a biyu hade da shafa’i da wutri, kafin na kwanta amma sai da na sanya Maama a tsakiyarmu, asubar fari kuma na shiga kitchen don yi wa su Khalil abinci breakfast da wanda za su tafi da shi school.

Shi kuma ya je ya hada kansu suka tafi masallaci, bayan ya dawo daga masallacin baccinshi ya koma, ni kuma na shiga taya su Affan shiryawa, ga Maama ta tashi ita ma, duk na zama busy.

Koda suka tafi ma ban huta ba, gyara kitchen Wanke-wanke, da gyaran gidan. Sai wajen 8:30am na kammala, sannan na zauna don yin break, bayan na gama kuma na shiga shirin zuwa asibiti.

Gefen gadon na zauna bayan na shirya, ina jin wani zafi a zuciyata, da ace ina da kudi kawai zan yi tafiyata ne ba ma sai na tambaye shi, amma ko don kudin asibitin dole ya sani.

Zaman nan na ba kwandalar da take shigo maka sosai yana damuna.

A hankali ya bude idanunshi hade da zube su a kaina, fuska na kara hadewa, shi kuma ya lumshe idon a hankali kafin ya yi doguwar mika, cikin muryar bacci ya ce “Me ya faru?”

“Asibiti nake son zuwa” na amsa murya a cunkushe.

“Yin me?”

“Ni dai ina son zuwa ne kawai”

“To Allah Ya kiyaye hanya” ya yi maganar hade da gyara kwanciyarshi ya juya min baya.

Tsawon 5mns bai juyo ba, kuma komai bai ce ba, yayin da zuciyata ke ta wani irin zafi, yana jiran in ce ya ba ni kudin zuwa asibiti. Ni kuma ba zan fadi hakan ba, tun da ya san ba ni da su ai.

Mikewa na yi hade da saba Maama na nufi kofar fita

“Yaran nan sun tafi school kuwa?”

Ban amsa shi ba, na yi ficewata, zan zauna da yaran ne har tara basu tafi makaranta ba.

Raina bace nake jefa kafata, har na isa family house dinsu, haka nan na ji Ina son barin gidan.

Tun da na shiga gidan ake tambayata lafiya, ban cika zuwa da safe haka ba, ba ma sosai nake zuwa ba, to ko wane lokaci cikin aiki nake, babu hutu in gama wannan in fada wancan.

Da lafiya ƙalau na rika amsa musu, har na shiga bangaren Inna, wanda aka zagaye da doguwar katanga, aka kuma buge shi da rufi mai kyau na zamani, ga interlock shimfide a farfajiyar wajen.

Lokacin da na shiga wangalelen falon nata mai dauke da kujeru masu kyau ya sha tiles, sagale ta yi da kofin kokon hade da tambaya ta “Lafiya?”

Maama na kwanto hade da dora ta saman kujera, ni kuma na dire kafafuna kasa ina gaishe ta, ta amsa cike da kulawa kafin ta ce “In ji dai lafiya?”

Cikin murmushi na ce “Lafiya ƙalau fa Inna, kowa sai tambayata yake yi wai lafiya”

“To ai dole, tun da ba a saba ganinki haka da sassafe ba, sannan ciwon nan na Abbansu Khalil kamar da iska, yau sauki gobe kuma sai godiyar Allah”

Kadan na murmusa kafin na ce “Alhamdulillah, jiki ya bi da haka ai sai dai mu godewa Allah.”

“Haka ne kam” ta yi maganar hade turo min kular kosai tana fadin “Ga mutuminki nan, ya su Affan din har an tafi makarantar”

“Sun tafi tun dazu” na amsa ina cin kosan, sosai ina son kosai

“Wannan makaranta ai ta hana su rashin ji kullum aka tafi tun safe sai yamma, kuma babu Asabar ba Lahadi”

“Wallahi fa, hutun kawai ranar Juma’a ne”

“Ai kuma kin huta da bari-bari”

Na yi murmushi ba tare da na ce komai ba.

Ta kai kallon ta kan Maama da take bacci ta ce “ita wannan lafiya ko take?”

“Lafiya kalau, muna kan hanyar zuwa nan ta yi bacci”

“To madalla. Kin tabbatar dai ƙalau ko?”

Cikin murmushi na ce lafiya ƙalau Inna, kawai na ga na gama aikina da wuri ne, shi ne na ce bari in zo nan in gaishe ku”

“To madalla aiko kin kyauta.”

Haka muka shiga hira sosai, a hankali kuma falon ya rika cika da matan gidan, Sai na ji zuciyata ta yi sanyi, sun mantar da ni takaicin Bashir.

Ban baro gidan ba sai da na yi sallahr magriba, na san dai na taro match Kuma ba ni da ƴan wasa.

Lokacin da na isa gidan duk suna masallaci, kitchen na yi wa tsinke, saboda na san kaf rigimar tana a cikin kitchen din

Wani kamshi mai dadi ya bugi hancina, da sauri n isa wurin tukunyar na bude, jalof din taliya ce ta sha kayan miya ga kifi ice fish manya-manya a ciki.

Duk da na ci tuwo sai da yawuna ya tsinke, Bashir kam gwanin iya girki, amma ko ya aka yi ya yi yana zaune oho, duk da yana iya mikewa tsaye, tafiya ce dai bai iya wa. Kuma da alama suna kashe gas din suka tafi masallaci.

Da kaina na tayar da injin, kafin na shiga wanka, ina fitowa na ji kiran sallahr isha’i, Sai kawai na yi sallahr, bayan na idar na saka wando baki wanda da kadan ya wuce gwiwata, na dora riga armless pink wacce ta tsaya daidai kwankwasona. Komai ban shafa ba, Sai humra. Falon na dawo inda Maama ta nutsu tana kallo cartoon kamar ta san abin da ake yi, ban zauna ba sai da na je kitchen din na zubo abinci na zuba kifi wajen yanka bakwai manya, sannan na dawo falon na zauna, ina ci ina ba Maama, ban fi spoon biyar ba suka shigo gidan, na yi fuska abuna, su Khalil dai murnar na dawo suke yi, ita kuma Maama murnar ganinsu take yi. Bashir kuma poster ya ajiye a kofar falon yana kallo na, ni kuma na ki yarda in kalle shi. Loma ta kawai nake yi hankali kwance.

Keken ya murzo ya shigo tsakiyar falon sosai kafin ya ce “Lallai yarinyar nan ba ki da kunya, dole ki ƙi kallo na”

Dariyar da nake ta dannewa ta kwace min, don haka na kai hannuna saman bakina ina yin ta a hankali

“Lafiya zamu rabu Khadija” ya fada yana kokarin sauka daga Keken, Khalil da Affan suka taimaka mishi, kuma sune suka zubo abinci, ina jin Khalil na korafin duk babu kifin, na yi banza abuna kamar ba na falon.

Bayan sun gama mu ka yi homework, na karbi hadda, kafin suka wuce dakinsu, zuwa lokacin tuni Maama ta yi bacci.

Na dauka Bashir zai tambaye ni ina na je, amma bai yi hakan ba, abun da ya fi so kawai ya yi, ya baccinshi.

Tun ina fushi da sanya ran zai tambaye ni ba’asi har na gaji na warware, na ci gaba da hidindumu na.

A satin kuma Dr Nura ya zo, yadda suke ta kus-kus na san akan maganar siyar da gidan Abuja ne, yadda basu sanya ni ba, ni ma sai na yi gum abuna.

Kwananshi daya ya juya, still a satin sai ga Mustapha (mijin Maman Hana) shi da wani Dr Jamil, su ma dai kus-kus dinsu suka gama, suka tafi, bayan na nemi tsarabar kauye na bayar a kaiwa Maman Hana.

Sosai jikin Bashir ke sauki, saboda yanzu tafiya yake koya da crochet, Sai dai baya taka kafar dage ta sama yake yi, duk lokacin da yake koyan tafiyar sai in yi ta mamakin ikon Allah, dakyar yake yunkurawa minti 2-3 zai ce ya gaji. Har haki yake yi. Alamun da gaske ya gajin.

A kullum dai ya kan yi hakan sau biyu, safe da kuma yamma.

Wani lokacin kuma idan ya fita majalisar kofar gidanshi, abokan zaman majalisar kan kara sanya shi ya gwada yin tafiyar, koda ba ya so.

Ni kam zuwa yanzu na fahimci da gaske ina da ciki, saboda har ya fara motsi, dadina daya bai sanya ni laulayi ba, haka bai taba Maama, kila Allah Ya tausaya min ne, yadda Maama ke da rigimar nan, ace kuma ciki ya taba ta ai na shige su, ban san da me zan ji ba.

Ranar Asabar misalin karfe biyu na rana kwatsam sai ga Ummana da kanwata Yusrah, zuwansu ba karamin dadi ya yi min ba.

Tun da suka zo nake hidima dasu, sosai mu ka sha hira, Sai biyar na yamma suka tafi, Bashir ya yi musu kyauta sosai, haka ma yan’uwanshi, ina jin dadin yadda yake girmama yan’uwana. Ni ce dai idan rashin kirkinshi ya motsa zai yi min shi sala-sala.

Kasancewar yau juma’a su Khalil babu makaranta, hakan kuma bai sanya sun zauna a gida ba, suna gidan kakanninsu, ni kadai ce a gidan hatta Maama wata diyar Kawunta ta zo ta fita da ita.

Zaune nake cikin falo na tasa turtsersen cikina a gaba, abubuwa da yawa ne suka bata min rai a wannan satin. Kuma na san kila haka zan gama fushina Bashir ci kanki ba zai ce min ba, iyaka ci dare ya yi ya zo ya biya bukatarshi ya juya min baya. Ki tausayina ma ba ya ji

Abin da na fahimta kamar idan ina fushi to ya fi matsa min, kuma baya damuwa da ina performing Ko ba na yi.

Abu na farko da ya bata min rai shi ne, jin labarin Bashir ya sayi fili a Katsina har yana gini amma ba. Sai dai na ji a gidansu da na je, da na kasa dannewa na yi mishi maganar, Sai ya yi min kallon shekeke, kafin ya ce “komai zan yi sai kin sani, abin da ya kamata ki sani din ba ina sanar da ke ba. Waye zai zauna a gidan ba ke ba. Ni fa ba na son tsokano tashin hankali”

Haushin da ya ba ni ne, ya sa ban kara ce mishi komai ba. Abu na biyu kuma a kan yayen Maama ne, mutane sun damu in yaye ta, saboda sosai cikina ya yi girma, shi ne na sanar mishi, na ce idan babu damuwa zan kaiwa Ummata ita, ni kuma in ji da cikin da hidimar gida sai cewa ya yi wai yaronshi baya zuwa wani gida. Sosai maganar ta bata min rai da ba ni mamaki, wai yaronshi baya zuwa wani gida.

Gidanmu ne wani gida “Mtswww!” na ja bayyanan ne tsoki, lokaci daya kuma Ina amsa sallamar da aka yi daga can gate.

Ido na zubawa kofar falon, har zuwa lokacin da wasu mata biyu suka shigo, ɗayar dai gajeruwa ce, sanye cikin riga da zane na atamfa, ta yafa bakin mayafi, dayar kuma doguwa ce siriruwa, ita ma riga da zanen ne a jikinta amma hijab ta sanya. Dukkansu fuskokinsu dauke da irin zanen fuskar Bashir, Sai dai su na su a saman kumatu suke a kwakkwance guda uku, Sai kuma a, gefe kunne guda biyu. Kamshin turaren Safiyya ya cika falon, lokacin da suke kara doka min wata sallamar.

Na kuma amsawa ina fadin “Ku shigo, sannunku da zuwa”

“Yauwa” suka amsa a tare, hade da neman wuri a falon suka zauna.

<< Hasashena 21Hasashena 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×