A falon na dawo na same shi, kamar in yi banza da shi a kan maganar na shi abincin, Sai kuma na shige kitchen na hado mishi komai da komai na kawo mishi.
Na wuce dakina, yau gabadaya duk bata min rai yake yi, sosai raina yana baci a kan yadda baya sakani cikin ko wacce sabga ta shi, Sai dai kawai in ga ana yi, ko in ji an yi, sabanin Sakeena, da komai da shawararta yake yi.
Aiki gonarshi na bana ban san ko me ya samu ba, zakka da ya fitar ma ban san yadda ya fitar. . .