A tsarin gidan shi ne, ranar da miji zai bar ɗakinki, ke za ki yi abincin dare, sai ya ci sannan ya baro dakin. Don haka yau Maman Khalil za ta miko min Abbansu Khalil, shi ya sa tun da na idar da sallahr isha’i na shirya cikin (English wears) da suka yi matukar karbar jikina. Ni ma yau so nike in burgeshi, in nuna mishi ni ma fa duk abin da matarshi ta iya na iya kuma zan iya.
Riga da wando ne, masu kalar ruwan madara, wandon dogo ne har kasa bai kamani sosai ba, rigar guntuwa mai siririn hannu da ta zauna kan kwankwaso na.
Na kama gashina na matse da ribbon mai kalar far. Na dawo falo na kame ina jiran dawowarshi. Ba jimawa kuwa na ji horn din shi, Ina jin lokacin da maigadi ya bude mishi, shi ya sa na yaye labulen windown falona ina kallon shi, har shige part din matarshi.
Zaunawa na yi, zaman jiran tsammani, na san dai ba zai wuce awa daya a can ba.
Sai dai sama da awa biyu, ban ji duriyarshi ba.
Duk yadda na so danne zuciyata abun ya ci tura.
Saboda yadda ya dade din, bai taba dadewa haka ba, bayan kuma ba aikinta ba ne.
Haka kuma idan aikin ta ne ba ya jimawa a wurina yake fita,
Sometimes ma Idan ya dawo Sai ya leka bangarenta, sannan ya taho nawa, koda kuwa
a dakinta zai kwana.
Amma ni yanzu ga shi har goma saura bai shigo ba turare sai fesawa nake da gyara powder amma shiru har na gaji.
Ba abun haushi irin ka yi abu don mutum kuma bai gani ba.
“Allah ma ya kara min! Da na auri saurayi babu abin da zai hada ni da wannan takaicin. Duk inda yake da abin da yake yi hankalinsa dai yana kaina. Amma yanzu yaransa sune farko sai uwar yaransa kafin ni in biyo baya.”
Kai karshen tunanina ya yi daidai da jin karar bude gate, Sai kuma na ji tashin motarshi, wannan ya tabbatar min da fita suka yi.
Na ja tsoki hade da mikewa zuwa doguwar kujera na kwanta. Raina a matukar ɓace
Tun ina tuna banza da wofi har bacci ya dauke ni.
A cikin bacci na ji kamar ana jan kafata, dalilin da ya sa kenan na bude idanuwana a hankali cikin yanayin bacci na zubasu a kanshi.
” Da ace ɗana ne, da kawai mari masu zafi zan wanke fuskarshi da su” A zuciyata nake saka wannan amma a zahiri, kuma lumshe idanuna na yi.
“Bacci kike yi?”
“A’a rawa nake yi” a zuciyata na kuma yin maganar.
Amma a zahiri ko idona ma ban bude ba, bare ya yi tunanin zan ba shi amsa.
Ina jin shi ya wuce wurin abincin da na shirya mishi, na yi amfani da damar wajen kallon agogon da ke falona, karfe shadaya saura.
Wani gululu ya tsaya min a kirji duk kwalliyar da na yi, ta tafi a banza kenan bai gani ba.
Mikewa na yi cikin yanayin bacci na nufi bedroom
“Daga karshe dai na ga kwalliyar” ya fada a daidai lokacin da ya mike tare da nufo inda nake
Da sauri na shige bedroom, amma sai da ya cimma ni
“Ba za ki cire wannan kwalliyar ba, kin yi kyau kuma na yaba, na gode sosai”
“Ba za ki ce komai ba?” ya tambaya ganin ba ni da niyyar magana
“To me zan ce?”
“Abin da ke ranki.”
“Ai babu komai” ina kokarin zama gefen gado na yi maganar.
Shi ma zaman ya yi kusa da ni “Ki yi hakuri, wallahi Affan ne ba lafiya muka kai shi asibiti”
Ai dama na san tatsuniyar gizo ba ta wuce koki. Kullum cikin hidimar yaranshi da ta matarshi yake. Ni kuma ko oho. Ko yaushe ma Affan din ya dawo oho. Saboda tun last week ya je hutu gidan kawar Mamanshi, daga can ake kai shi makaranta, a kuma dakko shi
“Allah ya ba shi lafiya” Na yi maganar daidai lokacin da nake kwanciya. Don gaskiya na kasa dannewa.
A yanayinsa na ga kamar bai ji dadin yadda na karbi abun ba, ta hanyar nuna halin ko in kula, amma ni bai dame ni ba, don gaskiya na fara gajiya da yadda yaranshi da kuma matarsa ke shiga lokacina.
Bayi ya shiga, ya yi wanka, na dauka ba zai neme ni ba, sai kuma na ga ya yi hakan, duk da ni ban bayar da hadin kai dari bisa dari ba. Don har zuwa lokacin zuciyata zafi take yi.
Ni ce na tashe shi zuwa masallaci sallahr asuba.
Ni ma kitchen na shiga bayan na idar da sallah, doya na fere, yam balls nake son yi.
A nutse nake yin aikina duk da dai bana jin dadin zuciyata
Don ma Bashir mutum ne da ya san mace, sosai ya tafiyar da kashi saba’in cikin dari na damuwata a daren jiya.
Sai dai yadda har yanzu da agogo ya nuna karfe bakwai na safe bai fito daga sashenta ba, kuma yana dawowa masallaci ya shiga bangaren nata. Yana kara tunzura min zuciya. Ni ba haka yake yi min ba. Yana shigowa ya dade 30mns.
Wani lokacin ma sai ya yi shirin office kafin ya leko ni
“Kai!!!” Na ji an fada a bayana, da sauri na saki cokalin da nake kwashe yam balls din cikin Mai, lokaci daya kuma na zabura bayan na saki siririyar kara
Da sauri ya rike ni yana dariya “Wallahi kin faye tsoro, to waye zai shigo har nan ya ba ki tsoro idan ba ni ba?”
“To dana san waye zai shigo din zan tsorata ne.” Na ba shi amsa ina harararshi cikin fuskata mai nuna alamun shagwaba.
“Uhhhhhhh! Kamshin dadi” ya fada yana bubbude hancinshi
An yaba kaza mika, ta ce ga cinya
Sai na ji kaina ya yi fadi, kamar kitchen din ba zai daukeshi ba.
“Maman Khalil ta tashi ne?”
“Eh” ya ban amsa a lokacin da yake tsoma dunkulalliyar doya cikin kwai cike da kwarewa
“Ka iya girki fa”
“Maman Khalil ta koya min abinci da yawa ai, da ta tare muke shiga kitchen lokacin aiki bai yi min yawa ba”
“Ai fa” na fada a zuciyata a zahiri kuma cewa na yi “Ta kyauta”
“Zan dubo Affan ne, in bar ma kitchen din a hannunka?”
“Eh je ki dubo shi, zan kula da komai”
“Na gode”
A corridor muka hadu da ita, hannunta rike da lunch box guda biyu ta fito daga kitchen.
Sanye take cikin farar doguwar riga da aka yi mata a don duwatsu masu kyau.
Kamshinta mai dadi da kama jiki har yanzu yana manne da ko ina na dakin nata gami da jikinta
“Barka da safiya amarya, Allah ya sa ba hukuntani kika zo yi ba, jiya da yau duk na rike miki miji.” Cikin murmushi take maganar lokaci daya kuma tana tafiya zuwa ainihin falonta
“Yarona na zo gani.” Ni ma cikin dariyar karfin hali na yi maganar.
Yaran sanye cikin kayan makarantarsu gwanin sha’awa, dalilin da ya sa kenan ma na fitar da wayata na yi masu hotuna, don gaskiya sun burgeni tana kokari wajen gyara yaranta.
“Wai har Affan din ma makarantar zai je?”
Na yi tambayar ina kallonta
“To ya matsa sai ya je, shi ne Babanshi ya yi masu wanka ya shiryasu” Ta fada a lokacin da take ba Affan magani.
“Kenan tun dazu da ya shigo yaranshi yake shiryawa” na yi maganar a zuciyata, saboda ganin ba abin da nake zargi ba ne, duk lokacin da zai zauna a dakinta, kawai ji nake soyayya suke yi.
Tare muka fito da ita bayan ta gama shirinta da yaranta.
Hannuna daya na yi amfani da shi na bude wa yaran mota suka shiga
Bayan ta daidaita zamanta ne na dora mata Ramla a kan cinyarta.
Na dan ja kumatun yarinyar ina fadin “Ki yo min tsaraba.”
ta wangale bakinta mai dauke da hakora hudu, kamar ta ji abin da na fada.
“Ki dauketa ta zauna da ke?” Cikin tsokana ta yi maganar
“Ashe zan biyo ki yau”
Mu ka yi dariya dukkanmu lokaci daya kuma ta murza kan mota cikin kwarewa ta yi hanyar fita.
Mamaki na yi sosai ganin yadda ya gyare kitchen din tsab kamar dai ni ce na gyara shi
Ina mamakin irin saukin kanshi, da kuma yadda yake yanke shekarunshi su daidaita da nawa idan muna tare.
Alhaji Bashir Balarabe Ruma, dan asalin jihar Katsina ne a karamar hukumar Batsari kuma a kauyen Ruma.
Mutum ne mai saukin hali, iya mu’amala da juriya a kan duk abin da ya sa gaba.
Yana da ilmi mai zurfi a ko wane bangaren sannan ya kan yi amfani da ilmin nashi ta hanyar da ta dace.
Yana aiki da ma’aikatar fansho ta kasa, sannan yana kasuwanci na sayi da sayarwa, bugu da kari babban manomi ne a kauyensu.
Shekarunshi zasu kai arba’in zuwa da daya in da yake da yara uku biyu maza sai mace daya wacce matarshi Sakeena ta haifa mishi.
Mace mai kokarin boye damuwarta, iya zama da mutane kawar da kai hade da kawaici.
Tana da ilmi sosai musamman na addini, don har yanzu Sakeena na zuwa Islamiya Asabar da kuma Lahadi, a ilmin zamani kuwa tana da degree ne a bangaren education, tana matsayin vice principal a Wata makarantar private da ke cikin garin Abuja.
Ita ma yar asalin garin Ruma ce, kila shi ya sa wani lokaci nake ganin kamar suna kama da mijinta.
Alhaji Bashir Ruma, dogo ne mai matsakaicin jiki, sannan yana da hasken fata da take nuna irin jin dadin da yake ciki, yana da matsakaicin gemu da saje wanda ya zagaye fuskarshi ya kuma kara mata kyau da cikar haiba
Tsagenshi na rumawa wato biyu-biyu a gefen kunnensa ba ƙaramin kyau ta yi mishi ba.
Ita ma Sakeena haka yanayin jikinta yake, duk da yar kibarta mai ban sha’awa ta kan rage tsawon nata.
Yanayin hasken fatarsu daya da mijinta, zanen fuskarsu ma daya, bambancin kawai nata ya fi fita sosai da kuma yi mata kyau.
Ni kaina zanen nata burgeni ya ke sosai, yaranta uku babu wanda ba a yiwa zanen ba. Su ma sosai zanen ya yi musu kyau. Musamman Ramlah
Yau dai wannan ranar tawa ce don kuwa Bashir wunin ranar zuwa masallaci ne kawai ke fitar da shi, saboda koda su Maman Khalil suka dawo bai yi cikakken mintuna talatin tare da su ba. Ga shi yaran babu wanda ya zo part dina, har suka wuce Islamiya. . Maganar irin farin cikin dana tsinci kaina a wannan ranar ma ba zai misilti ba. Na rika jin, ina ma ace kullum hakan ne ke faruwa.
ina ma ni kawai ce da Bashir , lallai dana mori rayuwar amarcina, na aje tarihi mai yawa kuma mai dadin bayarwa.
Karfe takwas na dare na fito cikin kwalliyata dana tabbatar za ta ja hankalin mijina.
Riga ce mai laushi baka, ta wuce gwiwa kadan tana da siririn hannu, yau so nake in ba shi mamaki.
Sai da na tabbatar ko ina dake bangaren nawa ya yi fes ga kamshi mai dadi mara hawa kai.
Sai dai me? Yana dawowa masallaci ya zarce bangaren Gimbiyar tashi.
Yau ne, gobe ne har goman dare bai shigo ba, ɗan baccin ma da nake yi da, idan haka ta faru yau kam kwata-kwata na kasa yi, zuciyata tafasa kawai take yi, ina kuma shirya irin yadda zan nuna mishi bacin raina.