Skip to content
Part 28 of 50 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Halima ta kasance cikin Laulayi me zafi yau ciwo gobe lafiya kullum suna hanyar Asibiti ita da Mai Kano Wanda Bai gajiya ba da jikin shi da aljihun shi. Kullum ADDU AR Halima ga Mai Kano ta ALHERI ce matsalar ta guda dashi ta yaki yarda azubar da cikin Wanda a kullum ta dubi cikin nata da ya tura ta Kan ji Bakin cikin yadda ya samu Amma Kuma shi Mai Kano ya na ganin zubar da cikin tamkar kishin Kai ne shiyasa yaki yarda a zubar yace ta Bari ta haihu zai Mika abinda ta haifan gidan marayu kafin ya maida ta gida.

A yau Halima da begen hajiyar ta ta tashi da Kuma son sanin halin da Husna da sulaiman suka har bata boye mishi ba ya Kuma yi Mata alkawarin zuwa gobe ya dubo Mata su ba tare da ya fada Mata su Husna suna gidan Alh Aminu ba.

Washe gari kuwa ya bugo hanya ya sauka garin katsina Kai tsaye ya sauka gidan hajiya wadda ta karbe shi da wata shegiyar harara…

“Me Kuma ya kawo ka? Ko Nima zaka farke cikin nawa ne kamar yadda ka gano a can? Yayi murmushi Yana fadin

“Ke din ma na Gane wancan mutumin Yana Baki cin hanci ai na Rantse Miki Yana mutuwa kece Zaki bi bayan shi…

“Kai dai duk inda butulu yake ka Kai Mai Kano. Kana wa mutumin can bakar fata shi Yana maka fatar ALHERI. Kaga inda ya zauna can Yana fadin zaije Legos ya Kai maka zakka ka Kara jari…

“Shine matsiyaci Ni a wadace nake . Kuma zaiyi bayani ne Wallahi zakkar banza gareshi an Gaya mishi zakkar shi nake jira? Allah yasa ya nufeni da zakkar na Rantse a Nan zai Daina numfashi don kamar yadda na fada Miki nine ajalin shi…

Ya Mike Kai tsaye ya nufi gidan Alh Aminun don dama Koda Halima ba ta turo shi ba zaizo yaji dalilin Kiran wayar shi da yake yi a SHIGA gidan Alh Aminu fuska murtuk Yana huci inda ya tako Rashin sa a Alh Aminun baya gida

Da Amal yayi karo wadda tun daga nesa ta kafe shi da ido tanajin gabanta na dukan Tara Tara
Bata taba kallon namiji irin kallon da takewa Mai Kano

Har ya karaso Yana mata sallama ba tare da ta iya shaida Mai Kano ba . Saboda sun Jima Basu hadu ba ta Kuma San shi a da can tunda abokin Yaya muhsin ne Amma yanzu Bata Gane ko waye ba hasalima wani kwarjini yayi Mata

Bayan yayi Mata sallama ta amsa murya na Rawa ya tambaye ta ko Mai gidan Yana Nan? Ta amsa da baya Nan Amma Bari ta Kira mishi shi…

Ya dakatar da ita…

“No barshi Zan kirashi.

Ya juya ta bishi da kallon wannan Gaye ya na da kwarjini

Har ta biyo bayan shi tana son Kara kalle shi inda taga ya hau mashin ya wuce abinshi ta sauke ajiyar zuciya

Tana tunanin Ina Kuma zata sake ganin shi?

Tana tsaye Bakin gate har ya kulewa ganinta Husna ta iskota tana fadin.

“Anty Amal wa kike jira anan?

“Ba komai Husna. Suka shigo gidan a tare husna ta shige kichen tana Fadin
Bari nayiwa Yaya muhsin girki Kar ya dawo gida Yana Jin yunwa…

“Akwai fa abinci husna a kichen…

“Ai yace girkina yake so nayi Masa Anty barni nayi Masa din…

“Kina fa zakalkalewa da yawa Husna maza fa sai da Jan aji duk yadda kike macewar Nan Akan shi Bai Hana ko ya Aure ki ya kasa hada son ki da na wata shiyasa nake cewa kija ajinki…

Husna ta dubi Amal zuciyar ta na kadawa don idan akwai abinda ta tsana to Bai wuce Yaya muhsin ya hada sonta da na wata mace ba don Haka sai jikin ta yayi sanyi amma Bata tankawa Amal ba.

Haka ta gabatar da girkin jikinta a sanyaye tana ta lissafin maganar Amal

Karfe uku dai dai muhsin ya dawo don tuni ya Soma fita Aikin shi ba tare da sanin Alh Aminu ba don baya Jin zai iya Barin aikin Nan.

Da sauri Husna ta fito bayan tayi wanka ta shirya tamkar me Shirin fita unguwa.

Ta karbi takardun hannun shi Yana kafeta da ido Yana Jin wani azababben son ta na keta zuciyar shi

Ya zauna inda ta kawo mishi abincin da lemu Mai sanyi tana fadin ko sai yayi wanka.?

Ya bude mazubin abincin kamshi ya daki hancin sa ya dago yana kallon ta…

“Anya kuwa Zan iya hakuri har inyi wanka? Zuba min kawai my darling ai dama ance ci na gaban salla ko?

“Babu abinda ke gaban ibadar Allah Yaya mutane suna gwamutsa maguzanci da addini. Amma Ubangiji yayi sauki acikin dukkan bautar sa.

Ya bita da kallo kafin yace da kyau malama ta ya Naga fuskar ki kamar Akwai damuwa?

Ta zauna suna kallon juna na wani lokaci kafin ta dauke kanta tana fadin.

“Yaya kaji abinda Anty Amal tace kuwa? “Me Amal din tace ne? Kafin tace komai sai ga Amal din ta shigo saboda jiyo wautar Husna

Ya kalli Amal Yana tuhumar ta da idanu. “Me tace ne Amal din?

“Wai fa cewa tayi na Rika ja maka aji don wata Rana zaka iya son wata macen ko bayan munyi Aure Wai maza Basu da mutunci.

Amal ta Dora hannunta akai kamar zata kurmo ihu tana Jin kamar ta buge Bakin Husna.
Ya wurgawa Amal harara Yana fadin

“Ashe mu Yar bakin cikin mu ma agidan mu take.
“Yar ta Adda Kika Zama Ashe har kike zuge min ita? To zakuwa mu daura zare dake

Ya maido hankalin shi kan husna dake Dariyar hararar da Amal ke Mata

“Karya take kiji Darling shi so ba Haka Yake ba duk Wanda ke sonka baya hada ka da kowa Ni Babu wata mace da nake so sai ke Daya Kar ki yarda da duk maganar da zata fada Miki makaryaciyace Kuma Bakin ciki take Baki ga ita babu me sonta ba? Don taga ke kin samu ita Bata samu ba shine zata za tai haka.

“Ai kuwa irin su Anty Amal ne idan suka samu saurayi sai sun baka tausayi Kuma Nima Ina Nan duk Ranar da Naga saurayin ta da irin yadda take son shi zance Ashe Haka NE?

Amal ta harareta kafin tace
“Shine ke munyi magana ta sirri dake Kika Zo Nan Kika kwance min zani a kasuwa.

“Yo Baki San bana boyewa Yaya muhsin komai ba? Mijina ne fa? Yayi murmushi Yana fadin
“Yauwa fada Mata dai darling

Amal ta wuce tana fadin. “Ni dai bance Mata haka ba Yaya Amma idan Haka ka dauka Allah ya baka hakuri.

“In dai ba bakin ciki kike ba to kema kiyi zuciya ki fiddo naki Koko sai Yar yarinya Zaki sakawa ido?

Bata tsaya ba bare taji abinda zai Kuma fada ta wuce tana fatan Ina ma zata sake ganin Gayen can da ta gani? Da Bata ko shakka zata tallata mishi soyayyar ta don indai Haka so Yake to Bata ga laifin Husna da yaya muhsin ba

Mai kano da ya dauki jakar shi zai wuce Legos ya na cikin mota ya Kira wayar Alh Aminu bugu Biyu kawai wayar tayi aka dauka tamkar ana jira.

“Mai kano kana lafiya?

“Ba damuwar ka bace lafiya ta da Rashin ta don ko kowa zai Rayu da tallafin ka Ni ai ka Dade da sanin komai a wurina halal ne Amma Kai dai Haram ne. Don Haka Kiran me kake min har kana neman adireshi na? “Kaga Mai Kano kana Ina yanzu ? Gani a cikin garin katsina kana son ganin na ne?

“Kwarai kuwa Ina son ganin ka akwai maganar da nake so mu tattauna da Kai

“Ka kuwa shirya gani na? Ya tambaye shi da wani Abu Akan harshen shi.

“Sosai kuwa na shirya Mai Kano.

“To yanzu kuwa zaka ganni tunda ka shiryawa ganina Amma kasani gani na Yana nufin Abu biyu Wanda Dole ayi Daya yanzu kuwa zaka ganni Amma Ina Zan sameks yanzu? Ina Nan gidana dake sardauna Estate ok to gani Nan Zuwa.

Ya katse wayar inda Alh Aminu ya sheke da Dariya Yana Fadin yaro nafika iya kulla tsiya har kana Fadin in kazo za ayi Abu Daya? Ya daga wayar shi ya na Kiran yaron shi Dan ta Adda wato zarto. Zarton ya daga wayar Yana gaishe da uban gidan nashi inda yace mishi

“Zarto kana Ina? Gani a dabar mu Mai gida nazo ta samu ne?

“Kwarai kuwa zarto maza kazo Kuma kayo min hayar Yan ta Adda kamar goma ko fin hakan don zaku daka min wani karamin Dan iska ne.

“An gama Mai gida cewar zarton ya Kuma kwaso Yan iska suka nufo unguwar sardauna Estate.

<< Hawaye 27Hawaye 29 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×