Skip to content
Part 33 of 50 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

“Ban Gane abinda kake nufi ba? Ya Miko Mata hannu. “Bani key din Nan kafin nayi Miki yadda Zaki Gane. Ta Miko mishi tana binshi da kallo ya karba yana kwalawa Husna Kira

Suka fito ita da Amal inda Amal din ke cewa Daddy gaskiya motar Mami ta burgeni Allah yasa Nima zaka sauya min motar ko da ba irin ta Mami bace…

“Zan sauya Miki mana Amma ba yanzu ba. Ya fada idon shi Akan husna dake kallon Amal.

“Karbi Nan Husna makullin motar ki ne wannan ai Ina Jin yanzu hannun naki ya fada da iya tukin ko?

Tuni ta iya Daddy. Cewar Amal. Ta karbi makullin haj wasila na Raba musu kallo.

Daddy wannan ai na motar Mami ne.

“Dama naki ne ba nata ba itama Zan sauya Mata Amma ba yanzu ba dama ke ce Baki da mota to gata Nan sai a kiyaye da tukin ganganci.

Su duka tamkar wuta taja su haka jikin su yayi shock suna duban juna Husna da Amal kafin su dubi hajiya wasila dake Shirin fashewa ganin hakan ya tsorata Husna don yadda ta ga Haj wasila ta San akwai magana Wai gawa ta Rike Mai wanka don Haka ko kusa bataji kaunar motar ba har tayi nufin mayar da key din.

“Daddy tunda an bawa Mami ko abari Ni tunda ga ta Anty Amal sai muyi amfani da ita.

“Ba fa Tata bace itace tayi hasashen tatace dama da sunan ki na siyo ta itama ai Zan canza Mata wannan ai ta Yara ce tayi Mata yarinta tashi kuje.

Dole suka Mike suna godiya inda haj wasila ta bi Husna da wani matsiyacin kallo har ya kula da irin kallon da tayi Mata.

“Karfa kice Zakiyi wa yarinyar Nan wani Abu motace nace Zan canza Miki sai Kuma meye? Bata tanka mishi ba sai dai wani mugun kallon da take wurga mishi.


Yayi murmushi Yana shafar sumar kanshi. “Yarinyar Nan kinajin wani Abu kwanan nan…

Anty maimuna ta shigo gidan suka gaisa da Alh Aminu kafin ya Haye sama ya barsu.

Anty maimuna ta dubi haj wasila. “Wai Yaya har yanzu shiru nakeji maganar muhsin da Safina gashi ta isheni da koke koken Wai tana tsoron Kar muhsin yace yarinyar gidan Nan Yake so ita dai ayi maza ayi Auren Nan bayan kuma kince na saurare ki Zaki Zo mu tsara yadda komai zai tafi Kuma sai najiki shiru shine na biyo naji Haj wasila ta dubi maimuna.

“Maimuna Auren Nan da muke kokarin hadawa duk don mu Kara hada damkon zumunci ne . Kin San shi tushen Aure da iyaye suke kokarin hadawa da yayi Dadi sunfi kowa murna . Bacin shi Kuma zumuncin Yake shafa shine Naga kawai Safina tayi hakuri da muhsin ta bawa Daya daga cikin masu son ta Dama kar mu Bata goma daya bata gyaru ba. Kar sanadin Yara mu Zo munajin tsamin juna tun kafin mu same su muke uwa daya uba Daya.

“Uhum Yaya kenan haka kika ce?

Haj wasila ta bita da kallon mamaki don taga tana neman maida maganar ta koma zance.

“To maimuna da muzo muyi abinda zai damemu ba gara muyi hakuri ba?

Maimuna ta Mike tsaye tana fadin “Duk zaman jiran da Safina tayiwa muhsin Sakayyar da zata samu kenan daga gareki? Ta ki kowa saboda muhsin ta ki sauraren kowa saboda shi sai yanzu bayan ya gama Bata Mata lokaci kice tayi hakuri?

Hargagin da take yi yasa haj wasila biye mata Dama cikin zafin kyautar motar da akayi mata aka kwace take?

“Ahab kice dama kinzo don ki Gaya min magana maimuna? To ki koma ki tambayi yarki idan muhsin ya taba furta Mata kalmar So tunda kuwa yace bayayi Dole ne sai ya Aure ta? Gara ma da akayi Haka da ya Aure ta Allah ne kadai yasan Rashin mutuncin da Zaki Tata.

“Dama tuni Safina ke fada min kece Baki so muhsin ya Aure ta da kinso da tuni anyi angama sai Kuma yanzu na yarda don Ina ganin kamar ba Zakiyi min hakan ba Ashe duk wani Abu ya taso ne daga gareki to alhamdulillah dama naka shike bada ka Amma ki sani na Rantse Miki muhsin ba zai batawa Safina lokaci a banza ba na Rantse Miki sai ya Aure ta idan ba ayi hakan ba kice min shegiya ga uwata. Tunda an biyo ta hanyar Rashin mutunci za kuwa ayi shi Wallahi.

“To maimuna ayi hakan na gani zanga gidan uban da za ayi hakan Kuma ko anyi Zan maido Miki yarki gabanki don ki Ida yarda Ni dince bana bukatar ahalin ki tunda Haka Kika dauka ke da Safina bana kaunar ku sai Yaya.

“Nice dai babu Dole ki yini Amma Safina ki Soma yin ta tun daga yau din Nan muhsin Kuma kiyi mishi albishir da Auren Safina Nima Zaki Gane da kwanji na.

Da Haka maimuna ta fice daga gidan Yar Uwar ta bayan sunyi kace kace abin Babu dadin saurare.

A kullum kwanan Duniya Amal da soyayyar Mai Kano take kwana da tashi amma batayi kasa a gwiwa wurin fadawa Ubangiji ba inda haj wasila take Jin tsanar Husna tamkar ta dannata wuta

Muhsin ya dubi Husna da take nuna mishi key din motar da Daddy ya bata….

“Kai darling gaskiya Daddy Ni ya burge Kuma dama irin taku ce Yan beautiful girl Zan aje tawa motar kike kaini a Taki ko darling?

“Sai na kaika Mana har ma nake komawa daukar ka Amma gaskiya banji Dadi ba da Daddy ya karbi key din daga hannun Mami ya bani ba da sai ya bar Mata Ni ko da Bai bani mota ba tunda ga ta Anty Amal ai ta ishemu.

“Karki damu ko ita mamin ai zata iya siyen mota ta Baki bare Daddy ya Baki. Da Haka dai ya Rarrashe ta

Washe gari kuwa Husna ce ta Kai Yaya muhsin kotun su wurin aiki ta Kuma koma ta dauko shi inda Alh Aminu ya hango su yayin da wani matsiyacin fushi ya taso mishi yanajin tamkar ya shake muhsin yayin da Kuma zuciyar shi ke darsa mishi wani Abu tsakanin Husna da muhsin.

Ba Alhaji Aminu kadai ba hatta haj wasila Bata son shisshigin muhsin cikin Rayuwar Husna har dai yau ta Kira shi tayi mishi Jan kunnen ya fita Rayuwar yarinyar tun suna shaidar juna idan kuwa ta sake ganin ya shiga motar Husna da sunan zata kaishi wurin Aiki to shi da ita Husnar duk sai ta wulakanta su…..

Ko zaiji kashe din hajiya wasila kafin muga inda Alh Aminu ke shirin sauka

<< Hawaye 32Hawaye 35 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×