Skip to content

Masifar da Alhaji Aminu ke zubawa ta bawa su muhsin mamaki tamkar Wanda ya kamasu da kayan laifi.
Sai da suka bashi hakuri kafin ya nufi saman benen shi Yana fadawa Husna ta sameshi a saman.

“Na Rasa abinda mukeyiwa Daddy Haka da zafi da Yake yawan fada musamman idan ya ganmu da Husna ban San Dalili ba.

Husna ta Mike zata bi bayan Alh Aminu dake Kiran ta Amma sai Amal ta Riko hannun ta ta dawo ta zauna

“Yaya muhsin ya kamata ka San abinda kakeyi na Rantse maka in ba sannu kayi ba to Daddy zaiyi maka ba zata . Ba komai ke bashi haushi ba sai kishi ! Ce min kishin wa? Husna!

Azabure ya Mike Yana Rabawa Amal da Husna kallo wadda itama Husnar take kallon Amal.

“Na Rantse maka da sarkin da ya jera awazu na Daddy son Husna yakeyi ka Kuma Dora ayar tambaya tun a yau baka lura da kyautukan da yakeyi Mata ya hanani ba? Baka kula da irin kallon da Yake binta dashi ba?

“Zanyi murna kuwa idan hakan ta tabbata don dama tuni yarinyar Nan ta tsaya min a makogoro gara Daddyn yayi wub da ita da dai akawo min ja iba. Cewar Safina dake shigowa tana dauke da kayan abincin ta Wanda ya ji makaman Aiki tare da budado turaren tsafin ta inda muhsin ya Mike Yana dakatar da ita.

“Koma da tsiyar ki ban kiraki ba in don ni Kika kawo koma dashi Kar ki Kuma zuwa inda nake.

Kamar ba da ita Yake ba fatan ta dai tayi nasarar da ya shaki turaren ai kuwa ta taho zata Rungume shi kamar yadda tayi wancan karon sai Jin saukar Marika tayi a fuskar ta hagu da Dama inda taga wata koriyar walkiya.

Muhsin da Amal suka fice inda Husna ta Haye sama wurin Daddy inda Amal tace Mata idan ta fito ta same su a waje.

Ta samu Daddy Yana waya har ya gama kafin ya juyo gareta Yana kallon ta da Jin wani masifaffen sonta kamar ya hadota da jikin shi har ta tsargu da kallon da Yake Mata ta sunnar da kanta kasa.

Cikin wata murya me nuna tsantsar muradi ya kusanto ta Yana Mata magana kamar me Rada

“Husna magana ce Mai muhimmanci nake so muyi dake duk da nasan ba Zaki iya sakewa Dani ba bare muji dadin tauna ta Amma zanso ki bani amsar tambayar da zanyi Miki.

Ta gyada kanta Alamar zata Bashi

“Idan na zabi mutum na yaba da hankalin shi Naga Dacewar na hadaku Aure kina ganin na Isa nayi hakan a Dan matsayin da kike Jin Zaki bani? Ta kada kanta tana Jin faduwar gaba don ita da kanta tana hango wani Abu a idon shi Wanda Bata jure kalla.

“Na Gode da wannan Alfarmar da kikayi min Amma Kuma kina Jin mutum me irin suffa ta da kamanni na da hali na yayi Miki Zaki iya Auren shi.

Da sauri ta dago kanta dake kasa ta zuba mishi ido cikin dukan kirji don yazo gabar da ta kasa karyawa.

Ta faru ta Kare, Ta Raya hakan a Ranta.

Ga mamakin ta sai ta tsinto yatsun hannun ta anashi Yana Ruko ta tare da tsira Mata ido cikin karkarwa da barin jiki take kokarin zamewa inda Kuma suka ga haj wasila Akan su kamar wadda aka wurgo.

Ta zuba musu Ido cikin kunar zuciya tamkar ta shake Husna don masifar kishi. Ya saki hannun Husna da sauri Yana muzurai.

“Wane irin dabbanci ne haka ki shigo min Babu sallama?

“Sallama Kuma? In maka sallama don ka kauce daga abinda idona Yake son tabbatar wa? Har Anzo gabar da zaka Rika kawo min yarinyar Nan dakin ka don ka nuna min nice karamar tantiriya? Anan gidan kake kokarin Rufe kofa da yarinyar Nan Aminu?.

Bata Rufe Baki ba taji saukar Mari a fuskar ta.

“Ni Zaki kawowa maganar banza? To duk abinda kikji a Ran ki hakan NE . Haj wasila dake Rike da kumatu tana kallon shi Yana zuba masifa inda Kuma Husna tayi hanzarin mikewa tana zubar HAWAYE yayi saurin Riko ta Yana fadin. “Karbi kudin Nan Husna kije masanawa hajiya tana neman ki zata karasa Miki maganar da nake fada Miki yanzu zata sanar dake komai.

Ya zube Mata tarin kudin inda tsoro me tsanani ya kamata Amma duk da Haka Bata kawowa Ranta maganar da take Ranta ba ta dauko kudin ta fito HAWAYE na bin idonta inda Kuma haj wasila ta Dora kwandon jarabarta.

“Me kake so kace Akan yarinyar can? Naji kana Fadin murum me irin suffar ka da kamanni Wai ka Aure ta kake nufi? Ashe kuwa garin Kano Babu mota Dama Rakumi da shanye Ruwan tsakin da na fada shi kake Shirin yi? Ashe kuwa girma zai Fadi don duk abinda kakeyiwa muhsin shi takeyi ba Kai ba ko shi din Kuma Wallahi Bai Isa yace zai Aure ta ba bare Kai Wallahi ba zanga wannan Ranar ba.

Ta fice da sauri tana sauka kasa inda Kuma Husna ta fito inda Amal da muhsin ke zaman jiran ta sai gashi sun sameta fuska da HAWAYE.

“Lafiya? Muhsin ya fada Yana duban tarin kudin dake hannunta.

“Akwai matsala ta fada tana Rushewa da kuka inda hankalin su duka ya tashi suka zuba Mata ido tana kuka su Kuma suna zancen zuci.

Da kyar tayi shiru tana fada mishi Akan abinda sukayi magana har zuwa Bata kudi da cewa taje masanawa haj na neman ta.

“Ahaf baga maganar da na fada ta bayyana ba? Cewar Amal.

“Gashi dai t tabbata har Daddy na Mata explanation da kanshi me Kuma yayi saura?

Haj wasila da ta sauko ta nufo su cikin sauri ta karaso inda suke tana duban Husna da wani irin duba na kaskanci da wulakanci.

“Me kike jira da Baki tafi ba? To ki Rufawa kanki Asiri Kar ki Kuma waiwayar gidan Nan don abinda idona ya gani Akan ku ke da kanki kinsan ba Wanda Zan jura ba ne alkunya nayi Miki ta karewar zaman ki a gidan Nan don Haka Kama hanya ki fice sahunki a likkafa idan kuwa tsautsayi ya sake maidoki to duk abinda ya faru dake laifin ki ne don Ruwa ake dadewa ba wuta ba har gidana azo min da wannan abun Husna ko ke Zaki yarda da hakan Akan mijin ki? To wannan ne na farko Kuma na karshe in shi namiji ne bashi da ta ido kema macece marar kunya? To tafi hakan Nan ladar ko zunubin duk sun Isa na yarda ya biki can gidan naku.

Husna ta zube Agaban haj wasila tana kuka. “Mami wallahi banyi abinda kike zato ba Ni har yanzu acikin duhu Daddy ya barni ban fahimci abinda Yake nufi ba ki gafarce Ni don Allah.

Wani banzan kallo ta bita dashi kafin tace, “Ai ya tura ki inda za ayi Miki tafin ta kije duk abinda hajiyar ta fada Miki ki kirani ki fada min.

Da Haka haj wasila ta bar wurin a fusace.

Amal da muhsin ba karamin tashin hankali suka SHIGA ba inda muhsin ya kamo hannun Husna ya bude Mata mota ta SHIGA yajata suka fice daga gidan.

Har kofar gidan haj ya direta Yana faman Bata Baki.

“Yaya muhsin na Gama Gane inda kalaman Mami suka sa gaba kamar yadda anty Amal ta hasaso haka Mami take hasasowa idan hakan ta tabbata Ina makomar sona gareka?

Yayi shiru kafin ya tanka.

“Zan barwa Ubangiji komai Akan yayi Mana zabi Amma indai da gaske Haka daddy Yake nufi to Zan saka Dan karfi na har Naga baiyi nasarar Raba mu ba don Haka SHIGA gida da confidence duk abinda haj ta sanar dake ki kirana ki fada min Zan nunawa Daddy na shigo zamani.

Ta amsa da tabbacin da ya Bata ta bude motar ta fita shi Kuma yaja ya tafi tana tsaye tana kallon shi har ya kurewa ganinta kafin ta afka gidan da sallama inda ta Tara’s da gidan ya Sha sabon fenti har da tiles an zuba komai na gidan ya dawo sabo . Bata tsinke ba sai da ta shiga dakin hajiyar inda komai ya zamo sabo Dal tamkar dakin wata Amarya.

Hajiya tayi Mata oyoyo tana Rungume ta abinda Bata taba ganin hajiya tayi Mata ba. Ta Mika Mata kudin da tazo dasu tana fadin.

“Baba Aminu ya bani wannan kudin Yana fadin Wai akwai maganar da zaki fada min.

Ta kamo hannun ta tana fadin, “Taho ki Fara ganin kayan gadon da Alh Aminu ya tsantsaro Miki Kai wannan mutum bana ko tantama Dan aljanna ne . Husna ta bita zuwa dakin da kayan katakan suke Kaya Kam na gani a bada labari komai ba irin na Rayuwar talaka ba irin na Rayuwar da ake mantawa da gobe can saman sama.

“Ni yanzu ba wannan ba nafi bukatar kiyi min bayanin dake Raina shin Aure ake so nayi Koko mijin ne aka samo min da ba a Bari na zabi Wanda nake so?

“Yo ai mijin da aka zabo Miki in Zaki kewaye Duniya bana Jin Zaki iya katari da irin shi.

“Karya ne, Ta samu Bakin ta da sabul da bakan fada, Hajiya ta dubeta fuska akwabe
“Karya nayi Miki kenan.

“Ba Haka nake nufi ba Ni fa na Fi son kawai ki gajerce min labarin Nan kice min kawai ga Wanda baba Aminun ya kawo mini.

“Shi da kanshi ne Yake son Auren ki saboda tausaya Miki da Yake Akan Bai San irin mijin da zai Baki ba Kuma har mun gama magana don har mutanen kurfi yaje musu da maganar sun Kuma karba shiyasa nace ya maido ki gida Kar matar shi ta samu labari ta lalata zancen don na samu labarin Bata tsoron Allah.

Husna ta wurgawa hajiya harara.

“Amma hajiya ai kin San ban Ritso zamanin da ake hada Auren da sai dai a hade a gidan mijin ba ko? Wane irin Kama karya ne wannan? Don ubana ya mutu uwata Kuma ta Bata shine ake neman kasa Rayuwa ta a tire? Me zai Hana ba Zaki shawarce Ni ba idan Ina son hakan ayi in kuwa ban so a hakura? Ke yanzu saboda Allah in tashi gidan mutum gaban matar shi sai kawai matar shi taji Zan aurar Mata miji in ke akayiwa Haka Zaki yarda?

“To ba Baba Aminu nake so ba Dan shi Yaya muhsin shi muke soyayya ana Kuma barin halak ko don kunya Wallahi ba Zan taba Auren baban Yaya muhsin da Anty Amal ba in ma kun shirya to ku Rushe ban son shi ban kaunar shi.

Sai kawai hajiya ta Rufe Husna da duka.

“Yar iska butulu har kin samu Bakin fadin Baki son Alh Aminu? Mutumin da ya Rufa muku Asiri ya ciyar daku ya shayar daku shine kike bude Baki kina fadin Baki son shi? To zanga uban da zai tsaya Miki wallahi sai kin Aure shi ko da Zaki mutu sai an Kai gawar ki gidan shi kafin a wuce dake makabarta.

Tana cikin jibgar Husna sai ga Mai Kano ya diro gidan hajiyar inda ya Tara’s hajiya sai dukan Husna takeyi.

1 thought on “Hawaye 48”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×